Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 86


Gurbin Ido 86
Viral

86

*BAYAN WASU SHEKARU*

Babban dakin taro ne wanda ya cika maqil da zallar mata,manya mata masu ji da aji da kuma jin sun kai wani matsayi sun kuma taka mataki na rayuwa.

Daga can step inda mai gabatarwa take,ta qarashe bayaninta da fadin

“We will call our star that we have gathered here to honor her……maimoon abubakar muhammad” ta qarashe kiran da madaukakin sauti.

Shuru dakin taron ya dauka,kowa ya tattara hankalinsa gami da zuba idanuwansa yana jiran ganin bullowarta,wasu sun santa,amma kuma ako da yaushe basu gajiya da ganinta,ita din ta dabance,tun daga yanayin halitta zuwa suttura da kuma yadda tasan mutuncin dressing,idan akace dressing to dressing mai nuna zallar kamala da kuma aji a rayuwa,dai dai da qamshinta na musamman ne,baa maganar sauran abubuwa,wadanda kuma basu santa din ba,zumudi suke suyi tozali da kyakkyawar fuskar da labarinta ya cika kunnuwansu kafin zuwan wannan rana,fuskar data zama ta alkhairi kuma jirgin fito ga duk wani mabuqaci mai neman taimako,fuskar data hadu da qalubale da gagwarmayar rayuwa iri daban daban,amma tayi hobbosa ta tabbatar bata koma baya ba.

Cikin nutsuwa sautun takalman qafarta dake da tsinin dunduniya maras tsaho suka ratsowa ta cikin mutane,sai ta dauki hankulan mutane da dama nima na juya don ganin tahowar tata.

Kyakkyawar farar bafulatanar usul,mai wani irin haske daya cakude da surkin jaja jaja,tamkar jini zai diga a jikinta saman lallausar fatarta mai santsi da sheqi,wadda ke nuni da zallar hutu wadata da kuma jin dadi,ma’abociyar wani irin kyau mai fusgar hankali da wani irin kwarjini daya cakude da zallar kirki da son jama’a dake saya mata soyayyar mutane duk inda ta tsoma qafarta.

Sanye take da dark blue din wani yadi na mata,wanda aka yiwa ado da light blue da kuma yarfin gold din zare,kalar data sake fitar da kyanta,wani lafiyayyen mayafi ne a jikinta da bashi da shara shara ko kadan mahadin lafiyayyan takalmin qafarta mai madauri,hannayenta kana iya hangen warwaraye masu fashion masu tsadar gaske,wanda zaka tsammaci gold ne,amma ba shi bane,kasancewar sam bata da sha’awar amfani da gold din.

Ci gaba tayi da takowa har ta iso wajen,ta karba abun maganar tana duban fuskar mc din,tata fuskarta dauke da murmushi,sanna ta maida dubanta ga matan dake gabanta,gyara zaman fararen eye glasses din data sanya don qawata adonta tayi,sannan tayi bismillah ta fara magana cikin tataccen turancinta daya cakuda da zazzaqa kuma lallausar muryarta.

Duk wata hayaniya tsaiwa tayi,muryarta tacu gaba da tashi har ta gama ta koma yarenta na fillanci,a nutse ta waiwaya tana miqawa mc din loud speaker din tana dan kare fuskarta da hannunta da yasha jan lalle saboda hasken flashes na kyamarori,karban abun maganar tayi tana kiran sunayen wasu matan manya da sukayi fice wajen bada taimako,suka qaraso wajen suka miqa mata dukka kyaututtukan da aka tanada saboda ita.

Fuskarta dauke da murmushi da kuma hawayen farinciki ta sake karbar abun magana

“Inama mijina yana kusa!” Maganar da taja hankalin kowa a wajen,sai suka maida dubansu gareta,dan qaramin murmushi ta saki

“Eh haka nace,inama mai gidana yana kusa,shi yafi cancanta da ya karba dukka wadan nan karramawar….kunsan dalili?” Kusan hada baki sukayi wajen fadin

“A’ah”

“Saboda da bazarsa nake rawa,hakanan shine tsanin dana taka har na zama abinda na zama a yau,da shawarwarinsa taimakonsa da kuma gudunmawarsa nake dukka wasu abubuwan yabawa da kuke gani a yanzu,ina fata a duk inda yake Allah ya karemin shi da kariyarsa ya dawomin dashi gida lafiya don sirrin hasbunallahu wani’imal wakil” kabbara duka matan suka saki,dai dai da sanda ja’afar ya lumshe idanunsa yana lafewa a bayan mota,live yake kallon yadda taron ke gudana,da taimakon d’ansa as’ad dake dauko masa komai ta wayar hannu video call ta watsapp.

Sai yaji.kamar lokaci yaqi gudu,awa hudun da zaiyi kafin jirgi ya saukeshi a nigeria saita koma masa kamar shekaru hudu,wani kewar matar tasa ta dinga ninkuwa cikin ransa,shikam da dan adam yana kyautar aljanna a duniya,tabbas da ya yiwa maimunatu kyautarta tun a nan halak malak,baisan wanne irin so take gwada masa ba sa kullum qara gaba yake.maimakon yayi baya,baisan wacce irin kulawa bace wannan tamkar jariri sabon haihuwa.

Duk yadda mutane suka kai ga tsareta suna son gaisawa da ita,wasu suna daukan hoto da ita hankalinta yana kan lokaci,duk bayan mintuna sai ta duba agogo,yau rana ce mai.muhimmanci a wajenta,kuma lokacinta mai tsada ne a yau din,saboda ja’afar zai dawo daga tafiyar da yayi,bayan ya kwashe wata guda baya nan,normally koda office yaje ya dawo bata wasa da bashi kulawa,koda kuwa tare da waye take,zata katse komai ta bashi hankalinta tunaninta jikinta dama lokacinta,takan ce shine kadai dan abinda zata iya masa,tunda ta fuskanci a duniya abinda yafiso kenan,ya jita ko yaushe a kusa dashi,koda zama tayi masa hira ne ya wadatar.

PA dinta taja gefe ta kuma yi mata bayanin uzurin da take dashi,da qyar ta samu ta sulale ta qofar baya ta samu ta fice inda driver yake kiranta,sauke wayar dake hannunsa as’ad yayi yana duban fuskar mahaifinsa ta cikin screen din wayar yana murmushi

“Abyy…..ummu ta gudu fa” murmushi ne ya subucewa masa yana gyada kai,yasan ta gudu ne saboda shi,a duk sanda yace mata gashi a hanya zuwa gida…..kome takeyi hankalinta yabar kansa ya koma gidan,har sai ta tabbatar ta samar masa da duk abinda zai iya nema ko buqata

“Kace ina mata sannu tare da ban gajiya kafin na iso”

“Zataji abby….amma abyy,pls saqona fa?,baka manta ba?” Kai ya gyada

“Ina sane ranka ya dade✊🏽” ya fada yana dunqule hannunsa

“Thank you aby” ya fada yana dariya gami da kashe wayar,ya kuma fella yana bin bayan mahaifiyarsa da sauri.

Daga nesan farfajiyar wajen take iya hangensu,gajee ce goye da nasma tana riqe da hannun nasim tana musu ‘yar tsere,fuskarta dauke da dariya sosai,dukkan alamu sun nuna tana jin dadin kasancewa da yaran.

Daga gefe kuma saman kujerun da aka tanada a farfajiyar dai,sa’ad ne zaune riqe da tab dinsa shi daya yana faman dannawa,kamar mahaifinsa,shi ko da yaushe ba mai hayaniya bane,hakanan ba mai son damu bane,yafi ganewa zaman shuru,rashin son hayaniyarsa ya sanyashi baro hall din,ya gwammace surutai da maganganunsu nasim akan qarar amsa kuwwar hall din.

Daga gefe asim ne yake musu tafi yana biye da waqar da gajee keyi musu,shikam kusan halinsu daya da as’ad din,ba ruwansa,dan wasa ne,ya dauko kawunsa uncle JB kamar yadda suke ce masa.

Idanuwanta ta maida kan gajee,gaba daya ta canza shekaru biyar kenan da suka shude,tun bayan mutuwar inna furera wadda ta rasu saboda lalacewar qodarta guda daya data tabu,dayar kuma an yanke an dauke,bayan ta rasun gajee data auri saurayin ta bayan ta gama zuba rashin kunya da diban albarka kan shi takeso,wata biyu kacal ya ajjiye mata saki cikin dare suka kada shanunsu suka qara gaba,haka ta dawo gida cike da nadama da darasin rayuwa,rasuwar inna furera ta sanyata tattara ya nata ya nata ta koma gembu,saboda tana ganin babanta bazai yarda ta zauna dashi ba,tuni ya qara aurensa,kuma amaryarsa ta riqe laulo da kyau,tunda dama matsalarsa kadance,kuma zuwanta sai yasa yaron ya daidaita,bayan ta koma wajen inno mahaifiyar furera wadda tuni ta makance sai zaman yaqi yiwuwa,kaf ‘yan uwan furera da suka fito ciki daya aka rasa me riqeta,hakanan ta dawo gidansu.

Da farko.jauro yace bazai zauna da ita ba,amma amaryarsa ta tsaya tsayin daka kan nan din gidan uban gajee ne,bata da inda yafi nan,haka ya haqura,dama kuma shima ba yayi hakane don tauna tsakuwa don aya taji tsoro.

Zamansu lafiya lau,gaba daya gajee ta canza,saidai tun dawowarta babu wanda ya nuna sha’awar aurenta,don kowa yasan yadda abubuwa suka kaya,har wasu na mata qazafin cuta mai karya garkuwar jiki,tayi kuka ta sake dadawa,ta kuma ji yadda sharri da qazafi yake,ashe haka maimunatu keji duk sanda suka jefeta da kalmar mayya?,ko barauniya?.

Lokacin da maimunatu tazo garin yiwa yuuma ta’aziyyar rasuwar baffa labaran taga gaaje sai taji hankalinta ya gaza kwanciya,zuciyarta kuma ta kasa samun nutsuwa,daga bisani tabi shawarar da wani gefen na zuciyarta take bata,domin cikar dan adam ya zamana me yafiya,saidai ba lallai ne ko kuma tilas zuciya ta manta nau’in azaba ko cutarwar da wani dan adam yayi mata.

Kasa tsaiwa ta saurareta gaaje tayi,saboda tsananin kunya nadama da kuma dana sani,sai data saka akayi mata tara tara,sannan ta tsaya ta saurareta cikin matsanancin kuka

“Bazan iya hada muhalli dake ba maimunatu,iya girman cutarwar da mukayi da yafiyar da kika mana ma kawai ta isa,kiyi tafiyarki kici gaba da rayuwarki cikin farinciki,ki barni naci gaba da karbar sakamakon abinda na shuka” maganar gaaje ta sake karyar mata da gwiwa,sai taji hawaye kawai yana sauko mata,meye rana ko ribar cutar da dan adam?,indai kyautatawa riba ce ga rayuwa tabbas zata kyautatama gaje,baa saka sharri da sharri,da wannan tayi magana da jauro,wanda shima da farko yace ta barta kawai a haka har Alllah ya sake fidda mata miji,saidai daga baya titi matar daya aura ta saka baki gaaje ta biyo maimunatu,wannan shine asalin zamansu tare,gaba daya rayuwar gaaje ta sauya,idan ka ga yadda ta canza kai baka ce ita bace, maimunatu bata barta da duhun jahilci ba,ta maidata islamiyya ta manya,saida ta sauke ta kuma iya litattafai da dama,wanda wasunsu a wajen maimunatu take daukan karatun,tana musu karatun ne ita dasu as’ad duk dare na litafin hadith da kuma fiqhu,gaajen bata da sha’awar karatun boko sam,don tace iya na addini ya isheta rayuwar duniya,gaba daya ta tashi daga gajen ta koma barira(asalin sunanta),saidai gajen bata bace ba a bakinsu.

Kusan ita ke taya baaba tabawa aikace aikacen gida da rainon yara,duk da maimunatu da baaban sunso hanata amma tace wannan kadai take ganin zatayi ta sakawa maimunatu,ta kuma shafe munanan abubuwan da suka aikata mata ita da innarta wadda har yau nema mata gafara takeyi.

Abu guda ke damun maimunatu,shekara goma sha uku kenan da auren ita maimunatun,amma babu zancan aure wajen gaaje,yanzun haka su asad shekarunsu sha biyu kenan,takanyi murmushi kawai duk sanda aka mata zancan aure.

Ana haka himu ya bayyana a matsayin ma’aiki a qarqashin dr marwan,gaskiyarsa jajircewarsa da riqon amanarsa ya sama masa matsayi wajen dr,randa suka fara haduwa da maimunatu kamar bai taba saninta ba,duk da sun gaisa cikin mutunci,shima yayi aure amma sun rabu da matar sai yaransa guda biyu dake hannun daadarsa,wadda nauyin kulawarta take wuyansa tun bayan rasuwar mahaifinsu baffa labaran.

Yana yawan zuwa saboda yuuma data dawo gidan wajen anni,burin annin kenan na shekara da shekaru sai yanzu Allah yayi sanadin mutuwa,sanin alaqarsa da yuuma ya qara masa matsayi a wajen dr marwan,ya sake jansa a jiki,tare da matsayin da yake samun albashi da kyau.

Kuka sosai daadarsa ta dinga yi sanda taga abinda Allah ya yiwa himunta,ya samu rufin asirin da kai tsaye zaa kirashi da mai kudi a yankinsu,duka ta dalilin yuuma da maimunatu,mutanen da bata kallonsu a baya a matsayin wasu abubuwa masu daraja.

Yuuma ce ta bashi shawarar idan ya gama gininsa ya nema aure,ya kuma dauko daada ta dawo nan,amma kunya tasa daada tace ba zata iya zama kusa dasu ba,batasan da wanne ido zata kalli anni ba,hakan ma da suke ci susha daga alfarmarsu ba tare da sunyi duba da dabi’arta ba godiya take musu.

To shima himun tsoron zabar matar aure yake a yanzun,don baiji dadin aurensa na fari ba,duk da sauqinta zabin daada ne,yuuma dai nata bashi shawari tare da jan hankalinsa akai.

To gaurayen marasa auren nada yawa,cikin ikon Allah hankalin maimunatu afrah da anni ya karkata akan yiwuwar hada yuuma da abbuuun maimunatun aure,suka kuma gabatarwa da abbi wato dr marwan

“Na dade ina qiyasta hakan a raina,saboda dacewa da sukayi da junansu,zan jarraba,Allah yasa a dace,Allah kuma ya sanya alkhairinsa da albarkarsa a ciki”.

Cikin ikon Allah kuwa dukkaninsu suka bada hadin kai,abun ba qaramin dadi ya yiwa su maimunatu ba,hadi kuwa yayi albarka,cikin wata qudurar ubangiji isa tsarki da kuma buwayarsa saiga yuuma da ciki,abunda ya girgiza tunanin kowa,yuuma da ciki?,ita kanta ba qaramin girgiza tayi ba,ta kuma qaryata har sai da laulayi ya kankama

“Allahu akhbar,Allah buwayin sarki,duk zaman nan ashe rabon yana ta wani waje daban yana jiranki ramatu?” Anni ta fada tana qwallar farinciki,ita kanta yuuma kuka ta dinga yi sosai,kafin daga bisani kuma ta dinga jin kunya,takan kalli kanta,taga yadda shekaru suka fara tarar mata amma wai ciki gareta?.

Ta fannin hajja kuwa kamar ta zuba ruwa a qasa tasha

“Allah mun gode maka,ashe abubukar akwai sauran qwanka a duniya” shiko abbu fadin irin farinciki daya samu kansa ma bata baki ne,haka ya dinga bawa yuuma kulawa dai dai da shekarunsu,cikin girma da kulawa,har Allah yasa ta haife abinda yake cikinta ta hanyar CS da akayi mata,aka samu yaro namiji wanda kai tsaye abbuu ya sanya mata sunan mahaifinta ita yuuma din,yace shi ‘yan uwansa sun saka sunan nasa mahaifin,wannan ya isar masa,itakam gwara a bar mata abinda zata dinga tunawa.

 

Ajiyar zuciya maimunatu ta saki,yadda gaaje kewa yaran kawai zai gaya maka zallar shaquwa dake a tsakaninsu,tausayinta yana cikata,shekarunsu sun fara turawa,a qalla yanzun dukkansu suna neman shekara talatin da hudu zuwa da biyar,so ya kamata ace ta ajjiye itama zuri’ar da zata tuna da ita ko bayan ranta.

“Ummeee” nasim wanda ya fara hangota a cikinsu ya fada da qarfi yana wara hannayensa gami da qoqarin gangarowa zuwa wajenta,abinda yaja hankalin sauran kenan,asad ya ajjye tab din hannunsa ya taso a nutse ya karba hand bag dinta yana cewa

“Sannu ummee,amma an gama ko?” Dubansa tayi da murmushi bayan ta duqa ta dauki nasim

“Ka gaji kenan?” Shafa kansa yayi kamar wani babba

“Hayaniya….hadisan da kika kara mana shekaran jiya da daddare naketa qoqarin haddacewa,so gurin ba dadin zama na kasa riqewa” murmushi tayi tana duba hannun nasma dake nuna mata wai ya baci da qasa

“Mun gama sai tafiya gida” ta fada tana sauke dubanta ga gaaje

“Antyn yara,basu barkima kin shiga ciki ba bare kiji duka abinda aka tattauna” murmushi tayi

“Na jiyo wasu abubuwan ta nan…..”

“To Allah yasa mu amfana”

“Ameen ya hayyu ya qayyumu” gaaje ta amsa,sai maimunatun ta fara takawa a hankali tana cewa da as’ad ha hado kan yaran gaba daya anty barira ta huta

“Amma gidan yuuma zamu tafi ko?,kwana biyu bamuje ba” da murmushi maimunatu ta kalleta

“Zaki fake da haka dai ki gudu,aikin saba duk sanda daddy zai dawo a tafiya saiki tarkata kansu ku gudu da sunan ziyara” murmushi tayi mata

“Aiba laifi bane,sai sunfi barinki kin sake kin hadawa daddy hankalinki waje daya” murmushi kawai maimunatu tayi,gaajenta ta canza,ta yadda kullum mamaki take sakeyi.

“Ki bari ya iso,kuyi masa sannu da zuwa,sai na tambayar muku zuwan tunda gobe ba school,an shiga hutun makaranta”

“To shikenan” ta amsawa maimunatun,tana takawa zuwa inda motar ke girke tana jiransu,asad ne kawai a ciki.

lafiyayyar motar suka shige gaba dayansu driver yaja,yaran sunata hirarrakinsu,kowa na fadin sautun daya bawa captain J din,a haka suka dauki hanya.

Sai da suka biya ta wani babban guri,ta karba saqonta a wajen sannan suka isa gida,a gaggaucw ta fita a motar ta barsu da gaajen,yau ko rabiyar fadan da sukanyi sanda zasu fita a mota na “kin takani” bata tsaya bi ta kansu ba, mayafinta ma dashi ta wuce kitchen din.

_ZAFAFA BIYAR_
_ZAFAFA BIYAR_
_ZAFAFA BIYAR_

_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI MASOYA MABIYA, KUMA MAKARANTA ZAFAFA BIYAR…_

_ALBISHIRIN KU… INA MASU JIRAN *COMPLETED DOCUMENTS NA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR DA AKA KAMMALA WANNAN KARON* ?_

_KU MATSO.. DOMIN JIRAN DA KUKE YA KARE… LITTATTAFAN NA ZAFAFA SUN KAMMALU DAGA FARKO ZUWA KARSHE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA…_

_GA MASU TAMBAYA…. ZAFAFAN DAI GA SU KAMAR HAKA_

_*FARHATAL QALB* (NA NANA HAFSAT MSS XOXO) NERA 400_

_*GURBIN IDO* (NA SAFIYYAH HUGUMA)NERA 400_

_*SANADIN LABARINA* (NA HAFSATU RANO)NERA 400_

_*INAYAH _RIBA BIYU* (NA MAMUH GEE)NERA 400_

_*BABU SO* (NA BILLYN ABDULL)NERA 400_

*_DUKA COMPLETED DOCUMENTS DIN AKAN NERA DUBU BIYU 2K (2,000)_*

_YADDA ZAKU BIYA_

_IDAN BANKI NE_

_ACCOUNT NAME: HAFSAT UMAR KABIR_

_ACCOUNT NUMBER: 2270637070_

_BANK NAME : ZENITH BANK_

_SAI KU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902_
[11/25, 4:47 PM] Safiyyatulkiram: _ZAFAFA BIYAR_
_ZAFAFA BIYAR_
_ZAFAFA BIYAR_

_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI MASOYA MABIYA, KUMA MAKARANTA ZAFAFA BIYAR…_

_ALBISHIRIN KU… INA MASU JIRAN *COMPLETED DOCUMENTS NA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR DA AKA KAMMALA WANNAN KARON* ?_

_KU MATSO.. DOMIN JIRAN DA KUKE YA KARE… LITTATTAFAN NA ZAFAFA SUN KAMMALU DAGA FARKO ZUWA KARSHE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA…_

_GA MASU TAMBAYA…. ZAFAFAN DAI GA SU KAMAR HAKA_

_*FARHATAL QALB* (NA NANA HAFSAT MSS XOXO) NERA 400_

_*GURBIN IDO* (NA SAFIYYAH HUGUMA)NERA 400_

_*SANADIN LABARINA* (NA HAFSATU RANO)NERA 400_

_*INAYAH _RIBA BIYU* (NA MAMUH GEE)NERA 400_

_*BABU SO* (NA BILLYN ABDULL)NERA 400_

*_DUKA COMPLETED DOCUMENTS DIN AKAN NERA DUBU BIYU 2K (2,000)_*

_YADDA ZAKU BIYA_

_IDAN BANKI NE_

_ACCOUNT NAME: HAFSAT UMAR KABIR_

_ACCOUNT NUMBER: 2270637070_

_BANK NAME : ZENITH BANK_

_SAI KU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902_

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply