Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 16


Gurbin Ido 16
Viral

16

Da sallama tabawa ta tura dakin,ta ajjiye ledar kayan hannunta fuskarta dauke da murmushi tana duban maimunatu

“Ki shiga kiyi wanka,ki canza kayan jikinki maimunatu ko?” Kai ta gyada mata,saidai ta maida dubanta ga jikinta,bata ga wani datti da zai sakata yin wanka ba,don yau din da safe Allah ya ‘yantata,ta samu tayi wanka kafin su baro gida,kuma bataga wani aiki da tayi wanda ya bata mata jikinta ba,hasalima ta jima bata samu cikakken hutu da yanayi me kyau irin na yau ba

“Muje ko na nuna miki bayan gidan” abinda tabawa ta fada kenan bayan ta ajiiye wasu maya mayai saman madubi,sai kawai ta miqe tabi bayanta.

Komai na cikin bandakin ta nuna mata tare da yi mata bayani,maimunatu na biye tabawan har ta gama nuna mata komai sannan tace

“Idan kin gama kin fito ki dannan nan ina daga falo,zan shigo na gyara miki kanki” kai kawai ta gyadamata,har ta fice tana tsaye tana bin toilet din da kallo.

Yadda ta nuna mata komai haka tayi amfani dashi,sai gashi ta dauki lokaci me tsaho tana wanke jikinta lungu da saqo,irin wankan da daadanta ta koya mata ta dinga yi a sanda take da gatanta.

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana shaqar qamshin sabulun da tayi wanka dashi,ga wata iska tana ratsata tako ina,bata buda ledar da tabawa ta shigo da ita ba,sai ta zauna qasan tiles din tana qanqame da jikinta waje daya,saboda har wani sanyi sanyi takeji,ta kuma danna inda tace matan,a haka ta share wasu mintuna tana zaune.

Gajiya da zaman jira tabawa tayi,gashi anata kiraye kirayen sallar magariba,don haka ta dawo dakin,ta samu maimunatu zaune

“Ya kike zaune haka?baki kirani ba baki kuma saka kayan naki ba?” Qas tayi da kanta,tabawa ta karanci akwai baqunta sosai da kuma takura kai ga maimunatu,wataqila rayuwarta ta baya ce tayi tasiri sosai a kanta.

Kayan ta fidda mata harda half vest tace ta koma bandakin ta sanya tazo suyi gyaran kan.

Ta jima tana jujjuya kayan a hannunta,tamfar ba zata iya sanyasu ba,sai kuma ta tuna jiranta akeyi,abinda yasa ta budasu ta saka sannan ta daure kanta da dankwalin tayo waje,daf da zata fita ta hangi kanta ta wani dogon madubi da akayi cikin bandakin,harta gota ta dawo tana duba kanta.

Farat daya ta fara canzawa daga maimunatun bafulatanar riga,babu mudukajenta(kayan saqi) babu wuffije,babu komai na fulani tattare da ita sai duwatsun hannunta da na kunnenta,hakanan fatarta haskenta ya qaru koda ba’a gaya mata ba idanuwanta sun gaya mata hakan,sai ta soma takawa a hankali tana saqe saqe masu yawa cikin ranta.

“Babu ma wani datti me yawa akan naki ai” tabawa ta fada sanda maimunatu ta bude mata yalwatacciyar sumar kanta,tabbas babu datti,amma kuma tana da buqatar qyara,ita da kanta idan ta samu sarari take guzurin toka duk sanda taji kan nata ya dameta,ta tsaya daga bakin rafinsu sanda shanunta ke shan ruwa ta badeshi da toka ta wankeshi,saidai tana shan wahala qwarai,saboda wata irin suma Allah ya bata ga tsaho ga cika,babu mataimaki,a baya daadarta ke gyare mata shi fes,ta xauna duk tsahonsa ta bata lokaci ta zuba mata kitson fulani a bishi da wasu irin duwatsu nasu masu kyan gaske,duk randa zatayi mata irin wannan aikin wuni guda suke kashewa kafin a gama,amma fa duk wanda ya kalla kan sai ya kalla ya sake kalla ya kuma tanka,daadarta kadai ke iya mata wannan aikin,ita kanta duk randa ta wareshi ta wanke saidai ta cukuikuyeshi cikin dankwali ta maidashi yadda yake taci gaba da rayuwa dashi a haka,babu cikakkiyar taza bare ta samu kitson arziqi.

Tabawa batayi tsammanin aikin zai daukesu lokaci mai tsaho ba,sai gashi kafin ta gama wanke mata shi ta busar a hand Drayer sun dauki kusan awa biyu,har anni ta aiko laila.

Tsaye laila tayi tana fiddo idanu sanda ta shigo dakin

“La la laaaaa……maimunatu,dama haka kike da suma?,ma sha Allah,kice mu fulani kawai muka rako duniya,ga inda ainihin fulanin suke” murmushi kawai maimunatun tayi,kasancewarta bame yawan son magana ba,zama laila tayi tace tare zasu tafi,tana ta qarewa maimunatun kallo,cikin zuciyarta tana tadinta,yadda cikin awanni kadan kamanninta da kyawunta sun fara fita tun ba’aje ko ina ba.

Duka su ukun da sallama suka shiga falon anni,a lokacin ta nutsu tana amsa wayar jabir,sun fahimci waya take mai muhimmanci harda maimunatu dake baquwar gidan,sai suka samu waje kowa ya zauna,laila ce ta qarasa gaban tv ta dauka remote kafin takai ga zama ta canza channel sannan ta dawo itama ta sama waje ta zauna kamar su.

“Shikenan……amma ka zama cikin shirin kai jabiru,ba lallai sai ka sanar masa ba,ka rabu dashi kawai kaci gaba da sabgarka…..toh….Allah ya bamu alkhairi” shine maganar qarshe da annin tayi tana sauke wayar daga kunnenta tare da bin wayar da kallo,kana ta dauke idanunta tana maidowa kansu.

“Sannu tabawa,kun gama kenan?” Ta fadi tana murmushin jin dadin yadda taga maimunatun fuskarta ta sake fitowa fayau,sannan kuma tayi tarwai

“Eh hajiya anni,aikinma bamai yawa bane”

“Kedai sannunki da qoqari” anni ta fada tana sake kallon maimunatu

“Me zakici maimunatu?” Kanta a qasa ta girgiza kai,don har yanzu cikinta a cushe yake,tana jin daga nan har gobe da hantsi zata iya zama babu komai a cikin nata

“Bana jin yunwa anni”

“Badai a gidan nan ba,ke lailaa,shiga madafi,ki cewa lami ta zubo tuwon nan da aishatu ta kawo,cin mutum biyu ta kawo mana” ambatar sunan da anni tayi sai taji ya tsarga mata har cikin ranta,a duk sanda aka kirayi me irin sunan,babu abinda yake tuna mata face mahaifiyarta.

Sanda laila ta kawo tuwon zama tayi zataci,amma anni tace batasan wannan zance ba,ta koma can wajen uwarta taci

“Wallahi anni ke kadai ta yiwa tuwon nan duk gidan nan,ko abbi babu shi a ciki”

“A nan kuka fi kauri,wajen bada gudunmawar ci,da wani cikinku nace yayimin babu me katabus” ita dai laila bata damu ba,ta saka hannu a kwanon maimunatu ta fara cin abincinta tana sakowa maimunatu hira,abinda yasa anni fa sake qyale lailan kenan,saboda hakan da tayi tasan zai bawa maimunatu damar sakewa.

Ta kuwa dan sake din,tana tsakurar abincin,iyakarta da hirar laila uhmm ko um um,sai kuma murmushi wani lokacin,duka anni tana ankare da ita,tausayin maimunatu take ji sosai cikin ranta,gefe guda kuma tana sake shiga ranta,komai nata mai sanyi ne,cike kuma da nutsuwa a cikinsa.

A hankali a hankali ‘yan mata matan gidan suka fara shigowa da daya da daya kamar yadda suke yawancin darare,suna shigowa anni su kuma dade wajenta,don ma fadanta yakan sanya wani lokaci suqi zama,amma idan suka sameta akan laushinta har kwana sukanyi.

Duk wadda ta shigo sai tabi maimunatu da kallo,wasu suce

“Ma sha Allah,anni baquwa mukayi?,ina kika samu balarabiya?”

“Yar uwarku ce” amsar da take basu kenan taci gaba da harkar gabanta,cikin girmamawa maimunatun take gaida duk wanda ga shigo,har suka dan cika a falon,sunata hirarrakinsu tana jinsu,koda sun sakota saidai tayi musu murmushi kawai,abinda ta lura dashi,su din mutane ne masu mutunci da girmama dan adam,hakanan suna da sauqin kai,duk da adan taqin zaman nasu ta fuskanci wani yafi wani sauqin kai a cikinsu,dama haka halittarmu take,kowa da dabi’a da kuma yanayin da Allah yayi masa.

Ranan kusan a nan duka suka sukaci abincin dare,maimunatu nata kallon banbancin rayuwa da kuma gaskiyar karin maganar nan ta bahaushe da yake cewa ‘Allah daya gari bam bam’ kowa yakanje ya diba zabinsa ne da abinda yakeson ci,ya kuma buda ma’ajiyar abunsha ya dauka kalar lemo da ruwan da yakeso,wasunsu kuma su sanya ma’aikatan gidan su kawo musu,babu kyara babu tsangwama,akwai alamun hadin kai da zaman lafiya bakin gwargwado tsakaninsu.

Tabawa anni data jima da tashi a falon ta aiko kan maimunatu ta tafi ta kwanta,kusan dama ta gaji da zaman,don bata saba hira da mutane ba,duk sai zaman ya gundureta,amma ta rasa ta yadda zata tashi ta wuce dakin,don haka tabawa na idar da saqon ta miqe

“Balenjam” ta fada da tattausar muryarta,sai kuma ta danyi sak ganin yadda suka zubo mata idanu

“Sai da safenku” ta fada da harshen hausa,laila ce ta saki murmushi

“Allah ya tashemu lafiya fillo” murmushin tayi itama sannan ta juya zuwa ciki,tana mamakin yadda suna fulani amma basu damu da yin yaren a tsakaninsu ba,don tunda tazo da hausa taji suna hira har yanzun data tashi,wala’alla shi yasa suka bita da kallo sanda ta yaara musu.

“Gaskiya yarinyar nan kyakkyawa ce,tana da hankali da alama” salma data miqe dauke da.plate din data gama shan farfesun kayan ciki ta fada,dubanta laila tayi

“Sosai,tana da nutsuwa sosai,tana burgeni”

“Ni kaina haka” fa’iza ta amsa musu,daga haka laila bata ce musu komai ba,don tasan cewa ba wanda yasan komai kan zuwan maimunatu gidan,bai kuma kamata ita din ta fara cewa komai ba.

Sanda ta shiga dakin idanunta sun fara mata nauyi saboda bacci,qullin kayanta data hana tabawa dauka daxu ta janyo ta tasa kanta dasu,bayan tayi kwanciyarta qasan tiles ba tare da tayi gigin hawa gadon ba,babu jimawa wani nannauyan bacci mai dadi yayi awon gaba da ita.

*********Kyakkyawar macace wadda shekarunta na haihuwa suka kusa arba’in da bakwai,kana mata kallon farko zakasan cewa sanda take da qananun shekaru ba qaramin kasa maza dr marwan yayi a kanta ba,tana da siffa me kyau ko a yanzun ma,fara ce sosai kamar yadda akasan asalin farin bafullace,hakanan bata da tsaho can can,kamar yadda ba zaka kirata gajeriya ba,saidai alamun tsafta da qamshi da suka samu wajen zama a tattare da ita sun nuna kansu muraran.

Cikin nutsuwa kamewa da kuma sanin kimar kai take shigowa bangaren surukar tata,sanye cikin atamfa england me ruwan ganye,dinkin riga da plain zani,bayanta masu aikin gidan ne wadanda ke qarqashin bangarenta masu kula da bangaren kitchen dauke da trays,sai kuma salma dake riqe da wani warmer me kyau guda daya a hannunta,a shirye take tsaf da alama wani wajen zata wuce,tana daga gefan mahaifiyarta(Aishatu amma) suna magana ita da salma din.

Dakatawa masu aikin sukayi har zuwa sanda amma da salma sukayi sallama cikin qawataccen falon annin,wanda sam baiyi kama da falon tsohuwa ba,dai dai lokacin da DR marwan ke zaune gaban mahaifiyar tasa yana gaisheta,shima sanye da wata dakakkiyar shadda fara qal,kamar kusan ko yaushe kansa nannade da tattausan farin rawani na zallar auduga,da alama shima din fita zaiyi.

Jinin sarauta ce ita amma sam ba zaka dauka haka ba,saboda sauqin kai da take dashi da kuma sanyin hali,Gefan anni amma ta qarasa tana zama a qasa kamar yadda ta samu me gidanta,wannan din wata dabi’a ce tasu ita da dr marwan tun suna da jajayen sahunsu,dabi’ar data maida aishatu tauraruwa a zuciyar anni cikin kafatanin surukanta,ya sanya kuma wasu daga cikinsu suke kishin hakan,duk kuwa da cewa anni tana matuqar qoqarin boye hakan,saidai ko daga yadda ja’afar keda matsayi a wajen annin kadai ya isa ya fallasa maka wace aishatu a zuciyarta.

Sai data fara gaida anni sannan ta waiwaya ga me gidanta shima ta gaidashi,duk da cewa sun gaisa a ciki kafin ya fito,ya amsa mata cikin kulawa kamar ko yaushe,salma ta matsa kadan ta gaida dr sannan ta maida dubanta ga anni,murya qasa qasa tace

“Ranki ya dade hajjaju anni” wani kallo ta jefi salman dashi,tasan duk me salman take wa

“Allah ya baki haquri anni ina kwana”

“Lafiya sumul natashi ‘yar nema,duk take takeki kar nake kallonki,gwara kiyi ta kanki ‘yar nan” wuri wuri salma tayi,da alama tonin silili anni keson yi mata a gaban wadanda take gudun yin maganar a gabansu,bata gama tunanin ba kuwa maganar annin tayi mata saukar aradu

“Wai marwanu…..ita wannan kazar mayun har yanzu bata isa ayi maganar aurenta bane?” Ji salma tayi kamar qasa ta tsage ta shige,maganar da tayin tana nuna kuma yasa dr maida idanunsa kan salma

“Me ya faru anni?” Gyara zamanta tayi

“Yo ni na gaji da hada kafada dasu idan ku baku gaji ba,ina buqatar ganin wasu ‘yan dagwai dagwai din,ko ka aurar dasu ko ka auro,zuri’a nake da buqatar gani me tarin yawa……yawwa……duk gidan nan billhillazi babu yaron da bai isa aure ba,ramatu ce kawai za’a iya dagawa qafa,amma ace babu me aure?,baga mazan ba baga matan ba?,to idan baqinjini garesu zan buga gangar bada sadakarsu mazansu da matansu” kafin ta diga aya salma ta kwashi takalmanta a hannu tayi waje,don taga alama yau annin me manya manya take barota.

“Ayi haquri anni” abinda dr yake fada kenan,don yasan da biyu take wannan fadan,tana tunanin kamar shike qin bada auren yaran nasa,bayan kuma yaran da kansu suke sha’awar karatu shi yasa ya qyale kowacce da zabinsa,uwa uba ma duka duka salma hafsat da laila ne a makarantun gaba da secondary,samma hafsa nadiya fa’iza da khadija sune ‘yan candyn bana,zahra’u na ss one,sai rahama dake j.s,mazan kuwa dukkansu ba wanda ya gama jami’a banda ja’afar da haisam,sai Mahmoud dake ajin qarshe

“Yanzu fisabillahi….salma zaman me take?,shi karatun da take cewa akayi bashi yuwuwa ta qarasashi cikin dakinta?”

“Ta fiddo wanda takeso anni,ai baza’a qi aurar da ita ba”

“To ta fitar kuma shi take ta raragefan gaya maka kai da uwar tata” qas amma tayi da kanta,wal’alla ta gayawa anni sunyi zancan da ita kenan

“To ba damuwa anni,zanyi magana da umar(qaninsa kenan me bi masa),saita turashi can yaje ya gaidasu”

“To ba laifi” annin ta fada tana sassautan fadan,dai dai sanda salma tayi dake labe daga waje tayi tsallen dadi,anni tasu,anni ta wajensu,ayi tsiya ayi dadi,ga tsiya ga aiki,lallai yau dole ta yiwa annin wani tagomashi,saita juya cikin jin dadi zuwa ma’ajiyar motocin gidan,inda driver yake jiranta,ranta fari qal.

Daga can falo kuwa duban dr anni ta sakeyi

“Shi kuma jabiru da ja’afar fa?,da aka barsu suke zaune a wata uwa duniya,ga wancan qaton tuzurun haisam?” Miqewa amma tayi saboda kara da yakana irin tata,tana ganin ya kamata ta basu waje suyi maganrsu sosai

“Ina kuma zuwa?” Anni ta fada tana binta da kallo

“Zan duba meye baku dashi a kitchen”

“Idan kin shiga,kiyi waya can gidansu marigayiya,ya kamata a dawo da amna,jimawar da tayi a can wannan karon tayi yawa”

“To anni” ta amsa mata cikin girmamawa tayi ciki,dawo da dubanta tayi ga dr marwan tana tattara hankalinta sosai a kansa sanda ya fara mata bayani

“Maganar da nakeso muyi kenan…..a jiya da kika sameni da baqi kamar yadda na gaya miki ministern ilimi ne na qasa ya kawomin ziyara,bayan mun gama tattaunawa kan batutuwa irin namu,sai kuma ya jefomin maganar diyarsa unaisa,ya yimin tayin aurenta da ja’afar kamar sanda ya taba yimin a baya ban karba ba,lokacin ja’afar din yana aviation school,magana kuma tayi nisa tsakaninsa da marigayiya,to a yanzun inajin nauyi na sake qin karba din,kada yaga kamar banason hada zuri’a ne dashi ko kuma wani abu makamancin haka,na amsa masa ne duba da cewa gaba dayanmu dama muna laluben masa abokiyar zaman da zata iya zama dashi bisa juriya da kuma haquri kan sauyin hali da dabi’arsa,na kuma tabbatar kema idan kikaji hakan zaki farinciki,tunda burinmu kenan gaba daya”

Shuru anni tayi tana duban dr marwan,bawai don yayi kuskure ko kuma maganganunsa ba’a kan hanya suke ba,a’a……saidai tana tunanin wace unaisa?,akwai yiwuwar samun dacewar zama tsakaninta da ja’afar din?,uwa uba kuma ga batun maimunatu da take tafe dashi,sai takega kamar akwai matsala.

_To masu karatu,muje zuwa,shin al’amarin zai yiwu?,duk da bamusan wacece unaisa ba,abbi baisan wace maimunatu ba,kamar yadda wanda aketa abun a kansa baisan wainar da ake toyawa bama_
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply