Dare Daya Hausa Novel Hausa Novels

Dare Daya 49-50


Dare Daya 49-50
Viral

PAGE 49&50

 

Yana zaune MAHELET ta zauna a kusa dashi yana mata magana a hankali bataji me yake ce mata ba amma taga sun mugun burgeta, sallama tayi musu da sauri Ya dauke kansa daga kallon MAHELET ya zame jikinsa daga kan kujera ya duƙa yana gaishe da ita amsawa tayi cike da farin ciki tana Cewa Ango murmushi yayi yana shafa kansa, gu ta samu ta zauna tana cewa tashi ka zauna kaji tashi yayi ya hau kujera suka gaisa kafin ya fara magana momma an siyar da gida amma ba kowa ne ya siya gidan ba nine kallonsa tayi sai kuma ta basar tana cewa Jameel me zaka yi cikin wannan tsohon gida mai mugun tarihi ko nace baƙin tarihi, a hankali yace momma nayi bin cike ne kuma alhamdulillah naci nasara akan binci kenda nayi MAHELET tana yawan mafarki konace mafarkaiya daban daban wani lokacin har tace ɗakin ki takeso ta kwana ehhh sai daga baya da take gayamin ashe ba lokacin Abbi ya fara neman taba ya dade yana bin *DARE* Allah bai basa sa’a, da yake Allah karimun rahimun ne sai gashi *DARE ƊAYA* ya tona masa asiri shiru Dr Jameel yayi yana kallon ta kafin yace momma ba Abbi ne ke shiga ɗakin MAHELET ba da dare da nayi bincike na gado an warware daga daga cikinta windows din ɗakinta ta baya ajiye ne kawai take da an tashi shiga sai a dauki window din a ajiye gefe idan an fito kuma sai a mayar, kin kuwa ga da Abbi ne! Shiru falon yayi daga Momma har MAHELET suna jiran suji waye yake aekata wannan aeki, a hankali yace ba kowa bane ke aekata wannan aeki face ILIYA domin shine mai bayawa flowers ruwa kuma shine mai kula da bayan gida ma’ana bayan ɗaku nan ku na gano hakane bayan rufe su danasa akayi a Police station kuma nasa aka tsananta bincike akansu runtse idanu momma tayi sai kuma ta buɗe a hankali tace aekuwa na gama masu aeki kenan har abada tashi tayi tashiga bedroom ta fito da kuɗi masu yawa sosai a hannunta ta fita suna nan zaune MAHELET zata miƙe yasa hannu ya riƙe ta momma na zuwa bakin gate tana ƙwalawa masu gadi kira jiki na rawa suka taso duka su uku din tsohon cikinsu shine driver Naira dubu 50 ta cire ta basa sai guda biyu da suke samari ta cire dubu talatin talatin ta basu tace duka na sallame kuh kuma banaso ku tambaye ni dalili abunda yasa kuwa na baku wadannan kuɗaɗen sbd kuyimin aeki na tsawon kwanaki biyar ko nace sati ɗaya nan sukayi godiya Baba tsoho harya jiuya momma tace Baba tsoho jiuyo yayi jiki na rawa yace na’am hajiya sosai taji tausayin sa a hankali tace kai zaka zauna amma ba’anan zaka ringa kwana bah zaka zo da safe sai da yamma kuma ka tafi ta To!!! To!!! Hajiya nagode Allah saka da alheri har jikinsa ke rawa kamar zai duka mata girgiza kai tayi kawai ta koma cikin gida MAHELET da Jameel suna zaune a yanda ta barsu komawa tayi itama ta zauna tana cewa bazan ƙarayin masu aeki ba koda nayi kuwa babu wanda zai ƙara kwana a cikinsu yanzu haka duka na sallamesu Baba tsoho kawai na bari ko shi sbd yanda yake abun tausayi ga ‘ya’ ya ga mace har biyu, girgiza kai Dr Jameel yayi MAHELET kuwa sai yan matan hawaye take tanasa bayan hannunta tana sharewa tashi momma tayi tace zan koma ciki ka gaishemin da Umman taku idan ka koma gida to momma ya amsa ita kuma ta shige ciki jiuyowa yayi gun MAHELET dake kuka yana cewa wai miye haka? Na gaya miki komi ya wuce ILIYA yanzu haka yana can a kulle Abbi kuma….. Sai yayi shiru haka yaringa janta da fira harya samu ta saki jikinta, sai guraren 9:30 yayi mata sallama sbd Gida zai koma ba hospital bah har mota ta raka sa yanata zolayar ta Yana kiranta Amarsu ta Ango itama kuma tana cewa Aekaine Angon, haka suka rabu cike da annashuwa yana isa gida ma saida ya kirata suka sha fira yana ƙara tuna mata cewa go warahaka ta zama tasa sai yanda yaga dama,
Yaufa safiyar dauri aure sai hidima ake a gidaje biyu Baba kuwa ya aekawa mutanansa yan Bugudu Abba ya bayar da Bus biyu duk maiso yazo sai ya shigo bus ba laifi sosai mutane suka shigo bus domin zuwa daurin aure ƙarfe 2 na rana daidai duban jama’a suka shaida ɗaurin Auren DR JAMEEL AHMAD JAMEEL & MAHELET KAMALU IMAM sai ABBAS AHMAD JAMEEL & HAFSAT KAMALU IMAM ko waccen su akan sadaki Naira dubu dari dari Baba harda kuka yayi yanaji inama matarsa na raye taga wannan rana kuka yake amma na farin ciki ne da jin daɗi, cikin gida babu wani taro da yawan sai ƙannan Abba da Ƙannan umma kosu wadanda ke nan cikin Zamfara domin Abba cewa yayi ya dauke wa duk wanda ke nesa ba sai yazo bah kawai yayi ma ma’auratan fatan alkhairi aekuwa yanata samun saƙonni a wayar sa kama daga abokanan aekinsa harma da waɗanda yake taimakawa, Ummi ce zaune da Umma ummi ƙanwar Ummace ciki ɗaya ita ke Binta suna tattaunawa akan yanda zasu haɗa waleema kafin su Abbas su tare da matan su wayar Umma ta fara ringing sunan Abbas ta gani a screen din wayar murmushi tayi kafin ta daga wayar tana dauka yace Ummmma an daura murmushi umma ta saki tana mamakin rashin kunya kalar na Abbas Sam ba haka yake ba ada yarone mai kunya amma Hafsat na shigowa rayuwarsa duk yabi ya canza mata, a hankali tace Barakallahu lakuma wa. baraka alaikum wa jama’a baynakuma fii khair Allah ubangiji ya baku zaman lafiya da zuri’a ɗayyaba, shima a hankali yace Ameen Umma, girgiza kai Ummi tayi dake gefe tana cewa wannan yaron yaushe ya canza haka Abbas ne ko Jameel dan nasan Abbas dina bazaiyi wannan danyen aekin bah murmushi umma tayi kafin tace aekuwa Abbas din ne,nan suka ci gaba da firar su Ummi tace ga wannan Ki bawa Abbas wannan kuma na Jameel ne girgiza Umma tayi tana cewa wlh Ummi babu abunda zan bawa yaran nan kar suje su illata yaran mutane kin kuwa ga yanda suke rawar ƙafa? Saidai idan kin kawowa ‘yata Hafsat shine zan ƙarba girgiza kai Ummi tayi tana cewa to na kawo mata itama haɗi na musamman daga Sokoto idan kinji Ana faɗi MAMAN KHALIL LIKITAN MATA TO GURIN TA NA ƘARBO WANNAN HAƊI NA MUSAMMAN KAYANTA TANA HAƊASU NE DA INGANTATTUN ITA TUWA KUMA NATURAL NE BASUDA WATA MATSALA washe baki Umma tayi tana cewa to masha Allah dama haka nakeso tasa hannu ta karɓa nan Ummi tashiga yi mata bayanin yanda za’ayi amfani da kowanne sosai Umma taji daɗi, a hankali tace bara kiga na tashi nabar baƙi a waje zan turo miki ‘yartaki okay toh ina jira Umma tafita falo taci gaba da tarban baƙi
Zaune take ta rafka uban tagumi tayi shiru Zahra ta faɗo ɗakin tana cewa an daura an daura tazama matar Dr Abbas dago wa tayi sukayi 4 eyes ta sakar mata murmushi tana ƙokarin ɓoye damuwarta murmushi itama tayi tana zama kusa da ita a hankali tace daga yau zan mayar dake Mrs Abbas Zahra yar Ummi ce itace ma Auta kuma ita kaɗaice mace duka yaranta maza ne kinga yanzu zansa ayi Adding dinki a classes Groups na yan gayu kuma matan aure amma fah ki iya bakinki kuma ni matar aure ce a group din, ta kashe mata ido ɗaya dariya tayi tana cewa toh sannu matar Oga 😂🤣Uhmm Ummi tayi gyaran bakinta dauke da sallama Zahra ta tashi tana cewa Ummi meet Mrs Abbas ungo kinci gidanku ni sa’arki ce ƙyalƙyacewa tayi da dariya tana cewa ae Ummi baki santa, Oya tashi ki bamu guri zamuyi magana idan kika biye wa wannan yarinyar ko Hafsat nida kece Sam batajin magana kinji ko ɗaga mata kai Hafsa tana murmushi, turo baki Zahra tayi tana cewa Allah Ummi ni gud girl ce kawai dai….. ba zaki fita ba Ummi ta katse mata magana tashi tayi tana turo maki ta fita Hafsat ta ƙyalƙyace da dariya, gu Ummi ta samu ta zauna ta fara magana Hafsa na’am Ummi hafsa ta amsa cike da ladabi da kuma girmamawa murmushi Ummi tayi kafin tace hafsa Inaso ki zamo mace ta gari kuma mafi soyuwa a gurin mijinki
Hafsa kinga fira da dare yana hana mai gida fita yawon dare, ki kula da wannan idan bakya yi masa fira shizaisa ya ringa hirar dare sbd baya samu hira daga gare ki kuma galibi idan suka fita, sai su raba dare ana taɗi a waje, lokacin da zai dawo ke kuma lokacin kinyi bacci, kinga irin wannan ina amfaninsa Hafsat, ki ringa jawo hankalin mijinki ga reki kiyi iya bakin ƙokarin ki na ganin kin janyo hankalinsa gareki muddin kika saba masa masa da wannan ba zai dinga fita ya yawo ba amma idan kikayi saka ci ya saba da fita to duk randa kika so ya bari bazai bari bah wlh Magana ta gaba shine abinci Hafsa karkiyi wasa da ƙwanon mijinki, wato abincinsa kinga barin mai aeki ta girka miki abincin da zaƙi bawa mijinki babbar matsala ce ana samun wannan matsalar ne ga matan masu kuɗi da kuma mata masu zuwa aekin gwamnati da kuma mata masu son jiki da wadanda suka mayar da waya abokiyar firarsu basu tiktok basu WhatsApp basu Instagram, amma fah banace kar ki shiga wadanda Apps bane sbd suma ana neman ilimi ta hanyar kama daga ilimin Addini ilimin zaman takewa kula da miji da dai sauran su karki kuskura ki sakarwa mai aeki wadannan abubuwa guda hudu aekin abinci, kula da yaranki, aekin gida da kuma gyaran dakin mijinki musamman ma dakin mijinki domin ɗakin mijinki shine sirrinki, infact hafsa ni bana maso ki dauko wata Wai HOUSE GIRL kinji ko ƙasa tayi da kanta tace to ummi
Sai kuma abu na gaba karki zauna a cikin duhun kai duk abunda baki sani ba ta fannin kwalliya, kula da hakkin miji, girki tarairayar miji, to ki nemi masa su koya miki ko kuma ki ringa shiga kafafen sadarwa Facebook, WhatsApp da dai sauran su karki yarda ki zauna cikin duhun kai kina cutar kanki kinji hafsa gyaɗa mata kai tayi tace yawwa,
Sai kuma fannin Jima’i wato kwanciyar aure ki kasance mai faran ta masa a wajen kwanciya, kema zakiji daɗi kuma idan kina faranta masa sonki zai ƙaro a zuciyarsa, ga kuma uwa uba kyautar da zai dinga miki koda baki tambaye saba, tunda kina kyautata masa wajen kwanciya doli shima ya kyautata miki, kuma hakan zai ƙara muku zaman lafiya kuma ya rage muku samun saɓani a tsakanin kuh, sai kuma hanyar mallakar miji cikin sauƙi ba tare da boka ba ko malam ina fata kina jina ehhh Ummi yawwa, hanya ta farko ki iya kissar kwanciya, da nuna masa kauna a wajen kwanciya Sam karki nuna masa gajiyawar ki a gurin kwanciya, ki soshi kiso yan uwansa gaba ɗaya, ki bar duk wani abu da bai so, ki ringa yin wanda yakeso, ki kasance mai masa ladabi da biyayya da bin dokokin daya gindaya miki, karki ji kunya a duk lokacin ya dawo kiyi masa tarba mai kyau ko a gaban waye domin yanasa namiji yaji matarsa tafi ta kowa kinji, sai kuma tsaftar jiki da kula da tarbiyyar yara idan kin haihu, ki zama mai tausayin sa akan al’ummaran sa da kuma idan yana cikin wani hali, ki kasance mai kyautatawa iyayen sa da danginsa, kinga wadannan abubuwa dana gaya miki mudun kika riƙeso banu wani wanda zai iya juya miki hankalin mijinki, daya wuce ke zakiyi masa mallakar da babu wata macen da zata iya juya shi sai ke, sai magana ta ƙarshe dazan gaya miki karki kuskura ki ringa amfani da ruwan sanyi a HQ dinki ki kasance ko yaushe mai amfani da ruwan ɗimi ruwan zafi ma kawai idan kika riƙe shikenan domin ruwan sanyi na lalata gaban mace, banda yin matsi kinji duk wani magani da kikaji ance ki matsa a gabanki karkiyi amfani dashi kinji ko banda shanye shayen kayan mata barkatai, ki ringa samun Kankana🍉,Gwanda, Citta, Abarba🍍, lemon tsami🍋, ki haɗe su guri ɗaya kiyi blending kina sha Habawa zaki bani lbr, ko kuma ki samu Kankana ki yanka ta ki cire ƙwallaye ki zuba mata ruwan kanunfari da kika tsiƙa ya jiƙu sai ki zuba peak milk daidai yanda kikeso ki na sha koda bayan 2, 2days ne wannan har Abbas din ma idan zai sha ki basa yasa yana saukarwa mutun da Ni’ima sosai kinji ko, Allah ubangiji ya baku zaman lafiya da kwanciyar hankali da zuri’a ɗayyaba wacce Annabi Muhammad S.A.W zai yi alfahari da ita a ranar tashin ƙiyama
Iyaye mu farga mu tashi daga bacci zaki aurar da yarinya amma kin zama busy sai ɗura mata kayan mata kike kina yi mata yan tushe tushe a gabanta baki zauna kin gaya mata yanda zata kula da miji ba ko bara na gaya miki kinyi aekin banza ne kinbar baya da ƙura🤌🏻…………
[8/2, 3:58 PM] Typing….✍🏻: *DARE ƊAYA*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply