Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 87


Bibiyata Akeyi 87
Viral

Page 87

*
Fad’in irin tashin hankalin da marshall yashiga wannan ma tsayawa, bata lokaci ne, gabaki d’aya yazama wani iri, bud’e idanuwansa ma wahala suke bashi, balle aje ga cin abincii ko wani abun.” nauyii idanuwansa ke masa, alokacinne yak’ulla mugun alaqa da ciwon kai, wanda akullum kansa ke barazanar tsagewa gida biyu,
Baida sukunii, baida wani sauran kwanciyar hankali, kullum cikin zullumi da tunanin yanda *hanna* tashiga yake, tunaninsa ko awana irin hali take, baisani ba.” a kullum har wani hucii ne mai d’umi yake fita daga jikinsa, idanuwansa kuwa idanya bud’e yanda kasan garwashi, har shakkarr bud’esu yakanyi, dan har indai mutum yana kusadashi sayyya razana, sa’ii-sa’ii yakanyi aman jini, amma bai bari kowa ya lura ba, koda sallah ma ad’aki yakeyi, ummiii tayi kukan harta gajii,

Ganin bbu Wata mafita yasa umma takira mama akan tanason ganinta idan zata samu dama suzo suda baba, dafarko mama tayi tunanin su hassana da hussaina,
Hakan tafad’awa umman, amma umma tace mata tabarsu ma ammah tazo, ganin zancen mai k’arfii ne yasa tasanarda baba, kiran k’aninsa yayi awaya, abba yacewa baba gaskiya yanadakyau zuwannasu, haka suka shirya washe garii suka d’auki hanyar kano, sha d’aya tamusu acikin garin kano, gidan Abba suka wuce kai tsaye, ganin Wata irin ramar da umma tayi mama ta matuk’ar tsorata, dasaurii tak’arasa kusada ita, riqo hannunta mama tayi cikin kid’ima tafara magana, yaya menene yasameki haka?” yaya dama bakida lpy ne baki fad’amunba?, girgiza mata kai umma tayi kawai hawaye nabin fuskarta, da sallama abba yashigo falon, ganin umma na hawaye yasa yace ashsha assha, yanzu daga zuwansu kintaryesu da kuka, hava da Allah wai kekam bakyada hakurii ne, kuma bakida juriya, hava, idon mama har yacika da hawaye tashi d’aya yafara zubo mata takalli abba tace dan Allah kafad’amun ko wani abun ne ke damunta, rintsawa abba yayi kafin yace, kuzauna ku huta kafin namuku bayani, girgiza kai mama tayi tace, nidai bazan iya wani hutawa ba, bayan Ina kallon y’ar uwata cikin wani hali, juyawa abba yayi batareda yak’ara cewa komai ba, yanufii babban palour wajan baba.”
Duk yanda mama taso tambayar umma abunda ke faruwa takasa sanarda ita, abba baifii 10minute da tafiya ba ya leqo yace, sutaso su tafii, tunda suka d’auki hanya bbu wanda ya iya magana, ganin sun nufi fadah yasa gaban mama da baba yayi mugun fad’uwa tunainsu d’aya badai wani abun bane yasamu *hanna* sunfii ma karkata da ko batada lpy ne, har suka isa fada, bbu wanda yatofa ko da kalma d’ayane, dama ansan da zuwansu, dan haka falon mai martaba, aka sauk’esu marshall na kwance tun shigarsu afalo, amma bai iya d’aga kansa ya kallesu ba balle susaran zai gaidasu abun bak’aramun mamaki yabawa baba da mama ba, banda umma da abba dan dama sunsan irin halinda yake ciki, tunda *hanna* ta6ata bai k’ara furta ko kalma d’aya ba, ummii da mai martaba ne sukayi sallama suka shigo falon daga d’akinsa, waje mai martaba yasamu yazauna, sannan yabawa su abba hannu suka gogaisa da addu’a yabud’e taron sannan yafara magana.”
Kusani cewa Duk wani abunda yafaru muqadda rine daga Allah, kuma Allah subhanahu Wata ala yace, la yukalliful lahuu nafsan illa wus’aha, yace Allah baid’aura rai abunda bazata iya ba.” sannan Kusani kowani d’an adam da irin hanyardaa Allah ke jarabtarsa, sai dai muyi addu’a Allah yabamu damar cinye tamu jarabawar data fad’o mana, sannan d’aukan qaddara yana d’aya daga cikin cikon imani, musani Allah baid’aura mana abuu har sai dan yagwada imaninmu
Yaga yaya jamuyi dan yajarabcemu, tundaga wannan lokacii ummii tafara hawaye tana goge hawayen idanuwanta, nan mama tak’ara karyewa sosai tace,” ku gayamun maiya samu *hanna* mu musulmaine tabbas zamu kar6i kaddar mu hannu bibbbiyu, zamu riqe wannan jarabawa, dakyau mumata kyakyawan duba yanda idan skamakon mu yatashi futowa zamu samu sakamako mai kyau.” ita kanta duniyar nawa take?” kan ummii nak’asa takasa d’agowa takallesu tace *hanna* ta 6ata wallhy *hanna* ta6ata, gaban mama ne yafad’i rass, wani irin jirii ne yafara ebanta, amma kuma duk dauriyarta ta tattaro, da mamakin mutanen wajan gabaki d’aya, murunushine kwance afuskarta, sannan cikin dakiya tace, kada ku damu da sanin Allah in sha Allah zai bayyanata, addu’arda zamu mata Allah yasa tana wajan kyakyawan hannu.”
Shima baban dukda cewa abun yadakeshi addu’ar kawai yayi, share hawayen idonta umma tayi sannan tace, Aisha abun damuwar d’aya shine *hanna* bata cikin hankakinta lokacin da ta 6ata, *hanna* tahad’u da ta6ewar hankali, abunda yasa bangaya miki ba, bawanda yad’auka, zata dad’e cikin wannan jinyar, dan Allah kiyi hakuri, girgiza kai mama tayi tace hava yaya wani irin hak’urii kike bani?” bayan kuma mahaifanta ne, nasan kulawarda zaku bata, ko da inanan bazan bata hakanba.”

Inada yak’inin kunfinii jin zafin 6atan nata, dan Allah kudena fad’in haka, kum,,, tarinda marshall yad’aukane yasa tayi saurin yin shiru, bai dad’e yana tarinba yalafa, mama ta kulada yadda wani abun da yafito abakinsa, amma yasa hannu yarufe, duk wannan abunda yakeyi, tashi mama tashi tak’arsa gabansa, batayi magana ba, kawai tasa hannunta tad’ago nasa hannun razana tayi ganin wani irin bak’ik’irin d’in jini, ga lebb’an bakinsa ma duk yaa6ci da jinin, dasaurii tajuyo tallaeshi tace abdallah tashi mutafii asibiti bakada lpy fa, shiru yake kamar yanda yasaba idan anmasa magana, ummii ne tace, kirabu dashi kawai ko zaki kwana kina masa magana ba kulaki zaiyii ba.”
Koda bazai kulaba yakamata akira doctor yadubashi, umma tace, mamane ta amshe da cewa aman jinifa yakeyi, sai alokacin kuma duka hankalinsu yatashi, dan duk cikinsu bbu wanda yasan yana wannan aman.”
Dasaurii mai martaba yad’aga waya aka kira likita, ba’a dad’e ba ya iso, dube-dube yafarayi, nan yajuya yakellesu yace, idanda hali asibiti yakamata mutafii, dan likitoci da damane yakamata su kasance akansa ayanzu haka, babane yace, doctor bafa zaije ba, ka kira likitocin nan suzosu, hakan kuwa akayi, nan yakira doctor’s dakuma nurses, sukazo da motan hospital, hadda gado, buk’ata sukayi akan afita abarsu ad’akin, hakan kuwa akayi, sun d’auko awowi masu yawan gaske, kafin su fito, ababban falon mai martaba suk zaune, dukansu, anan likitocin suka semesu, bayanii likitocin sukayi sosai yanda hankalin mutanen falon gabaki d’aya ya tashi, d’ayan likitanne yace, gabaki d’aya zuciyarsa ta buga, kuma alamu yagwada ta dad’e cikin wannan halin, dan yanda muka duba tqkai kaman 2weeks, gaskiya abun yabamu matuk’ar mamaki, bamu ta6a kallo, kuma ko alabarii bamu ta6ajin wanda zuciyarsa takai wannan stage kuma yarayu ba.”
Amma sai daiamakinmu ragaggene, idan mukayi la’akari da wanene shi, ayanzu haka dole yana buk’atar taimakon gaggawa daga nan, kafin ad’aukeshi, zuwa k’asar waje, abba ne yace yanzun abunda za’ayi kakira ambulance daga asibitin ku, akaishi can, sai ayi masa alluran bacci, dan jinya anan bazaiyiwu ba, nisawa d’aya litikan yayi yace, alokacin da zamu fara dubashi bbu irin alluranda bamuyi masaba, amma bawai yayi bacci bane kokuma hankalinsa yagushe ko d’aya, ahakan mukayi aikin, yanzu haka idonsa biyu sai dai kawai ba’a bud’e suke ba, sannan duk abubuwanda akeyi yanajii.”
Ummii kam takasa magana, sai mamane tayi k’arfin halin cewa, kud’aukeshi ahaka, mutafii tare tafad’a had’eda miqewa, nurses ne suka tura gadon har zuwa gaban ambulance, tareda mama suka shiga, aminu kano suka nufa, nan aka kaishi aminty,”
Adakinda aka kwantardashi, mamane zaune itada umma da ummii,”
Satin marshall d’aya yad’an fara samun lpy, lokacin yakama 3weeks kenan da 6atan *hanna* mamane ke jinyarsa asibitin, tana nuna kamar bata damu bane amma zuciyata nacike da kewa da kuma zulumin hainda y’artata take ciki, baba kuma yakoma, gabaki d’aya hospital d’in sanda aka zagayeshi da soldier, balle d’akinda yake kwance, doctor’s ne suka samii mai martaba, akan ad’aukeshi daga wannan hospital d’in zuwa k’asar waje, dan sai sunyi kamar zasu shawo kan matsalar sai abun ya faskara, shawararda mai martaba yayanke kenan, shiga d’akinda aka kwantardashi yayi, yana kwance kamar kullum ba umm ba um umm, mai martaba yakalleshi sosai sannan yadubii mama da ummii yace, yaronnan kawai xan fiddashi ne hankalina yakasa kwanciya, haryanzu bbu wani takakkammen halinda yake ciki, yadubii mama sannan yace zankira Alh muhammad na fad’a masa zuwa jibi zaku wuce.”
Muryarda yau watansu guda kenan, wanda suka dad’e basu jitaba, ne yakatsesu da cewa, ni bayanda zanje, ku barni anan, haryanzu ban fiddaran dawowar *hanna* kwana kusa ba.”
Zaro idanuwa sukayi suna kallon ikon Allah.”

To be continued

Ur’s

Z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

.

“`Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi ya ce Wanda ya yi sallar nafila rakaa goma sha! biyu tsakanin dare da rana Allah zai gina masa gida a cikin gidan Aljanna.“`

“`Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace, Wanda ya kiyaye yana yin nafila raka’a hudu kamin sallar azahar da kuma raka’a hudu kamin sallar la’asar to Allah zai haramta masa shiga wuta.“`
.

“`Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace, Wanda yake karanta ayoyi goma da daddare to baza’a rubuta shi cikin gafalallu ba, wanda ya ke karanta ayoyi dari to za’a rubuta shi cikin masu bauta ga Allah, wanda kuma ke karanta ayoyi dubu a cikin dare kullum to za’a rubuta shi daga cikin masu arzikin lahira.“`
.

===============

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply