Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 93


Bibiyata Akeyi 93
Viral

PAGE 93

*
Da sassafe Ahmad yaje gaida mai martaba, bayan Sun gaisane maiartaba yadubi, Ahmad yace, dama Ahmad insonyin magana dakai, inajii abba yace, wai meke tsakanin ka da er uwar matar yareema ne, sunkuyarda kai yayi, sannan yace abba da ma munhad’u da ita abikin ya, yallabai ne, kuma tunda nace akan zanmuku magana aturo, toh 6atan er uwarta ne yatsayar da komai.”
Nisawa mai martaba yayi yace, tashi kaje ka, zan maka tambayar yarinyar, sunkuyarda kai yayi yace na gode abba.”
D’aga kai kawai mai martaba yayi.”

Kilishi dake cikin d’aki ne tafito, tace yallabai wai menakeji ne kamar Ahmad ne zaiyi aure.”
Nisawa mai martaba yayi yace, wallhy abunne yazoda sark’akiya, kamar yaya tafad’a tanason jin abunda ke faruwa, batare wata fargaba ba, yafad’a mata komai, cikin munafurci tace assha ranka shi dad’e, ai bahaka yakamata ayi ba, tayaya za’ace ya aurii budurwar k’aninsa, dabadan yadace yayi auran bama danace abarshi, amma tunda anaso yayi saiya barwa kaninsa budurwar sa, dan kada mutumcinsa yazube a idanuwasu, naraba musu soyayya dayayi.”

Mai martaba yace, nima abunda nayi tunani kenan, Murmushin mugun ta tayi tace aiko cikin dangi kuwa baza’a rasa wacce za’a had’asu ba.”
Mai martaba yace, eh hakane ke yanzu wace yarinyace kike gani yadace adangin, eh toh kasan bakayi tarbiyar mutum ba bzaka yi shaidansa ba.”
Nidai intisar kawai nakeda shaida dan ita nagoya nasan halinta, mai martaba yace toh ki tuntu6eta kiji nima zanmasa magana, toh Allah yasa yayarda, dan nasan intisar tanada biyayya, ina fad’a mata zata amince.”

Ahaka sukayi tsayada zancen, mai martaba yakira ummii yafad’a mata, bak’in ciki bai bar ummii tace komai ba, tashi kawai tayi tabar d’akin tana, shiga d’aki takira afeeya tasanarda ita, sosai ranta ya6aci, tana cewa yanzu shi ummii baida tsa6in kansa kenan?”
Toh ni mai zanje, wallhy nasan duk kilshi ne tahad’a wannan zancen.”
Labba kam tattara kayanta tayi gabaki d’aya tawuce dubai dan bazata iya zama taga wannan kayan bakin ciki ba.”
Halima har gida tazo tasqmu mahaifiyarta, bbu yanda batayi da kilishi akan subar zancen aurenba tak’i.” daga k’arshe ma sai tabita da zagi, halima tace wallhy umma wulakamcii, nake ji mata, tunda tasan baya sonta akwai wanda yakeso, wulakanci kam tashirya gani.”
Dan duk abunda yasameta wallhy kokad’an bazanji haushi ba.”
Tana fad’in haka tazari gyalanta tafice agidan.”

Shiko ogannaka, yarasa nacewa ido kawai yazuba musu, wai shi za’a aurawa intisar abun yana matukar bashi mamaki.”
Mai martaba yakira baba yashaida masa abunda ke faruwa, baba dama abba yasanrda shi, nan aka nemawa Ahmad auran hameeda, za’a had’a dana hafsat, anso ahad’a dana rabi’at amma abun bai yiwu ba, dan ita nata saurayin bai fito ba.”

 

Ranar aure d’aya za’ayi dana Marshall Ahmad dakuma captain bilal hafsat, baki yarage saura 2weeks lokacin, tako wani bangare shirye shirye ya kankama, intisar event kala-kala zasuyi, amma Ko idon ango bata gani balle tasaka ran cewa zaije wajan event d’in.”

 

Hameeda da ahmad soyayya sukeyi sosai, yanda kasan ba had’asu akayi ba.”
Aranda aka shiga satin biki Marshall ya tattara, shida soldier’s d’insa sukabar k’asar.”

Duk wannan abunda akeyi fulani, kakar Marshall bata sani ba, dan bazata bari ba, shiyasa akayi gargad’i akan kar agaya mata.” 6acewar *hanna* kawai tasani.”

 

Tunda aka shiga satinnan *hanna* kullum cikin kuka takeyi, tunda cikin yacika 9month take wannan kukan amma nayanzu yafii tsanani.”

Wata Ranar alkhamis *hanna* tatashi ta ciwon baya, da kuma na mara, da abun ya isheta kawai tafara ihuu, dan ita ba hankaline da itaba, balle tafad’i yanda yake mata ciwon, bakuma zata iya jurewa ba.”

 

Dasaurii diddi tazo kusada ita tana cewa, bodd’i menene?”
Ganin tana riqe bayanta, yasa tafita dasaurii, tasamu su inne afalo tace, inaga fa yarinyar nan, haihuwa zatayi, da’alamu, tazo kusa, dasaurii inne tatashi tayi d’akin, ganinta Ahaka yasa suka futo da ita sukace, sadiq yad’auko mota sutafii asibiti, isshaq har yarigashi saurin fita, nan suka d’ugun zama zuwa asibiti.”

 

To be continued

 

Ur’s

Z33iiyyb3rw3r
[9/1, 6:26 PM] Maryambawa: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

“`Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace, (man mata) Manzon Allah yace duk wanda yamutu, (wahuwa yad’uu ma’allahi iddan) alhali yana kirawa Allah kishiya, wato yanayin shirka, yana had’a Allah dawani, (dakalan nara) Manzon Allah yace zai shiga wuta.”
Allah karabamu da yin shirka, domin na d’aya daga cikin munanan ayyuka.”“`

Wannan shafin nakine *ZAYNAB UBA AHMAD (momyn yasmeen)* inasonki irin sosai d’innan Allah yaraya mana *yasmeen* musha biki, har shoki saina kwaso.”
Mummynta zeeyy na gaidata, yasmeen d’ina agaishemunda *baabaa(ameerah)*😜 ace mummy na gaidata, itada *iyah(ummii)*🙊🙊

“`Raheenat mahmoudouu, tunatarwane agareki, inasonki, irin bohut bohut d’innan, Allah yabarmu tare, ranar aurenki sai naje nijar fa.”😜
Niamey zatayi bak’i.”“`

.

==============

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply