Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 39


Gurbin Ido 39
Viral

39

*************Karfe biyar da rabi ne na yammacin ranar lahadi,cikin dakin kwanan dalibai na makarantar,maimunatu ce zaune saman gadon afrah,ta baje litattafai kai kace duka litattafan data mallaka ne a gadon.

Sanye take da chiffon fabric,material ne da aka yiwa dinkin simple gown brown color da ratsin coffe,sai milk color da akayi adon flower din jiki,dinkin dogon hannu ne,amma daga tsintsiyar hannun an sanya masa roba,abinda ya rage fadin hannun kenan ya zama tattara,abinda ya zama kamar wani ado na musamman,saman kanta wani silk v-shape vail ne data yafashi ta kuma daureshi qasan habarta,fuskarta da labbanta sai glowing suke tamkar ta shafa musu wani abun,saidai kuma ba abinda ta shafa din,nutsuwa da hutu data samu ne koda yaushe yake qara bayyana sirrin kyanta.

Tsaki taja ta ajjiye pen din hannunta tana lanqwasa yatsunta,karatun exams take,saboda rana ita yau zasu zana jarabawar da daga ita sai ss two,ta riga taci alwashin wannan karon sai ta kawo first position da izinin ubangiji,tunda jarabawar farko tazo ta sha biyar,ta second term tazo ta uku,wannan karon ta daya take buqata.

Kanta tadan daga sama kadan,inda afrah tun dazun ta haye gadonta tana waya,abinda yasa sukayi exchanging gado kenan,a boye take wayar,saboda duk lokaci irin wannan ana karbar wayoyinsu ne sai sun kammala jarabawa kuma.

Har ta bude baki zatayi magana afran kamar ta sani sai gata ta motsa tana saukowa,harara maimunatu ta bita da ita,sai ta bushe da dariya tana fadin

“Am sorry moon,afwan,bazan iya skipping amsa wayar nan bane”

“Bansan me yake damunku ba afrah,exam around the corner amma ta waya kike?”

“Ke kuwa kinsan dadin soyayya?” Tambayar ta tuna mata da himunta,sai kuma tayi hanzarin yin ta’awizi

“Ban sani ba” ta amsa mata kai tsaye saidai cikin gatse,tana kuma miqewa tare da zura slippers dinta,dariya afrah ta saki,duk da ta fahimci gatsen ne

“Naga alama ai,tunda duka tarin English novels din dana baki wancan hutun haka kika dawomin dasu,banga alamar kin karanta kowanne a ciki ba”

“Kanki akeji,don na karanta kuma sai nazo na zauna ina baki labarin abinda na tabbatar kema kin sanshi” ta qarashe maganar tana shigewa toilet dinsu,saidai a zuciyarta afran ta motsa mata tasirin da labaran sukayi mata,kuma har yau idan ta tuna sai taji shauqin,saidai kuma bata son abinda zai shiga karatunta,shi yasa bata sake neman wani ba,tana jiyo afran tana mata shaqiyanci

“To ban taba jin sunan kowa a bakinki ba idan ba ya hisham ba,ga waya kina da ita amma kinja kin aje,ke bakya zancan kowa fa a rayuwarki,dole nace bakisan dadinta ba” koda a dakin take ma ba zata tanka mata ba bare tana bandaki,don tana da attitude na qyaliya sometimes,ita afra ta saba da wannan,tace ta saba zama miskilai irinta,haka sister dinta take,da itace zamansu zai bada kala sosai.

Har ta gama fitsarin data shiga yi ta dauro alwala bata sake jin afra tace komai ba,don haka ta bada a ranta ta fita ne a dakin,don indai ta fara dauko yi mata shaqiyanci irin wannan…..duk da itama gwanar miskilanci ce idan taso,amma bata shuru da wuri,wani lokaci har sai su fatima sun shiga maganar take barta ta sarara.

Ga mamakinta sanda ta fito afran na dakin,tana zaune inda maimunatun ta tashi,wani littafi ne a hannunta,amma kuma ba shi take karantawa ba,wata takarda ce riqe a daya hannun hagun nata,ta tattara hankalinta kacokam a kanta,kamar zata koma cikinta,yadda taga afran ta nutsu yaja hankalin maimunatun,sai ta fara takowa a hankali itama tana duban hannun afran.

Tana sake matsowa tana kuma sake fahimtar meye a hannun afran,invitation ne,invitation din kuma bana kowa ba face nata,na daurin aurenta,gabanta ya fadi sosai,tsoro kuma ya tsarga mata,ya akayi IV din ya shigo cikin kayanta?,litattafanta na karatu?,bayan kusan gaba daya a gembu tabarsu tun randa kawu sama’ila ya bata ta danqawa inna saratu bata taho dasu ba.

Cikin matuqar dakiya maimunatu ta miqa hannu zata karba IV din tana cewa

“Ba wannan aka ce ki karanta ba,litattafan makaranta zaki duba” gocewa tayi da katin yadda maimunatu ta gaza kamashi,sannan ta watsa mata harara

“Anqi ayi karatun,sai aukin cewa mutum yayi karatu amma ashe bada zuciya daya kika daukeni ba moon?” Afra ta fada kamar idanunta zasu fado

“Me kuma ya faru?” Tayi tambayar kamar batasan komai ba

“Indai masu irin dabi’arki ne ai zasuyi fiye da hakan,wannan katin daurin auren waye?” Tambayace takai tsaye,wadda babu hanyar da zata kauce mata,suna dai gashinan ya fito baro baro a jiki full name nata,tace sunan waye kenan?.

“Yanzu har a miki aure cikin hutun nan amma koni ki kasa gayamin moon?,ashe yadda na daukeki daban yadda kika daukeni daban,na gode,na gode sosai” ta fadi tana miqewa daga gadon bayan ta ajjiye mata katinta.

Da hanzari ta kamota tana dubanta

“Ni ba cikin hutun aka dauramin aure ba,da aurena na shigo school din nan” amsar tata ta bawa afra mamaki matuqa,ta kuma taimaka wajen sauke fushinta,mamaki ya maye gurbin hakan.

Janta tayi suka zauna tare,sannan ta dubi afran

“Sai da nayi watanni da aure sannan na fara zuwa nan” a nutse ta warware ma afrah komai,babu wani abu data boye mata,don itama tana jinta da gasken gaske har cikin zuciyarta,asali ita bamai yawan magana da dogon surutu bane,kuma tun zamansu tare suka fuskanci ba kasafai hirar samari data aure take burgeta ba yasa basu fiya irin wannan hirar ba muddin tana cikinsu,hakan yasa babu wani abu da ya tado maganar bare su sani.

“Captain ja’afar marwan akko?,shi na gani a rubuce,da gaske shine mijinki?” Afra ta fada wani murmushi na fita saman fuskarta,kai maimunatu ta jinjina mata

“Dama ance yayi aure,mata biyu,ashe harda aminiyata ta gobe a ciki, congratulations…..congratulations once again sister,kin ciri tuta,ke dashi kun tsinci dami a kala” ta qarashe maganar tana duban idanun maimunatu,fuskarta fal da murmushi,maganar ta bawa maimunatun mamaki,ta waro idanu tana duba afrah ba tare da tace komai ba,ita kuwa batayi qasa a gwiwa ba ta dora da

“Duk yadda zan fasalta miki kyanki haduwarki da kuma nutsuwarki ba zaki fahimta ba maimunatu,tunda a kanki ake magana,kina da dukkan wani qualities da nake da tabbacin babu namijin da zaisan kina dasu ya iya dauke kansa a gareki ki wucess,infact…….ba namiji ba,koni macen na gama yiwa brother na kamu,ashe J ya riga dsya qwamshe wannan rabon” takai qarshen maganar murmushinta na sake yawa zuwa dariya dariya,dole kuma ta dora murmushi kan fuskar maimunatun,tasan halin afrah sarai,duk da cews ba wai yaune ranar farko da ta fara ko suka fara kodata ba ita dasu ayman

“Well……abinda yasa nace ke kuma kin tsinci dami a kala?…..hmmmm….. captain ja’afar…….matashin da yake sanya razani da yawa a zukatan ‘yammata,matashin da ya sanya idanuwan ‘yammata da yawa zubda qwalla,matashin da ya sanya zukata da yawa cikin bege da qauna mai tarin yawa,ciki harda cousins dina su biyu,wanda har yau basu debe tsammani a kansa ba” ta qarashe tana sakin dariya,tare da tuna irin dambarwar da suka sha,tana cikin masu yi musu dariya kafin ta fahimci girman jarrabawar da suka fada,kafin ta fahimci waje ja’afar data fara yin hankali ta fara tausaya musu.

Dubanta maimunatu takeyi kwanyarta na tafiya cikin nazari da tunani afran ta dora,saidai wannan karon cikin seriousness take maganar

“Qawa,kada kiyi wasa da damarki…..kada kuma ku tsaya kallon ruwa kwado yayi miki qafa,kina da dukkan komai da zakiyi wining a kansa da zuciyarsa,karki barwa kishiyarki waje ko fili ko kadan,kada kuma ki sake wadan nan alamomin rainin daga wajenta suci gaba da fitowa a kanki,ta yaya zaki sakar mata rayuwarki tayi yadda taga dama?,mijinki rayuwarki ne ko yaya kika gai ga qinsa,wannan zaiyi amfani ne kafin ki amsa sunan matarsa,duniya ta fara kallonki da sunan,amma bayan kin amsa din kuwa,baki da wani zabi daya wuce ki gyara komai,indai bakiyi hakan ba….baki kyautawa anni ba,sannan bata cancanci wannan tukuicin daga gareki ba” maganganun afra sun ma maimunatu nauyi a ka,ta saqa abubuwa masu yawa a zuciyar maimunatu wanda suka dinga yi mata kai kawo aka,saidai tana duba abin,tana duba yadda lamarin zai kasance,ba zasu fahimta bane cewa yadda suke kallon lamarin dashi kansa mutumin ba haka abun yake ba?.

To sai da tayi mugun da gaske sannan ta yakice tunani me qarfi da ya kamata daga ranta,ta koma karatunta ka’in da na’in,itama afrah bata sake ce mata komai ba,saidai a fakaice take mata karatun yadda soyayya take,sau tari a gabanta take wayoyinta yanzu,ta daina kebewa kamar yadda takeyi a baya,wani lokaci saidai ta tashi ta bata waje,idan taga dama ta qyaleta,idan kuma bata so ba ta biyota nan ma ta addabeta.

*************Tsararriyan books shelve,wadda ke dauke da tarin litattafai a jere cikin tsari da tsafta da kuma sanin makamar aiki,tsaye yake a gabanta,daya daga cikin qofofinta a bude,da alama wani littafi yake nema,hannunsa daya dauke da wani littafi daya nutsu qwarai yana dubashi shafi bayan shafi,yayin da daya hannun nasa kuma ke riqe da cup dauke da matsatsen ruwan tuffa da inibi,sanye yake da wasuSlim fit suit Korean design royal blue color,shigar da a duk sanda ya yita take masifan karbarsa,kamar dama anyi suits da blazers saboda shi ne,kallo daya zaka yiwa kwantacciyar fatarsa kasan cewa hutu da jin dadi sun ratsashi,duk da cewa babu cikakken hutun ba ma’ana a ruhinsa,saboda uban tulin tarin ayyuka da kullum yake jibgama kansa,duk don yayi keeping kansa busy,ya raba kansa kuma da dukka wani tunani da kuma damuwa.

Fuskarsa nan mai cika da haiba da kwarjini tana nan a yadda take,babu faraa ko walwala sam kamar bashi daya bane a cikin qawataccen office din nasa ba,sumar kansa zuwa ta fuskarsa nata sheqi tare da fidda qamshin hair mist mai kwanatar da zuciya.

Taku daya yayi zuwa baya kadan da qafafunsa dake sanye cikin wasu lafiyayyun baqaqen takalma,wanda zaka rantse da Allah ba’a fita waje dasu saboda yadda suke sheqi,babu alamun saukar qura a kansu,ya dan jingina da teburinsa yana furzar da iska daga bakinsa bayan yakai shafin qarshe,yana tuna sanda shaheeda ta bashi gift na littafin,sai ya dan rufe littafin kadan yana kulle idanuwansa na wasu sakanni,kullum kwanan duniya yana jin cewa ya rasa babban bango kuma majingina a rayuwarsa,tunda ya rasata kullunm rayuwarsa sake jigata takeyi,babu wani sassauci tako ina.

Idanunsa ya buda a hankali sanda akayi yaji ana scanning key din office din nasa,qofar kuma ta bada qara alamun an budeta kenan,bai wani motsa ko kuma ya damu ba,saboda yasan duk duniya mutum daya ya bawa wannan damar wato jabir,shi dinne kuwa,ya sako kai cikin office din bakinsa dauke da sallama,hannunsa dauke da file yayin da idanunsa suke kan fuskar ja’afar,yayi kyau shima cikin tashi suit din da take kamanceceniya data ja’afar,ya qara haske da kuma qiba yayi fresh,alamun duk yadda yakeso haka take samuwa a gareshi.

Bakinsa ya motsa yana amsa sallamar tasa,kana ya miqe tsaye sosai saman qafafunsa,ya sanya hannu a nutse ya maida littafin inda ya daukoshi,ya rufe sannan yafara takawa zuwa kujerarsa,jabir din na biye dashi da idanuwa,yana kuma karantarsa,ransa da zuciyarsa na masa rashin dadi,don ko kowa baice komai dashi ba,yasan akwai abinda ya motsa zuciyar ja’afar din.

Sai da ya zauna sosai sannan ya tura file din gaban

“An gama hada komai,na gama nawa signing din,saura naka,zaka duba inda yake da gyara sai kayi,ka saka hannu mu miqa musu takardun, withing one to two weeks ya kamata a gama” ya qarshe maganar yana maida dubansa ga wayarsa daya zarota daga aljihu,saboda qarar shigowar text,murmushi ya subuce masa ya buda text din yana dubawa,yayin da hankalinsa kacokam ya koma kan wayar tasa,abinda yaja hankalin ja’afar,ya tsaya ya zuba masa ido,kana yadan bugi table din dake tsakaninsu.

Daga kai jabir din yayi yana dubansa,har yanzu murmushi bai bar kan fuskarsa ba

“Ina jinka”

“Baka tare dani” ya amsa masa kai tsaye da tsayayyar muryar nan tasa

“Yes…..gaskiya ne,hankalina bai wajen magana ta gaskiya,yanzu me ya rage?,inason naje gida lunch ana jirana” zube masa idanunsa yayi sosai kafin ya janyesu,kana yace masa

“Kana iya tafiya” da wani irin low tune da ya sanya tausayinsa sauka a zuciyar jabir,yafi kowa sanin yadda shaheeda tayi tattalinsa a lokacin rayuwarsa harma fiye da haka,amma a yanzu duka yayi loosing wannan caring din,dole abubuwan su dinga tabashi,duk da cewa shi yaqi bada wannan damar,yana da hope akan maimunatu shima kamar yadda yaji anni tana fada,ya sake samun gamsuwa akan yarinyar tun ranar da suka zauna sukayi magana ne tsaho a kanta da anni amma ya tattarata ya kaita makarantar kwana,annin kuma ta hana kowa masa magana,tace su xuba masa idanu suga iya nasa gudun ruwan.

A dan shurun da ya ratsa ta tsakaninsu ne tex ya shigo tasa wayar shima,sai ya jawota yana dubawa,qaramin tsaki yaja

“this is nonsense” furucin ya fita can qasan maqoshinsa,idan ba kunne kasa sosai ba ba zaka ji me yake fada ba,kira yayi ya aje wayar saman table bayan ya sakata a loud speaker,bugu biyu ya daga

“Me kake cewa ne?,ace duk gidan a rasa me daukota?” Yace da hisham kai tsaye,lumshe idanunsa hisham yayi daga wancan bangaren kafin ya amsa shi

“Babu yaaya,drivers din duka sun fita tare da abba,yana da baqin da suke zirga zirga dasu,ni kuma nan da minti goma akwai wanda zanwa surgery,kuma emergency ne har mutum biyu,kafin na gama kuma an ja lokaci” katse kiran kawai yayi,ya fara laluban number anty maama.

Itama bugu biyu ta daga suka gaisa

“Driver dinki yana kusa ki bani aronshi?”

“Wai…..ai kuwa yau tun sassafe ya debi yara abbansu yasa ya kaisu qauye”

“Ok” yace a gaggauce

“Akwai wani abu ne?”

“No,ki gaida yaran, thanks ”

“Okay” itama ta bishi dashi,tasan halin kayanta fes,bama fadar zaiyi ba

“Waye ya bawa drivers na gidan nan hutu ne gaba dayansu?” Ya jefawa jabir dake nanuqe da wayarsa yana maidawa fatimansa reply na dinta tambayar,sai a sannan ya daga kai ya dubeshi,duk nema neman drivers da yakeyi yana jinsa,ya kuma san dalilin hakan,don kusan da goyon bayansa anni tayi wannan hukuncin

“Hey man,kai ne mana?,ka manta kenan ka zauna ka sani a gaba zaka fara tuhuma?” Tsaki ya sake ja yana tattare files din da suke gabansa

“Bari na fito maka a mutum,duk wannan goce gocen da kake bazai maka bafa,ka tashi kaje dauko yarinyar mutane kawai,three months bata nan amma don zaka bata just thirty to fourty minutes ka daukota a school sai ya gagara saboda adalci irin naka?” Wani kallo ya masa,tunda yaji amsar daya bayar yasan da issue din kenan,sai ya dakata daga hada takardun

“Idan kaji haushi me zai hana kaje kai” dariya ya sake sosai

“Ba dole na bace,ga dole na can tana jirana,kuma inda itace da tuni na tsufa a school din,don bazan bari Allah ya kamani da laifin rashin sauke haqqin dake wuyana ba” yana gama sai ya miqe yana ‘yar dariyarsa zai fice daga office din,har ya kusa qofa sai ya tsaya

“Da zaka zo sai mu wuce gida tare ka fara yin lunch kafin ka tafi” ya fada with full caring in his voice,saidai kallo dayan da ja’afar yayi masa ya bashi amsarsa,sai ya kada kai kawai ya fice a office din yana murmushi,ya gode Allah daya bashi juriya da hikimar zama da ja’afar din,mutumin da yake jinsa tamkar cikin mahaifa guda suka kwanta dashi.

Riqe da suit dinsa a hannu ya fito,kana ya sauko kai tsaye zuwa floor din qarshe ya kuma wuce parking lot na ma’aikatar,key dinsa already yana hannunsa,tunda ya sallami driver dinsa,don yau din ya tsara lokacin tashinsa,zai iya kaiwa dare,don haka ya bashi umarnin tafiya idan akai azahar,sai gashi kuma wani abun da babu shi cikin schedule dinsa na yau ya taso masa.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: *GURBIN IDO

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply