Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 90


Bibiyata Akeyi 90
Viral

PAGE 90

*
Wucewa yayi yazo falon yasamu inne yace, tana zuwa sannan yajuya da ihsan ahannunsa yawuce d’aki.”
Sun kai 15minute kafin hussentu tafito hannunta riqeda na *hanna*, bata k’arasa kusada inne ba tasake ta, saka hannu inne tayi takamota, har zuwa gabanta, tanajin son yarinyar aduk wani ga6o6i najikinta,
Kallonta tatsaya yi, sannan tadubi diddi tace, asshha wannan ai yarinya ce, shakaf, hussentu ta girmeta, d’aga mata kai kawai diddi tayi, sannan tasake cewa, zan aika baban ihsan ya d’aukomin malam daga ruga, yazo yadubamin ita.”
Murmushi diddi tayi kawai sannan tace Allah yakawoshi lpy, tunda dama bawai tasaba da hira da inne bane, kokad’an bataga wannan fuska ba.”
Sunyii shiru dukansu natsawon mintuna da dama, inne ta dubi diddi tace mata kuma wani irin abincii takeci?”
Mamakine yakamasu sosai, wai yau inne ce ke tambayar su, koda gaisheta sukayi saita ga damar amsawa, kokuma tad’aga kayinta kawai, diddi baki yana rawa tace, kayan itacuwa kawai tafii cii.”
Koda za’ataci abincii saidai kayan zakii, duban hussentu inne tayi tace, maza tashi kije kikira sadiq yazo yak’aro mata, kayan itacuwan kada tatashi ba k’ata kuma yak’are.”
Tashi hussentu tayi tanufii d’akin sadiq, tana shiga da sallama tace wai kazo injii inne, gabansa ne yayi wata mummunar fad’uwa, shidai yasan idan kaji kiran tsohuwarnan to masifa ce, jiki bbu kwari yatashi yasako rigansa sannan yabi bayan hussentu.”
Yanda isa afalo yagansu, durkusawa yayi har k’asa yana gaida ita, bawai dan yayi zaton zata amsa ba, Amma ga mamakinsa dawuri ta amsa kuma fuskarta bbu yabo, bbu fallasa, kud’i tamiqa masa sannan tace, sadiq da’allah kaje kasiyowa yarinyarnna kayan itatuwa, karban kud’in yayi har yana had’a kafa wajan saurii mamaki, yagama kasheshi.”
Baifi 40 minute ba yadawo, hannunsa d’aukeda ledoji, inne tadubi hussentu tace, karba, sannan ku daga frigde na corridor kukai d’akinki kuzuba aciki, dasaurii ta tashi, tatamakawa sadiq suka shigar da frigde d’in.” sannan tajuye kayan ledan aciki, wanda yayi saura kuma tafita dasu zuwa kitchen.”

Sosai suke kulawa da *hannna* , jinta sukeyi kamar er danginsu.”
Abuhuwa suke saya su ajiye, kozata gani tace tanaso, dan babaki take dashi ba.”
Wata ran alkhamis da safe, ishaq yatashi yanufii ruga, yaje yad’auko malamin, zuwa 11:00.am sundawo, tareda shi, bai hutaba, yabukaci ganin marar lafiyan.”
Hussentu ne taje tad’auko ta, tashigo da ita, y’an wasu addu’oii yabata, sannan yace, duk abunda yafaru sukirashi, zai zo danjin yanda jikinnata yake ahaka sukayi sallama, sadiq yamaidashi har gida.”

Yauma Marshall kamar kullum yana zaune, idanuwansa abud’e amma yanutsa cikin tunani, ummii ta dad’e akansa amma baisanda zuwanta ba, da d’an karfii Yanda zaijita, tace, yakamata karage tunani, dan zai k’ara haifar maka da wata illa ce, tashi yayi yakalleta sannan yace ummii ni tunanina d’aya yanzu awani hali take?”
Abun damuwar kenan ummii tace, sannan tace, amma in sha Allah tana kyyyawan hannu, Allah zai bayyana mana ita aduk yanda take.”
Allah yayarda yace, sannan yakoma yakwanta, ya lumshe idanuwansa, ganin haka yasa, ummii tashi tashiga d’aki, dan tasan bawani abun zai k’ara cewa ba.”
Tana shiga saiga intisar ban, kamar kullum, tazo tazauna akujeran dake facing nasa, tagaidashi dakyar ya amsa, sannan taci gaba da zaman kuramen da takeyi kullum, sanda yqjii kiran sallah yatashi yatashi, yabarta awajen sannan itama tatashi tafice. ”

Kwance hanna take asaman carfet, ta danne cikinna ta, sosai kamar zaifashe, gashi dama cikin yafito sosai, sai murkususu takeyi, ahaka hussentu tashigo tasameta, dasaurii tak’arasa wajan ta, tana cewa haba bodd’i yanzu banhakanki kwanciya akan cikiinnan bane?”
Sokikeyi kiyiwa abunda ke cikinta illah?” sa hannu tayi tad’agota, amma firr *hanna* taqi d’aguwa, dan tayi nauyii cikinta yayi girma, juyawa tayi falo, tasamu, diddi tace, diddi bodd’i nanan tadanne cikinta, kuma zata iya yiwa abunda yake cikin illah, diddi tatasi tana cewa subhanallahi, kekuma baki d’agata ba? Diddi taki nefa, d’akin diddi da hussentu suka nufa.”
Suna isa k’ofar tabud’e tashiga ihuu hussentu tasaka wanda yaja hankalin mutanen gidan, gabaki d’aya sukayi d’akin, jinine kebin *hanna* tako ina, ta fafasa glasses ta yayyanka jikinta, dasaurii ishaq yayi kanta tana ihuu, yariqota gamm, yad’auketa yayi hanyar mota da ita, duk mutanen gidan suka wuce hospital d’in.”

Suna isa aka amsheta, treatment kawai aka mata, basu riqesuba, aka sallamosu, gida suka nufo dukansu.”

Suna isowa Kuwa kowa yabud’e yafita inne ce takamo hannun *hanna* tana cewa, zonan er albarka, mutafii d’akina yanzu, acan zakina kwana, kin koma d’akina daga yau, kallo kawai sukabii inno dashi, basu ta6a Ganin taso wani mutum kamar yanda take nuna kulawarta akan *hanna* ba.”
D’akinta tashiga da ita, tana zuwa tashiga da ita, taja hannun ta ta kwantarda ita kan bed, tana cewa, maza zonan er albarka, ki yi bacci ki huta kinjii.”
Haka tayita buubbugata kamar k’aramar yarinya har sanda tayi bacci tukunna.”
Da dare kuwa suna zaune dukansu afalo, ishaq yafito cikin shirin fita, yadubi ihsan yace, my girl zamuje anguwa ko, dasaurii ta tashi, ta nufo shii.”
Juyawa yayi yqkalli *hanna* sannan yace mata itama, zo sutafii, kallonsa *hanna* tatsayayi, galala kamar mai son gano wani abun, hannu ya miqa mata had’eda d’aga mata kai, nan ma batasan maiyake fad’i ba.”
D’an rusunawa yayi yakamo hannunta, yamiqar da ita, sannan yajuya yakalli, hussentu yace, tashi kije kid’auko mata hijab, da saurinta ta tashi, tashiga d’aki, tad’auko hijabin tazo tana k’okarin saka mata, tsayarda ita yayi yad’an rusuna, yasaukarda ihsan, yakarbi hijabin yasaka mata.”
Sannan yad’auki ihsan yajuya yakalli iyayensa yace barii mufita, kowa da Murmushi dauke fuskarta, tace adawo lpy.”
Kai tsaye wajan wani sha ice cream suka nufa, dasu duka suka shiga, amma hannunsa yana riqeda na *hanna*dan kada tayi musu barna, yasiya musu nasu itada ihsan, dakuma sauran mutanen gidan, itakuma inne fura da nono kawai yasaya mata, sannan yad’an zaga dasu suka nufii gida.”
Suna zuwa yasauke ihsan yamiqawa *hanna* robar ice cream, yawuce d’aki.”
Wajan inne taje tazauna, inne takar6i roban tasa d’an k’aramin cokalin cikin ice cream d’in, ta fara bata ahankali, tanayi tana goge mata baki, har tagama.”
Tajawota jikinta, ta kwantarda da ita akan cinyarta, tana bubbuga bayanta, jefi-jefi kuma suna hira, wanda hakan yafaru ne ad’an kwanakinnan, nazuwan *hanna* har inne kesakewa tana hirada su.”

Haka sukaci gaba da kulawa da *hanna* sosai har cikin ta yakai 7month, tacika 6month da 6acewa kenan, yanzu yakasance awannan dangi bbu maijin haushin wani kokuma wani yak’i kula d’an uwansa hira sukeyi sosai, ta shiga ransu, itama Kuwa tasaba dasu sosai.”
Dan koda batasan mai suke fad’aba idan sukayi magana tasheke da dariya suma Haka zasu bita suyita dariyan.”
Wani lokaci kuma idan anyii magana sai ta amsa da kayi kamar wanda tajii mai suka fad’a.”
Kuma alamun ma yanuna cewa ta fahimta.”

To be continued

Ur’s

Z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

.

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply