Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 63


Gurbin Ido 63
Viral

63

Ta ja tsaki ya kusa sau goma sanda ta koma sassan nata,batasan abunda yasa abinda unaisa tayi matan yayi mata zafi sosai a ranta ba,bedroom dinta ta fara qoqarin gyarawa,sai ga amna ta turo qofa ta shigo,ta waiwayo tana dubanta,sai taga ran yarinyar a hade tana tura baki

“Lafiya amnee?”

“Waccan antyn mana,wai don ta kirani banje ba shine ta harareni” sakin duvet din da take take ninkewa tayi ta kama hannunta

“Manta kawai,ke da zaku tafi da daddy,kullum kuna tare?,me zai dameki” murmushi ta sauke

“Yauwa yace kizo” sakin hannun amnan tayi, kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa,batason wasu abubuwan su dinga faruwa gaban idanun yarinyar,yarinya ce mai wayo sosai,akwai abubuwan da ba zata manta dasu ba idan suka farun.

Closet dinta ta bude ta ciro madaidaicin blue black din hijab ta zira ba tare da ta fidda hular kanta ba,ta kama hannun amnan suka fito.

Suna fitowa ta hangi unaisan a zaune,ta dora qafa daya kan daya tana girgiza su,da biyu tayi wannan zaman,tanason ta sanya idanu a gidan game da takun kowa,gefanta breakfast dinta ne da bayin nata suka yi suka kuma jere mata.

Mummunar faduwa gabanta yayi sanda taga maimunatu ta kama stairs din tana hawa,suna hira kuma tartar da amna abinsu,miqewa tsaye tayi,tayi kamar zata bisu take wata zuciyarta ta tsawatar mata

“Karkiyi,ba girmanki bane” sai ta koma da baya a hankali ta zauna, zuciyarta na mata wani irin suya,dole yarinyar ta samu zarrar tsayawa ta maida mata magana,tunda har ta samu darajar hawa sassan ja’afar din,kai tsaye har haka?,ja’afar fa?,tasan ba qaramin abu bane mai sauqi ace ka samu irin wannan damar daga gareshi,damar data dade tana nemanta,wataqil ma sunsan juna sani irin na ma’aurata

“Kai qarya ne,ba zata taba iya dauke wannan qaton ba,duka duka nawa take?,yaushe qashinta yayi qwari,ni na razana na janye bare ita?” Wannan tunanin ya rage mata tashin hankalin data shiga,sai ta koma ta zauna tana jiran taga saukowarsu.

A bakin dining ta sameshi a tsaye,da alama shima ya gama dukka shirinsa,shirt da trouser ne a jikinsa na kamfanin armani,sai qafarsa dake saye cikin wani rufaffen takalmi na fata slip on,me wani irin qawataccen ado,batasan yadda kayan maza suke ba,amma ita kanta takalmin ya tafi da ita,kayan sun dace dashi sosai,sun kuma fitar da qirar sa sosai wadda suit ke yawan boyewa,kana dubansa zakasan yana shiga gym sosai,short sleeve shirt din ta bayyana baiwar gargasar dake dukka hannuwansa masu tarin yawa.

Da ita dashi dukka tare suka dauke kansu,dukkansu suna basarwa,saidai cikin jikinsa yaji wani abu ya tsarga masa,baisan ko baiwa bace,ko ta musamman ce a cikin mata?,duk sanda tatashi a barci sai fuskarta tayi wani fresh,idanuwanta suke garai garai su kuma fito ba.

Cikin kayan abincin data kawo masa ne yake shan tea,ta tako a hankali tana basarwa,qamshin turarensa daya cika falon yana kada mata hankali

“Ina kwana?” Ta fada da muryarta da ko da yaushe take tuna masa da mafarkinsa,ko a yanzun ma sai daya ji tsigar jikinsa ta tashi

“Kin manta da qa’idata kenan?” Ya fada yana dire cup din hannunsa saman table din,hadi da qoqarin zaro wayarsa da tayi qara na alamun shigowar saqo,kai ta daga kadan ta dubeshi sanda yake kallon fuskar wayar,fuskar nan a dinke tsaf kamar bai taba dariya ba,abinda yasa girarsa guda biyun dake da wani irin shape dake burgeta sukayi kaman zasu hade da juna,sai ta kau da kai tsigar jikinta na zubawa,bata gane me yake nufi ba,kafin ta sake cewa wani abu kuwa yace

“Minti ashirin ya rage mana mu wuce,bakiyi wanka ba?” Idanu tadan fitar tana kallonsa,ta sake gazawa jure kallon nasa kamar ko yaushe

“In…..” Ta bude baki da niyyar tambaya,amma sai ya katseta

“Don kince baki zuwa,sai nabi umarninki,ni dake waye a sama?” Take ta fara abinda ya tsana din,wato hada ruwan hawaye akan fuskarta,ta kuma fara girgiza kanta,murya a karye kamar qaramar yarinya qasa da shekarun su amna ta fara magana

“Kayi haquri,zan rasa makaranta,mun kusa komawa” idanunsa ya kafeta dasu,baisan me yasa yakejin haushi yana kamashi ba idan tayi zancan makarantar nan ba,wato makarantarta tafi komai?,zai tuna mata idan ta manta,matar aure ce ita,mijinta ya kamata ya juyata bawai tunanin komawa makaranta ba,ya kamata taji wani abu a jikinta da zai dinga tunasar da ita tana da igiyar wani,yaga kaman ta shagalta bata tuna haka.

Kanta yana qasa tana qoqarin tsaida hawayenta,don haka batasan ya iso inda take ba,har sai da turarensa ya shaida mata.

Kanta ta daga a hankali,sai tayi yunqurinja da baya da sauri saboda rage kusancin dake tsakaninsu,saidai kuma tuni ya kaima hannunta cafka,ya kuwa damqeta da kyau saman duwatsun hannunta.

Tare suka kai dubansu shi da ita kan duwatsun,a hankali ya sakar mata hannu,sai kuma yayi mata qofar rago,taku daya idan ta qara da niyyar yin gaba ko baya to zata tsinciki kanta kane kane ne a faffadan qirjinsa

“Wipe these tears…..,daga yau kika na sake magana kikamin kuka ko na sake umarni kikamin musu,Allah….Allah…biyu ko?,kalli ki gani” ya fada yana ranqwafowa dai dai fuskarta,kan yin musun yayi magana,don haka ta daga kan nata kamar yadda ya buqata,saida numfashinta ya kusa daukewa sanda taga irin kusa da kusan da sukayi,suka fara musayar numfashinsu me dumi,wani abu ya tsarga cikin jikinsa,fararen idanuwanta suka sauke masa wata irin kasala,sai ya daga hannunsa ya dora yatsuntsa guda biyu saman lips dinsa

“Da nan zan goge hawayen tas,na kuma cinye bakin musun” tsareta yayi da idanun da a yau takejin saukarsu cikin kowanne sashe na jikinta sama da ko ina bayan ya ciro handkerchief dinsa ya bata ta goge fuskarta

“Na baki minti goma ki shiga bedroom dina ki shirya” tana son tace wani abu amma tana tsoron rantsuwar hukuncin da yace zaiyi mata,don haka saita juya kawai zuwa bedroom din nasa gabanta na faduwa saboda rashin sabo,qafafunta basu taba taka cikin uwar dakin ba sai yau.

Da kallo ya bita har ta shige,sai ya daga handkerchief din nasa yana kallon inda yayi danshin hawayenta,bakinsa ya tabe,qasa qasa ya furta

“Its the consequences of marrying young girl” murmushin gefan baki ne kuma ya subuce masa daya tuna haka suka dan sha daaru da shaheeda ma,me yasa wasu abubuwan nasu ke manceceniya?,hakan na nufin itama haka zaisha fama da ita tare da koya mata yadda yakeso ta kasance?

“are you ready to accept her as your wife?”, Katsam tambayar tazo daga wani sashe na zuciyarsa,sai yayi shuru yana son rarrabe meye amsar data dace da tambayar?.

A hankali take takawa cikin tsakiyar dakin tana nufar toilet dinsa,idanunta take wulwulgawa cikin dakin,komai na dakin taji yana burgeta,komai cikin tsafta,babu datti ko qura,saidai kuma ba’a shirye wasu abubuwan suke ba kamar yadda aka san dakin mace.

Duk kyau da girman dakin da kuma tsadajjen marbles da aka saka masa an mamaye kusan fiye da rabinsa da wani tattausan carfet mai daukan sanyin acn dake kadawa cikin dakin kamar yanayin hunturu,kalolin dakin gaba daya dusty pink and beige color ne,sassanyar kalar da babu hayaniya a ciki,kama daga curtains zuwa komai ma na amfanin ciki,ta wuce toilet din tana kallon katafariyar walk in closet dinsa dake cike da himilin sutturu,kai zaka tsammaci ba’a nan qasar bane,da alama wadanda suka tsarata sun qware sosai a aikinsu.

A toilet ma bata yima kanta qauron kallo ba,a nutse take bin toilet din da kallo,kamar ba muhallin wanka ba,tuna abinda ke gabanta da kuma wanda ke jiranta yasa ta qara gaba zuwa jacuzzi bathtub,ta hada ruwa dai dai da ra’ayinta sannan ta koma gaban wani oval shape glass sink dake da wata qaraman drower a qasa,gaba daya kayan amfaninsa ne a ciki kana hangosu tarwai kamar ruwa bai taba wajen,kama daga brush toothpaste sponge da tarin shower gel masu tsadan gaske,sai kayan shaving nasa,clippers da sauransu.

Wadda ke a bude ta dauka tare da sponge din dake wajen data tabbatar dashi yake amfani,lumshe idanuwanta tayi sanda qamshinta da dumin ruwan ya hadu waje daya,sai taji kamar kada ta gama wankan,sosai qamshin ya burgeta ya kuma zauna mata a kwanyarta.

Rarraba idanu ta shiga yi data tuna bata ko shigo da kayan da zata canza ba,hakanan bazata iya maida rigar data cire din ba,ta koyi wata irin tsafta da gayu na daban,bata da wani sauran zabi,dole ta matsa jerin fararen towels din dake maqale a wata silver hanger ta cira daya,tun kafin ta raba shi a jikinta qamshinsa yayi mata maraba,ba kasafai ta fiya son cudanya da duk abinda ke qamshinsa ba,sai ta maida ta dauko wani,saidai.shima din dai sammakal,ganin tana bata lokaci yasa dole ta daurash cike da fargaba,bata manta waccar ranar ba da towel din yaso zamewa daga jikinta,Allah ya taimaketa batayi me gaba daya a gabansa ba,sai ta sake dauko wani ta lullube kanta sannan ta fito.

Da amna ta fara cin karo,zaune kan sleeper sofan dake gaban gadon da game a hannunta,bisa dukkan sabuwa ce yau din ta fara amfani da ita,sam ta mance da yarinyar,dazun tana ina sanda suke magana?,Allah yasa bata a wajen.

Kai ta daga tana duban maimunatu dake riqe da towel din dake kanta wanda ke shirin zamewa

“Anty moon,ga kayanki” duban inda ta nuna matan tayi,sai ta gyada kai,ta qarasa gaban mirror dinsa.

Kaman madubin mace,cike da kayan shafa designers amma irin na maza,bata da sauran xabi,hakanan ta bude mayukansa ta shafa na shafawa,duk amna anyi shuru an nutsu an sami game,sannan ta dawo tana daga kayan da amnan tace nata ne.

Tana duba kayan pant da breezier dinta suka fado daga tsakiya,sai ta fidda idanu cikin mamaki,ta daga kai tana duban amna

“Amna….waye ya daukomin kaya?”

“Daddy ne,nina rakashi” wata irin kunya ce ta kamata kamar zata nutse a wajen,musamman da taji suna fidda qamshin musk,saita qanqamesu kamar ta fasa kuka, knocking da taji anyi ya sata kwashe kayan da sauri,ta kuma koma toilet ta sakasu,tana sake jajantawa kanta,shikam baiji kunyarta ba?, dakinta ma ya shiga kenan?,bayan wannan dame dame ya gani nata?,Allah yasa baiga wani abu na kunya ba a dakin.

Sanda ta tsaya a gaban madubi ita kanta tayi mamakin yadda kayan suka karbeta,suka dace da fatarta,a gurguje ta shirya,ta sanya takalmanta ta kuma yi rolling silk vail din dake mahadin kayan,take ta qara wani kwarjini sosai,saidai gaba daya ranta a jagule yake,hakanan akwai raguwar fara’a sosai daga kan fuskarta,sam sam bata shirya yin wata tafiya ba,musamman ma ace dashi,bugu da qari ma tana ji da tsoron kada tafiyar ta shiga qarewae hutunsu a koma makaranta banda ita,batason tayi missing koda kwana daya ne,amma a yadda taga ya dauki abun serious bata da wanin sauran zabi.

Yana tsaka da waya suka fito ita da amna,gaba daya ilahirin jikinta qamshin turaren yake,turare ne daya ajjiyeshi ya daina amfani dashi,saboda yadda yake kashe masa jiki da zuciya,ta wani glass dake jikin space din da aka maqala babban plasma din ya hangota,duk da bai juyo ba amma yana ganinta tarwai,sai ya lumshe idanunsa sannan ya sake budesu,yana ci gaba da qare mata kallo ta glass din ba tare data sani ba,har suka iso inda yake bai juyo ba bare yayi alamun ya gansu,saidai duk wani taku nata akan idanunsa ta saukeshi,kusantowarsa wajen d qamshin turaren sai ya fara raba masa hankali,da coolness din nan nasa dake bayyana kansa wasu lokutan yace

“I will call you later” ya zame wayar daga kunnensa ya jefata a aljihu,ya kuma bita da hannuwansa da yake yawan sanyasu a aljihun,sannan ya waiwayo.

Yawun bakinsa ne ya kusa daukewa,gaba daya kallon daya mata ta glass din gaibu ne,yanzun yake ganin ainihin zallar reality,inda ace ita ya bawa damar dauko kayan zaice tayi da biyu ne,saidai da kansa ya dauko saboda favourite color dinsa kenan,sai gashi sun mata wani mugun kyau fiye da tsammaninsa.

Idanunsa ya aza bisa fuskarta,baby face dinta a hade babu sauran fara’a,idan ma ya kula da kyau ta sake tsuke dan qaramin bakinta data zizarawa man lebe daya sanyashi yake qyalli,sai yadan rage kaifin kallon da yake mata,ya maida dubansa kan agogon hannunsa,ko bai magana ba tasan qorafi zaiyi kan ta bata musu lokaci,ta zaci zai amsa,sai taga ya kama hannun amna sunyi gaba,dole tabi bayansa.

Ta zaci zai bata dama ta koma sashenta ta kintsashi ko ta dauko abunda take da buqata,amma sai taga baice komai da ita ba,hakanan ta bishi kamar zatayi hawaye,wannan mulkin kama karya ne da kuma qarfa qarfa,ai ba ita daya bace a gidan,me yasa bazai dauka unaisa su wuce ba?, Da wannan mitar da take tayi can qasan ranta ta qarasa motar,ta kama daya side din ta bude murfin ta shige.

Har suka isa airport bata ce ko uffan ba,yana ankare da hakan,haka kawai ya samu kansa da monitoring mood dinta,wanda shi kansa baisan dalilin hakan ba.

Sosai take kallon tsarin airport din,karon farko a rayuwarta abinda ko kusa bata taba kawowa zuciyarta zai faru a rayuwarta ba,saidai tayi qoqarin kame kanta,bata wani zarme da yawa ba,tana bin komai da lura,sai kuma abinda taga sunyi sannan,hakan ya sanya batayi wani abu daga kwafsa ba,dama kuma a idanu batayi zubin wadda zaka tsammaci ba sananniya bace a fagen,duba da jibga jibgan motocin da suka yima ja’afar din rakiya bisa jagorancin shugaban ma’aikata na kamfanin nasa.

Bayan an gama checking luggage dinsu suka amsa boarding pass sannan suke wuce gates,wannan karon amna ta dawo hannunta,dukka passingers ne dake jiran tashin jirginsu daga gomben zuwa Lagos,cikin kujerun dake wajen ta hangi jabir da fa’eemansa,tana kwance sosai ajikinsa,da alama wani abu yake nuna mata cikin waya.

Yaga jabir din amma baiyi ya ganshi din ba ganinsu tare da fatiman,miskilancin ya motsa,muryar amna tana kiran sunansa yasa ya ankara da shigowarsu wajen,da sauri fatiman ta gyara zamanta abinda ya bawa jabir daman tashi yana sanya wayar a aljihu,yayin da fatima ta budewa amna hannunta,akwai sabo tsakaninsu saboda tana da son yara fatiman,don haka ta nufeta, maimunatu ta bi bayanta,sai taji ta fara sakewa,don da alama da fatiman zasu wuce gaba daya.

*_To masu karatu, honeymoon za’a je ne ko yawon bude ido?,meye zai faru?,😂,nidai bana ce ba,ku biyoni mu qarasa bin qwaqwafin labarin tare daku_*
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply