Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 84


Gurbin Ido 84
Viral

84

Kallon kallo suka yiwa juna na wasu daqiqu kafin hajiya Aayah ta janye idanunta,ta sake tabbatar da izzar sa da kuma jin kan da akace yana dashi,ta sani,jinin gidan marwan akko ne,kuma jikoki ga maryam farouq kumo,ta wani fannin kuma shi din jinin sarautar wani yanki ne na qasar gombe daya gada daga kakansa mahaifin aishatu mahaifiyarsa,bai tsintsa a qasa ba

“Sai yau suka turo ka ka maidata kenan?……” Ta fada tana dubansa kai tsaye cike da burin nuna nasa martaba da darajae diyarta,daure masa kai maganar tayi,kafin yace wani abu duk da baida niyyar tofawar ta sake magantuwa

“Wato ga mara galihu wadda aka gaji da ita aka baka sadakarta,kq koromin diya gida babu abinda ta aikata maka,bayan ka jingineta cikin gidanka ba sid’i ba sad’ad’a…..lallai munubiya tayi gaskiya,duk sai yanzu zancanta ke bayyana sosai,na yarda nayi sake dana bar unaisa tabi zabin ranta……to wai shin ma kai ke aurenta ko wadan can tsofaffin da ka baro a gida?” Kai tsaye ya qanqance idanuwansa cikin nata yana dubanta,mai takeson fada?,martaba da muhibbar mahaifansa take shirin tabawa ko kuwa yaya

“To bari kaji,ina raye unaisa ba zatayi zaman boranci ba,yanda suka rayu ba wanda ya takura musu haka ‘yata zata rayu,kaje ka gaya musu,indai sun shirya zama da diyata dole su martaba ta su kimantata su kuma daukaka darajar ta,don ita din me daraja ce,indai kanason zamanka da ita dole kasan darajar ta da kimarta”

“Idan kuma akaqi fa?” Ya fada yana jin wani abu na tsaye masa a wuya saboda taba masa ababen da duk duniya bashi da kamarsu,cikin mamaki take kallonsa

“Saika sawwaqe ma diyata,tunda dai aisha ko maryama ne suka haifamin ita ba” gam ya runtse idanunsa,tabbas da haduwar hanya sukayi da matar nan ba abbi bane sila sai ya nuna mata zallar kuskure da kuma wautar data tafka yau din.

Da gudu kuma cikin kuka unaisa data gaza gamsuwa da tahowa mommyn nata ita daya,ta biyo bayanta ta kuma labe tana sauraren abinda ke afkuwa ta afko dakin cikin kuka

“Haba mommy…….ya zakice haka?” Da mamaki take kallonta

“Ai biyoni kikayi?,to idan bance haka ba me zance,shashasha kin tsaya kamarki namiji na wahal dake kamar shine autan maza,to indai bazai sanyaki a gaban kowacce diya mace ba ciki harda uwarsa wallahi bazan bari kici gaba da zama dashi ba,don ke din mai daraja ce” idanu ya zubawa unaisan yana son hango darajar da hajiya Aayah ke magana akanta tattare da unaisa,hala bata da masaniyar komai,darajar daya tabbatar babu ita sam,amma zai basu assignment mai wahala,zai kuma bar musu tabo,ya zaro hannunsa dake dunqule a aljihunsa,wanda sai sannan yaji saman receipt din da aka basu a wancan eatery din ya dora,ya maida hannunsa ya zaro reciept din tare da ciro wani irin biro mai hade da pen perfume.

Yana dora hannunsa saman takardar unaisa ta saki mommyn ta taho da sassarfa tana isowa gareshi

“Don Allah kada ka aikata,zan zauna zan kuma zama duk yadda kakeson gani na,wallahi mommy laifina ne,nice nayi masa laifi,ni na jawo yacemin na taho” ta fada cikin kuka gami da dana sanin gayawa haj Aayah duka magangun da haj munubiya ta kitsa mata,hadi da janyo hajiyar tazo har gida ta sake tsarawa mommyn tata zance,duk tayi hakane don a sake azawa ja’afar rashin gaskiya,a kuma yi masa kaca kaca a nuna masa martabarta,ta yadda zai riqeta da kyau,kuma kowa a gidan ya shiga hankalinsa,yasan ita din ba abar banza bace.

“It’s too late” ya fada a ransa,bai gama ayyanawa ba haj Aayah ta dakawa unaisan tsawa

“Kika sake kika isa gabansa ko kika sake furta wani abu sai na tsine miki albarka,nono na kuma da kikasha ban yafe miki ba,ya sakekin,da ana aure kafin a gama idda zakiyi aure”.

A nutse ya rubuta mata saki uku kyawawa,ya tura kardar gefe,sannan ya maida abun rubutun aljihunsa,har yayi taku biyu ya dakata

“Ko gobe kikeso zaki iya daura mata aure,don ban dora mata idda ba,amma ban sani ba ko tana buqatar yin istibra’i,saiki tambayeta”

“Istibra’i ba idda ba?” Hajiya Aayah ta fada tana maida dubanta ga unaisa dake riqe da takardar baqinciki kamar zai kasheta,wadda sai dafa fara duba bayanta dake dauke da sunan maimunatu abincin da taci da kudin daya kashe na abinda suka biya,da yake haka tsarin reciept din nasu yake,har yaushe maimunatu diyar ruga baqauyar bafulatana qanwar cikinta ta samu wannan matsayin a wajensa?,gashi ita ta buge da saki sakinma na wulaqanci har guda uku?.

Cikin mota ya dinga sauke ajiyar zuciya,har ransa yaji babu dadi karon farko kuma tausayin unaisa ya ratsashi,saidai ci gaba da zama da ita abune da bazaiyiwu ba,inda batazo da alfasha ba,bata kuma dauki maganganu ba da zai iya haquri taci darajar soyayyar da take masa,a hakan ma sai idan ta yarda zata zauna dashi din,saboda yasan kansa da zuciyarsa,wani mahaukacin so ko qi garesu,wanda shi kansa baisan ta yadda zai canza kansa ba,indai zasu zauna tarenma cutuwa zatayi,bazai taba iya adalci ba,shi yasa ya yima kansa alqawari,indai ba wata babbar lalura ba ba abinda zai sashi zama da mata biyu,kamar yadda alqur’ani ya bawa maza shawara ga wanda yasan bazaiyi adalci ba,shima zai aikata hakan ne don gujewa azabar Allah ranar gobe qiyama.

Kai tsaye ya karya kan motar tasa zuwa unguwarsu,ya duba lokaci qarfe tara na dare,ya tabbatar abbi yana gida,gwara yakai.kansa da kansa,ya kuma shaida masa abinda yayi da kansa,duk hukuncin da abbin zai yanke masa ya yanke masa.

Tun a gate ya hadu da khadim,ya kuma gaya masa abbin yana ciki wajen anni,don haka ya bude murfin motar ya doshi sassan anni kai tsaye,ko kadan baya jin wata fargaba,yana da wannan tsaiwar tun quruciya,yana da juriyar karba da fuskantar hukunci,kuma a duk sanda yayi irin wannan din zaiyi wuya idan ba shine ke da gaskiya ba.

Da fari anni ta tsorata,ta dauka wani abune ya faru ganinsa qarfe tara na dare,sannan yanayin fuskarsa ba cikin walwala yake ba,kai tsaye ya zube gaban dr marwan

“Abbi……kayi haquri ka yafemin,nasan na maka na dai dai ba,na saki unaisa saki uku,gani a gabanka,kayimin duk irin hukuncin da kaga ya dace dani” duk da anni taji maganar wani iri,amma kuma batayi mamaki ba,tasan dama za’a rina,manya ne fa?,wanda zuciyarsa ke tsaiwa kan abu daya

“Innalillahi wainna ilahi raji’un” abbi ya fada,sannan ya dubeshi

“Mai ya kaika aikata irin wannan mummunan aikin ja’afar,abgadul halalu ilallah fa?” Fada sosai abbin ya rufeshi dashi, duk da yasan komai,amma bai nuna goyon baya ba

“Ya isa marwanu” anni ta dakatar da abbi,don batason fadan da yaketa faman yi,

“Kayi gaggawa manya,baka kuma kyauta ba,nan gaba koda wasa billhuwallazi karka ce zaka kwata,koda mummunan kallo kuwa” can qasan ransa dariya ta kamashi,yasan jirwaye mai kamar wanka take masa,kashedi kan maimunatun ta take bashi a fakaice,batasan a yadda yakejin maimunatu a ransa ba,zai iya sadaukar mata da rayuwarsa bama

“In sha Allah,a yafemin”

“Tashi kaje,Allah ya kiyaye gaba” anni ta fada,sai yaji wani abu mai sanyi yana saukar masa,kamar kuma an zare masa qaya,qaunar anni da martabarta na qaruwa a ransa,haka ya miqe ya fice yana yiwa Allah godiya da komai yazo masa da sauqi.

“Marwanu” anni ta kirashi bayan fitar ja’afar daga falon,ganin yadda yayi shuru yana nazari

“Na’am anni”

“Kada ka saka wata damuwa a ranka,duk da baka gayan ba nima nayi bincike akan yarinyar,kwata kwata ba kinin manya bace,kuma kaima ka sani ka boye ne kawai,to Allah ya dubi zuciyarsa,baida hakkin diyar kowa ya rabashi da aurenta,saboda haka kada ka wani damu,Allah yasa hakane yafi alkhairi” kai ya jinjina

“Tabbas anni,ni kaina na sani,amma minister yana da kima a idanuna,hakanan shi din na gari ne,bansan me zance masa ba,wanne bayani zanyi masa”

“Allah zai duba zuciyoyinmu ya kawo.mafita” da wannan suka rufe zancan sukaci gaba da lissafin nisabin zakkar da anni zata fidda a shekarar cikin dukiyarta data mallaka.

Washegari abbin yana zaune yana duba wani babban littafin fiqhu bidaayatul mujtahid wayarsa tayi tsuwwa,ya duba yaga minister ne,sai yaji nauyin dagawa

“Subhanallah,dan yau,dan yau sai addu’a” ya fada,har wayar ta katse bai samu qwarin gwiwar dagawa ba,sai kuma yaga gwara ya kirashi da kansa,don haka yaja wayar yabi kiran.

Bugu daya ya daga,yadda suka saba faran faran suka gaisa,saidai muryarsa sam babu karsashi,wannan ya tabbatarwa abbi akwai damuwa

“Ni naso na fara kiranka,kunya da nauyi suka hanani”

“Wallahi kada kaji komai doctor,kai ya kamata na bawa haquri,bansan haka diyata take ba na dauketa na bawa tsakakakken danka ba,abinda yaron ka ya aikata kuma shine dai dai,Allah yayi masa albarka,dama lalatacciya sai lalatacce,tsarkakakku sai tsarkakakke haka qur’ani ya fada” cikin rashin jin dadi abbi yace

“Subhanallah,wanne irin zance kake haka yallabai?,ka daina fada bai kamata ba”

“Dole na fada haka doctor,ace matar aure sa bin wani yaro zuwa dubai kwana da kwanaki?,ko sanda zasu dubai din su duka munafuntata sukayi akace an gayawa mijinta shi ya amince,ashe satar hanya tayi,ta kuma sake komawa a randa suka dawo din ba tare da sanin kowa ba ita da yaron,nima ina da laifi da giyar mulki ta rudeni na sakar musu daula suke zabar dukka qasar da sukaso karatu ko zama,duk da cewa yaran daya dakin aiba haka suke ba,kaga naga izina naga ishara ko?,ni banga laifin ja’afar ko in zargeshi ba ko kadan,ita kanta jiya ta fadi komai da bakinta,tsahon zamanta a gidan bai wulaqantata ba,bata rasa ci sha ko suttura ba, kulawar auratayya kuma tun kafin ta aminta da aurensa akayi mata bayanin sai tayi haquri ta koya masa sonsa ta jashi a jikinta,tunda kowa yasan matsalarsa,ta amince da hakan,ta yarda ko shekara nawa ne zata iya zama,kuma ya bata zabi tunda ya fuskanci ba zata iya jurewa zama dashi ba,duka ta fada,yanzu abokiyar zamanta ta tsinci kanta a wannan halin?”

“Ya salam,ya Allah, jarrabawa ce yallabai,ka daina fadan magangun da zasu sake munana abun” maganganun masu kwantar da hankali abbi yayi masa kafin daga bisani suyi sallama bayan sunyi dogayen maganganu,abbi ya ajjiye wayar tare da littafin hannunsa a gefe,sai yaji shima gaba daya hankalinsa ya karkata ga aurar da yaransa dake gabansa,sai yanzu yake sake ganin gaskiyar anni data tashi hankali kan a aurar dasu,duk da baya shayi ko shakkar tarbiyya ko daya daga cikinsu,dai dai gwargwado ya tsare yi musu addu’a da tarbiyya bakin gwargwado,yana musu kyakkyawan zato.

*BAYAN WATA BAKWAI*

Yammaci ne dake dauke da wani lullumi saboda haduwar hadari a garin,dai dai lokacin cikin private hospital din dake government house road din,dakin dake dauke da sunan amenity one,daga doguwar qawatacciyar varender data qunshi dakunan,tun daga amenity one zuwa four da asibitin ke dashi kana iya jin tashin hayaniya sama sama daga dakin.

Idan ka samu nasarar sanya kanka cikin dakin,zaka hangi mutane zaune cikin dakin,dukkan wanda ka kalli fuskarsa a cikinsu zai bayyana maka zallar farincikin dake kwance tun daga saman fuskarsa tasa har zuwa zuciyoyi.

Anni ammi anty maama,hajja su laila gaba dayansu harda matan kawun nan maimunatu guda hudu,a hannuwan laila da salma fararen shawula ne dake dauke da wasu kyawawan baby boys a ciki,wadanda dukka wanda ya kallesu bazaya so dauke idanuwansa daga kansu ba,wani irin kyau suka dauko daga uwa da uba suka cakude,duka duka basu haura awa guda da zuwansu duniya ba,saidai soyayyar dake kewaye dasu mai tarin yawa ce.

A hankali qofar toilet din ta bude, maimunatu ce tare da umma sa’adah,gefe kuma afrah ce,suna riqe da ita a hannu tana takawa a hankali,sai kuma duka hankula sukayi kansu,kowa yana zabga mata sannu

“Anya maimunatu ba zaki bar kukan nan haka ba?,ko babies dinne bakiso?” Hajja ta fada tana kama baki,dubanta umma sa’adah tayi

“Daadarta take tunawa,wai dama haka tasha wahala ta haifeta?,ta sake shan wahala.bata haifa abinda ke cikinta ba ta rasu?” Kowa saida jikinsa yayi sanyi,suka fara bata baki cikin nuna kulawa.

A mugun sukwane motocin guda biyu suka dira farfajiyar asibitin,motar farko bata ko kai ga kammala tsaiwa ba aka bude murfinta aka sauko da wani irin kuzari hanzari da kuma sassarfa.

Captain ja’afar ne,sanye da wani farin kaftan da aka qawata shi da dimki na musamman,tamkar yana da masaniyar yau din rana ce ta musamman a rayuwarsa,biye dashi kuwa manyan ma’aikatansa ne,don ya baro company ne babu shiri.

Dukka baya suka rufa masa,jabir ya qara hanzari ya cimmasa

“Relax mana captain,ance lafiya qalau fa ta sauka”

“I know dude,na qagu na ganta ne” ya fada yana sake qara hanzarinsa harda sassarfa.

Daga baya dukka suka tsaya,banda jabir da yaci gaba da binsa har suka isa bakin qofar, ja’afar dinne a gaba,don haka yana bude qofar hankalin kowa yayi kanshi,yayin da shi kuma idanunsa gaba daya suke kan maimunatunshi dake zaune saman gado,umma sa’adah na qoqarin bata tea tasha ko za’a samu ruwan nono ya samu,don yaran sun fara qananun rigingimu.

Suna hada idanu sabbin qwalla suka cika mata idanu,abubuwa ne mabanbanta cikin zuciyarta,farinciki takeji mara misaltuwa da a yau ta bawa ja’afar din muradin ransa wato ‘ya’ya,tunda cikinta ya girma baya cikakken bacci,don ta fishi samun barci me kyau ma,kullum cikin addu’a yake ba dare ba rana,hidima yake mata da jikinsa da aljihunsa,ya qwallafa rai matuqa akan cikin,har ta dinga jin anya ba mutuwa zasuyi ita da yaran ba?,anya itama ba wucewa zatayi yadda daadarta ta rasu ba?,sai gashi komai yazo ya wuce kamar ba’ayi ba.

Abu na biyu zallar shagwaba ne da kuma tuna irin wahalar data sha,yazo yanzu zaa sauke masa nasa rabon da bai samu ba a dazun d tana labor.

Dukka gaidashi suke,yayin da manyan ke masa barka,yana amsa musu amma hankalinsa ya karkata gaba daya a kanta,miqewa sukayi suka fara basu waje,afra da laila suka isa gefan gadon suka ajjiye yaran suma sukabi bayansu.

Shuru dakin ya dauka bayan ficewarsu, hannayensa saye a aljihun rigarsa yana qare musu kallo daga nesa,yana jin komai tamkar a mafarki,idan ya kalleta sai ya maida dubansa ga yaran,duk da baya iya ganin fuskarsu sosai

“Angel” ya kirayi sunanta a tausashe,yana jin wata sabuwar soyayyarta tana ratsa qashi bargo da kuma jijiyar jikinsa,kasa daga kai tayi ta kalleshi,sai ya haqura da kiran saboda yadda yakeji kamar ana fusgarshi zuwa gareta ya soma takawa a hankali,har ya isa bakin gadon,jikinta na gogar gwiwoyinta data zubo qafafunta qasa ta jingina da bangon.

Hannayensa ya sanya ya daga fuskarta da kyau yana kallonta,sai itama ta zube masa idanuwanta da sukayi wani tarwai, tausayinta ya kamashi,yaso ace dukka gwagwarmayar naqudar data sha yana tare da ita,sai gashi ya qunsa mata ciki ya barta da wahala ita kadai
[11/25, 12:59 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply