Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 28


Raina Kama Book 1 Page 28
Viral

?2?8?

………..Bansan yanda zan musalta muku farin cikin damuka tsinci kanmuba nida ‘yar uwata Munubiya, abin kawai ba’a magana.
Duk da bata yarda zan zo d’inba amma bata fasa tanadar min duk abinda tasan inasoba, tarasa inda zata sakani dan dad’i, gaskiya gidan munu yayi k’yau sosai, gashi an cika ko ina da kaya, kasancewar harda nawa aka had’a mata, muna yin salla muka 6arke da hirar yaushe gamo, a haka yaa marwan yazo ya samemu, yaukam abin mamaki naga fara’a a fuskarsa, nace lallai aure yayi citta kenan, yanda yake bama Munubiya kulawa sai abin ya birgeni, kamar Na lashesu kuwa Dan dad’i. Haka muka yini muna tad’i har lokacin sallar la’asar yafita salla.
A lokacinne aunty Salamah tazo gidan, Ashe Munubiya ce takirata ta fad’a mata zamu tafi India yau da daddare, mun tarbeta da murna sosai, yayinda ita kuma taketa yaba wai munyi k’yau. mukaita rufe fuska alamar kunya.
Shawarwari taita bamu akan rayuwar aure da yanda zamu tattali mazanmu, babu ko kunya take 6aro mana komai, sai mune muketa sunkuy da kai, itakam ko a jikinta, ta rarraba mana wasu buks da ke d’auke da abubuwa masu amfani dazasu bada gudunmawa a zaman takewar aure, nidai bawai na d’auki nawa da muhimmanci baneba.
Wajen 5 tatafi, tafiyarta babu dad’ewa saiga Galadima da yaa marwan sun shigo, Ashe wai ya dad’e a k’ofar gida zaune, ya kira yaa marwan yace baya gida amma gashinan zuwa.
Shine yajirashi amota harya iso suka shigo tare. Sun gaisa da Munubiya a mutunce, ta shirya musu abinci, da yace yagode sauri yakeyi, amma munu ta marairaice wai yaza’ayi mijin ‘Yar uwarta yak’i cin abincin gidanta, in baimasa baneba ta sake masa.
Murmushi yayi ya zauna yaci kad’an, yayinda mukuma muka shiga d’aki dan mu basu waje suci abincin, d’an kuskus d’inmu mukayi muma, takuma kwantar min da hankali akan auren nawa da wasu ‘yan shawarwari, da nunamin fushinta akan abinda nace nama Galadima d’in, ta nunamin wannan ba tarbiyyar da iyayenmu suka bamu baneba, gaskiya karna sake irin haka, kuma nabashi hak’uri akan hakan, nace “to amma tayaya zan basa hakurin?”.
‘Yar takarda ta d’auka tayi rubutun tabani wai nabashi.
Na kar6ane kawai badan ina tunanin zan bayar d’inba, duk da nasiharta ta shigine gaskiya, kuma nima tun a ranar nayi nadamar ce masa azzalumin gaskiya, Duk da nasan a cikin fushine Nima Na fad’a, Dan nashiga rud’ani sosai akan abinda yayimin daban zataba.
tabani kayan da aunty salamah takawo a Leda, batareda na dubaba na amsa.
Itama k’yauta mai tsoka yamata sannan muka fito, nida ita kowa yana sharar kwalla, bamason rabuwa da juna, amma yazamuyi? aure ya rabamu.
Daga nan gz yaa marwan muka nufa gaida mama rabi’a, namayi mamakin yanda yasanta, nankam tare muka shiga, su Ayusher suka rukunkumeni cikin tsantsar farinciki da kewa.
Bamu dad’e sosaiba itama ya ajiye mata alkairi muka fito, su Feena ma yabasu kud’i wai su sai kayan kwalliya, hakama Ahmad, yaa Fadeel dai mun tarar baya nan, yakoma inda yake bautar k’asa.
Nanma saida nayi kuka dazamu taho.
Saida muka shiga mota ina sharar hawaye sannan ya kalleni cikeda k’asaita yana ta6e baki, “ke wai bak’ya tsoron hawayenki su k’are ne?”.
Bance masa komaiba nacigaba da kukana, shima saiya shareni.

???***???

Koda muka isa Masarauta bamu wuce sashenmu kai tsaye ba, wasu 6angarorin gidan mukaje mukai musu sallama, harda sashen mama Fulani, yauma dai babu magana mai dad’i tsakaninta da Galadima, nifa lamarin nasu na d’aure kaina gaskiya.
Mai martaba kam munsha addu’a a wajensa, sannan muka fito.
Mun shiga sashenmu ana kiran sallar magriba, zan shige yace “kiyi azamar shirya kayanki trolley d’aya, karki wani kwashi kaya dayawa”.
Da to kawai na amsa nayi shigewata ciki.

*_7:30pm_* Muka bar masarautar, nida shi da Samha motarmu d’aya, muna baya tana gaba.
d’ayar motar kuma Sauban da aunty Mimi da khaleel ne aciki.
Mun sami rakkiyar Harun da Muftahu sai wasu k’alilan daga masarautar.
Tom nidai ba k’auyace a airport, dan banta6a shiga jirgiba, amma kunsan mutuniyar taku da Jan aji,?? saina Fiske abina nima inajan citta tamkar wadda ta saba.
Duk abinda yadace ayi anyi mana, musamman ma ni danake sabuwar fita k’asar, harun yad’an sha cukuniya a kaina tunda rana.
9pm dai-dai jirginmu ya shilla a gajimare??????.

Lokacin da akace asaka belt ban sakaba, sai shine ya jawo yasakamin batareda yace uffanba, yana jikin window nikuma ina gefensa, sai bayan mu khaleel da Samha, can baya kuma aunty Mimi da Sauban.
Ina lafe jikin kujera, yayinda shima yake kwance ya jingina bayansa, wani English novel ne a hannunsa yana karantawa, dama tun amota yake rik’e da kayansa.
Da akazo tambayarmu mi muke buk’ata Coffee kawai yace yacigaba da karatunsa, nima ta tambayeni saina girgiza mata kai alamar bana buk’atar komai.
Janye book d’in yayi yana kallona, saikuma ya janye ya maida kanta, harta bar wajen ya kirata, yace takawo min abinda su Samha sukace sunaso.
Bance komaiba nidai, shima saiya cigaba da karatunsa.

(*************)

Alhmdllh mun sauka kasar India, k’asar da nake gani a films, abin mamaki sainaga dogarawa ne sukazo tarbarmu, saikuma Akash dawani danaji Galadima yakira da beejay.
Bamu 6ata lokaciba mukabar airport d’in, a nawa tunanin sainaga rayuwar tasu kamar dai tamuce gaskiya, saidai banbancin sutura zuwa wasu mu’amullat haka, mutane sunata hidimarsu da kai kawo hankali kwance.
Masha ALLAH na fad’a yayinda muka isa gidan danake k’yautata zaton nasu Galadima ne. gidan kam yamin k’yau gaskiya, su beejay basu shigaba suna saukemu suka juya, mune muka Shiga hannuna aunty Mimi tarik’e, yayinda su Samha suke agaba.
Galadima kam mun barsa a harabar gidan yana waya.
Ai kaina bai gama kwancewa ba saida muka shiga falon gidan, hummm manyan k’asarmu sunajin dad’insu gaskiya, yo kanada irin wannan gidan a k’asar daba takaba to k’asarka kumafa?.
A falo muka zube bayi suka Shiga hidima damu, muna zaune a wajen Galadima yashigo, shima zaman yayi ya aza k’afa d’aya bisa d’aya, Sauban yazuba ruwa a cup yabashi, kar6a yay yana fad’in “thanks”.
Ya kalli baiwar datake shirya abinci daga can gefenmu, “k zonan”.
Da sairi ta ajiye spoons d’in hannunta tanufo inda muke, agabansa ta zube tace “gani ranka ya dad’e”.
“kisamu wata ta tayaki Ku gyara d’akin can nakusada Samha yanzun nan”.
“angama ranka ya dad’e”. tayi maganar cikeda tdantsar ladabi.
Aunty Mimi Na najinsa batace uffanba. Shigowar momma tasaka khaleel tashi da gudu yaje ya tarbota, itama Samha zuwata ta kwakwameta, tunkan ma afad’amin nagane mahaifiyarsu Galadima ce, koda yanda fuskar kowannensu ta washe da farincikin ganin juna.
Hankalinta Na kaina tana murmushi da fad’in “oyoyo d’iyata”.
Zamowa nayi daga kujerar na durk’usa har k’asa ina gaisheta, ta k’araso inda nake ta kama hannuna ta tadani nakoma saman kujerar, “zauna kinji, sannunku da zuwa, kinsha hanya ko?”.
Murmushi nayi ina duk’ar da kaina.
Galadima yace “wai Momma dan ALLAH duk baki ganmu baneba?”.
Kallonsa tayi cikin Hararar wasa, tace, “yo naganku bata taku nakeba”.
Su aunty Mimi dariya suka Sanya, yayinda Galadima yad’an 6ata rai yana fad’in “da tsohuwar Zuma dai ake Magani Momma”.
“a fad’arka ba, amma sabuwa ma aitafi aiki da dad’i”.
Nidai murmushi nakeyi, Dan wasan nasu ya burgeni, inason ganin family haka cikin farinciki, gaskiya sai sunfi jin dad’in zaman nan fiyema da masarautar sun can.
Gaishe-gaishe aka shigayi, kowa yana k’ok’arin bama Momma labarin yanda biki ya kasance, sai dad’i takeji da sanya albarka, nidai nida Galadima babu mai cewa komai.
Mik’ewa Galadima yayi, “bara nad’an watsa ruwa Momma”.
“to afito lafiya Muh’d”. ta kalleni nima, “d’iyata tashi kibi mijinki kiyi wanka kuzo ga abinci”.
Harya fara tafiya saiya tsaya, juyiwa yayi yana mata magana a yaren daban saniba.
Ta galla masa harara da masa dak’uwa, itama bansan mitace masaba. naga dai ya tura baki yaci gaba da tafiyarsa. ita kuma tace natashi naje.
(Wai ashe cayay mata ai yasa a gyaramin d’akin da zan zauna, shine tamasa dak’uwa tana cewa d’akin safa?, shi idan ance Araba mana d’aki saiya amince?, to tare zamu zauna, shine yakuma cewa ammafa d’akinsa ai ba kowa ke shigaba, tace tasani aii, muje nima sirrinsace ai, shinefa ya tura baki gaba).

Kamar an maken k’afafu haka nabisa abaya muna taka steps d’in benen, har muka isa k’aramin falo mai k’yau, komai farine a wajen, TV ce kawai takasance bak’a.
Falon yad’anyi k’ura alamun ba’a gyaraba (babu mai aikin dake hawa samansa, gashi kuma sunyi tafiya suduka, Momma kuma batada time d’in gyara masa d’aki).
Guntun tsaki yaja yana yamutsa fuska, d’an zaman danayi dashi na fuskanci bayason k’azanta komin k’ank’antar datti yata yamutse fuka kenan, bamu tsaya ananba muka shiga bedroom d’in bayan yabud’e, mayataccen k’amshinsa yana manne da d’akin, sai dai nan d’inma yayi k’ura, waya yazaro yayi kira, ashe Samha yakira, yace “k zoki gyaramin d’aki”.
Bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
Bance masa uffanba nima nataka nawucesa, bina yayi da kallo dan yaga ina zanje?.
Zanin gadon na yaye duka, nacire rigar filaluwan tareda rumfar da akama gadon, shidai kallona kawai yakeyi, yana tsaye jingine da bango (baiyi tunanin zance zan gyaraba).
Knocking d’in da akayine yabada izinin shigowa, Samha ce d’auke da kayan tsintsiya, ta zubesu a k’asa tana fad’in “aunty kibarsa zan gyara”.
Kaina na girgiza nace “barshi Samha, nunamin kawai yanda zanyi, kije kema ki huta”.
Nunamin komai tayi, har inda bedsheets suke, tafice a d’arare da zaton Galadima zai hanata yace takoma ta gyara.
Amma saitaji baice komaiba, yama kauda kansa gefe kamar baisan munayiba.
Bathroom nashiga, nazage sosai na tsaftaceshi, Dana k’urarce kawai, duk abinda zaisa toilet k’amshi da tsafta nasakashi, saida naganshi need sannan nafito, ban iskeshi a d’akinba, Dan haka hankali kwance Nagyara bedroom d’inma nagama, nasaka kamshi sosai. falon nafito danufi gyarawa, sainaga Samha harta gama itama tana saka air fresheners masu dad’in k’amshi, da turaren wuta irin namu na gargajiya.
Sannu da aiki namata, itama tamin, Galadima yafito daga wata k’ofa yawucemu batareda ya tankaba, bedroom d’in yakoma.
Kallon Samha nayi nace, “saura wannan d’akin daya fito cikin ko?”.
“ai Aunty wannan d’akin dakansa yake gyarawa, babu mai shigarsa duk gidannan inba Momma da Mummy na da shiba”.
Cikin mamaki nace “miya sa to?”.
“d’akin sirrinsa ne aunty”.
Ban fahimci maganarba, bankuma tambayeta ba, ta tattara kayan damukayi amfani dasu tafice tana fad’in “aunty bara naje nayi wanka, dama wankan zanyi yakirani”.
Kaina kawai na iya d’aga mata, saman kujerar na zauna shiru ina nazarin maganarta, miye kuma ma’anar d’akin sirri? nashiga k’ololuwar nazari banyi zaton time yawuce hakaba, k’afata yad’an shura, nad’ago idona ad’an firgice na kallesa, haryayi wankan yana sanye cikin jajayen kaya na Adidas, sun masa k’yau sosai.
Juyawa yay zai sauka k’asa yana fad’in “kitashi kije kiyi wanka”.
Bai jira cewata ba ya sauka.
Nima saina tashi nayi yanda yace, d’akinsa sosai ya had’u gaskiya, harma bansan Yaya zan fasalta mukuba, nasan farin Abu namai tsaftane, lallai yanada tsafta, daga bedroom parlour zuwa bathroom nashi komai farine, bedroom d’inne kawai keda d’an sirkin Golden kad’an-kad’an shima.
Nidai ina wanka da d’unbin tunani, haka kawai naji kwad’ayin son Shiga d’akin sirrin nasa.
Koda na fito saina saka zani da riga na atanfa, ban shafa komaiba na d’auki turarensa na saka saboda neman magana??. ina tsaka da saka turaren Samha tashigo kirana.
Ajiyewa nayi na d’auki gyale nabi bayanta.

Falon k’asa muka sakko, inda aka shirya abincin saman wata lallausar darduma, duk suna a zaune har Momma, kusada Galadima daketa cin abincinsa ko kallon mutane bayayi Aunty Mimi ta nunamin wai na zauna.
Kamar nafasa kuka haka naji, Sauban dake gefen haggunsa yace, “auntynmu har yanzu amarcin bai k’are bane? kin shige d’aki kinyi bulum”.
Murmushi kawai nayi na k’asa ce masa komai, dan yabani kunya gaskiya, nakula kuma yanada yawan tsokana, aunty Mimi kam dariya tayi, yayinda Samha tarufe baki tanayin tata.
Momma tamasa dak’uwa, “o kai Sauban ALLAH ya shiryeka, kowama bazaka d’agama k’afaba?”.
Dariya ya kumayi yana satar kallon Galadima dayay tamkar baya wajen, yace “to ai gaskiya nafad’a Momma. dan ALLAH aunty ba haka bane?”.
“gaskiyarka fa Sauban”. Aunty Mimi ta fad’a tana dariya.
Momma tace “barsu kinji my daughter, ci abincinki”.
Kai na jinjina mata cikeda kunya.
Galadima dai har yanzu baice k’alaba, baima d’ago ya kallemu ba.
Haka muka ci abincin nidai duk a takure nake, kamar yanda yafara cin abinci haka yarigamu kammalawa, tashi yay yabar wajen, yakoma can saman wasu kujeru guda biyu ya zauna, laptop d’in dake saman table d’in wajen ya d’auka ya kunna, da alama shiya ajiye kayansa.

Bayan mun gama duk muka mik’e, kowa ya hau shirin zuwa asibiti duba Abie, time d’in barcin sane shiyyasa ma Momma tasamu tataho, jakadiya kawai aka bari a wajen, itama a waje, da yake in time d’in barcinsa yayi kowa fitowa yake daga d’akin a barsa shi kad’ai.

Galadima saboda aikin da yakeyi yace muyi gaba shima zai taho.
Momma tace “to matarka ta zauna ta jiraka, mudai mun tafi”.
Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru, cigaba yayi da aikinsa harsuka fice, jinai kamar nace nidai zan bisu kawai. Amma na makaro, dan harma sun fice abinsu.
Ganinai tsayuwa ta isheni, shikuma d’an latsin baice na zauna ba, sai kawai naje na zauna d’ayar kujerar dake kallon tasa, nima na d’ora k’afa d’aya kan d’aya tamkar yanda yayi. nayi gefe da kaina cikin basarwa.
Daina danna System d’in yayi, ya d’ago idanu yana kallona, yayinda yake Murza hannunsa na haggu daya d’ora guywar a hannun kujera hannun yana sama, yinai tamkarma bansan yana kallona ba kwata-kwata.
cije lips d’insa yayi kad’an, ya janye idonsa ya maida ga system d’in, aransa yana mamakin izzar yarinyarnan, tabbas data fito gidan sarauta da anga mulkin tsiya.
Falon shiru babu kowa, tunda kuyangin suka gama hidimarsu duk suka koma 6angarensu dake can baya.
Kusan mintuna 40 yagama abinda yakeyi, laptop d’in ya kashe sannan ya mik’e, batare da ya kalleni ba yace “muje”.
Saida na d’an ja wasu seconds sannan na mik’e, saidama ya juyo ya kalleni, dan har yakai k’ofar fita.
Gyalena na maida saman kai nabiyo bayansa, a k’ofa na iskeshi tsaye, na fito shikuma ya daddana wasu madannai agefen k’ofar, Ashe wai security yasaka.
Ranar farko danaga yayi tuk’i da kansa, dogarin dasuke gate suka bud’e mana muka fice.
Tunda muka tafi ba Wanda yayma wani magana, shi yanata deriving d’insa nikam ina kalle-kalle abuna, mun Isa katafaren asibiti mai k’yawun gaske, inma badan sunanba da saika d’auka wani wajen shak’atawa ne, asibitin ya had’u gaskiya, har ciki muka shiga bayan security sun mana ‘yan tambayoyi dakuma gaisawa da sukayi, naga alamar sun sanshi sosai, amma duk da haka saida akai searching d’inmu.
Abin ya birgeni gaskiya, inda aka tanada domin parking ya tsaya, ya kashe motar sannan muka fito kusan a atare, bai tafiba saida na zagayo, muka jera zuwa ciki, yanata gaisuwa da jama’a, ina mamakin yanda ya iya yarurrukansu, nikam dai saidai da turanci nake gaishesu, kuma ba kowaba.
Mun fara zuwa office d’in wani doctor, suka d’an tattauna akan cigaban da aka samu na jikin Abie, mun gaisa dashi yaymana murnar aure, murmushi kawai nayi, sai Galadima ne ya amsa masa.
Daga nan muka shiga d’akin da Abie yake jiyya, iyalansa su aunty Mimi duk suna zagaye dashi, nidai a raina danaga d’akin nace oni kamar ba Asibitiba?.
Tunda muka shigo fuskar dattijon dake kwance a gadon ta fad’ad’a da murmushi, kallo d’aya namasa naga kamanninsa dana hoton d’akin Galadima na Nigeria.
Gabansa muka k’arasa, Galadima ya durk’usa yarik’o hannunsa, nima saina durk’usa ina gaidashi da Hausa.
Momma ce tazo ta kamani na tashi, cikin wani yanayi tace, “d’iyata ai Abban naku baya iya magana kinji”.
Da sauri na kallesa, ya sakarmin murmushi, sai kawai na mayar masa hawaye nabin kumatuna domin tausayi, duk kallona sukeyi sukam, harda Galadima.
Kuma zamewa nayi na durk’usa a gaban gadon, cikin rawar murya nafara jera masa addu’ar samun sauk’i wajen ubangiji. duk suna amsamin da amin.
Murmushi yakasa barin face d’in dattijon, Wanda k’aunata take shigarsa har zuciyarsa, Momma takuma d’agoni a karo na biyu ta rungume tana lallashina.
Galadima ya had’iye hawayen dake Neman zubo masa shima, yafara gaida Abie dake murmushi, da ido ya nuna masani wai ya lallasheni mana.
Sai Galadima yayi murmushin jin kunya yana susar k’eya.
Murmushi Abie yayi sosai, har hakwaransa na bayyana.

Ban ta6a jin tausayin Galadima ba sai yau, dama haka suke cikin tashin hankali? Lallai dan ba’aga dariya a fuskarsa ba ba laifi baneba, nama yabama k’ok’arinsa yanda yake zirga-zirga tsakanin Nigeria da nan d’in.
Ahaka akaita firar dani bana fahimta, danshi Abie da idanu yake maganar.
Bamu baro asibitinba sai dare sosai, a can mukayi salloli dacin abinci.
Mun taho muka baro Momma a can, jakadiya ma ta biyomu, dama Momma kad’ai ke kwana a wajensa, shima ba kullumba, dan wasu ranakun basa bari a kwana dashi, a sati sau uku take kwana a wajensa.

**********

Tunda muka baro asibitin tsohonnan ketamin yawo a zuciya da ruhi, sai cud’awa nake da kwancewa, inason jin labarin masarautar su Galadima gaskiya.

Yanzun ma iza k’eyarmu aunty Mimi tayi muka wuce d’akinsa, muna zuwa bathroom yashiga, kusan mintina 25 saigashi yafito, da Alama wanka yayi, harya sauyo kayan barci aciki, dama da abinsa yashiga.
Nima tashi nayi nashiga da nawa masu kauri a hannu. Wankan nayi da shirin barci, sannan nasako hijjab na fito.
Saman gado na iskeshi yawani barbaje a tsakiya, alamar baya buk’atar wani ya hau.
Na ta6e bakina, a raina nace koma bakayi hakaba ai bazan ta6a had’a makwanci da kaiba, aikin banza kawai, naja tsaki a zuciyata.
Saman sofar d’akin na hau na kwanta, inata tunanin Abie da ma tsalarsa.

Kasa daurewa nayi, na kallesa nace, “ wai miye matsalar Abie (kamar yanda naji suna fad’a)”.
Shiru yamin, harma na zata yayi barci, sai can yacemin “ciwone dai kawai”. daga haka yaja bakinsa yay shiru.
Nima shirin nayi, dan bakuma nida abin fad’a, musamman yanda yabani amsar.
Nidai zan iya cewa barcina na daren ranar rabi da rabine, kewar ‘yan uwana da bak’unta, gakuma matsalar babansu Galadima data k’asa Barin zuciyata.
Da asuba narigashi tashima, na fito toilet bayan gama d’aura alwala na iskeshi zaune bakin gado dafe da kai, k’ala bance masaba nad’au abin salla na shinfid’a, tashi yayi ya shiga bayin yana Jan tsaki a zuciyarsa, Shifa wlhy dukya takura, yasaba zamansa shikad’ai a d’akinsa, yanzu duk anzo an cika masa??.
Haryaje k’ofar toilet d’in yadawo baya, doguwar riga ya d’auka ya shige, saida yay wanka da brush sannan yayo alwala yafito sanye cikin jallabiya blue.
Turare yad’an fesa sannan ya d’au key d’in mota yafita, Ashe inda yake zuwa sallan can gaban gidanne, kuma daga sallar asuba yake wucewa asibiti ya kar6i Momma tataho gida itakuma, duk ranar weekend haka yakeyi, yanzu kuwa yana cikin hutune.
Da yake ina sallah yafita, banyi zaton yafita kenanba, bayan na idar saina d’an kwanta, maganar d’akin sirrinsa ce taita cin zuciyata, namik’e nafita, saida na lek’a falon k’asa naga babu kowa sannan nadawo, cikin tantama na murd’a k’ofar d’akin, sai naga ta bud’e, banyi zaton hakaba gaskiya, musamman danaji an kira d’akin dana sirri. (bakisan ya manta bane bai rufeba Munaya?? dan harda security a d’akin).
‘Dakin k’aramine bashida wani girma, gaba d’aya bangon d’akin zagaye yake da hotuna, sai Computers guda hud’u da kuje d’aya gabanta akwai deck’s babba, wanda duk Computers d’in akansa suke, sai pens da yawa cikin wani d’an Abu, gefe kuma k’aramar loka Ce ta glass cikeda takardu, gakuma tarin wasu takardun kashi-kashi da akayi kamar files a seman decks d’in, matsawa nayi jikin bangon nafara kallon picture’s d’in, hotunan mutanene daban-daban, harda wasu manya dana Sani a TV, mafi yawa yayi rubutu a k’asan kowanne photo, bana fahimtar rubutun gaskiya, danhaka nacigaba da kallon picture’s d’in kawai, harda na mama Fulani,??
??
Kutu melesi hotona fa jama’a a d’akin sirri, naga idi, nakaranta rubuntun k’asan yafi sau goma ban fahimci komaiba, saiwasu lissafi-lissafi kamar mai rubutun Mathematics??.
Na Muftahu nagani a k’arshe, abinfa ya d’aure minkai, mu kuma ni da amininsa Muftahu miya kawomu d’akin sirri?????.
Agogon d’akin na kalla naga 7am tayi, da sauri nafita gudun karya zo ya sameni.
Na rufe k’ofar a hankali nakoma bedroom d’insa, ajiyar zuciyata na sauke ganin bai dawoba.
Zama nayi na zabga tagumi ina tunanin ma’anar wad’ancan pictures d’in dana gani, danma a tsorace nake, ban nutsu tsaf naganiba??????.

Ban sauka k’asaba saida 9am tayi agogon k’asar, na iske su Samha suna breakfast, harda Momma, na durk’usa har k’asa na gaidasu itada aunty Mimi, cikeda fara’a suka amsa.
Momma tace “ai nayi zaton barci kike, shiyyasa na hana a tadoki”.
Cikeda kunya nace “a’a na tashi tun d’azun”.
Aunty Mimi ta zaunar dani kusada ita, Sauban ya had’omin komai na breakfast d’in.
Yanzun ma a kunyace naci abincin, kunyata na burge Momma sosai.

Bayan mun kammalane Momma ta kama hannuna muka shiga d’akin ta, a bakin gado ta zaunar dani itama ta zauna, anutse ta kira sunana.
Hakan yasani maida hankalina a kanta nima dan nakula magana mai muhimmanci zamuyi da ita…………???

*_tofa, mi Momma zata fad’ama Munaya kuma?._*??

*_Ya ALLAH ka gafartama Iyayenmu??????_*
*_Typing??_*

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply