Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 70


Gurbin Ido 70
Viral

70

Seat din kusa da ita fareeda diyar sa’ade ta barwa maimunatu,dukkansu suna ta kallon maimunatu cike da zumudi a zukatansu,saboda suna da.labarinta sarai,sannan ita fareeda tana dan tuna wasu abubuwa da suka faru,tunda da dan wayonta suka bar gembu.

Cikin tafiyar awannin da suka cur hannun sa’ade yana cikin na maimunatu,kaf maimunatu ta labarta mata dukkan abinda take da buqatar sani,saade ta lumshe idanu hawaye masu dumi suna fita akan fuskarta

“Wata shari’ar sai a lahira,inno taci amanata taci amanar shatu,Allah ya jiqanki ‘yar uwata,matsala na samu akan dukka abinda ya shafi bayanaina,aka samu wasu suka dauka sukayi amfani dasu suka aikata laifi,ya zamana ni ake zargi aketa nema,wannan dalili yasa abbansu yayimin kyakkyawan boyo,sannan akaci gaba da bincike,don yasan muddin ya fiddani aka kamani babu mai fitar dani sai Allah,wannan dalilin ya hanani dawowa gareku,saidai duk da haka nayi amfani da abbansu nayi aike gembu,waya kudi da kaya,ina amfani da wani boyayyen layi ina yawaita kiran inno akan yaya kuke ya lafiyarku?,koda yaushe nunamin take kuna nan lafiya,bana jimawa akan waya shi yasa bana samun damar cewa a bani ku,aike nake akai akai na kudi da kaya ashe baya samunku,ashe sun gama shirya abinda suka shirya,ashe sun cutar min da shatu na,sun kuma cutatar dake kema” sai suka sanya kuka gaba dayansu hannuwansu cikin na juna.

Dogon numfashi ja’afar dake daga can bayansu ya saki,tunda suka zauna hankalinsa da nutsuwarsa tana kansu,duk da baijin abinda suke fada amma yana iya fahimtar kuka suke,yana kuma ji a zuciyarsa maimunatun kuka take da gasken gaske,yana ta son ya daure amma ya gaza,yana jin kukan nata yana tabashi sosai

“Please,ka gaya mata ta daina sakata kuka haka” ja’afar ya fada idanuwansa a kansu,kallonsa jabir yayi baki galala

“Kai,surukarka ce fa,sannan kuma mamanka ta wani fannin,ita za’a cewa ta daina saka matarka kuka?,bazan iya ba” shuru ya ratsa tsakani,kawai sai ganin ja’afar jabir yayi yana miqewa tsaye,da alama zuwa zaiyi kenan ya shaidar mata da kansa.

Saurin damqoshi jabir yayi,don yasan tsaf xai aika

“Haba mana,kayi haquri mana romeo,dole fa suyi kuka,don bakasan komai bane” da mamaki ya juyo ya dubeshi,duba na son sanin abinda bai sani din ba,ba tare da yace komai ba jabir ya karanceshi,sai yace dashi

“Zauna na fada maka” ba musu ya koma ya zauna din,ya kuma tattara dukka hankalinsa ga jabir,yayin da jabir ya soma magana a nutse,dama.ya jima yana fatan zuwan wannan lokacin da ja’afar din zai san labarin maimunatu,yasan halinsa sarai,yana da wani irin tausayi na daban q zuciyarsa,sanin labarin nata zai sake haifar da wata alaqa mai girma a tsakaninsu,inda a baya ne,yasan halinsa……bazai taba tsaya ya saurareshi ba,coz bashi da interest,idan kuma yayi loosing interest akan abu babu mai sanyashi dole face mutum biyu zuwa uku a duniya,anni abbi da amma.

“Ashe nesa a kusa take?,ke din matar ja’afar ce,ja’afar kamar d’a yake a wajena,saboda dan qanwar abbansu fareeda ne”

“Amma?” Maimunatu ta fada tana dan fidda idanu cikin mamaki,a karon farko sa’ade ta gyada kai

“Qwarai,wala’alla banda matsalar dana samu…..wadda sai yanzu ta warware,dani za’ayi bikinku,nasan anyi bikin,amma ban san amaryar ba,don a sannan ba cikin hayyacina nake ba,yau sati daya kwata kwata da bayyanar gaskiya,aka kuma damqe wadanda suka aikata laifin,wanna shine ya bani ‘yancina” kai maimunatu take jinjinawa,lallai soyayya ta gaskiya abace mai kima daraja da kuma wahala,ta jinjinawa abbansu fareeda da yadda ya bata dukkan kariya,duk da cewa basa a qasarsu,amma ya tsaya mata kai da fata don ganin ya kula da amanar da aka bashi

“Yaranki nawa diyam dita?,duk da nasan ba zai wuce guda daya ba tunda baku fi shekara da auren ba,saidai idan kinyo gadon dangin tamu daadar masu haifar twins” kunya ta kama maimunatu,saita kifa fuskarta a kafadar sa’ade,tana jin kamar ita da daadarta suke magana

“Babu ko daya” murmushi tayi tana gyada kai

“To Allah ya kawo masu amfani da albarka,yasa kiyita haifa mana bibbiyu,zuri’ar shatu na tayi dogon baya” tayi maganar cikin rauni dajin zafin mutuwar ‘yar uwarta,wanda bata sani ba gaba daya sai kwanan nan.

Hawayen fuskarta ta dauke,ta waiwaya kadan baya inda su ja’afar suke

“Amma naji dadi da naga yadda ja’afar yake miki,da alama akwai tsaftatacciyar soyayya a tsakaninku” a kunyace ta saki murmushi tana yin qas da kanta,sai takejin kamar umma sa’aden tana iya karanto abinda ya faru tsakaninta da ja’afar din kwanaki biyar din da suka shude,don har yau bataji tafiyarta ta koma dai dai ba yadda take ada,sannan kuma ta fahimci akwai sauran dan ciwo ciwo a jikinta.

Jin bata amsa ba sai ta dora

“Haka nake fata,ki samu mijin marainiya,kuma ina da cikakken fatan cewa zaki samu haka daga ja’afar,indai yaro yana gadon dabi’u daga mahaifiyarsa,aishatu mutum ce nagartacciya,kawai qauna mai tsafta tsakanina da ita,bansan yaya zataji ba sanda labarin KE JININA CE ya risketa” sa’ade ta qarashe maganar tana gyada kai murmushi na kubce mata.

Duk yadda umma sa’ade taso ja’afar yabar mata maimunatu su wuce gidanta ko kwana daya suyi amma ya murje idanunsa,bai ma yarda ta ganshi ba,don tuni ya isa motarsa yayi zamansa a owners corner yana jiran isowarta,awannin data dauka ba tare dashi ba sai yake jinsa kamar wanda ya rasa wani sashe na jikinsa,ya sauke hannunsa da yake duban lokaci dai dai sanda take takowa zuwa gaban motar,fareeda da umma sa’aden suna biye da ita.

Sosai ya zuba mata idanu ransa yana motsuwa,yana kuma tuna labarinta da jabir ya bashi,wani irin nau’in tausayi na musamman na ratsa zuciyarsa kamar zai narkar da ita,how she survive?,rayuwa ba uwa ba uba?,babu yaya babu qani?,ba soyayya ba kulawa?…….tabbas ta cancanci samun komai,ta cancanci ta samu duk wani abu data rasa a baya,sai ya lumshe idanunsa sanda suke gab da motar,yana daukarma kansa wani alqawari,wanda ba wanda ya gayawa,tsakaninsa ne da ubangijinsa kawai.

“Ina fatan za’a kawomin ita ko ni ayimin alfarma nazo na ganta ko yallabai?” Sa’ade ta fada tana murmushi,kai ya jinjina mata da nashi miskilallen murmushin ya amsata a taqaice

“In sha Allah” tasan halinsa ba tun yau ba,don haka itama bata wani damu sosai ba,ta maida qofar ta rufe musu tana musu fatan sauka lafiya,kafin itama ta juya zuwa motocin da suka zo daukarta,zuciyarta cike fal da kewar maimunatu,wanda inda so samu ne su kasance tare,su kwana gado daya tana sake jin labarin rayuwarta.

Bata gama dai daita zamanta a cikin motar ba ta tsinci hannunta cikin nasa,ya daga hannun nata a hankali ya cusa cikin qirjinsa yana lumshe idanuwansa.

Shuru tayi kamar yadda shima yayi shurun,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa fat fat da qarfi bisa qaramar tazara sosai a tsakani,mintuna kusan uku suka kwashe a haka sannan ya bude idanuwansa ya azasu a kanta

“Awa shida kawai?,ta yaya zan jurema wasu awannin da suka fi haka tsaho da yawa?” Ya fada da mugun taushin,salon maganar daya haifar mata da wata kasala da kuma wani yanayi na daban a zuciyarta,saidai ta share ta kuma danne,taso ta zame hannunta amma ya hana hakan faruwa,yaci gaba da riqon hannun nata cikin nasa.

^^^^^^^^^^Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke sanda ta fito daga wanka,gajiyar da bata jita ba a daxun yanzu tana sauko mata,ta bata kusan awa uku,tunda ta shigo dakin take waya da ‘yan sannu da zuwa gami da zolaya a fakaice,su laila harma da afra,wanda wayar tasu ta sake qara mata kwadayin komawa makaranta,saboda ta bata labarin yadda aketa zuba karatu,don ba zasu jima ba zasu zana jarabawar qualifying su wuce zuwa ss three kai tsaye.

Tsaye tayi gaba mudubi sanye da towel hoodie robe fara tas,idanuwanta nakan kayanta data gama shiryawa tsaf na komawa makaranta tun kafin suyi wannan tafiyar,tafiyar data zame mata mabudi kuma mafari na kalolin rayuwa iri daban daban.

A hankali yake saukowa daga samansa hannunsa riqe da wayarsa yana dannawa,shima yayi wanka ya canza kayansa zuwa wata lallausar over size shirt da three quater wanda ya tsaya masa iya qaurinsa.

Karo na uku idanuwansa suka sauka a sashenta,ya sake canza akalar tafiyarsa zuwa qofar sassan,yayi knocking na wani lokaci,sannan yasa hannu ya murda handle din amma sai ya jishi a riqe gam,hannunsa ya daga yana kallon tafin hannunsa da ya danyi qura,mamaki ya kamashi,jikinsa kuma ya bashi lallai wajen ba kullewar dazu ko jiya bane,amma ina ta fita ba tare da izninsa ba?,ina taje?,bayan ya bar mata digits din da zata nemeshi?,bashi da wannan amsar,don haka ya juya yana barin wajen zuciyarsa na sosuwa,ransa kuma fal da bacin rai.

Samun kansa yayi da nufar sashenta,ya buda qofar ya tura,wannan sassanyan qamshin nata da ya kama sashen har yanzu yana nan daram,sai ya lumshe idanu yana nufar qofar dakin da yake jin tana ciki,tunda dashi tafi amfani.

Har ta gama igiyar robe din ta soma kwancewa taji an turo qofar dakin,sai ta tsaya cak cike da mamaki tana dubansa,don batayi tsammanin ganinsa a dai dai lokacin ba,tana ganin lokacine da zata sake tunda zaya zauna a sassansa.

Yana kuma kallonta yana sake takowa zuwa ciki,wani abu kuma yana narkar masa da zuciyarsa,wankan da tayi ya sake sawa fuskarta tayi fresh sosai,akwai sauran lema a gashin girarta da kuma gaban kanta,zuciyarta ta shiga bugawa sanda taga yana nufota direct,amma kuma sai ta gaza daga qafafuwanta har ya cimmata.

Dab da ita ya tsaya wanda taku daya zaiyi ya hade duk wata tazara dake tsakaninsu,a nutse ya daga hannunsa ya dora saman igiyar rigar,jaa daya yayi mata ta ware,rigar wankan ta fara ware kanta da kanta, tunda dama igiyar ke riqe da ita.

Cikin gigita ta sanya hannunta ta damqe gaban rigar,qaramin murmushi ne ya subuce masa yana duban idanuwanta da suka hautsine da tsoro,har yanzun da sauran aiki kenan ya raya a ransa,yana ci gaba da kallon nata ya zura hannunsa ta tsagar gaban rigar,bata ankara ba ta tsinci sassanyan tafin hannunsa saman cikinta saitin cibiyarta.

Cak numfashinta ya dauke na wucin gadi, kafin ta samu nasarar fusgoshi kuma hannunsa ya fara yin sama,har ya samu nasarar isa muhallin da taketa bawa kariyar,sai ji tayi ta ratsa hannuwan nasa a tsakaninsu da wani salo da ya sanyata dauke wuta.

Qugunta ya riqo da kyau sanda qafafunta suka soma rawa,ya matso da ita jikinsa sosai yana sanya hannunsa ya zare hannuwanta dake riqe da gaban rigar,sannan a hankali ya hada tafin hannunsa da ainihin fatarta mai santsi da laushi ya fara zame rigar gaba daya daga jikinta.

Qanqameshi tayi da kyau don hana faruwar hakan,ta tabbatar idan ya samu nasarar rabata da rigar komai zai iya faruwa,don babu wani abu daya rage a jikinta sai ita,cikin rarrabewar numfashi da yadda laushin fatarta ke shirin zautar dashi ya dora bakinsa saman kunnenta

“Don’t scare,baccin gajiya kawai nazo muyi” sake qanqameshi tayi tsigar jikinta na tashi,bakinta na rawa tace

“Ammm…..bar…..bari na saka riga” dago fuskarta yayi da kyau yana duban tsakiyar idanuwanta da idanunsa da suka soma kaduwa,kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace

“Waye ya gaya miki saka riga ya halatta a irin wannan lokacin?,this is unfair….kamar ha’inci ne fa?,ya zaki lullubemin abun rufar da babu kamarsa a duniya da wata suturar da bata kama qafarsa daraja ba?” Ya fada cikin wani irin shauqi da baisan gana bayyana ba,ya kuma juye mata dukka nauyin maganganun hade da nauyin qwayar idanuwansa,gaba daya jikinta sai ya saki,ta runtse idanuwanta,tana sauraren yadda yake rabata da rigar gaba daya,sannan ya dauketa kai tsaye zuwa kan gadon bayan ya sauke dukka labulen dakin ya kuma rage hasken qwayayen dake ciki,sai dakin ya bada wani ni’imtaccen yanayi.

Sosai ya manne fatar jikinsu waje daya,ya boyeta cikin faffadan qirjinsa,kusan tare suka saki ajiyar zuciya,ya sanya hannunsa saman kanta a hankali yana shafar sumarta,idanunsa a rufe yana jin bugun zuciyarta,kana daga bisani kuma yaji ya sauya,alamun dake nuna bacci ya dauketa,hannunsa ya dauke daga saman kan nata,ya jata jikinsa sosai yana jin kamar ya bude qirjinsa ya sakata a ciki,babu jimawa shima wani daddadan bacci yayi awon gaba dashi.

*Arewabooks:Huguma*

#gurbin ido

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K’ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply