Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 76


Gurbin Ido 76
Viral

76

A hankali ta rufe bangon littafin dake gabanta gami da sauke ajiyar zuciya,zuciyarta na wani irin karyewa da kuma samun rauni,a hankali ta zubawa wajen da afra suke zaune suna hira kallo,tun dazun suka ce mata ta bar karatun tazo tayi joining dinsu amma taqi,saboda bata da wani karsashi ko farincikin hirar,tunda ta dawo sati biyu cikin na uku zuciyarta a quntace take,ba wani walwala ko farinciki.

Wayarta ta zaro ta sake kallon fuskar wayar,cikin sarewa da gajiyawa ta dora wayar saman table din data aje littafin nata sannan ta zame ta kwantar da fuskarta saman table din,daga dawowarta zuwa yau batasan sau nawa ta duba fuskar wayarta ba,haka kawai taji tana tsimayin kira daga gareshi,saidai ko sau daya bai kirata din ba,tana ta sanya rai taji ance tazo gashi,duk da tasan ba bari ake azo ganin naka ba idan bada wani babban uzuri ko dalili ba,amma tata zuciyar nata shauqin jin hakan,saidai shuru,lumshe idanunta tayi tana jin yadda zuciyarta ke tabuwa,ba zata taba kiransa ko sau daya ba,sabida tayi alqawarin jan ajinta da mutuncinta,zata kuma cika burin anni in sha Allah

“Maimoon,lafiya?,me ya sameki?” Taji muryar afra saman kanta,sai ta bude idanunta da kyau a kan fuskar afran

“Me kike gani?”

“Kuka…..hawaye fa kike?” Bata yarda da zancan afra ba sai data sanya hannu ta shafi fuskar tata sannan taji danshinsu,abinda ya sake sanya zuciyarta karyewa,kawai sai ta saki kukanta sosai tana kifa kanta a table din.

Da sauri afrah taja kujera dab da ita ta zauna tana fadin

“Innalillahi,wai menene yake damunki maimoon?,meye matsalar?” Bata bata amsa ba,sai kawai tasa hannu ta zare wayarta dake gefe,tasan me zatayi mata.

Contact ta shiga ta fara laluben sunayen soyayya data sama wata contact,saidai babu ko daya a ciki data gani,haka ta haqura,ta sanya ainihin sunansa saiga number din ta fito,kallon maimunatu da batasan ma tanayi ba tayi taja qaramin tsaki,wai itakam yaushe zata bude zuciyarta ta yarda soyayya takeyi?,ta kuma gane ita ke wahalar da ita?,kawai saita canza sunan dake kan number zuwa honey bee,sannan kanta tsaye ta danna masa kira.

Dai dai lokacin yana kwance a wajen hutawa daya ware cikin office dinsa,tunda yazo yake zaune a wajen,ya gaza hassala komai,baisan me yake damunsa ba,gaba daya tunda ta tafi ta tafi da walwalarsa,hannunsa daya bisa fuskarsa,sai yaji shigowar kira wayarsa.

Har tayi ringing dinta ta katse bai dauka ba,ta sake shigowa ta kuma katsewa,ya shareta yana ci gaba da kwanciyarsa,har sai da yaji qishirwa,sannan ya miqe zaune ya jawo wayar yana son duba lokaci,don da wuri zai fita daga company din yau,saboda ya lura bazai iya aikata wani abun kirki ba.

Ganin miscall da number ta yasa ya tashi ya zauna sosai,bai zaci wayarsu na amfani ba a school,daga sama kuna tex ne

_ka kira pls yaa ja’afar,qawar maimoon ce_

Bai gama karantawa ba ya fita a saqon ya kira number din,yana jin yadda zuciyarsa ta tafi gaba daya ta kuma afu gason jin muryarta.

Da sauri afra ta duba kiran sannan ta dan matsa gefe kadan daga inda maimunatu ke zaune ta daga

“What’s happening?” Ya tambaya kai tsaye,jin ba muryar maimunatun bace

“Kuka dai takeyi,na tambayeta taqi magana”

“Bata wayar” ya fada cikin jin wani tashin hankali yana shigarsa,meye ya sameta?,itace tambayar daya fara yiwa kansa.

“Yaa ja’afar ne” ta rada mata a hankali,kafin ta gama fuskantarta har ta nana mata wayar a kunne

“Angel” ya furta cikin wani irin taushi,da zuzzurfar muryarsa data aike mata da wasu saqonni lungu da saqo na jikinta karo daya,wani nauyi taji zuciyarta tayi,hawayenta kuma ya dauke cak,ta zuqi numfashi sosai tanason fesarwa amma kamar ya riqe

“Hello…..angel,my moon” ya sake fada very softly,wannan karon fidda numfashin tayi gaba daya,wanda ya zame mata kamar ajiyar zuciya mai sauti,batasan sanda tasa hannu ta dafe wayar sosai a kunnenta ba,har yanzu idanuwanta suna rufe tana sauraren saukar numfashin sa daga cikin wayar,da alama shima ta taba zuciyarsa sosai

“Say something mana angel,bazan iya jurewa ba,meye ya faru?”

“Zazzabi” ta fada muryarta a mugun narke,kuka mara sauti me dauke da hawaye yana kubce mata

“Ya salam……jirani gani nan zuwa” ya fada yana katse wayar gaba daya.

A gaggauce ya maida takalminsa ya kira PA yayi cigiyar key din motarsa,ya karba ya fice ba tare daya tsaya sauraren kowa ko kuma meeting dake gabansa awa daya mai zuwa ba.

Kasa motsawa tayi daga wajen,sai kunnuwanta suka shiga maimaito mata abinda yace

“Ta jirashi gashinan?,da gaske zuwan zaiyi??” Zuciyarta dai ta cika da wasi wasi,amma duk da haka sai tayi likimo taci gaba da kwanciya a wajen,har zuwa sanda ta tsinci muryar afra na kiranta irin kiran gaggawa,idanuwa kawai ta bude tana jiran isowarta

“Ana kiranki office din principal,yaa ja’afar ne yazo” batasan ta miqe da hanzari ba sai data ji kanta ya saara,ta dafe kanta da hannunta sannan ta dubi afra

“Muje ki rakani please” hannunta ta riqe tana murmushi,tanason tsokanarta amma kuma yanayinta yana nuna seriousness dinta kan condition din duk da take ciki,don haka shuru tayi tana taka mata zuwa office din.

A nutse tayi sallama a office din,idanuwanta na kallon qasa,don ta tabbatar indai idanunta a dage suke kuma yana cikin office din,tofa lallai idanunsa suna kanta ne,ita kuma a yanzun batajin zata iya dauke idanunsa akanta,bata jin zata iya jurema wannan kallon nasa,qamshinsa kawai ya isa ya bata tabbacin yana cikin office din,taci gaba da takawa a hankali,sai zuciyarta ta gaza jurema rashin kallon fuskarsa,ta yanke shawarar ko satar kallonsa ne tayi.

Ta kuwa aikata hakan,saidai kuma ya kamata,don caraf idanuwansu suka hadu waje daya,yana binta da wani irin mayen kallon da shi kadai yasan fassararsa,gaba daya yaga kamar an sake canza masa ita,ta sake kyau ta sake fresh,saidai tadan faada kadan

“Zaki bishi zakuje ku dawo” principal din ya fada kansa tsaye,tunda yasan waye ja’afar din a wajenta

“Okay sir” ta fada kanta a qasa,sannan ta miqe ta soma takawa a hankali tana ficewa a office din da zummar zuwa dakinsu ta gani idan akwai abinda zata dauko.

A hankali taji an riqo hannunta ta baya a tausashe tana hanyar komawa hostel,da sauri ta waiwayo,tadan razana saboda hanyace da babu masu wucewa sosai a kanta,sannan kuma batasan ana biye da ita ba.

Idanuwansu suka sarqe waje guda,kowanne ya jefi dan uwansa da wani abu mai matuqar tasiri a ruhi da gangar jiki,suka shiga jin kamar zasu narke a wajen saboda abinda ke zagaya zugata da gangar jikinsu,sukaci gaba kuma da kallon junansu kamar an manne idanuwan nasu cikin na juna ne,bata ankara ba ba zato taji ya fusgeta zuwa cikin jikinsa da wani irin zafi,har takalmin qafarta yana zamewa daga qafartata.

Sosai ya riqeta a jikinsa saidai kuma cikin taushi,baiyi wata wata ba ya kama fuskarta da kyau ya riqe gam,ya fara sauke mata kisses,tare da lashe labbanta da yayi matuqar missing dinsu kamar hauka.

Gaba daya ya kunce mata noti,jikinta ya dauki rawa,tanata qoqarin tureshi amma yafi qarfinta nesa ba kusa ba,sai da dabara tazo mata,ta kama labbansa ta ciza da dan qarfi,sannan ya saketa ya d’an ja da baya yana fadin

“Wash Allah na amma na” a wahalce kamar wanda aka yiwa duka aka galabaitar dashi.

Da rinannu idanuwansa yake kallonta,yayi da ita kuma dariya taso kubce mata jin kiran sunan amma da yayi kamar wani qaramin yaro,amma saita danne,ya rigata magantuwa

“Wannan fa mugunta ce,so kike ki.kasheni ko?,tunda kika shigo kinqi kallona,sannan kuma kin fito kin barni ni daya irin baki damu dani ba ko?,kuma yanzun ina welcoming naki saiki cijemin labba?” Ya fada yana taba leban nasa da zara zaran yatsunsa guda biyu.

Bakinta tadan rufe tana fidda fararen idanuwanta waje,wanda hakan ya qara fidda girmansu

“Bafa haka bane,ban wani cijeka sosai ba,nan din hanya ce,wani yana iya zuwa wucewa” sauke yatsun nasa yayi yana ci gaba da jifanta da mayataccen kallonsa,sai ya fara takowa yana fadi a hankali

“I don’t care ni ko waye zai ganmu,ni ke kadai nake gani idanuwana da zuciyata gaba daya,kuma zakisan kin cijeni,you will pay” ya qarasa maganar yana riskarta gami da surarta gaba daya cikin hannuwansa.

Bugun zuciyarta ya qaru,tsoro ya cikata,kada a ganta fa mutuncinta ya zube,tunda ba kowa bane yasan alaqarsu ba,shi bayajin kunya ne

“Don Allah……don Allah,ja saukeni,akwai abinda zan dauko a daki”

“Bana buqatar komai,ke kadai nake buqata”

“To zan iya qarasa mota da kaina”

“Banaso shima,jikinki akwai dan dumi amma ba mai yawa ba” runtse idanunta kawai tayi sosai,ta buda suit dinsa ta saman ta cusa kanta a ciki tana jin tsoro da fargabar wanda zai iya ganinsu a haka,cikin taimakon Allah har suka kai bakin motar basu gamu da kowa ba,dama yammace,kuma hanyar bata jama’a bace.

“Sauka to madam karki hadiyeni,irin wannan riqon haka?” Ya fada yana duban fuskarta murmushi na qwacewa miskilar fuskarsa,wani zillo.tayi ta sauka jin fassarar da yayi mata,gefe guda kuma zuciyarta ta cika da mamakin dama.yana raha da tsokana irin haka?.

Da kansa ya bude mata motar ta shiga,ya tattara mata hijab dinta daya fito zuwa ciki ya rufe mata,sannan ya zagaya seat dinsa yana jin zuciyarsa wasai,duk wani nauyi da tayi ya nemeshi ya rasa cikin qanqanin lokaci,yayin da itama ta langabar da kanta a kafada tana kallonsa sanda yake zagayowa ta gaban motar zuwa seat dinsa

“Ya Allah,yashe ta fara sonsa har haka ne?” Saita lumshe idanunta itama sirritaccen murmushi yana kubce mata.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply