Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 12


Farhatal Qalb 12
Viral

_PG:12_

××××××

Marka ta yatsina fuska tana tabe baki hade da karkace kai ta juyar da shi baya.

Maaikaciyar lapiar ta girgiza kai kawai, Kafin ta cigaba da cewa,

“Cutar sikla mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al’umma baki daya. Dubi yadda jikokin ki ke fama.. Wannan cuta musanman, Aka ware ranar 19 ga watan yunin kowacce shekara a matsayin ranar yaki da cutar amosanin jini wato sikila a duniya. Rana ce da majalisar dinkin duniya ta ware domin fadakar da al’umma kan wannan cutar a matakin kasa da kuma na kasa da kasa. Yau kenan….

“Najeriya ta fi yawan masu cutar a duniya. Bincike ya nuna cewa duk shekara ana haifar jarirai 300,000 a duniya kuma rabi daga wannan yawan a Najeriya ake haifar su. Daga cikin 150,000 na Najeriya din nan 100,000 ne ke mutuwa duk shekara Iya..Alkaluma sun nuna cewa ma fi yawan masu cutar suna arewacin kasar ne.

“Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewar rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka rawa sosai wajen haifar yara masu dauke da cutar sikila a kasar nan. Masu fama da cutar sikila suna fara shan wasu magunguna tun daga lokacin da aka gano suna dauke da cutar har zuwa karshen rayuwarsu…”

“Ke dakta kina nufin ki ce me sunan Malam ne me dauke da cutar? Ke ki kiyaye ni.”

“Haba Iya .. Ni ba haka nake nufi ba. Ai daga Dan na ki har ya zuwa matar tasa basa dauke da cutar.”

“To ai gashi nan yanzu kin fada da bakin ki… Nide nasan wannan ciwo ba daga tsatso na ba ne.”

Maaikaciyar lapiar ta dafe goshinta da tafun hannun ta. Dan ba kadan ba Marka ta hada mata zafi. Sam ta kasa gane komai. Gata da tsatstsauran taurin kai.

“Ina mahaifiyar yaran?”

“Tana daka mana.”

Nan da nan Umma Hadiza da ke tana sauraron komai ta fita zuwa tsakar gidan ta tsakure daga gefe ta tsugunna.

“Ungo wadannan magungunan… Majalisar dinkin duniya ce suka tattalafawa gidauniyoyi na kasashe da dama kan masu fama da lalurar sikila.”

Umma Hadiza ta saka hannu biyu ta karba tana mata godia. Wata leda ce fara mai dauke da rubutun : Health is wealth. Long live warriors. #Spread the awareness. Magunguna ne kala kala aciki masu matukar tsada da kyawu.

“Allah ya saka muku da alkhairi ya biya bukatu Amin. ”

“Aamin…. Yauwa, Daga cikin magungunan akwai maganin karin jini, wanda ya ke kara musu jini, saboda kwayoyin halittar jininsu na yawan mutuwa da wuri. Akwai kuma maganin da ke kare su daga kamuwa da cutar maleriya don tana wahalar dasu sosai idan suka kamu. Sai maganin mai kare su daga cututtuka masu alaka da numfashi. Sai wanda ya ke taimaka wa kwayoyin halittar jinin siffarsu ta zama mai kyau, ya ke kuma taimaka musu wajen rage tashin ciwon. Amma yawanci ana shan shi ne ga wanda ciwon ke masa tsanani. Kamar dai yaran nan na ki. Sannan muna kara ja muku hankali akan ruwa, Yawan shan ruwa abu ne mai matukar muhimmanci ga masu cutar sikila saboda rashin ruwa yana tayar musu da ciwon kwankwaso da na gabobi, Sannan shan ruwan na sa jini ya dinga gudu yadda ya kamata kuma kwayoyin halittar jini su dinga wucewa cikin jijiyoyi, wanda haka ke hana ciwon yawan tashi.

“Tsananin zafin ciwon kwankwaso da masu cutar kan yi fama da shi lokaci zuwa lokaci yana matukar ta’azzara musu. Ƙwararru a harkar lafiya sun ce zafinsa ya fi na nakuda…. ”

“Haka yake likita.. Ai aikin ku ne. Kunsan kan sa. Zance na gaskia suna fama wallahi. Allah yasa kaffarane ”

“Aamin. Eh , Ai kinga su da ke cikin yanayin sunfi kowa sanin yadda suke ji. Suna jin ciwon kashi kamar ana kwankwatsa shi, jini ba ya isa wasu wuraren don haka idan suka taru a waje daya sai su saka ciwo. Wannan ciwo bai bar masu shi ta bagaren shafar lafiyar jima’insu ba. Ciwo ne da ke hana su rawar gaban hantsi sosai a wasu lokutan ta wannan fanni. Kinga, Ga maza dai yawanci, kwayoyin jini masu kamar lauje ne ke makalewa a gabansu sai jinin ya ki fita ya taru a wajen, sai al’aurarsu ta mike ta ki sauka.A wasu lokutan har sai an yi ‘yar karamar tiyata, wasu lokutan kuma da an sanya kankara sai ta taimaka wajen kwantar da gaban.

“Abunda yasa na ke sanar miki, Saboda jan kunnen da akace muyi don kara wayar da kai, sananin zafin da ciwon ke zuwa da shi kan sa masu yin sa su dinga gurzar kuka tare da gunji da gurnani. Ai kin sani, irin wannan yanayi ba babba ba yaro za a ga sun fita hayyancinsu. Domin da nake tsaye a waje ma ina jiyo kukan sa, Daga cikin wasu abubuwan mamaki dangane da wannan ciwo shi ne yadda a wasu lokutan sai kashin wata gaba ta jikin masu ciwon ya karye bal. Ba komai ke jawo hakan ba sai tsabar zafin ciwon da ke taso musu…..Kina sauraro ko?”

“Eh ,..Ina sauraro likita ”

“Yauwa naga akwai yammata agidan ko?”

“Eh akwai biyu…”

“Masha Allah…. Nasan da yardar Allah aure na nan tafe. Abunda nake son sa ni shine, Gwajin cutar HIV/AID, STD da Hepatitis B da C, A kan so kafin a yi aure ayi gwaji na wadannan
cututtuka da suke yaduwa ta hanyar jima’i. Wadannan cututtuka ne da za a iya daukar su ko namijin ya dauka ko matar ta dauka daga namijin idan dai akwai mai shi a cikinsu , Don haka idan daya a cikinsu yana da shi sai a
ba su magani su warke kafin auren, wadanda kuma ba a warkarwa sai a ba da shawara ka da su yi aure don gudun cutar da daya daga ciki. Ina fatan kuna fahimta…?”

“Ke dakta ni tsegumi ne banaso. Zance dai Najan Isubu ce da Hadiza zasu gayan ki akan Na’Ateeku. Bawan Allahn nan hidima da yake min. Rannan wallahi taliya ta kakkaryawa da tumatirin gwangwani ya aikon. Yarinyar nan wahidin batada mashinshi . Sa…..”

“Wallahi Iya bansan komai ba, Bangane kan maganar da kike ba ma. Kawaii dai yanzu zamanin yazo da wasu lalurori da dama wanda kafin auren ya kamata ace an gudanar da su. Kamar su: Gwajin rukunin jini: Gwajin rukunin jini ga masu shirin aure yana da fa’ida, saboda a wani lokaci idan aka samu bambanci na nau’in jini tsakanin uwar da kuma
jariri ko jaririya, ana iya samun matsala wani lokaci yara su zo da ciwo. Da su,

“Gwajin cutar HIV/AIDS: Shi ma wannan gwaji ne mai matukar
muhimmanci da ya kamata a yi kafin aure, don hana yada cutar mai karya garkuwar jiki ga wanda ba shi da ita.
dan har aka samu cikin masu shirin yin auren daya na dauke da ita, to ya kamata su ga likita don samun shawarwarin likitoci kan mataki na
gaba da ya kamata su bi don gudun yaduwar cutar. Musanman sikila data zama ruwan dare,

“Kusan kaso biyu ko uku na mutanen Nijeriya suna da ciwon sikila, yana yaduwa ne ta hanyar auratayya tsakanin mace da namiji da suke da
nau’in na ciwon da a ke kira career. To su kuma career din nan suna nan a cikin jama’ad. Kowane mutum daya cikin hudu a najeriya yana dauke da nau’in ciwon, wato kaso 25 kenan a yan Najeriya career ne. Don haka kafin a yi aure idan aka gwada aka tabbatar cewa shi namijin career ne matar career ce, wannan sai a ce bai kamata su yi aure ba, kun ga an rage wa al’umma da gwamnati da
kowa dawainiyar rashin lafiyar yara masu sikila. Zan sake nanata: Gwajin rukunin jini; Gwajin rukunin jini ga masu shirin aure yana da
fa’ida, saboda a wani lokaci idan aka samu bambanci na nau’in jini tsakanin uwar da kuma jariri ko jaririya, ana iya samun matsala wani
lokaci yara su zo da ciwon nan da ake kira jondis, wato matsananciyar cutar shawara, wanda idan an haihu za a ga idon yaron ya yi kamar rawaya, sannan kuma jikinsa ma ya sauya launi ya zama rawaya saboda jikinsa yana farfashewa. Wannan yana faruwa ne a dalilin bambanci a
tsakanin rukunin jinin mahaifiya da kuma na yaron. Wani lokaci akwai wani rukuni na jini da ake kira RH, idan uwar tana da RH da ya zama
korau (negative) shi kuma yaron na shi ya fito tabbacecce (positive).
Wani lokaci kuma ana samun matsalar haihuwar jarirai da jondis idan ya kasance uwar tana da rukunnin jini O kuma jaririn ya zamanto yana da rukunin jini A ko B ko AB. …

“To dika dika daga karshe dai tamkar yadda muka fada a baya. Nan gidan bakuda history na sickle cells sai dai mahaifi da mahaifiya wato Hadiza ta kasance AS, hakama shi mai gidan nan shima AS ne ta haka suka samu yara biyu SS sai guda daya AS. Na farko SS ta biyu AS career na uku SS . Sai bangaren abokiyar zamanta ita AA ce agwajin da mukayi. Don haka yaranta akwai AA da kuma AS amma babu SS aciki … Wannan shine kawowar karshen bayani na. Ubangiji Allah ya ba wa marasa lapia lapia. Masu lapiar kuma Allah ya kara mana mai albarka , Aamin…”

“Uhm. Kyaji da shi ” Marka ta miqe tana Kade zaninta tayi dakinta da sauri …

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*

*ZAFAFA BIYAR BACTH A*

1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*

2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*

3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4… _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5… _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*

1… _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2… _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3… _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4… _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5… _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1… _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2… _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3… _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4… _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5… _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1… _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2… _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3… _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4… _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5… _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1… _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2… _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3… _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4… _DAB’IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5… _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*

_Duk biyar 1500_

*______________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1… _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2… _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3… _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4… _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5… _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1… _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*

2… _GURBIN IDO_
*(Huguma)*

3… _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*

4… _INAYAH_
*(Mamu gee)*

5… _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*

 

_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*

 

*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply