Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 91


Bibiyata Akeyi 91
Viral

Page 91

*
Labba ce zaune sai dube-dube takeyi, Marshall dake kusa da ita, duk tabi tadameshi, da k’aran paper’s, tsaki yaja yadubeta yace, wai mekike nemane?”
Bata d’ago ba tace wallhy yaya wai takardan asibiti na affan ne da anty afeeya tazota ta manta, zasu koma ne, tsaki yaja kawai yatashi, yashige d’akin ummii nan ma ganii yayi tafito da takrdu duk ak’asa, tsaki yaja yakwanta akan bed, ya lumshe idanuwansa shi dai ba bacci yakeyibaa.”
Juyi yayi idanuwansa sukakai kan takardar dake cikin paper’s data futo dasu, ganin anrubuta Aminu kano hospital, yasa yayi tunani Ko itace takardan, kamar wanda baiso yakira Labba, Labba, amma bata amsaba, dan baiyi maganar yanda zatajishi bama, ganin Ko kad’an batajii ba, dama kuma bawai yayi maganar yadda zataji bane, tsaki yaja akaro bila adadin, yatashi yak’arasa har gaban takardan yasaka hannu yad’auka.”
Fita yayi zuwa falo batareda yadubaba ya miqa mata yajuya, k’arban takardar tayi tafara dubawa, zaro ido tayi, arazane tace yaya, tsayawa yayi batareda da juyo ba, bata damu da hakanba, tak’ara cewa yaya, wannan takardan *hanna* nefa, dasaurii yajuyo tacigaba dacewa, kuma yaya gani nayi kamar takardan da take nuna tana d’auke da cik,,,, bata k’arasaba yayi saurin karasowa yafauce takardan, ahannunta, kafin en secouns idanuwansa sun kad’a sunyii jajirr, idan ba idanuwansa gizo suke masa ba, gani yayi kamar takardan tana nuna *hanna* nad’aukeda ciki na 1month ba kenan, dasaurii yafice da takardan ahannunsa yanufii shahsin mai martaba.”
Afalo yasamu ummii ta abbansa suna zaune, Ko k’arasawa bai iyayiba, zuciyarsa na masa k’una yace, ummii yanzu dama *hanna* nad’aukeda ciki baki gayamun ba, ummii menene amfanin b’oyemun dakikayi, alhali kinsan duk daran dad’ewa zan sani.” bai kara cewa komai ba yajuya yafice, ummii tatashi dasaurii zata bishi mai martaba yayi saurin tsaida ita yace, rabuu dashi, kada kije kusadashi, dan yanzu yana cikin zafin zuciya, abun yaronnan yafarayin yawa, narasa maiyasa yakasa d’aukan k’addara, komawa ummii tayi ta zauna, tausayin d’anta fall aranta, dubanta mai martaba yayi yace, toke menene dalilinki na b’oye masa matarsa tanada juna biyu?”
Dakyar ummii ta iya cewa ina tunanin halinda zai shigane idan yasanii, damuwar sa ta yanzu zatafii tadah. Niasawa mai martaba yayi, yana tausayin kansu dan dukansu abun rausayine, yana tausayin *hanna* Ko yanzu wani hali take da juna biyu.”
D’aga hannu mai martaba yayi sama yace ya Allah kaga irin jarabawar da ka jarbci bayinka dasu, Allah ina roqonka da ka bayyana mana wannan yarinya, Allah kakare baiwarka cikin kowani irin hali take.” Allah kasada ta akykkyawan hannu. Amin ummii ta amsa dashi.”

Marshall yana fita shahainsu yawuce kai tsaye, mukarrabansa na biyedashi abaya, shahin yayi k’ura sosai tunda *hanna* ta6ata bbu wanda yak’ara shigansa.”
Zama yayi akan carfet dirsham bai damu da dattinsa ba yace, hava *hanna* yaya zakimun haka?” mena miki haka, zataki tafii kibar zuciya ta cikin kunci? ashe duk maganganun da kike fad’a da gaskene? ashe dama tafiya zakiyi ki barni yasa kike fad’amun irin wannan maganar?
Hawaye ne yabiyo kuncinsa, wanda rabonsa dasu tun yana yaro, yana yaronma bazai iya recalling lokacin ba.”
Baidamu daya goge hawayen ba, dan koya goge wasu zasu biyo baya, kuma aganinsa hawayen dake zuba a idanuwansa, sune sassauci agareshi, zaiso sufii haka yawa ma, zaiso ace yayita kuka, har indai hakanne zaisama masa sauki,
Lokacii d’aya kansa yasara yahau ciwo, cikin ransa yana tunani yanzu awani hali, *hanna* ke ciki da juna biyu.”
Sunbatu kawai yafarayi,
Hawayen na zuba yak’ara cewa meyasa zakimun haka, kinyi alqawari bazaki bazaki fad’amun irin magan ganunda ke sani cikin damuwa ba, balle yaje ga tafiya ki barni.”
Yanda kasan wani zaucecce yaketa maganganu , wasun kanma koya fad’i bazaka gane meyake nufii ba.”

Marshall yakai 3day’s bbu wanda yakalli kwayar idanuwansa, yana cikin shashinsu, koda anzo ana bugawa baya kula kowa, yanaji yake sharewa, mai martaba yakira baba yasanarda shi abunda ake ciki.”
Sosai baba yaji bbu dad’i aranar yakamo hanya yazo garin, yana isa ya wuce fada, dake shikad’ai yazo Ko driver bai d’auko ba.”
Sosai mai martaba yaji dad’in ganinsa, bayan sun gaisa ne mai martaba yasa aka kira masa ummii, takai 15minute kafin ta iso, duk tarame gabaki d’aya ta lalalce, bayan sun gaisa ne, baba yad’an nisa kafin yace, shawara ce nakawo, wanda ina tunanin shine mafita dashi damu kuma baki d’aya, mai martaba ne yace, muna jinka, dan yanzu dolen mafita muka zauna nema, baba yacigaba da cewa, ni aganina abunda zai zama maslaha damu dakuma yaronnan shine kawai, ak’ara masa aure, gaban ummii ne yayi wani mummunan fad’uwa, tace haba da Allah, wai ce muku akayi *hanna* baxata dawo bane Ko kuma?” girgiza kai kawai baba yayi yace Ko d’aya ba’ace *hanna* bazata dawoba, kuma shi ai mijin mace hud’u ne, koda tadawo saidai tayi hak’uri, amma Ganin wata kusada shi zai rage masa damuwa,zai rage yazauna yana tunani, mai martaba baice komai ba juya maganar kawai yakeyi, sai dayaji kowa yayi shiru sannan yace, amma kana ganin hakan shine mafita bbu wata hanya? Girgiza kai baba yayi sannan yace gaskiya idanma da’akwai wata hanyar nidai bansanta ba.”
Mai martaba yace, toh Allah yaza6ar mana mafii alkairi, da ameen baba ya amsa, sannna yacigaba da cewa, baka ganin er k’aninka, naga kusan kamarsu d’aya da ita *hanna* d’in ai sai ka tambaya masa ita, dasaurii ummii tacafe, tace wah wai hameeda kuke nufii, amma wannan babban cin amana ne, er uwartata xaku aurawa mijinta dan bbu idonta, wallhy Allah bada yawuna za’ayi wannan auranba, tatashi tafice tana sharar kwalla.”
Binta da kallo sukayi su dukansu, sannan mai martaba yace, kasan halin mata da wani irin abuu, abunda Allah ya halasta su zasu nemi haramta maka shii.”
Nan sukayi sallama suka tashi akan baba zai wuce su zauna suji yadda za’ayi shida, abba.”

Umma nashiga d’aki tafashe da kuka, kawai tana jajanta abunda ake shirin aikatawa baiwar Allah.”

Labba ne tamatso kusada ita tace, ummii menene yafaru?”
Wani abunne yasamu yayan?”
Girgiza mata kai ummii tayi, sauke ajiyar zuciya Labba tayi, ummii ne tace kayya er nan daina wata ajiyar zuciya ina maraban wani abu yasameshi, da abunda ake shirin aikata masa yanzu.”
Riqo hannun ummii Labba tayi tana zazzaro ido sannan tace, me za’ayi masa?”
Aure zasu masa, ummii tabata amsa atakaice, aure kuma ummii?”
Eh aure kuma wai er uwarta hameeda, subhanallahi hameeda ummii?” wannan wani irin cin amana ne, nan danan idanuwanta suka fara zubda kwalla.”
Tatashi dasaurii tafice dagudu, bata tsaya ba sai sashinsa, tana zuwa tafara bugawa kamar wata mahaukaciya, jin bugun yayi yawa yasa yatashi, dakyar yabud’e, kofan.”
Dagudu Labba tashige jikinsa tana kuka, bubbuga bayanta yafarayi, amma bai iya magana ba, sanda tagaji dan kanta tad’ago tadubeshi tace, yaya Allah aure zasu maka, suwa? ya tambaya, su abba, mana, d’agota yayi yace kai Labba kodai bakiji dakyau bane?” ni nace musu inason aure?” Allah kuwa yaya wai kuma da hameeda, zaro ido yayi yace hameeda kuma labba, eh Allah yaya, ajiyar zuciya yasauk’e yace to ai yazo gidan sauki, zuwa gobe, zanshawo kan matsalar har indai hameeda ce, dawatace sai in damu.”
D’agowa tayi tadubeshi tace Allah yaya, d’aga mata kai yayi yace, Allah kuwa acikin week d’innan zan shawo komai.”
Sai alokacin hankalin Labba yad’an kwanta, tadubeshi tace yaya kaci abincii ne, girgiza kai yayi yace banjin yunwa ne, yakamata kaci ai tabashi amsa takaice.”
Tashiga kitchen tahad’a masa abincii, dakyar yaci, sanda yaci kuwa tabar shashin, taje tafad’awa ummii Yanda sukayi, Allah yasa adace kawai ummii tace.”

Baba ya isa gidan abba suka zauna, sukayi magana, abba fur yak’ii yarda, sanda baba ya nuna masa bacin rai, ya ce, idan kanaso kanunamin bani nahaifeta ba shikenan, amma ni nadauka yarana da naka duk d’aya ne, nan danan abba yarikice, har idanuwansa suka ciko yace haba yaya, wannan wani irin magana ce, baba ne yace idan bahaka kake nufii ba, mai yasa zanyi magana kace bahaka ba.”
Kayi hak’uri yaya wallhy hameeda erka ce duk Yanda kakeso kayida ita.”
Tom nagode idan kashiga kayiwa matarka magana kajii, nima idannaje zanmata magana.”
Ahaka sukayi sallama.”
Abba ya tashi yashiga gida jikinsa bbu kwarii.”

To be continued

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

“`Alhmdllh am so much bless, addu’anku sunyi aiki, godiya Mai yawa“`

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply