Dare Daya Hausa Novel Hausa Novels

Dare Daya 55-56


Dare Daya 55-56
Viral

6:27 PM] Typing….✍🏻: Murmushi ya sakar mata yana cewa sannu Malama Hafsa ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta tashi yayi ya ƙarasa gunta yana cewa muje kona goyaki dariya ya bata tace Aa zan iya tafiya yace okay muje madam ta shiga gaba yana Binta A baya haka har suka ƙarasa gurin motar sa ya buɗe mata tashiga shima ya shiga ya jasu suka bar harabar hospital din, ya tsaya ya siya musu abinci suna tafiya ya ƙara tsayawa ya shiga mall ya siya mata 2set din kaya duka Abayas suna ƙarawa gaba taga ya tsaya pharmacy ya shiga ya fito yana fitowa tace yaya Lafiya murmushi ya sakar mata kafin yace gidanmu zamu tare shine nake saya miki kayan amfani kafin naje gurin Umma ta tattaro miki kayanki zaro ido tayi waje tana cewa yaya miyasa nidai gaskiya ka mayar dani gida nidai ka mayar dani gurin Umma ae…. Sai kuma tayi shiru kallonta yayi sosai kafin yace ae…. Me? Ki faɗa mana ganin da gaske ba gida zai mayar da ita bah yasa tace nidai dan Allah ka mayar dani Kaga Idan ma gidan kakeso muje mu bari saida safe saina shirya muje 🥲, yi yayi kamar baya jin me take cewa yaci gaba da driving dinsa, cikin rawar murya tace To ka tsaya zan sauka anan saina nemi abun hawa tunda bazaka kaini bah wani mugun kallo ya watsa mata da yasa tayi shiru bata ƙara magana bah har suka isa yayi horn aka buɗe musu gate suka shiga masha Allah gidan ko ina haske ga shiuke shiuke kala kala masu daukar ido bude ƙofa yayi yafita ita kuma tayi zamanta a ciki baya ya buɗe ya kwashe kayanda ya tsaya ya siya duka ya nufi part dinta taga ba’a kunna wutar gaban ƙofar ba yana zuwa ya kunna ya ajiye kayan ya dawo tana ganin ya kusa ƙarasowa gunta tasa kuka kamar wata ƙaramar yarinya baice mata ƙalaba ya ƙara daukar kaya ya fice abunda wannan karon har ƙofar ya buɗe yashiga part din duk tana kallonsa yajima bai fito bah sai gashi ya fito da born short da riga mai hannun singlet waro ido tayi tana cewa da gaske yake bazai mayar dani gurin Umma ba na shiga uku mezan cewa Umma idan naje gobe gida kamar daga sama taji yace ko goben ma bazaki jeba fashe tayi da kuka, shikuma ya dauke ta cakk kamar wata yar baby ya nufi part din da ita suna shiga ya mayar da ƙofa ya rufe 😂wannan lokacin ba’aso naga komi.
*After Ten Years*

Zaune tace cikin ɗaki babu abunda ke tashi cikin ɗakin sai ɗoyi da wari ga worm (tsu tsotsi) nabin jikinta suna fitowa daga Anus(dubura) dinta wasu kuma suna yin sama gurin nono dinta dake fitar da ruwa ga jini daga gani kasa cancer ce ta kama nonon sbd yanda ya cika yayi himm dashi ɗayan kuma duk ya zuƙe wata yar budurwa ta shigo ɗakin tana cewa gaskiya nikam INNA tafiyata zanyi Bungudu wannan ƙaunyen da kika kawo mu babu wasu samari masu zafi idan ma ka basu duri sunci Naira dari ce zasu baka zanje bungudu kozan samu kudi naso nakai ki a dinke miki duwawun nan naki dake fitar da tsu tsotsi idan kuma naga baba Zan gaya masa fashewa INNA tayi da kuka tana cewa Binta bazaki ga baban ku ba sbd ba shine mahaifin ku ba duka dake ƙanwarki Mariya ‘yayan mai gari ne, nima da mutuwa nayi na huta kamar yanda Mariya ta mutu tabar mana duniyar, Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ashe INNA dubura dinta ke fitar da tsu tsotsi sosai naji tsoho hankali ya tashi 😓hattara mata masu bawa majajen banza duburar su suna amfani dasu wlh maganar Allah gaskiya tun anan duniya yake hukunta duk wani dan Luwadi da madigo ba sai anje lahira ba😭muje tsoron Allah muji tsoron Azabar Allah mutuba mu koma ga Allah domin shi gafurun rahim ne, haka Binta tasakai tafiya tabar ɗakinda INNA ke ciki INNA taci kuka tana tsinewa boka da yayi amfani da ita ta baya tana danasanin abubuwan da ta Aeka tawa Malam Kamalu da yarsa Hafsat, sosai taji inama zata iya mayar da kanta Bunguɗu amma ina ciwo yaci ƙarfin ta bazata iya tafiya ko ina bah daga kwance sai kwance gashi ta rasa ‘yarta Mariya mai tausayi haƙuri yarinya mai hankali wacce take tunanin jinin malam Kamalu ce sbd ita Sam batada halin banza natsattsiya ce,, amma boka yace ta bada jinin ta Malam Kamalu zaizo neman ta duk garin da take haka ta dauki Mariya ta kaiwa boka yayi yanda yakeso da ita suna dawowa gida Tace ga garin ku shikenan ta mutu har tahira wani sabon kuka ta ƙara fashewa dashi tana roƙon yafiyar ubangiji 🥺INNA ba’ayi tsofan ƙwarai ba Allah ubangiji yasa mufi ƙarfin zuciyoyin mu kar zuciyoyin mu sufi karfin mu
Yarana ke guje guje su biyu mata wasu kuma na ball suma su biyu duka maza, sai guda biyu mace da namiji da bazasu wuce 2yrs ba suna wasa da Tap duk sun jiƙa jikinsu, Mannal ce taji ihun duk ya dameta gashi tana karatun Exams ta fito ESHAL hal, EHSAN lafiyar ku kuwa meye haka cikin haƙi Ehsan dake gudun tserewa Eshal tace Aunty Mannal Eshal ce wai saina bata kuma ba naba bane miye zaki bata? Ribbon ta fito dashi daga bayan hannunta tana miƙawa Mannal din, toh shikenan yanzu bazan bawa kowa bah cikin ku, dagowar da zatayi tace AMJAD, AAMIN kuna gani AEWARH DA ASHRAF suna wasa da ruwa bazaku ce su dena ba sai ball kuke, tafiya ta farayin a hankali ta nufi gurin yaran dake wasar ruwa aekuwa EHSAN ta bu muryarta duka tace ARWARH, ASHRAF ku gudu ga aunty Mannal nan aekuwa yara suka kwasa a guje sukayi cikin gida suna gudu ruwa na zuba a jikinsu, jiuyo tayi tana cewa aekuwa Ehsan saina zane ki itama da gudu ta bi bayan Arwarh da Ashraf Eshal ta bita a baya, girgiza kai Mannal tayi itama ta bisu a baya gurin ya rage daga Amjad sai Aamin, babban falo mai dauke da satin kujeru har uku masha Allah tsofaffine guda biyu zaune duka mata kowacce tasha Glasses wanda kallo ɗaya zaka yi musu ka gane cewa medical Glass ne Sai wayu mata guda biyu masu kama ɗaya Hakama kayan jikinsu kala ɗaya ne suna sanye da materials mai shegen kyau tun daga nesa yake shaning sai kamshin suke zubawa ɗaya daga cikinsu ce ta fara magana Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Arwarh bata ƙarasa rufe baki ba taga Ashraf yana buɗewa a bayan Arwarh, kamar daga sama sukaji muryar *AMMA*(Hafsat) tana cewa yau zakuci ubanku wace kuje gurin Tap, kuzo nan ta faɗa tana daga murya, baya sukayi alamun zasu gudu Tace Mannal karki bari su fita jiuyawa sukayi suka kwasa a guje zasu fita sukaji sallamar Daddy(DR JAMEEL) da Uncle(ABBAS) aekuwa sukayi kansau uncle ya dauki Arwarh dady ya dauki Amjad suna cilla su sama aekuwa suka washe baki suna dariya, ƙarasa shigowa sukayi suna kama kunnansu suna “Amma” we are sorry we would not do it again, suna su Abbas suka haɗa baki suka maimaita abunda yaran suka ce gaba ɗaya falon aka kwashe da dariya a hankali suka ce Momma ina wuni, Umma ina wuni ashe momma da Umma ne zaune 🤣🥺gaskiya sunyi saurin tsufa zaunawa sukayi gaba ɗayasu Sai lokacin MAHELET da HAFSAT suka gaishe dasu tare dayi musu sannu da zuwa Fuskokinsu dauke da murmushi mai dauke da ma’anoni daban daban😍✨

TAMMAT BIL HAMDALLAH

Anan na kawo karshen wannan littafi mai suna *DARE ƊAYA* Allah ubangiji ya bamu ikon daukar abunda ke daidai a cikinsa 🤌🏻👌🏻Allah ubangiji ya yafemin abunda na faɗa ba daidai ba da kuma wanda na faɗa akan kuskure

Complete document zan sakesa yau Friday 4th August 2023 akan Naira 500
Duk mai so ta yiwa wannan number 08143344386 magana ta WhatsApp

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply