Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 21


Raina Kama Book 1 Page 21
Viral

?2?1?

…….Har safiyar yau jikina sai k’amshin turaren Galadima yakeyi, feena dake kwance kusa dani tace, “Mrs Galadima! k’amshin nan nakufa yayi over”.
Harara Na dalla mata, tareda kai mata bugu ta kauce tana dariya, Bilkeesu ma dariyar takeyi, ta jawo wayarta tana fad’in “jama’a kunma tunamin, bara na duba comments d’in jama’a akan pictures d’in jiya”.
Zumbur natashi zaune ina kallon Bilkeesu, “Bilkeesu kinada kai kuwa? yanzu nan hotunanmu kika mik’ama duniya?”.
Da sauri Ameera tace, “to miye aciki, ai gamma mak’iya masu yad’a hotunan wancan 6atacin har 6utiyarsu Na rawa sugani yanzu kin zama halalinsa, ai wlhy jiya kusan kwana nayi karanta comments d’in jama’a akan pictures d’in, idanma mu bamu turaba wlhy abokansa sun yad’a a kowacce kafar yanar gizo, kuma yarinya harma a news wlhy an nuna, idanma baki saniba live aka nuna komai awasu gidajen tv”.
Hannu na d’ora aka kawai nafashe da kuka saboda bak’inciki, nace “dan ALLAH harda abinda yaymin?”.
“sosaima kuwa”. ‘cewar Ameera’.
Kukana yakuma k’arfi sukuma suka saka dariya harda rik’e ciki sukeyi, nikam wlhy kukan gaske nakeyi basu saniba.
Munubiya ce ta fahimci hakan, saita rungumeni tana k’ok’arin rik’e dariyarta data kasa rik’uwa.
Ahaka aunty salamah tashigo tasamemu, “kai lafiyarku kuna dariya kuma ita tana kuka?.”
Labari suka bata, ita kanta dariyar tayi, “yo miye abin kuka anan, koba komai ai ya nunama duniya yana k’aunarki, ‘yan bak’in ciki kuma yasaka musu ciwon zuciya”.
Kallonta nayi ina shar6ar hawaye, “yanzu nan aunty salamah kema haka zakice? mutum yamin wannan iskancin a bazama duniya sannan kuringa d’aukarsa abin kirki? yanzu dan ALLAH idan su Abba suka ganifa? tunda ance harma gidajen TV aka nuna”.
“kajimin yarinya, yo ina kuma ruwan su Abba, mijinki nefa yanzun, to ai su inna ma duk sun gani agida, haka suma su abban”.
Zumbur nayo tsalle tsakar d’akin hannuna bisa kai nace “galadima ka kasheni wlhy, ka cuceni ALLAH ya isana”.
Dariyarsu k’aruwa tayi, suka shiga yi harda hawaye. yanda kukasan Na bibbigesu haka nakeji.

Aikam yinin ranar ban yarda Na had’a ido da kowaba agidanmu, har lokacin da innarmu suka kiramu sukai mana fad’a itada mama Rabi’a da inna lami.
Munci kuka tamkar zamu k’arar da hawayenmu.
Zuwa la’asar fa anfara shirin kaimu gidajenmu, saifa lokacin hankalina dana Munubiya yakuma tashi sosai, domin abinda ake gudun yazo (rabuwa??, sabo turken wawa).
Muna d’aki nida munubiya kowa zazza6i ya rufeta, yayinda iyayenmu keta k’imtse-kimtse, ita kanta innarmu jikinta yayi sanyi lakwas, saboda ganin abinfa da gaske ake, tafiyar zamuyi mu barta.
Suma sauran amaren kowacce Na d’akin uwarta, wasunsu kam ko’a jikinsu, hankalinu kwance Dan d’okin auren sukeyi su.

Anayin sallar magriba inna lami tazo tasakamu mukayi wanka, ana shiryamu muna kuka, bayan mun saka atanfa iri d’aya da aka bamu da gyale aunty Salamah tafara zazzage mana turarurruka ajiki.
Duk wasu tarkace an had’a manashi kowa a handbag d’insa, sannan aka tarkatamu dukkan mu amaren zuwa falon Abbanmu, dukkan iyayenmu mata suma suka shigo, harda innaro da gwaggo Safiyya.
Nasiha aka shiga mana mai ratsa jiki, mukam sai shar6ar kuka mukeyi mu dukanmu, hakama iyayenmu mata bakowa ya iya yimana nasihar ba. tun ana mana fad’an naji ana rad’e rad’in isowar wasu daga cikin angunan, wani kukan bak’in cikine Yakuma tahomin saboda tuna ni nawa Auren nanda shekara 1 ya k’are.
Rungume innarmu mukayi yayinda akace mufito masu d’aukar amare duk sun iso.
Innarmu Itama kukan takeyi, da gyar aka ciremu daga jikinta, an fara fita dasu fiddausi saboda motocin d’aukarsu duk sungama isowa, nice dai basu isoba.
Suna kuka da komai aka fita dasu, yayinda dangin iyayensu mata kowa tabi tawagar mortar tasu amaryar, danginsu abbanmu kuwa rarrabuwa sukayi, domin su sami zuwa kowanne 6angare suma.
Motocinsu Na fita daga anguwar na gayyar abokan Galadima suka shigo, mitocine a Jere kuma masu yawa, abokan yaa marwan ma dama su suke jira, dan ance dole sai Munubiya tamin rakkiya sannan tunda nice k’arama.

Bushe-bushen algaita yafara tashi anguwar tamu, dukda darene hakan bai hanasu busa kayarsu ba, hakan ya tabbatarma da ‘yan anguwa tawagar gidan sarauta sun iso kenan.
Mata hud’u sun shigo gidanmu tareda kuyangi, Alk’yabba mai azabar k’yau da suka kawo aka sakamin, sannan aunty salamah takuma fesheni da tirare dagani har Munubiya.
Da k’yar aka 6an6aremu daga jikin innarmu, tana kuka munayi, haka aka fita damu k’ofar gida wajen motoci.
Motar datafi kowace tsari da k’yau aka sakamu nida munubiya, sannan inna lami da gwaggo Safiyya suka zauna a gefenmu.
Kuka muke rik’e da hannun juna, har aka Isa damu cikin masarauta.
Mom itace zaune a matsayin Momma uwar Ango kenan, Dan haka aka kaini sashenda take tareda dangin Momma.
Tarba ta mutunci aka mana, irin wadda kowad’anne iyaye suka kai ‘yarsu gidan wani aka mata wannan tarbar hankalinsu zai kwanta sosai.
Su inna lami basu wani dad’eba suka fara mik’ewa, saboda suna son mik’a Munubiya itama.
K’ak’a rak’a k’aka, yanzufa akeyinta, danni da Munubiya mun rik’e hannun juna gamma munk’i saki, anyi lallashin da ban magana amma munk’i, da k’yar aka rabamu muna kuka tamkar ranmu zai Fifa. mun burge jama’a da basu tausayi sosai, sai hotuna ake zuba mana kuwa a wayoyi, (yo gidanne kwanyar da lantarki ko ina????).
Mom tasakani a jikinta tana lallashina da bani hak’uri, bayan fitarsu aka kaini wani d’aki, har lokacin ina shashshekar kuka, su Ayusher duk suna tare dani, basubi Munubiya ba, dan sunsan ita yau yaa Marwan zai shiga daga ciki??????.
Har lokacin mom Na tare dani, zazza6ine mai zafi yarufeni kuwa, amma dukda haka saiga wata mata wai tazo shiryani, Ashe za’ayi Mother’s event ne acikin gidan dakuma wanu Abu dasuke kira wai tarbar amarya a masarautar.
Babu yanda zanyi, haka Na zauna tamin kwalliya Na shirya cikin less lemon green, aka sakamin alk’yabba mai k’yau itama, yanzuma har hular aka sakamin, Dan haka fuskata arufe take, saina sami damar yin kukana hankali a kwance.
Mom da kanta tazo ta kama hannuna muka fita, yayinda kuyangi ke binmu abaya.
Filine aka k’awata da haske, anmasa decoration da kayan sarauta Na kwalliyar gida, anutse kowa yake zaune, babu wata hayaniya sosai, (abinka da lamarin manya to??).
Yaukam Galadima cikin ainahin basarakensa yafito, domin komai Na jikinsa Na sarautane, yasha alk’yabba kalar tawa, sai dai tasa ta maza ce, hard’e yake a zaune bisa wata kujera 2sita, wlhy wanda baima saniba saiya d’auka sarkinne gaba bad’aya, yaci mur fuskarnan d’inke, yasha rawani abin zak’k’yau kamar nabama (gwaurayen group d’ina shi???????).
Gefensa mom ta zaunar dani, tunda aka shigi wajen dani suka d’auki tafi, fuskata a rufe take, ba kallon kowa nakeba, saima hawaye dake cigaba da zirara har yanzun.
Mom tad’an ja hancin Galadima ya murmusa, sannan takamo hannuna tasaka cikin nashi tabar wajen.
K’amshin turarena da nasa ya had’e yabada wani kalar k’amshin Na musamman.
Dukda kukana a hankali nakeyi mara sauti hakan bai hanashi jin ajiyar zuciyar danake saukewa ba, yad’an matsa hannuna dake cikin nasa amma baiyi magana ba, nima sai bance komaiba nacigaba da kukana.

An fara gudanar da addu’oin fatan alkairi da zaman lafiya agaremu, sannan akamin barka da zuwa cikin wannan masarauta mai d’unbin tarihi, Mom takar6a tayi jawabi irina uwar kwarai mai tarin mutunci da kamala. aka shiga tafa mata, saboda taburge kowa.
Hakama aunty Mimi tayi jawabi mai birgewa, sannan mama Fulani tafito cikin tsantsar izzarta da k’asaita tayi welcoming d’ina a wannan family, hakama matan Sarki, saikuma k’annen galadima mata da yayunsa, yayun momma da k’annenta, komai yana tafiyane cikin nutsuwa, nidai ba ganin kowa nakeba, amma ina sarrarensu, har lokacin kuma hannuna yana cikin Na Galadima, yakan d’an murzashi time to time.
Duk Na k’agara a tashi wlhy, dan jikina yayi masifar zafi saboda zazza6i, shikansa Galadima yanajin zafin a hannuna, ganin kamarma ina rawar sanyi saiya kwantoni jikinsa.
Ban musaba, saboda babu abinda nake buk’ata a lokacin kamar kwanciya, ga barci ga ciwo da gajiya.
Bayan angama jawabai da k’yaututtuka da kowa kan bani wad’anda aketa zuwa ana jibgewa a gabanmu aka fara gudanar da liyafar cin abinci kamar yanda komai yake a tsari, sai abinda kakeso za’a kawo maka.
Muma ankawo fruits salad da gasashen kaza da snacks sai drinks da wani abinci dabansan miyeba an ajiye agabanmu.
Da hannu Galadima yayi kiran aunty Mimi, ta k’araso inda muke.
“my k’ani lafiya dai? Ko abincin bai matabane?”.
“no aunty bama abinci baneba, batada lafiya fa, ta6a jikinta kiji”.
Hannu aunty Mimi tasaka a wuyana, tausayi nabata saboda zafin da jikina ya d’auka, “to yaza’ayi yanzu? ko tad’an k’ara hak’uri kad’an tunda naga ankusa tashi, kasan halin mama Fulani, kuna tashi yanzu zata d’aukeshi wani Abu daban, dama wannan d’an kwantar da itan dakayi ajikinka inaji tana maganar bakada kunya wai”.
Guntun tsaki yaja yace “canta matse mata, indan tagadama tacika masarautarnan da surutu, nanda minti 30 inba’a gamaba zamu tashi kawai”.
“karka damu zama’a gama insha ALLAH”.
duk maganar dasukeyi ina jinsu, sai naji tausayin kaina ya kamani, domin nafahimci nanma akwai mai irin halin innaro kenan. Wasu hawaye suka silalomin a kumatu, sauk’i nama auren 1year ne Na kama gabana.
Daga ni har shi babu Wanda yaci wani Abu har aka tashi a taron, lokacin 12pm, yanzuma mom ce takama hannuna muka koma 6angaren da aka fara kaini, muna shiga kwanciya nayi, bayan mom tasakani cire alk’yabbar jikina, duk kunya ta rufeni, ganin haka yasata ajiyemin kayan barci masu kauri ta fita, a hanzarce na shirya na saka hijjab sannan na kwanta, saida ta kintaci time sannan suka shigo itada aunty Mimi da Galadima sai wani ba’indiye, Ashe abokinsa ne dayazo biki, kuma doctor ne.
Galadima ya zauna a bakin gadon kusada kaina, dayake na juya musu bayane, bargon Dana rufa har fuskata yad’an janye, Idan Akash yay tambaya saishi ya d’an rankwafo Dan yaji amsar da zan bada, saiya maimaita masa abinda na fad’a.
Bayan gama tambayoyin Akash yace damuwa ce da gajiya kawai, ya rubuta maganin daza’a sayo min, (duk cikin harshen ingilishi suke maganar).
Kar6a Galadima yayi ya d’auki waya yakira Harun, sunan maganin ya Sanar masa sannan ya yanke wayar, mintuna 10 saiga Samha takawo maganin.
Ya kalli mom yace, “amma bataci abinciba ai”.
Kallon Samha mom yayi, tace “taje ta had’o min tea.
Samha na kawowa duk sai suka fice suka barni dagani sai shi, shima Akash fita yayi.
Bargon jikina ya yaye gaba d’aya, muryarsa a dake yace “tashi kisha”.
Shiru na masa, hakkane yasakashi kausasa muryarsa, “wai bak’ya jinane?”.
Yun k’urawa nayi na tashi da k’yar, kad’an na saci kallonsa, harya cice kayansa na d’azu, yana sanye da dogon bak’in wando da T-shirt mai gajeren hannu, gefen wandon anmasa zane layi 2 da farin zare. fuskarshi babu walwala kamar kulum.
Mug d’in tea n ya mik’omin bayan na gyara zamana na jingina da gado, ALLAH ma ya soni sanye nake da hijjab.
Kar6a nayi dan nima nasan harda yunwa ke cina, inaga rabona dawani abincin kirki tun ana jibi d’aurin aurenmu, (ranar kamu).
Nasha rabin cup d’in na mik’a masa, bai kar6aba yashiga hararata, cikeda k’asaitarsa yace “cup d’in kawai nake buk’atar gani, kina 6atamin lokaci zanje na kwantane”.
Tamkar na makeshi haka naji, na harareshi nima a k’asan ido, muryata na rawa nace “wlhy na k’oshi, zanyi amaine”.
Bai tanka minba kuma bai k’ar6i mug d’inba, hakan ya nunamin dole dai saina shaye kenan, haka na rumtse idanu na shanye na mik’a masa mug d’in.
Kar6a yayi ya ajiye saman table glass d’in dake gabansa, sannan yad’auki magungunan ya 6alla min, bana tsoron Magani sai allura, dan haka babu musu na kar6a nasha tareda ruwan daya bani a cup.
Ina gamawa na zame na kwanta, mik’ewa yayi yaja bargon ya lullu6a min sannan ya fice batareda ya tanka minba.

Babu dad’ewa barci ya kwasheni, bamma San su Ayusher sun shigo sun kwantaba suma. da yake gadon babbane duk sai ya d’aukemu.

Washe gari natashi dad’an sauk’i, sai dai kewar munubiya data innarmu, harma data gayyar tsiyar ‘yan gidanmu, sauk’i nama d’aya ina ganin su Feena.
Break fast mai rai da lafiya aka kawo mana, su Ameera sai zuba santi sukeyi, nidai uffan bance da suba, nad’an tsakura kad’an na turo, maganin jiya na d’auka nasha na safe, dan har lokacin kaina na ciwo kad’an-kad’an, babu dad’ewa barci yay awon gaba dani.
Ban farkaba sai 12, shima tadani akayi, wai za’ayi ko hawan mi, nidai wannan bidi’a ta isheni hakanan wlhy.
Shiri akamin yanzuma cikin farin less, sanan aka samin alk’yabba, yanzun ma fuskar tawa a rufe take.
Gaskiya gidan sarauta akwai girma, dan shimafa dole akirasa da suna wani gari guda kam.
A mota aka sakamu zuwa inda za’a gudanar da hawan, dukda kuwa acikin gidanne fa, nida Samha ne kawai a mortar, tana ta zubamin surutu har muka isa.
Wata daban santa bace ta fitar dani daga motar, tana rik’e da hannuna har gurin da aka tanada domin zamana, yanzun fuskata a bud’e take, ba’a sakamin hular alk’yabba d’inba, dan muna zama awajen matar data fidoni ta ciremin, sai dai kunya tasani kasa kallon kowa, duk tsiwata inada tsananin kunya da rashin son zama wajen da mutane suka cika yawa.
Aunty Mimi ce a gefena na haggu.
Ban iya kallonba saida ta min magana tana kamo hannuna, dole babu yanda na iya na kallesu, su Galadima ne a saman dokuna shida samari kusan biyar duk da irin shigarsa ta sarauta, dokunan suna a tsaitsaye, da alama umarni suke jiran abasu, dan kamar gasace zasuyi.
Caraf muka had’a ido dashi, murmushin gefen baki ya sakarmin, cikeda mamaki na janye idona daga kallonsa.
Ana busa wani k’aho kowa yabama dokinsa k’aimi suka rera da gudu, nanfa hankalin kowa yakoma kansu ana zufa tafi, babu wata hayaniya dan bawani yawane damuba, kusan ma wajen duk ‘yan matane sai abokan Galadima dasuke son ganin al’adar dabasu saniba. Saikuma yayunsa mata irinsu aunty Mimi, amma babu manya kamar su mom awajen.
Ni ban saniba Ashe wannan tafiya saisun zagaye masarautar su dawo, Wanda yafara zuwa shine na d’aya.
Muna nan kusan mintuna 30 saigasu aguje suna tada k’ura, ko ganin fuskarsu ma ba’ayi sosai bare kagane wanene a gaba.
Jinai kawai ansaki tafi kowa na ambatar Galadima! Galadima!!, wai Ashe shine yafara isowa. ya diro akan dokin yana murmushi da goge hannunasa da handkerchief d’insa daya zaro aljihu, sannan yagoge fuskarsa.
Ruwa wani dogari ya mik’a masa, ya d’auka daga saman tired’in da aka d’oro yabud’e Goran, batareda ya saka kofiba ya hau shan kayansa, tas ya shanye ya jefar da robar, suma sauran duk ruwan suke sha.
Daga nan hotuna akayi, sannan yazo har inda muke ya kama hannuna, wai Ashe nima yanzu dole saina hau dokin, ahakane zamuje sashe-sashe, dan kowa yanacan yafito waje yana jiran zuwanmu.
Banta6a hawa dokiba sai yau, dan haka jikina yakama rawa. Muryarsa can k’asan mak’oshi yace “k bak’auya ki nutsu”.
Maganarsa saida tabani haushi amma ya zanyi, da taimakonsa na hau dokin bayan dogarai sun baza rigunansu yanda baza’a ga hawa naba.
Saida na hau da k’yau sannan shima yaje ya hau nasa, kuyangine a gabanmu suna zuba flowers, a bayanmu kuma dogarai, gefe da gefenmu ma dogaraine, wasu suna busa algaita wasu suna kid’an taushi, sai gayyar abokansa biye damu abaya dasu Ayusher da ‘yammatan masarautar.
Ahaka muka dinga zuwa sashe -sashe inda duk sun firfito, duk muna akan dokin bamu saukaba, sai dai mukan risina alamar gaisuwa. fuskata kuma tana abud’e yanzun kowa Na ganina, saida muka zagaye ko ina a masarautar sannan aka maidani wajensu mom. Lokacin la’asar tayi.

Dukna damu saboda kiran munubiya danaketa yi wayar akashe, tsakin danakeyine ya saka Ayusher tambayata, na fad’a mata.
Dariya tayi, “yo banda abunki ina zakiji munubiya kuwa, yaa marwan nacan nashan amarci kema kin sani ai, kema zuwa gobe wazai kiraki ya samu, Galadima nacan yana kwa…..”.
Filo na d’auka Na jefa mata a fusaka, suka sanyamin dariya kuwa.

????

Nasha kuka yayin tafiyarsu Ayusher, inaji ina gani suka tafi suka barni nikad’ai cikin wad’anda ban saniba.
Tun magriba aka shiryani tsaf cikin wata tattausar atanfa, sannan aka d’oramin alk’yabba, wlhy nagaji da saka alk’yabba r nan, saboda nauyi sukemin, har mamaki nakeyi yanda su basu damuba.
Zan iya cemuku nidai yau wanka akamin da turare dan kowane lungu da sak’o na jikina saida yasha ruwan turare, ruwan danayi wanka dashi kansa na musamman ne, nayi k’yau harna gaji.
An fiddoni aka sakani cikin mota, sannan aka nufi sashen Galadima dani. Dukda nasan auren Contract nayi, hakan bai hana zuciyata luguden dakaba, tunda bamuyi wata yarjejeniya dashiba ta zaman da zamuyi, addu’a natayi a zuciyata ina tunano innarmu da munubiyata da kewarta ta gallabeni, jinake tamkar mun shekara 5 bamuga junaba, bamu ta6a yini ba’a tareba, saigashi yau munyi kwana da yinima, ko’a waya bamuji muryar junaba.
Duk da fuskata a rufe take hakan bai hanani shaida 6angaren Galadima ya had’uba, dan k’amshinsa ma da banne.
Muryar wata na tsinkayo a cikinsu tana fad’in wai falon Galadima za’a kaini, gabana yakuma fad’uwa.
Nidai naji mun iso inda turaren Galadima yafi ko ina yawa, inaga nanne falon nasa, gawani lallausan Abu danake takawa a k’afata, sun zaunar dani akan wani laushin dayafi Wanda nake takawar, sannan sukayi addu’a suka fice.
Tunda suka fita ban iya d’ago kainaba, dukda falon tsitt yake alamar babu kowa cikinsa, sai k’arar AC kawai da ni’im taccen k’amshin dake tashi, a falon, sai TV dake magana can k’asa an rage k’arar sosai, hawayen danaketa rik’ewa tun d’azun suka shiga ziraro min a kumatu. a hankali nakejin takun takalmi na tunkaro falon………???

Muhad’u tomorrow idan munkai da rai da lafiya, yau kaina namin ciyo kuyi manage da wannan please??????.

Ko Galadima zai angwance oho mar????.
??????????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
*_Typing??_*

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply