Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 89


Bibiyata Akeyi 89
Viral

Page 89

*
D’aki takaita, sannan ta kwantarda ita, tace bodd’i zauna anan, kijirani karki fito kinji, kamar wata mai cikakken hankali tad’aga mata kai.”
Yawwa bodd’i na kinada jin magana tashafo fuskarta sannan tafice.”
Wani kyakkyawan saurayi ne yafito daga motar, wqnda duk kyawunsu hussentu danake gani sainaga har sadik yafii kyau, hannunsa d’aukeda wata y’ar k’aramar yarinya wacce bazatafii 4yrs ba, gabaki d’aya saurayin bazai wuce sa’ar marshall ba.”
Ko kad’an fuskarsa bbu annurii dan baiyi kama da masu dariya bama, dasaurii diddi tak’arasa ta d’ayan kofan, ta sa hannu ta bud’e, wata y’ar dattijuwa, nagano, kamar su d’aya sakk, da d’an saurayin daya fito daga motar, wasshe baki diddi tayi tana cewa, usse inne, wanda aka kirada, inne ta d’aga kai tayi kawai alamun ta amsa, daga yanayin matar yanuna tanada jin kaii sosai, tafiya tafarayii, diddi nabinta abaya, dasaurii hussentu tafito ta nufii yayanta, yarinyar datake hannunsa tamiqawa hannu amma yarinyar tamaqe, sake miqa mata hannun tayi da niyyar tad’auketa Ko bata so, daka mata wata uwar tsawa yayi ke wuce irin marar hankalin ne? Tace bazata zoba ana dolene?” jada baya hussentu tayi tana tsoron tayi gunguni yamaketa,
Tsaki yaja yanufii wajan diddi ya tsugunaa har k’asa yana gaidata, ta amsa masa fuska sake, tana cewa ya hanya? ya wannan y’ar fitunan? Dan yake yayi sannan yace gata nan, sai abunda yak’aru,”
Wucewa inne tayi suka bita abaya, sanda tazo dabb yanda hussentu take ta dubeta tace, kinfi karfin gaida mutane Ko?”
K’asa tayi dakanta batareda ta gaishe tanba, muryar yayanta ne yadaki dodon kunnuwanta, yace dan ubanki bazaki gaishe taba?”
Duk wata fitsarar da kikeji zansauke miki ita, jkinta har rawa yakeyi tace sannu da hanya, batareda ta kulata ba tawuce abunta, bin bayanta sukayi, har cikin gidan, da sallama suka shiga nan suka zazzauna batareda dad’ewa ba aka gabatar musu abun motsa baki,”
Hanna tagaji da zama sosai dan har dare bawanda tashigo ga k’ofa akulle, sai can hussentu tashigo, riqo hannunta tayi tace bodd’i na sannu da zama, kin gaji Ko?”
Binta da kallo kawai *hanna* tayi kwallah tafara zuba sharr a idanuwanta, mamaki ne yakama hussentu dan tunda *hanna* tazo Ko abun kuka akayi, toh ita dariya takeyi, kamo hnnunta tayi tace yunwa kikeji?, ganin tayi shiru, yasa ta fahimcii abinci takeson tacii, futa tayi tad’auko mata kayan fruit dan tafi cinsu fiyeda komai, ta ciko plate tamm tayi d’akinta dashi, ya ishaq ne dake falo yadubii hussentu da tsawa yace ke ina zakije da wannan kayan haka d’aki, tsabar almubazzaranci, jiki na rawa tace ya ishaq zancine, c’mon wuce kiban waje, dasaurii tayi d’akinta gabanta yana fad’uwa, tana zuwa tazubewa *hanna* agaba, tad’auka dasaurii tafara cii, shafo kanta hussentu tayi tace, kiyi hakuri nabarki da yunwa, *hanna* batasan tanayi bama, cin abincinta kawai takeyi.”

Haka sanda sukayi kwana biyu agidan basuga *hanna* ba, hussentu ne a d’aki tagama yiwa *hanna* wanka tashiryata cikin, wata rigada skirt nata, wanda sunkama *hanna* sosai, cikinta yafito dan dai-dai, tad’aura mata kwalin tayi wani irin masifar kyau sosai, dubanta tayi tace bodd’i na kinyi kyau sosai, Allah duk wanda yamiki wannan abun sai Allah ya saka miki, itakuwa *Hanna* dariya kawai takeyi sosai, fita hussentu tayi tace barina kawo miki fruit kinji, bata kulataba dariyanta kawai take zabgawa, itakuwa tasaka kai tafice.”
Ya ishaq tasamu afalo shida diddi takuama inne, sai yarinyarsa agefe tana wasa, data shige ciki ya dubeta yace, idan kinshiga ki dafawa ihsan indomie kafin kifito, toh kawai tace amma badan ranta yasoba, tafiso takaiwa *hanna* abinci, tukunna. ”
Haka tatsaya ta na yin taka tsan-tsan dan kada taje tayi wani abunda ba dai-dai ba ya jibgeta.”

*Hanna* tazauna taga shiru, kuma gashi k’ofa abud’e, aikuwa tatashi tafito abunta, diddi na kallonta tayi saurin cewa bodd’i kona d’aki, hussentu nazuwa yanzu, itakuwa *hanna* Ko kulata batayi ba tacigaba da k’arasowa falon,
Jin diddi nacewa bodd’i koma ciki yasa hankali inne da ishaq yayi kanta, itakuwa hussentu tafito aguje tayi wajanta, tsayqwa tayi agaban *hanna* tarufeta dake tafita tsayi, ajiye jaridan hannunsa ishaq yayi, yatshi ya nufii wajansu.”
Kamar hussentu zatayi kuka tafara cewa yaya bbu abunda tamaka fa, karabu da ita, gwara ni kadakeni kaga ba lpy ne da itaba, bai kulata ba ya isa dai-dai wajansu, kuka hussentu tafashe tana yaya wallhy sai dai kadakeni, Allah kuwa bazan kauceba, sa hannu yayi ya ja hussentu tu yature gefe, numfashinsane yatsaya cakk yana k’arewa *hanna* kallo zuciyarsa tana bugawa dasaurii dasaurii, itama *hanna* ido tak’ura masa kamar maison gano wani abun, tamatso dabb dashi, tasaka hannu akan hancinsa, ai nan numfashin hussentu ya d’auke, aranta tace shikenan zai kasheta, jann hancinsa tayi ta k’arfii sanda yace auchh, itakuma tafashe da dariya sosai, tsayawa yayi yana kallonta dariyar tayi matuk’ar yimata kyau, dan gefensa ta leqa taga ihsan nawasa da teddy, dasaurii tawuceshi tak’arasa wajan ihsan, saka hannu tayi ta fauce teddy d’in, dake hannun ihsan, ihuu ihsan tafasa itakuwa *hanna* tayi saurin boye teddy din, abayanta, dasaurii hussentu tak’araso wajan takwace teddyn hannun *hanna* itakuwa *hanna* itama tafasa ihuu, tafad’ii tana shure shure, inne da ishaq harsuna had’a baki suna cewa, k’ar6aki mayar mata, wanda su kansu basusan lokacinda hakan tasu6uce abakin su ba.”
Karba hussentu tayi tamayar mata, ihsan tasa ihuu, shikuma yazo yad’auke ihsan yana cewa ki bata Ko, zansaya miki wani.” kinjii bebyn abba, d’aga masa kai ihsan tayi, hussentu taja hannunsa *hanna* sukayi d’aki, juyawa yayi yadubi mahaifiyar sa yace diddi wacece ita?”
Girgiza kai diddi tayi tace bansantaba, zama yayi kusada diddi yace bakisanta ba kuma diddi?”
D’aga kanta tayi, sannan ta jero musu labarin had’uwwarsu da ita, dukansu tausayinta ne yakamasu, inne cikin wata sassanyar murya wanda ita kanta batasan tanada itaba balle kuma su sauran mutanen gidan tace, hafsa watanta biyu hadda satii biyu amma baku nema mata magani ba?”
Sunku yarda kai kawai diddi tayi, mamakine yakasheta duk danginsu bbu wanda yakai diddi da ishaq d’agun kai, da kuma rashin tausayi, amma kuma wai sune suke nuna tausayinsu k’arara akan *hanna*.”
Abunda matukar mamaki wanda yagaza boyuwa afuskarta, ishaq ne ya nisa yace, cikinta harya fara girma, duk wanda yamata wannan abuu Allah bazai ta6a barinsaba, Ko tausayin cikin jikinta ayii abarta da hankalinta, ciki jikin mace mai baki ma ya aka kare, balle wanda bazata iya fad’in wani waje yana mata ciwo ba, yaya kenan?”
Inne ce tace, ai Allah bai bacci, Ko baka fad’i ba, zai mata sakayya, sannan ta
Tashi tayi tace kiramun hussentu nak’ara kallonta, tashi yayi yanufii d’akin hussentu for the first time, hussentu najin sallamrsa hanjin cikinta yakad’a tatashi dasaurii, tanufo k’ofar tabud’e, kallonta yayi yace, kawota kuzo inne nakiranta, tabud’e baki zatayi magana, yayi saurin juyawa yadda bazai jita bama.”

To be continued

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

“`Ankarbo daga bban dalhata, Allah yak’ara masa yarda yace,” Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi, yanacewa,(la yadkulal mala’ikatu baitan fihi kalbun wala sura.) mala’iiuku basa shiga gidanda yakeda kare kokuma photo.”“`

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply