Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 29


Gurbin Ido 29
Viral

29

Tafiyar mintuna ita ta sadasu da unguwar cikin gidan minister,sun samu tarba me kyau bayan haj Aaya ta samu sanarwar zuwansu,waje na musamman cikin gidan tasa aka kaisu,sannan tasa aka taso mata unaisa dake barci a sannan,ta fara shiryata da kanta bayan ta sanyata ta sake wanka,cikin wani material na alfarma mai dan banzan kyau da tsada.

Karo na biyu ja’afar ya sake duban agogon hannunsa,yayin da yake biye da maganar da jabir din ke masa kan dakunan da aka kamawa baqinsu sunyi kadan,za’a qara wasu da kuma yadda suka tsara event din da za’a gudanar

“Komai yayi,amma banda ni a taronku,saboda babu abinda zanje a ciki,walima ce kawai ta zama sunnah,ita dince ma nake tunanin zanje,anma fa babu tabbas itama,kada ka zura jiki da yawa” yayi dukka wannan maganar yana kallon lafiyayyen agogon dake kwance a fatar hannunsa

“Time up” yafada yana miqewa tsaye cak,sai jabiru ya bishi da kallo

“What do you mean?” Sai daya zuba hannayensa duka cikin aljihun rigarsa yana duban jabir

“Mintuna takwas nayi niyyar ware mata a yau din,kuma ta cinyesu wajen jira, you know…..i don’t wait for anyone,amma dai na cika maganar abbi tunda nazo” dubansa jabir yake cike da mamakinsa,ja’afar…..ja’afar?.

“Amma dai abbi ba cewa yayi ka shigo gidan ka fita ba ko?,cewa yayi kuga juna,ka ganta ne J?”

“Na meye sai na ganta?,no need” ya amsa masa yana dage kafadarsa,sai ya juya da zummar takawa yabar wajen,dai dai sanda ta iso,cikin matuqar ado,mutum uku cikin masu aikin gidan na biye da ita da.manyan trays da aka jerawa kayan ciye ciye da shaye shaye.

Idanunta a kansa,kamar yadda fuskarta ke baibaye da murmushi

“Hello” ta fada tana waving hannayenta,murmushin fuskarta na sake fadada

“Welcome our bride” amsar jabir kena data qara ninka farincikin dake zuciyarta

“Thank you ” ta amsa masa kafin ta sake maida dubanta ga ja’afar wanda har yanxun yake tsaye

“am sorry,i keep you waiting ko?” Ta fada tana murmushi,sai ya motsa kafadarsa

“Don’t mind,ina cika umarni ne” gatsal jabir yaji maganar tayi masa,bai murmure daga wannan ba yaji unaisan na cewa

“Have a set please?,kaman maganan zaune tafi ta tsaye”

“It’s too late……lokacin zamana ya cika,i have a lot to do,see you later” ya fada yana qetareta zai wuce abinsa.

Wani abu ne ya tsayawa unaisa a wuya,duka wannan lokacin data bata amma ko na minti uku cikakke bai kasance da ita ba zaice tafiya zaiyi?,uwa uba ma sau daya tak taga ya kalleta ya dauke kai?,tana da tarin.abubuwa masu yawa da takeson su tattauna dashi,don haka batayi qasa a gwiwa ba tabi bayansa tana tsaidashi

Cak ya tsayan,sai taji abun ya mata nauyi kasancewarta maje mai bala’in jin kai,sai itama fa tsaya tana duban ingarman bayansa take tsaye sosai tsakanin mayalwatan kafadu dake cike da siffar qarfi da cikakkiyar tsaiwa ta cikakken namiji,a hankali taga ya waiwayo,ya kuma tako zuwa gabanta ya tsaya,tsaiwar da taji ta har tsakiyar kanta,saboda tazarar dake tsakaninsu bata da yawa,uwa kuma wani shegen kwarjini yayi mata,wanda ya mamayeta kota ina,qamshin lallausan turarensa ya ziyarci hancinta,sa’annan kuma hucin fitar numfashinsa data rasa me yasa yake fita da nauyi haka?,bata gane amsar tambayar tata ba sai daya fara magana,ta fuskanci cikin fushi yake,ransa ne ya baci,abinda ya bata tsoro kenan,duk da cewa fuskarsa a murtuke take cike da rashin fara’ar da dama can kowa da ita ya sanshi,to amma wannan bacin ran dake kwance saman fuskarsa bai jima da samoshi ba

“Ki kula,ki kuma yi a hankali,banason matsi ko takura,zaifi kyau ki kasance me nisantata akan yunqurin kusantata da kikeyi,stay away from me…..na gaya miki wata gaskiya guda daya wadda babu lallai a samu wanda ya gaya miki ita?” Yayi maganar yana dage girarsa dukka biyun,bata amsa masa ba saboda wani yanayi daya shigeta,shima bai damu ta amsa din ba ya dora mata

“Bana buqatar rayuwar kowacce mace da sunan matata a cikin tawa rayuwar,already na rufe wannan babin,idan kin shirya ma kuma kutsa kanki ciki…… it’s okay for me” ya qarasa fada yana dage kafadunsa,sai ya juya cikin takun nan nasa mai cike da ginshira yana barin wajen.

Ko sau daya batayi yunqurin tsaidashi ba kamar dazun,sai kallo data bishi dashi qirjinta yana dukan uku uku har ya bacewa ganinta,kafin muryar jabir ta katse mata dukka hanzarinta

“Are you okay?” Ya tambayeta yanason karantar yanayinta,don baisan me ja’afar yace da itaba,kasancewar akwai tazara tsakaninsu,amma yafi kowa sanin halinsa,tabbas something bad happened,akwai abinda ya gaya mata,saboda yadda fuskarta ta sauya gaba daya ta kuma birkice.

Abirkicen ta girgiza kai

“Akwai damuwa tabbas” batayi qasa a gwiwa ba ta gaya masa maganganun da sukayi,sosai jabir yaji babu dadi,amma a zahiri sai ya kawar da hakan daga saman fuskarsa

“Karki damu,nasan J,a yanzun rashin sabo ne ya kawo yake gaya miki haka, with time zaku saba,zakiga kuma kaman bashi ba” sosai yayi qoqarin gaya mata maganganu masu kwantar da hankali,har sai daya fuskanci ta nutsu sannan ya taka mata gaban main entrance na gidan,sannan ya wuce zuwa inda suka ajjiye motarsu.

Hannu yasa ya bude murfin motar idanunsa na sauka kan fuskar ja’afar,wanda ya kwantar da seat din motar ya kuma miqar da bayansa sosai a kai,jin bude motar baisa ya motsa ba,har sai da jabir ya shigo,sannan ya bude kyawawan idanunsa da suka sauya kala a hankali ya watsasu kan fuskar jabir

“Kaci sa’a kaine,da saidai kazo ka samu empty din wajen”

“Yanzun ma me ya hanaka tafiya?,tunda kazo kayi abinda ranka yakeso?” Ya amsa masa yana dan nuna masa bacin ransa,duk da yasan ja’afar din dole abishi a sannu,saboda wata irin zuciya da yake da ita da bata iya qaramin so ko qi ba,hakanan ba qaramin riqo shaheeda ta yiwa rayuwarsa ba adan tsukin lokacin na zaman da sukayi.

Bai sake cewa jabir komai ba,sai dan qaramin tsaki da yaja yana tada seat din ya zauna sosai,tun basuyi nisa ba suna isa wani guri yace jabir din ya saukeshi qofar wani gini,kamar ya tambayeshi me zaiyi sai yaja baki ya qyaleshin,ya saukeshin ya kuma wuce da motar.

***********Dukkan tafukan hannayenta ta buda tans kallon tsakiyarsu,batasan me zata tuna ba,saidai ta samu kwanyarta fayau babu komai tun daga sanda taji ana hargowa sa hayaniyar zuwan al’ummar gombawa,ta dai tsinci kanta da matuqar sanyi da kuma faduwar gaba,wanda tunda aka fara bikin kwana hudu kenan yau cikon na biyat bataji irinsa ba sai yau,tasa ran ganin anni da amnanta cikin matan da suka iso,saidai babu daya cikinsu,kusan dukka baqin fuska ne idan ka cire anty maama wadda ita ta jagoranci tafiyar.

Ko ba’a gaya mata ba tasan cewa ayau qaramar hukumar ta gembu ta karbi baquncin manyan mutane irin wanda bata taba karba ba,jiniya da qarar ababen hawa kala kala ke tashi,hayaniyar da hatta cikin dakin da take zaune bai tsira ba,dakin dake cike da ‘yammatan fulanin da suke danginta ne,duk kuma cikinsu bataga gaje ko gilmawar inna furera ba,tun ranar da za’ayi mata kamu inna fureran ta iso,da tarin sharrikanta wanda ya zame mata tonuwar asiri saboda zuwan yuuma garin,wadda da ita ake gudanar da komai,batasan inda inna fureran tayi ba tun ranar da aka silleta,umarni dai na qarshe da aka bata maimunatu tayi yaqinin shine abu mafi tsauri a wajenta da zai iya sanyata batan dabo

“Ki tattaro duk wata dukiyar dabbobi ta shatu da maimunatu dake hannunki ki kawo mana ita” bammmm!!!!.

“Alhamdlh,aure ya dauru” muryar maroqin mai babban maqogaro ta kwararo cikin gidan,ta kuma isar da saqon nasa inda yakeson ya isa,lungu da saqo na gidan,sai kuwa mata suka dauki guda,gudar data zagwanyar da duk wani qwarin gwiwa na maimunatu,ta nannade kanta da kyau cikin mudukajenta(kayan saqi na zallar lallausar auduga na musamman da matan bappa sama’ila suka tanadar mata harda na yafawa saboda wannan ranar),take taji kamar zazzabi keson kamata saboda sanyi daya fara ratsa qashinta wanda batasan dalilinsa ba,tana jin ‘yammatan na waqe waqensu na fulani suna kuma tsokanarta amma ko motsawa batai ba.

Tana ji daga tsakar gida wata qanwa ga kakarsu ta wajen mahaifi tana fadin tare za’a wuce da ita da ‘yan daurin aure zuwa can gombe,sunce nan da awa daya a shiryata” gabanta yayi mummunar faduwa,tana jin fargaba sosai,tana jin kamar su annin baqinta ne,duk da zuciyarta na gaya mata,bawai dasu anni zata zauna ba,zataje ne tayi rayuwa da wasu mutane na daban da batasansu ba,batasan halaye da dabi’unsu ba,bakuma tasan yadda zata fusakanci zama dasu ba.

Tana jin sanda aka gama tiri tirin hada kayayyakinta tsaf,yuuma na tsaye akai,tamkar ba daga dangin ango ta fito ba,domin tace ita din a yanzun uwace ga maimunatu bawai suruka ba,ita ta riqeta ta rakata zuwa gaban baffaninta da wadanda ke a mazaunin uwayenta a yanzu,sunyi mata dukkan nasihar da akewa kowacce diya mace a al’ada sanda ta tashi tafiya gidan miji,dukkan wannan abubuwan maimunatu ganinsu take kamar a majigin film bawai a gaske ba,kamar raqumi da akala haka take biye dasu sanda suke riqe da ita zuwa jerin gwanon motocin dake jiran fitowarta,su kuma tashi dasu zuwa gombe.

Shi daya ne cikin motar sai driver kamar yadda jabir ya tsara hakan ba tare dashi ya sani ba,zaman da yayi cikin motar ya yishi ne yana jiran fitowar jabir da yace yayi mantuwa a inda suka zauna,duba daya zakayi masa kasan cewa ango ne shidin zammm,yayi wani irin kyau na musamman cikin wata arniyar shadda ruwan sararin samaniya,wadda ta lashe maqudan kudade tun daga wajen siyota har ya zuwa dinkin da aka yi mata,aikin hannu me matuqar kyau tsari da kuma tsada,takalmin sauciki kalar dark blue sosai daketa daukar idanu saboda sabunta kyau da kuma tsafta yana aje gefe,qafafunsa babu komai sai sock,gefensa ya fidda babbar rigar ya ajjye,a samanta ya cire hularsa kalar dark dark blue da ratsin light mai wani irin walqiya da daukar idanu ya ajjiyr hade da babbar rigar,hatta da links din hannun rigar gold color ya cireshi,ya nade hannun rigar zuwa gwiwar hannunsa,gargasarsa dame kwance luf ta bayyana sosai.

Wata magazine data wallafa sunayen fitattu kuma manyan kamfanunuwan gine gine a satin yake dubawa,kamfaninsu shine yazo a jeri na biyu,duba bayanan yake,amma can tsakiyar qirjinsa wani irin nauyi ne dake cunkushe a cikinsa,ranar ta yau gaba daya tazo masa ne kamar cikin mafarkai,tunda ya auri shaheeda kuma mutuwa ta rabasu bai taba tsammanin akwai rana irin wannan da zata zo ba,dukka wannan abun yanata qoqarin yaqi da abinda yakeji cikin zuciyarsa ne,amma a yau din,babu wadda ke ziyartar zuciya da kuma tunaninsa sai shadeedan,yana tuna rana irin ta yau cikin rayuwarsu data kafa masa tarihin da bazai gogu ba har abada.

Haske ne kadan ya bayyana a motar bayan an bude murfin motar,yana shirin daga kansa ga zatonsa jabir ne,sai yaji muryar mata suna fadin

“Shiga da bismillah,Allah yasa kin tafi a sa’a” wani abu ya tsaya masa a wuya sanda take shigowa motar a hankali,tana gama zama kuma aka maida murfin motar aka rufe,sai yaji driver yaja ya soma tafiya.

Shuru ne ha ziyarci motar,babu wani motsi ko kadan a cikinta illa motsin injina dake aikinsu can qasa,cikin jikinta take jin sauyin waje da yanayi tabbas ya fara daga wannan lokacin,duk da bata iya ganin komai clearly amma tasan tabbas ba ita kadai bace cikin motar.

Hannunsa ya zura a aljihun rigarsa ya fiddo wayarsa yanata qoqarin hadiye bacin ransa,shi jabirun zai rainama wayo?,yana nufin shi da ita zasuyi tafiya har ta wadannan awannin a mota guda don ya rainama kansa hankali?, numbers dinsa ya nema ya kuma kirashi,bugu biyu ya daga

“Jabir” ya ambata da wani irin sound dake nuna zallar bacin rai,saidai kuma ba wani da qarfi yayi maganar ba

Lumshe idanun
ta maimunatu dake qudundune cikin yalwataccen mayafin da aka rufa mata har ka
tayi,bugun zuciyarta dake qara bugu take qoqarin saitawa,sautin muryar ya doki kwanyarta,tamkar a cikin kunnuwanta aka furta sautin kalmar jabir din,saita hade jikinta waje daya sosai,tana jin takalminta ya zame daga qafarta,amma babu damar ta motsa bare ta maidashi,hakanan kawai takejin wani irin tsoro yana ratsata,tabbas wannan shine mutumin daya zama mijinta a yau.

“Kada kace komai,don muna tare dasu abbi,ga motarmu nan tasowa,wataqil zamu tsaya a hanya mu kwana saboda nisan tafiyar,please i beg you, don’t misbehave,ka dorar da farincikin dasu abbi suka samu a yau din” magiyar jabir ta yau ta tabashi,don haka baice komai ba,amma hakan bai hanashi jan tsaki ba bayan ya kashe wayar

“Stop the car solomon” ya fada da tattausar husky voice dinsa

“Okay sir” ya amsa masa cikin girmamawa,sannan ya gangara gefan hanya ya tsaya.

Rigarsa da hularsa ya dauka ya bude murfin motar ya fice ya koma zuwa seat din gaba,sannan ya bashi umarnin ci gaba da tafiya bayan ya gyara zaman kujerar yadda zaiji dadin jingina ya zama comfortable sosai.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply