Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 61


Gurbin Ido 61
Viral

61

Tunda suka gama komai ta sake wanka ta kuma gyara amna,ta shirya ta cikin wani Three quater mai kyau da shirt dinsa,itama ta shirya kanta,abinci ta zuba musu amma amna tace sam ita sai daddy ya dawo,duk yadda ta lallabata amma amnan taqici,yau kam kwanciya takeso tayi,tanason ta kalla qarasa kallon dramas dinta,idan da sauran lokaci ta duba karatuttukanta,bata son ma su hadu dashi kwata kwata,tana tunawa da abinda ya faru jiya,ji take kamar ta maido lokacin ta goge dukkan abinda ya farun.

Daki suka koma duka ita da amnan,saidai lokaci bayan lokaci tana zancan rashin shogowarsa,daga qarshe dole tasa maimunatu ta bude mata qofa ta tafi dubashi.

Yafi awa da shigowa cikin gidan amma ba wanda ya sani,sabida tarin ayyukan da yakeso.ya hattama,bayason barinsu su zame masa kaya,ga tafiyar dake gabansa jibi,wadda yake saka ran sai ya huta sosai kafin ya dawo din.

Idanunsa ya dauke daga kan system din yana duban amanan,gaba daya yarinyar ta narke fuskarta tana dubansa,sai ya sakar mata murmushi,yana jin dadi har qasan ransa,shigar tayi mata kyau,kuma ko ba’a gaya masa ba alamu sun nuna tana samun kulawa tare da jin dadin zaman gidan,kafin tace komai ya hade hannayensa waje guda

“Am sorry angel” dole ta saki dariya,ta tako da gudu ta fada jikinsa tana dariya,gefansa ta zauna tana qorafin dai

“I say sorry ko?” Ya tuna mata yana dubanta,dariya tayi tana tura kai lallai sai ta karanta abinda yake rubutawa a fuskar system din

“Daddy ka ajjiye don Allah muci abinci” sosai yaji dadin tayin data masa,don yunwa yakeji,ya kuma yo takeaway amma ya gaza ji,sai tattarashi yayi ya ajjiye,saboda kwata kwata taste din bai masa dadi ba,har yanzu taste din breakfast din safe yana jinsa akan harshensa,wannan yasa ya kasa jin dadin kome,amma kuma baison yarinyar ta fahimta haka,bayason raini,saidai kafin ya sake kowanne tunani amna tayi caraf da hannunsa,ta kuma riqeshi gam,babu damar ci gaba da aiki,dole yabar komai ya miqe yabi bayanta tana gaba janye da hannunsa.

Yankewa tayi kawai ta fara karatun bayan shigarta daki kada bacci ya dauketa bata karanta komai ba,har ta zauna sai kuma taji sha:awan shan gwanda,don haka ta miqe tayo kitchen,ta dudduba freezern gaba daya babu ita,da alama ta qare kenan,dama kuma last hisham ne ya siya ya bayar a kawo mata,ranta babu dadi ta rufe freezer din ta dawo daki,sai ta yanke kawai ta kirashi ta roqeshi ko zata samu wata,tana matuqar sonta.

A bakin qofar dakin amna ta sake masa hannu

“Daddy ka kirawo anty moon,yau tayi aiki sosai,zan dauko mana spoons da plates kafin ku qaraso,na iya zaka gani,anty moon ta koyamin” sai ta juya da hanzari ta bar wajen cikin zumudi ba tare data tsaya sauraren me zaice ba.

Da kallo ya bita har ta bacema ganinsa,baisan wanne irin qauna bace tsakaninta da ita ba,yana ganin zumudi sosai a fuskarta da farinciki duk sanda zasuci abinci tare,kansa ya girgiza yana sakin qaramin murmushi a fuskarsa sannan ya maida kansa ga qofar dakin.

Gaba ya matsa kadan ya dora hannunsa akan handle,sai a sannan ya tuna da abinda tayi masa dazun,hakan yasa ya qara hade fuskarsa,sannan ya murza qofar a hankali ya tura qofar dakin.

Tsaye take a gaban gadonta inda litattafanta suke ajjye,ta bawa qofa baya,sanye da farin high waisted skinny leggings da baqar armless robber shirt,gashinta data daure da siririn band mara fadi yana ta reto a bayanta,kanta babu dankwali,hannunta riqe a qugunta,ta kara wayar tata a kunnenta

“Ya hisham don Allah,Allah yasa ban takura ka ba” ta fada cikin karyar da murya,saboda batason matsanta masa da gasken,don dai batasan wanda zata kira din bane sai shi

“Kada ki damu matar yaaya,za’a kawo in sha Allah”

“Na gode sosai ya hisham,you are such a kind person” fusgar wayar da akayi da wani irin zafin nama yasa bata samu daman jin me hisham ya fada ba,sosai ta tsorata ta kuma juyo a razane,don ko kusa ko alama bataji shigowar mutum ba.

Dab da bayanta yake a tsaye,abinda yasanya ta kusa fadawa jikinsa kenan sanda ta juyo din,cikin sauri ta zare idanunta daga nasa,saboda wani kallo da yake mata,wani irin abu ne ke gilmawa cikin idanuwansa,yayin da qirjinsa ya cika da wani irin qunci fushi da kuma bacin rai,abinda ya sanya launin qwayar idanunsa canzawa kenan cikin qanqanin lokaci.

Taku biyu ya qara ya kawar da dukka tazarar dake tsakaninsu,fuskarta ta sauka tsakiyar qirjinsa saboda yadda ya bata tazara wajen tsaho,yayin da shi kuma habarsa ta sauka a tsakiyar sassalkan gashinta,da sauri tayi taku biyu baya saboda sake bata ratar daya hade a tsakaninsu,bata sauke diddigenta a qasa ba ya maara mata baya,sake jaa tayi da baya ya sake maida qafarshi inda ta sauke,bata gushe ba tana matsawa yana binta har ta qure da bangon dakin.

Idanuwanta dake cike fal da tsoro ta daga ta kalleshi,sai taji tsoronta ya ninka na baya,fushin data hanga saman fuskarsa da yadda idanuwansa suka sauya ya sake tsoratata,ci gaba yayi da aza mata kallonsa yana kuma sake hade gap din dake tsakaninsu,dab da ita ya tsaya ya daga hannunsa, abinda ya sanya maimunatu qanqamshe hannayenta tana jiran jin saukar duka ko mari,duk da batasan ainihin laifin data masa ba,amma wani sashe zuciyarta na gaya mata kashe masa wayan da kikayi daxu,ba abinda zuciyarta ke hasaso mata sai irin marin data taba karba daga wajensa shekarun baya da suka shude,da qyar idan yau ba za’a maimaita ba.

A hankali ya sauke hannuwan nasa yana morewa kallon fuskarta dake cike da tsoro,duk da idanuwanta a kulle suke amma hakan bai hana kyanta fita ba, siraran jajayen lips dinta nata motsi,koda ba’a gaya maka ba kasan kuka take shirin saki,bai gama wannan tunanin ba kuwa hawaye suka ratso rufaffen idanunta,bin hawayen yayi da kallo,sai yaja baya a hankali,ta gama karya lagonsa,baisan dalili ba bai kuma san me yasa ta shiga sahun mutanen da hawayensu ke saurin karya shi ba,ba abinda wannan ya tuna masa sai shekarun baya sanda ya mari marainiyar fuskarta,abinda ya tsaye masa a rai tun a wancan lokacin fiye da komai,zuciyarsa yaji tayi laushi,amma kuma bacin ran dake can qasan ransa har yanzu yana motsawa.

Daga hannunsa yayi yana kallon wayar da ya qwace din,number hisham din ce,sai ya danneta ya shiga wajen block yayi blocking nasa sannan yayi deleting number kwata kwata daga kan wayar,bai tsaya a nan ba ya sake shiga contact nata,numbers din dake kai ba masu yawa bane,duka duka na ‘yan gidansu ne sai na wasu mutum hudu afrah besty teema ummu,numbers dinsa ya saka ya shiga wajen kira,number batayi appearing ba,alamu dake nuna cewa kenan bata da number dinsa?,yaja qaramin tsaki can tsakiyan ransa,sai ya samu kansa da yi mata saving number,ya kuma sanya mata full name dinsa

_*ja’afar marwan akko*_,ya daga kansa a nutse ya sauke a kanta,tana tsaye manne da bango kamar zai tsage ta shige,fuskarta duk danshin hawaye,sauka idanunsa sukayi saman qirjinta wanda shape dinsa ya fita sosai saboda robbern da rigar ke dashi,komai a zaune das sun kuma cika rigar,sai sama da qasa qirjinta yake alamun tsoro da kuma bugawar zuciya.

Yana son ya tsaida ganinsa a nan amma ya kasa,sai ya samu kansa da zarto da kallonsa zuwa faffadan qugunta,cinyoyinta sun fita sosai kamar babu ma wando a jikinta sai fatar jikin nata kawai kasancewar leggins din skinny ne ya zauna mata yadda ya kamata,zaka tsammaci ciko tayi musu don sun fita yadda ya kamata,kai kace zana mata qugun zuwa cinyoyinta akai

“Allah….” Ya fada can qasan ransa tsigar jikinsa tana tashi,wani irin mahaukacin kishinta karo na farko ya sauko ya lullubeshi,karon farko da tunanin yaya uniform din makarantarsu yake ya taso masa?,wando ne?,ko kuwa doguwar riga ce?,wanne irin kaya take sanyawa a matsayin house wear?,hannunsa ya dunqule ya kuma yarfar,ya cije lips nasa na qasa ransa na masa suya,shi kansa ya yadda dari bisa dari yana da tsananin kishi,bashi da sassuci ta bagarori da dama,amma tasha yi masa fada ya dinga sassautawa

“Open your eyes” ya fada da wata tattausar murya da maimunatu bata taba tsammani ba,cikin kokwanto ta soma bude idanun nata a hankali,tana gama budesun sabbin hawaye suna sake wanke mata fuska

“Ya salam” ya fada a boye yana jin yadda zuciyarsa ta wani irin harbawa ganin yadda ta narke gaba daya tana sauke sabon kuka,rarrabuwa hankalinsa yayi,baya son kukan,amma kuma baisan ta yadda zai rarrasheta ko ya tsaidata ba

“Keep quiet” yafada da kakkausar murya,tsai da kukan tayi cak tana qanqame jikinta waje guda,sosai ya hade fuskarsa

“Waya baki izinin yin waya da wani?” A mamakance ta dago kai ta kalleshi,duk da taso tsirashi da ido yadda yake mata amma sai ta gaza,tadan kauda idanun nata dake cike da lema,hisham dinne wani?,ta tsammaci ya duba yaga waye tunda ya karba wayar a hannunsa ai

“Don’t let me repeat my question…..” Ya fada yana jin siqewa a ransa,wani sashe na zuciyarsa kuma najin damuwa da zubar da hawayenta keyi amma kuna yana danne hakan,sai data kauda kanta gefe,cikin muryar kuka tace

“Yaa hisham ne”
“who is hisham?” Ya fada yana goye hannayensa a bayansa,har yanzu bai rabu da kallon baby face dinta ba,dan daburcewa tayi,saboda bata fahimci inda tambayar tasa ta dosa ba,duk da haka tayi dauriyar cewa

“Yaa Hisham dai…..”
“Ba hisham qanina ba,koda ciki daya kuka fito dashi na sake ganin kuna waya sai nayi matuqar saaba miki?,kin fahimta?” Kai ta daga masa sabbin hawaye na fito mata,shuru yayi yaci gaba da kallon ta,haka kawai yaji baiso tsaiwar tasu ta yanke,kallon fuskarta kuma kamar yana qarawa lokaci gudu ne,tare da sanya wucewarsa nan da nan

“Me yasa kika kashemin waya dazu?,ni sa’anki ne?” Kamar zata kalleshi sai ta fasa,saboda yadda gaba daya ya dafa mata jiki da kallonsa,takejin kamar ba zata iya ci gaba da tsaiwa ba,zuciyarta kuma tayi raunin da bazata iya ci gaba da amsa tuhume tuhumensa ba,sai kawai ta soma sulalewa a wajen tana sakar masa kuka.

Baisan ya isa inda take ba sai da ya ganshi tsaye a kanta,ya duqa a hankali sai kuma amna ta turo qofan dakin da murnarta,turus tayi jin kamar sautin kuka,sauri ta qaro ta iso gaban maimunatu dake duqe a wajen ja’afar na tsaye

“Daddy kuka?,kaine ka sata kuka” Amna ta fada tana durqusawa a gaban maimunatu itama kamae zata fashe masa da kukan,rasa wacce amsa zai bawa yarinyar,ta fara qoqarin son dago kan maimunatu abinda yakeson yi kenan tun dazun,tambayarta take

“Anty moon,daddy ne?” Kai ta girgiza mata alamar a’ah,sai ta sake dagowa tana dubansa

“Daddy ka bata haquri…..ko zatayi shuru” wannan fa shi ake kira qaqa qara qaqa,sai ya debe hannuwansa zuwa aljihun rigarsa ya boyesu a ciki kamar baison wani ya gansu,a hankali labbansa suka motsa

“Am sorry” maganar ta fita da wani irin taushi da kuma qaramin sauti,sai ya juya a hankali yana barin dakin,amma kunnuwansa na ciki har sai daya fice.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply