Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 85


Bibiyata Akeyi 85
Viral

Page 85

*
Umma ce zaune itada ummii cikin aminity, suna hutawa, sunfita sunbar *hanna* ita kad’ai hameeda kuwa tatafii yin abinci, ko *hanna* zataci dan idan akayi sa’a, dan wani lokaci akanyi sa’a ta d’ancii abincin ko kad’an ne.”
*Hanna* na hango tafito daga cikin d’akin da take, doguwar riga ajikinta, kanta ko d’an kwali bbu.” hankalin su ummii kwata-kwata bayi wajan, kamar wanda wani abun yad’auke musu hankali.”
Har *hanna* tafice acikin wajan bbu wanda yajuyo, haka harta fice daga harabar asibitin bbu wanda yatsayarda ita, dukda alamomii dayawa ajikinta yanuna ba cikkken hankali atattare da ita.”
Tana fita ta tsaya atiti kamar mai jiran abun hawa, wata taxi ne tatsaya da wani mutum aciki mai wata irin halitta, wanda kollonsa kad’ai zai saka cikin shakku, kayi tunani koba mutum bane.”
Nikaina zuciyata tafii kar kata, dacewar aljanine, magana yayi cikin wata irin murya, mai rikitarwa yacewa *hanna* shigo muje, bbu musu hanna tabud’e motar tashiga gidan baya, nan kamar wata walqiya yaja motar yayi gaba.”
Kusan awah biyu suka shud’e.”
Can nahango *hanna* tana tafiya duk k’afofinta sun fashe alamun tayi tafiya sosai.”
Tana tafiya har tahau kan titi, unexpected wata mota k’irar jeep tazo wucewa ganin mutum akan hanya yasa tayi gefe da niyyar kaucewa, amma inaaa, sai dayazo dabb kamar wanda aka tunzurata, saijin kawai sukayi sun bigeta, salati mutanen cikin motar sukasa, nan suka samii waje suka tsaya, matan dake baya cikin motanne sukayi saurin fitowa sukayi kanta.” ganin jinii yanabin kanta yasasu, kwalawa wanda yake driving d’in kira, dasaurii yafito, wani saurayine kyakkyawan gaske, duk wani alamu najikinsa yanuna, cewa shi cikkken bafulatani ne, dan da fullan cinma suke yin magana, amma saidai yanda najii suna fillancin gabaki d’aya ya banbamta, dana k’asar nigeria, kinkimanta yayi yasata acikin motar dake seat ukune da ita, asibiti suka nufa lokacii guda, dake manyan mutanene ba’atsaya bincikeba aka k’ar6eta aka shige ciki da ita.”
Basu dad’eba aka futo aka shaida musu cewa, jikin alhmdllhy bataji, wani ciwo sosai ba.”
Sannan d’an dake cikintama lapynsa klau.”
D’aya matarne tadubi, D’ayan wanda da’aalamu tagirmi D’ayan, tace, diddii naga kamar k’qramar yarinyace kuma budurwa.”
Allah dai yasa bawasu mugayen bane suka mata fyade suka yasarda itaba.” nisawa wanda aka kira da diddii tayi tace,”
Allah shi yabarwa kansa sanii hussentu, abunda yakamata yanzu ina shii sadiq yashiga?” nisawa hussentu tayi Sannan tace,” ya tafii k’ar6o maganinne, to Allah yadawo dashi lpy.”
Bayan yadawo da 1hour *hanna* tafarka, duk iya tambayar duniyarnan anyi mata amma takasa bud’e baki tafad’i ko kalma d’aya,” da suka isheta da zantuka kawai saita sheqe musu da dariya, harda kyakyatawa, ganin haka yasa suka nemi likita.” yana zuwa yafara dube dube, nan aka shiga da ita d’akin na’urorii, iya bincikensu baigwada musu akwai wata matsala, akwakwalwarta ba.”
Hakan yafito yashaida musu sunyii matuk’ar mamaki, tunda duk wani alamu yanuna ta6in hankali attatere da ita.” 2days aka sallamesu gidansu suka nufa.”
Nan diddii tabuk’acii sadiq daya d’auki pics d’inta yazagaya ya aika gidan redio, television, dasauransu, ko za’a dace, Hakan kuwa akayii, and’aukii 5days sadiq yana sanarwa, amma bbu ko batan hanya da wani yazo dan nemanta.”
Agajiye liqis sadiq yadawo yazauna, wata mata wanda daga ganii y’ar aikice takawo masa ruwa, bai iya shan ruwanba, yadubii diddii yace,” diddii duk iya cikiya nayishi, aksarnan bbu yanda bankai cikiyaba amma bbu.”
Nifa atunanina yarinyarnan ba y’ar k’asar camroon bane, camroon na maimaita cikin raina😳🙆,
Allah kawai yakamata mu miqawa komai mucigaba da mataa addu’a, kuma muna nema mata maganii.”
Diddii bata iya cewa komai ba sai Allah yabata lpy.”

Basu ankara da cewa *hanna* batanan ba saida hameeda takawo abincin tazo da samesu, aresting room d’inda suke zaune tace,” Umma nakawo abincin, dasaurii ummii tamiqe tace barina je toh ko zata cii na rarrasheta, d’akin tanufa tana shiga taga wayam, koda mamaki ne yacikata dasaurii tayi toilet nan ma bbu kowa, fitowa tayi nufii gun Umma tana cewa kinga yanda *hanna* tayine? Dasaurii Umma tamiqe tace banganeba? Aimuna zaune dake anan, *hanna* bata d’akinne? Ummii bata tsaya bata amsaba, tawuce tafara dube dube a cikin asibitin, Umma ma tabii bayanta jikinsu duk rawa yakeyi.” duk girman asibitin acikin few minute suka zagayeshi, bbu ita bbu dalilinta, bakin gate suka yi suna tambayar masu gate ko sunga fitarta,”
Aikuwa sukace basu ganiba, dan kamar wanda aka rufe musu ido.”
Waje sukayi suna tambaya nanma bbu wanda yace yaganta, sunshiga tashin hankali kam sosai, kowacce kuka takeyi bbu mai lallashin wani.”
Wani d’an tsoho dazaikai 80yrs, wanda tun fitowar *hanna* shi kad’aine yalurada ita kasancewar, yanada d’an bud’edd’en ido, yamatso kusada su yace,” bayin Allah wa kuke nema haka?.” dasaurii Umma tace y’armuce tafice daga asibitin kuma kowa yace baiganta ba.” shiru yayi nawasu lokaci kafin yace,” kafin yace naganta da doguwar riga ajikinta, dasaurii ummii tatashi tace itace wallhy itace.”
A’ina take?” girgiza kai yayi yace kucii gaba da addu’a, Allah zai bayyanata, Su kansu wanda suka d’auketa basufii k’arfin Allah ba.” zaro ido sukayi mekake nufii kenan da Hakan?” wata y’ar dariya yayi yace, ai addu’a da kuke yi, da wanda mijinta keyi, da wanda ita kanta keyi yasa basu cutarda itaba, yanzu haka tana hannun mutanen arziki, idannace ku kwantarda hankalinku nikaina banmuku adalci ba.” kawai kuyita mata addu’a, bbu abunda yafii k’arfinta, atake ummii tazube awajan sumammiyya, dasaurii sukayi kanta, dai-dai tsayuwar motan abban wanda yad’auko middibbo,”
Dasaurii yak’arso baitsaya tambaya ba, ya kinkimi ummii yayi cikin asibitin da ita, Umma kuwa alokacin suka nemi mutuminnan samada k’asa suka rasa, dasaurii sukayi ciki, duk iya tambayar affan bbu wanda ya iya bashi amsa,” ganin Hakan yasa yak’ira marshall ya shaida masa yazo hospital.”

_Kuyi hak’uri kuyimun uzuri, bayadda na’iya, amma in sha Allah cikin month d’innan zangama_

To be continued

Ur’s
z33iiyybawa

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

“`Dan Allah kada mu gaza wajan taimakawa y’an uwanmu akan buk’atunsu, dan Allah damuwar wasu ta Zama tamu damuwar, koda bazaka iya taimakawa, ta wani hanyarba, yanada kyau, ka taimakeshi tahanyar addu’a, dan kaima watarana, zaka buk’acii ataimaka maka koda tahanyar addu’a ne danshine babban tainakon da mutum zaimaka aduniya.” nidai zaynab bawa ina buk’atar addu’oiinku daga bakunan ku masu albarka.”
Balaifii bane kuma ba gazawa bane ko kankastar dakai neman taimako na addu’a ba, tabbas bakasan bakin wani ba, danna roqii alfarmar addu’a awajenku nasan zakuyimunne, nagode.”“`

================

“`This page is dedicated To you, FATIMA IBRAHIM(MUNEERAT)
and SAWWAMA QAWWAMA (doughter) Allah yabarni tare daku har abadan.”“`

.

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply