Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 27


Raina Kama Book 1 Page 27
Viral

?2?7?

………..A gajiye yadawo gidan, daga masarautar su papi yake, dan shine yamasa kiran gaggawa a daren jiya, yau tunda safe ya tafi, dan jirgin 7am yasamu, shine sai yanzu yake dawowa.
Saman kujera ya zube yana furzo iska, sarkin mota daya biyoshi dawasu kaya ya ajiye, yana niyyar fita yajiyo maganar Galadima d’in. tsayawa yayi yajuyo yana kallonsa.
idonsa a rufe yace, “kunnamin AC ”.
“to ranka ya dad’e”. sarkin mota yafad’a yana risinar da kai alamun girmamawa.

Ya dad’e zaune a wajen idonsa a rufe, jin ana kiran salla a masallacin masarautar yasashi mik’ewa da k’yar yanufi bedroom d’insa. makunnar fitilar ya laluba, haske ya gauraye d’akin, komai normal kamar yanda yabarsa. anutse yafara zame sky blue d’in shaddar jikinsa. wanka yashiga, bai 6ata lokaci sosai ba yafito, jikinsa ya goge tsaf yajawo jallabiya fara tas mai dogon hannu yasaka, tamasa k’yau sosai, yad’an fesa turare yafita da hanzari jin za’a tada sallar magrib.

Nagaji da jiransa har zuwa magrib, bansan hawaye sun fara bin kumatuna ba, ahaka nayi sallar magrib, nayi alk’awarin ko yanzu yazo yabani sakina a gidanmu zan kwana, bayan na idar yau ko doguwar addu’a banyiba nadawo kan sofa na zauna tareda rabga tagumi na zubama akwatina idanu.
A wannan yanayin yashigo ya sameni, cikeda mamaki yake bin akwatin gabana da kallo, shi yama manta dawani maganar saki da mukayi.
Ban San ya shigoba saida yad’an bubbuga hanun sofa d’in, firgigit nayi ina kallonsa, bansan murmushi ya su6uce minba da ambatar Alhmdllh.
Idonsa ya janye a kaina ya zauna bakin gadon “lafiya na ganki da trolley?”. Yay maganar cikin kuma d’aure face.
Nikam ban damu da yanayin nasaba na rashin walwala, dan narigada na fara sabawa ma da hakan, nad’an murmusa ina ta6e baki, nace “kayan tafiya gida na had’a”.
Yi yay tamkar bai jiniba ma, ya zaro wayarsa dake ring yana kallo, a mamakina sai naga yayi murmushin gefen baki tareda saka wayar a kunne. “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki my Momma”.
“tare dakai Muh’d d’ina, yakuke? Ina d’iyata?”.
Murmushin yakuma yi tareda satar kallona, yace, “gata a gefena Momma, Yaya jikin Abie?”.
“jiki Alhmdllh wlhy, yaushe zaku tahone? kun barmu mu kad’ai nida jakadiya”.
“kai Momma duk kuyangin gidanann kice kuna cikin kad’aici?”.
“to Muh’d ai d’a dabanne a zuciyar iyaye, musamman ma mu damuka k’agara muga sabuwar d’iyarmu”.
Bakinsa yad’an ta6e yana murmushi, “karki damu Momma zaku ganta wataran, amma su aunty Mimi ai inaga gobe zasu taho jirgin darema suka samu”.
“haka tacemin, amma kufa to? dan banjiKu a lissafin masu tahowaba?”.
“nima insha ALLAH zan biyo bayansu bada dad’ewa ba Momma, dan nayi missing d’inku, bazan iya gama hutuna ananba gaskiya”.
“ita kuma d’iyar tawafa?”.
“nan zan barta mana Momma, duk k’arshen wata zanzo na ganta kamar yanda na saba”.
“lallaikam, to yanzu dai saika nemi tickets kafin Safiya, gobe idan ALLAH ya kaimu kutaho dasu Haneefa domin takawa yaga d’iyarsa, idan kun k’are hutun tare anan zuwa k’arshen watan saika maidatan”.
Tunda tafara maganar gabansa yafad’i, yawani marairaice murya tamkar yana a gabanta, “please Momma wannan shawaran kumafa? dan ALLAH karkice haka ba yanzu ba sai nan gabafa zatazo?”.
“to nidai nagama magana Muh’d, za6i kuma yarage naka ai, bani ita mu gaisa time d’in gogema takawa jiki yayi zan shige”.
Ransa a 6ace yamik’omin wayar, banyi magana ba na kar6a dan naji yana Momma ai nasan mahaifiyarsa ce. gakuma yanda yaketa kwantar da murya irinna ladabi da shagwa6a.
Cikin nutsuwa da tsantsar girmamawa na gaisheta, daga can ta amsa min cikeda kulawa, bayanin daya firgitani naji tanamin, na waro idanu waje cikin tashin hankali, amma sai na kasa musa mata, na shiga amsawa da to cikin rawar murya.
Duk da AC d’akin zufa nakeyi, nida ke shirin fecewa gidanmu yau da takardar saki amma shine ake rok’ona nayi shiri gobe zamuje India, na taresu ni Munaya, ban kuma fahimtar dukkan sauran zantukan nataba, sai maganar k’arshe naji datace nabashi wayar.
Murya na rawa namata godiya da Addu’ar samun lafiya ga abban su Galadima, taji dad’i sosai kuwa, dan har sautin murmushinta ina jiyowa, hannuna har rawa yakeyi namik’a masa wayar, yana kwance idonsa a lumshe, damuwace a fuskasa karara, muryata na rawa nace, “gashi tace abaka”.
Batare da yabud’e idonba ya kar6a, a kunne yasaka wayar, cikin kwantar da murya yace “haba sweet Momma na a sassautamin mana”.
Murmushi kawai tayi daga can, tace “ai iya sassaucin dazan maka kenan Muh’d, gobe idan ALLAH ya kaimu ka kaita gidansu tama iyayenta sallama da ‘yar uwar tagwaicinta”.
“amma Momma….. ”
“kasan banason maida magana baya ko? kayi yanda nace kawai”.
Shiru yay bai iya cewa komaiba harta yanke wayar gaba d’aya.

Ransa a6ace ya tashi zaune, wayar Harun ya kira, yana d’agawa ko gaisuwar bai amsaba yace, “Harun inason tickets guda biyu na India”.
“lafiya dai ko Galadima?”.
“Normal” kawai yace ya yanke wayar.
Harun ya girgiza kai, dan yaji alamar ransa a 6ace yake.
Mintuna basu wuce 5 ba yakirashi yace an samu naka, sai dai ita kuma batada passport ai, dolene da safe sai Anje anyo, amma na darene jirgin.
“yayi” kawai yace nanma yay shiru.
Harun nason masa wata tambayar amma babu dama, sai kawai ya yanke wayar.

Nidai ina dafe da kai abin duniya dukya isheni, shikenan an ruguza min plan d’ina.
Tashi yay yafice batareda ya kuma ko kallona ba, ban damuba, dan nima tawa ta isheni, yana fita hawayen bak’in ciki suka zubomin a fuska, ban samu damar sharewa ba na zame na kwanta a sofar.

Yana fita sashen mai martaba yaje, bayan jakadiya tamasa iso yashiga, gaidashi yayi cikin saisaita yanayinsa kafin yamasa bayanin zai koma India gobe, saboda kiran gaggawa daya samu daga doctors d’in Abie.
Fatan alkairi mai martaba yamasa, kafin ya tambayesa maganar nikuma fa.
Kansa a k’asa yace, “ranka ya dad’e da ita zamu tafi, idan komai ya dai-daita saina maidota”.
“to shine nan, hakan yayi ai” nasiha sosai mai martaba yayi masa, tareda jan doguwar addu’a wa jikin Abie, ya dad’e a can sannan yafito.

????

d’ayar wayarsa daya manta a kan gadona tashiga ring, ban d’auka ba harta tsinke, aka kuma kira ta yanke, saga nan ba’a sake kiranba, tunanin kiran Munubiya ne ya zomin, Dan haka na tashi zaune ina share hawayen fuskata na d’auki wayar nasaka number, Dan na haddace ta akai, harta tsinke bata d’agaba, saida na sake kira sannan tad’aga.
Acikin rashin sanin wanene tayi sallama a d’arare, amsawa nayi ina jan ajiyar zuciya, cikeda d’oki tace, “Sweetheart kece? ykk?”.
“lafiya lau munu…., ke kad’aice a gidan dan ALLAH”.
“eh nikad’aice yaa marwan bai dawo masallaciba. miya farune?”.
“magana zamuyi Munu…. amma kiyi hak’uri da 6oye miki da nayi tun farkon matsalar, banason ki tashi hankalinkine shiyyasa” tun daga farkon maganar aurenmu da Galadima a randa suka saceni har zuwa yau ban 6oye mata komaiba, inayi ina kuka, itama daga can kukan takeyi harda shashsheka.
Cikin Jan aziyar zuciya tace, “Naso nafahimci wani Abu tunkan aurenmu, amma ganin bakicemin komaiba na share, banga laifinki ba na aminta da auren yarjejeniyar kamar yanda ya buk’ata, domin kowaye a irin matsayinki abinda zaiyi kenan inhar yana tausayin iyayensa. Abu d’ayane gaskiya sai naga kamar bazai aikataba”.
“mikenan?”.
“Saka miki desire tabs dakikace, kiduba yanda kikace yadamu sosai, Munaya kofa saka mikin yayi babu laifi, tunda hakinsane, sadaki yabiya ya aureki, inma banda wautarki koda auren Contract d’inne kukayi ai ba’a fatar sakin ko. atunaninki innarmu wane tashin hankali zata shiga idan ance aurenki ya mutu cikin kwanaki 5 kawai da arenmu, ni yanzun shawarar dazan baki ki kwantar da hankalinki kuje India d’in, ki duba mahaifinsa, saikiga tarbar da parent nasa zasu miki, daga nan samu san mafita, idan sakin zaki nema kinga saiku rabu, idan kuma zaki iya zama da shine shikenan, saimuyita addu’ar ALLAH ya dasa masa sonki a zuciya”.
“Humm, Munubiya kenan, kinga kuwa tashin hankalin danake ganowa a masarautarsun nan, wlhy akwai babban lauje cikin nad’ifa, bazan iya wannan rayuwarba gaskiya, dan tanada wahalar gaske, shi kansa ba ta6a sona zaiyiba, dan tun farko dawata manufa ya aureni ai”.
Murmushi Munubiya tayi mai sauti, tace “amma ke kina sonshi?”.
“ALLAH ya kiyaye, ni wlhy bana sonsa, kuma ban tunanin zansoshi ko anan gaba”.
Dariya Munubiya tayi, harda kwantawa a gado, cikin dariyar take fad’in “to badai asan maci tuwoba sai miya ta k’are, kika sanima kona samu baby’s d’ina a jiyan”.
Kwafa nayi kawai, nace can dai a bakinki, kedai mukema fatan ALLAH yasa mun samu, ki shirya min kayan dad’i gobefa zanzo kinji Sweetheart ”.
“karki damu habibati, a gaidamun Galadima ango”. tayi maganar cikeda tsokana.
Aiko sai Munaya ta saka mata kuka.
Dariya ta tuk’e Munubiya tayanke wayar tana mamakin yanda Munaya tayi sanyi, dawuya Munaya kaga ta zauna yima Abu kuka, koyafi k’arfinta tanada jimirin wahala, lallai Galadima baije da wasaba ashe.????
Koda tayi sallar isha’i saida ta saka ‘Yar uwarta a addu’a, fatanta wannan auren ko igiya d’aya karta samu rauni barema akai ga saki. ta d’au alk’awarin cigaba da sakata a addu’a a kowacce sallarta.
https://2gnblog.blogspot.com/
Nima ina ajiye wayar tashi nayi nayo alwala nayi sallar isha’i d’in.
Kallon hotuna na zauna yi awayarsa, duk kusan ma bawasu pictures bane na azo agani, daga hoton wayoyin salula sai na kamar kayan waya Daba a had’aba da computers, mamaki ya kamani, saikace mai k’era waya?, nidai gajiya ma nayi na ajiye wayar, har barci ya kwasheni ban kuma jin labarin Galadima ba.
https://2gnblog.blogspot.com/

Shikam tunda yabaro wajen mai martaba suka fita shida sarkin mota, birnin gayu plaza yaje, yayi wasu ‘yan abubuwa sannan ya gana da ma’aikatan wajen. Sai kusan around 11 ya dawo gidan, ko sashena bai kallaba ya shige d’akinsa, abinda duk zai buk’ata yad’an harhad’a, yakira Wanda zai kira awaya akan wasu harkokinsa sannan yay shirin barci ya kwanta..
Washe gari da asuba ko tadani bai zoba kamar jiya, ALLAH yasama nariga da na saba da tashi sallar tun a gidan mu, dan haka akan lokacin na tashi nayi kayana. barci nakuma komawa, ban tashiba sai 9am.
Wanka nafarayi, ina tsaka da shafa mai yashigo da sallama ciki-ciki, na zawo hijjab da sauri na saka.
Bakinsa ya ta6e yana kauda kai gefe. “ki shirya zamu fita”. ya juya ya fita.
Da kallo na bishi ina girgiza kai, oh ni, saikace anmasa dole sai yayi maganar?.
Dukda bansan inda zamuba saina d’okantu da fitar, kobabu komai nasha iska ai, danni gidannan jinsa nake tamkar wata duniya daban ba duniyarmu ta mutaneba, yo komaifa gidan akwaishi, makaranta ne asibiti k’aramine, wajen wasan yarane, babufa yanda zaka fita waje inba doleba, musammamn ma mu matan aure, garama mazan da masu fita karatu kuma.
https://2gnblog.blogspot.com/ Shiri nayi cikin zani da Riga na atanfa, sunmin kau sosai, danni fa saima naga kamar fatata tawani d’an murje hakannan??..
A falona na iskesa zaune, muka had’a ido kowa ya janye nasa cikeda basarwa, saida yagama k’asaitarsa da mulki sannan yatashi, sanye yake cikin milk d’in shadda datasha ainahin aikin masu sarauta, takalmansa ma hakanne, sai fidda k’amshin turarensa mai narkar da mutane yakeyi, sajennann ya kwanta luf bisa face nashi, hular na hannunsa bai sakaba.
Gaba yayi nabisa abaya ina takuna d’ai-d’ai, takalmana masu sauk’in tsini sai bada sautin kwas-kwas sukeyi.

Mun tarar da motocin dazamu fita dasu a shirye guda 3, an wankesu sai d’aukar idanu sukeyi, gaisuwar da hadiman gidan suke mana muketa kar6awa, nikam banason abunnan wlhy, amma shi ko’a jikinsa.
Bud’e mana motar akayi muka shiga, nida shi muna baya, sai sarkin mota agaba, yayinda mota biyun kuma dogarai suka shiga.
https://2gnblog.blogspot.com/
Babu Wanda yay magana tunda muka fita, nidai kawai kallon hanya nakeyi da mamakin ina muka dosa?, mun Isa immigration office Ashe passport za’amin, abinka da manya, cikin 1hour aka kammala min komai. Bamu bar office d’inba saida harun yazo ya kar6i passport d’in domin nema min visa, daga nan muka fito.
wani dad’ine ya rufeni danaga mun doshi hanyar gidan mu, shi kansa ya hango farin cikin dake shinfid’e a face d’ina, ya janye idonsa daga kallona ya maida kan kallon mutanen anguwar daketa hada-hadarsu hankali kwance.
A dai-dai k’ofar gidanmu motocin suka paka, da hanzari na nemi 6alle murfin zan fita.
Caraf ya damk’e hannuna, juyowa nayi ina kallonsa tamkar zanyi kuka, idonsa a lumshe yake tamkar ma baisan miyayiba.
“dan ALLAH ka sakar min hannu naje”. ‘nayi maganar tamkar zanyi kuka’.
Banza yamin, saida yamula dan kamsa sannan yabud’e idonsa a kaina yana hararata, “ki nutsufa, ko an fad’a miki haka akeyi?”.
Baki na tunzuro gaba.
Ya janye idonsa daga kallona yana kuma matse hannuna cikin nasa.
Ni ban saniba Ashe wai dole sai an nema masa ison shiga gidan namu, sarkin mota dai tuni yafita dama.
‘Yan anguwarmu sunyi cirko-cirko suna kallon motocin, jira kawai suke suga Wanda zai fito aciki, dukda sunga masu jajayen riguna a tsaitsaye, alamar daga masarauta ne.
Muna a haka saiga yaa hameed yafito daga cikin gidanmu dad’an hanzarinsa, inaga yazo gaidasune, dan kullum Safiya duk sai sunzo shidasu yaa Shafi’u.
Jikin motar damuke ya k’araso, sarkin k’ofa yay knocking d’in glass d’in 6angaren Galadima. duk da yasan yana kallonsu shi.
Sauke glass d’in yayi a hankali, sannan yama sarkin k’ofa nuni daya bud’esa, har yanzu hannuna yana cikin nasa kuma. Ya d’auki hularsa ya saka.
Cikeda fara’a Yaa Hameed yake masa barka da zuwa, sai lokacin ya saki hannuna, sannan yazura k’afarsa d’aya yafito, nima dogari d’aya yazagayo da sauri yabud’emin, na fito, handbag d’in hannuna dogarin ya kar6a yana zubomin kirari.
Kallofa Yakoma sama ga ‘yan anguwarmu, kowa sai kallona yake yana fad’in ashe munaya Ce, kai masha ALLAH, kugafa auren sati d’aya harta canja kamanni, lallai sarauta dad’i.
Inda yaa Hameed da Galadima suke na zagayo, suna rik’e da hannun juna sunyi musabaha, fuskar yaa Hameed a washe, yayinda ta Galadima ke d’ukeda wani munafukin murmushi.
Cikin murna nace “yaa Hameed I miss u”.
“miss u too Darling sister. bismilla ranka ya dad’e kumuje ciki to”.
Atare muka shiga ciki, ina gaba suna bina a baya shida yaa Hameed.
Matan gidanmu kowacce na mak’ale jikin window d’inta tanason ganin Galadima, yayinda Aryaan da Aiyaan suka shek’o da gudu kaina, ganin haka suma sauran yaran sai suka shek’o, duk na tarbesu cikeda farinciki da kewa.
Ni nama manta dawani Galadima muke tare, Ashe shi yanata kallonmu cikeda sha’awa.
yaa Hameed yamasa jagora zuwa falon Dady.
Nikam ai d’akin Innarmu sha, tareda gayyar ‘yan tarbata.
A zaune na iske innarmu tana ninke kayan su Aryaan, da alama wankewa tayi, sai tausayinta ya kamani, yanzufa kowanne aiki dole itace zatakeyi, babu mai tayata, jikinta na fad’a ina hawaye.
Itakam tace “kajimin ja’irar yarinya, to miye abin kukan kuma? wai nikam yaushe kika lalace da sauri kuka haka Munaya?”.
“innarmu kewarku cefa wlhy”. nashiga gaidata, cikeda farincikin yanda na koma a kwana 6 kacal take amsamin, sai jero hamdala take a zuciyarta.
Zainab k’anwar Fauziyya tashigo d’auke da tire an d’oro zo6o da ruwa akai.
“inyee, kaga su zee anzama ‘yan matafa, kace bad’i sai aure kenan?”.
Fuskarta ta rufe tana fad’in kai Aunty kibari please, innarmu kice ta daina”.
Innarmu dariya take mana itakam, saiga Rahma itama tashigo, saiga Ameenatu da Khadija ma, lallai bad’ima Ashe zamu aurar da yawa, a kwana ki 6 d’innan sainaga yaran duk sunmin girma a ido. Nasha mamakin su na zuwa gaisheni, dan bansa akaba nikam, araina nace ko jama’ar gidanmu dun fara canja haline dai?.
Muna haka saiga innaro tamkar an jehota, kowa ido ya zuba mata, dan shigowa tayi tana masifar wai bamu fara shiga gidan taba nida Galadima.
Na kalleta a d’age ina ta6e baki, “yo banda abinki innaro ai sai nafara ganin Uwata, dan banida kamarta kaf duniya”.
Ha6a tarik’e tana kallona “eh lallai kam, yo ai Dama ke halin uwarki gareki, ba mutuncine dakeba, ballan tana yanzun kuma ido yak’ara fetsarewa ansan komai na aure”.
Zan maida mata murtani innarmu ta harareni, shiru nayi na k’yaleta badan nasoba.

Shima Galadima yana falon Dady yasamu tarbar mutunci daga maman Fauziyya, dan matan gidanmu babu wadda ta aika masa dako ruwa, yaji dad’in tarbar daya samu kuwa, musamman yanda su Abba suka nuna masa tamkar d’ansu, baiyi dubi da sarautar dake kansaba ya duk’a har k’asa yakwashi gaisuwa wajen iyayena uku.
Hakan yamusu dad’i, domin ya mutuntasu, kuma sun kuma tabbatarwa shid’in mai tarbiyyane.
Anan yamusu bayanin munzo musu sallama ne zamu tafi India.
Fatan alkairi su abbanmu sukai mana da k’yak’k’yawar addu’a, daga nan sukad’an ta6a hira dashi, dukda yana nonnok’ewa saboda kunya irin ta jinin hausa Fulani.
Nikam can innarmu ta iza k’eyata nashiga kowanne d’aki na gaidasu, sai kallon k’urulla suke bina dashi, anason ganin wata makusa a jikina, amma sai basuganiba kuwa, komai sai sambarka. Aikam bak’in ciki tamkar ya karsu, kowa hassada nacin zuciyarsu (kai jama’a ALLAH yarabamu da cutar hassada komai k’ank’artatta??????)
Na dad’e d’akin maman Fauziyya sosai, dan acanma naci abinda tad’an girka mana mara nauyi, yaa Hameed yazo ya d’auki na Galadima da kansa.
Sashenmu na dawo inatama innarmu shagwa6a, duk nabi na nanik’e mata, dukda tureni datakeyi. Nashiga tsohon d’akinmu harda kukana, komai nanan yanda yake, harma dawasu ‘yan tarkacenmu daba a gama badawa ba, haka kawai bamu mutuba d’akinmu Yakoma kango, anan na d’akko cajata da wayar Galadima daya barmin a filin idi, sai wad’ansu ‘yan abubuwa danake buk’ata.

Na fito ina tambayar innarmu waye ya d’auki wani hotonmu dake saman mirror nida Munaya?, tacemin maybe Ameeran inna lami Ce ko Bilkisu, dan taji suna rigima akan d’aukar Horton.
Shigowar Galadima da yaa Hameed tasaka innarmu yin shiru, nikam ban daina daddaga k’afa k’asaba ina k’unk’unin miyasa tabari suka d’auka?.
Galadima dake k’ok’arin zama yad’ago ido yad’an kalleni sannan ya janye.
Yaa Hameed ne yace kekuma lafiya?.
Fad’a masa nayi tamkar zanyi kuka, yace “to kuka zakiyi?”.
“ALLAH yaa Hameed inason hotonfa”.
“ai saiki hak’ura yanzun tunda sun d’auka ko?”.
Innarmu da Galadima dai gaisuwa sukeyi, babu Wanda ya tanka mani. shi saima mamakin ta6arar danakeyi yake a zuciyarsa.
Nikam bansan yana yiba.
Sosai yaji innarmu ta burgesa, yakula ko kad’an ba halinta nabiyoba, dan ita tanada sanyi, dagani batada hayaniya, amma nikam ai sai addu’a.

Yad’an jima anan dukda ba hira sukeba, kowa kunya na cinsa, a raina nace dama yanda kunya guy d’inan ashe?.

Alkairi mai yawa ya ajiyema innarmu, dawata leda da yaa Hameed yabiyosa da ita, sannan yafita innarmu na saka masa albarka yana amsawa cikeda jin dad’i, jinta yake tamkar Momma d’insa.
Daga nan saida yashiga kowanne d’aki, sannan yaa Hameed ya rakashi gidan innaro.
Abba ne yashigo yana fad’in a tattaro lefena muwuce da kayanmu.
Na marairaice fuska nace Abba abarsu anan, kagaba tafiya zamuyi can d’in babu kowa.
“a’a Munaya bazai yuwuba, idan mun ajiyesu anan mizamuyi dasu?, kitafi da kayanki, duk randa dai kuka dawo suna d’akinki ai.
Badan nasoba na amince, amma naje wajen kayan ina fitar da wasu, ni saima yau naga lefen, gaskiya su Galadima sun zuba kud’i a wajennan.
Duk matan gidanmu atanfofi na fidda musu, maman fauziyya kam guda biyu, sannan yaran gidanmu ‘yan matan yanzu kowa nafidda masa wani abun, su Aryaan ma dukda mazane kowa na fidda masa abinda zai iya amfani dashi.
Sai su Ayusher da inna lami da Ameera, Bilkeesu ma da nata, hakama mama rabia, na ware akwati guda na lodama Munubiya kaya sosai aciki, aunty salamah ma da nata, sai gwaggo Safiyya da yaranta mata, itama innaro jarabatu na fidda mata, su Abbanmu ne dai narasa mizan basu aciki.
Innarmu na kira tagani, ta kalleni tana fad’in “munaya bazasuga an kwashe kayanba?”.
“a’a wlhy innarmu bazasu ganiba, kowafa da sashensa a gidan, kuma babu mai shiga harkar wani, idan na barsu mizanyi dasu? Kayan sunmin yawa ai”.
“to shikenan, ALLAH ya saka da alkairi”.
Na amsa da ameen ina fad’in “ganaku nan keda su Aiyaan innarmu”.
“a’a ni bazan d’auki komaiba, bakiga yama kawomin abuba, ga kud’i dama bansan ko nawa bane”.
Kuka na Sanya mata akan saita kar6a, babu yanda ta iya ta amsa, amma saida tarage. Sai dai tana fita na maida mata harda k’arima.
Zainab Ce ta kaima kowa nasa, kowacce rai babu dad’i ta amsa, sotayi ace daga ‘ya’yantane wannan abun arzik’in yafito bawai innarmu ba, (basusan shi Ubangiji babu ruwansaba, yakan azurta Wanda yaso Yakuma k’ask’antar da Wanda yaso a lokacin dayaso).
Babu wadda tazo godiya sai maman fauziyya, nace “oho dai, aikin banza wai talaka ya girmi sarki??????”.
Banyi maganar su d’auki motarba, dan sonake nasami cikon d’ayar nabasu su duka ukun.
Nima naje na gaida innaro, dasu Abbanmu, naje gidan innaro lokacin su Galadima harsun fito,, na iske Ashe gwaggo Safiyya tama koma jiya, sai d’iyarta Habiba datake zawarci aka bari anan.
Munsha hira da ita, tanata yaba k’yan da nayi.
Innaro kam dukda jana datake ajiki sai basar da ita nakeyi, amma hakan bai hanata yaba Galadima ba, catake wai na more miji, nafi kowa morewa a gidanmu.
Nidai banda ta6e mata baki da bak’ar magana babu abinda nakeyi, bata damuba saboda neman gindin zama take ajikina.

Bamu baro gidanmu ba sai gab daza’a shiga sallar juma’a, an taho da motata da lefena, duk kayan daza’a bana mutane kuma na barsu a can, harna Munubiya.
Su Abba sunsha alkairi awajen Galadima Ashe, hakama matan gidanmu d’akin kowacce daya shiga saida ya ajiye alkairi, sunata kukan zuci da fad’in inama-inama ‘ya’yansu ne a wannan daular????.
Zamu shiga motane ina sharar kwalla baba k’arami yace namusu godiya wajen Galadima, kaina kawai na iya d’aga masa.
Innarmu bayan tafiyarmu har ‘yan kwalla tayi, matan gidanmu kam duk haushinta sukeji, idan kacire maman fauziyya.

Daga nan gidan Munubiya muka nufa, amma anan bai shigaba, yace naje zuwa anjima zai dawo mutafi, dan yanzu zaije sallar juma’a.
Kai na kawai na d’aga masa, nafita bayan dogari d’aya yabud’emin k’ofa, basu bar gate d’inba saida sukaga na shige ciki, ya maida kansa jikin kujera ya kwantar tareda lumshe ido, abinda yafaru a gidanmu kawai yake tariyowa, yakula family nawama sai a hankali dai. Sunada shigen irin halallayyar family d’insa.

Nikam da gudu nashiga ina kwala kiran sunan Munubiya, itama yafito aguje muka rungume juna, sai muka fashe da kuka kawai, ALLAH ma ya somu yaa Marwan yarigada yafita masallaci……………..???

*_Masoya bansan yanda zan nuna muku tsantsar farin cikinaba, amma tabbas inajin dad’in Comments naku, kuyi hak’uri da rashin amsawata d’ai-d’ai, kunmin yawane wlhy, ga massages na PC, idan kuma nagama typing d’inan kaina d’aukar zafi yake, ko son ta6a waya banayi wlhy, naga wasu suna d’auka kamar wulak’ancine rashin amsawar, wlhy ba haka bane, kumin afuwa da uzuri please & please, duk da nasan bazan iya k’yautatama kowa acikinku yanda yakamata ba, dole wani yaga gazawata koyayane tawani fannin??._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu??????_*
*_Typing??_*

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply