Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 3


Raina Kama Book 1 Page 3
Viral

………Fad’a sosai innarmu tamin akan Marin Safara’u danayi, sannan ta d’ora da nasiha kamar yanda tasaba, wani kam yashiga kunnena, wani kuwa tabaya yabi, dan harga ALLAH Na daina zama kowa yana taka mana mahaifiya a gidan.
Innarmu tace, “ku shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Ku tafi gidan mamanku Rabi’a Ku k’arasa hutunku, banason zamanku a gidan nan tunda fitina yake kawowa”.
A sanyaye Munubiya ta amsa da “to innarmu”.
Amma ni saina tunzuro baki gaba ina k’unk’uni, dan banason tafiya ko ina, canma saboda d’an mama Rabi’a d’inne Marwan, ko kad’an bama shiri dashi, saboda masifarsa. “kai innarmu, yanzu dan ALLAH saboda wasu can bazamu mik’e kafa yanda mukeso ba agidanmu, duka fa hutun sati biyu ne kacal, amma saimunje wani waje?, ni wlhy inkika barni babu mai k’ara mana koda kallon banza a gidannan, harma innaro bazan bartaba………”
Maficin danaga innarmu tajawo yasani tashi da sauri nabar gurin, Na tabbata shirin bugamin takeyi. Munubiya ta saka dariya tana kallona, “ke ga rashin arzik’i ga tsoron tsiya, dukan maficin kikema wannan gudun?”.
Harara Na balla mata, “yo k’ya fad’i haka mana tunda ba jikinki baneba, tsoro kam kinsan waye matsoraci acikinmu ai”.
Munubiya ta ta6e baki “naji dai, koma mizaki ce kije kiyita cewa, inama kayana dakika saka jiya? na wanke, dan dasu zanje”.
Wayar innarmu Na d’auka ina dannawa, batareda na bata amsaba Na nuna mata laundry basket d’inmu.
Innarmu tace, “to Aljanar waya ajiyemin kafin ki k’ararmin kud’in ciki, ina taki?”.
“kai innarmu, please mana, zan kira Ayusher nefa nasanar mata muna zuwa gobe, ALLAH wayata babu ko nera aciki Munu ta cinye min jiya”.
“kiji tsoron ALLAH munaya, Nina cinye mini kud’in waya? bake kika kira Balkisu ba da kanki?”.
“to dana kirata sai nace kuyita surutu har kud’ina ya k’are”
innarmu Na shirin yin magana muka jiyo kururuwar kukan Safara’u da Rahama. dariya Na k’yalk’yale da ita, ina fad’in “o, ALLAH ga yaa hameed can yana gwajin kwanji a jikin gayu”.
Harara innarmu ta ballamin, saikuma tamik’e tana shirin fita, nasan kar6arsu zataje, nai saurin fad’in “kai innarmu, kid’an barsu su lallasu mana”.
Dakk’uwa ta watsomin tareda fad’in “K’aniyarki Munaya”.
Dagani har Munubiya dariya muka sanya harda tafawa kuwa.

Ba’a rufa mintuna 3 da fitar innarmu ba muka fara jiyo hargowar Maman safara’u (dama ita bata magana a hankali) Yaa hameed takema masifa akan dukansu safara’u dayakeyi, maman su yaa hameed babu hak’uri, itama tafito suka fara cacar baki, yaa hameed kam ficewarsa yayi bayan innarmu ta kwaci su Rahama a hannunsa da k’yar. kafin kace mi gidan yakuma kaurewa.
Munubiya tace, “kai jama’a ko breakfast ba’ayi agidanba har antafi wrestling zagaye na biyu”.
Na fad’a saman gado ina Dariya, danni mamaki ‘yan gidanmu nakeyi da bala’insu. wayar Innarmu tayi ringing, da Sauri Na duba sainaga Abbanmu ne, cikeda d’oki Na amsa tareda masa sallama sannan Na gaidashi.
Yace, “Munubiya ina maman takune?”.
“Abba ba munu bace, nicefa”.
“to to munaya ce? hayaniyar mi nakeji haka agidanne Munaya?”.
K’yafta min ido da zungurina Munubiya tashiga yi wai karna fad’a masa (dayake a Hans free nasaka wayar, tana jin komai) amma saina harareta da murgud’a baki nace, “Abba Mama Ce da maman safara’u suke fad’a”.
Tsaki yaja da fad’in “ALLAH ya shiryesu to, ina maman taku ne?”.
“Amin Abba, Innarmu tana can wajen rabon fad’an ai”.
“shike Nan, idan tashigo kice takirani muyi magana”.
“to Abba bye”.
Yace, “ok dear bye”. Sannan ya yanke wayar.
Ina yanke wayar Munubiya ta kaimin bugu, Na kauce ina dariya “yo da bakina a hanani fad’ar gaskiya”.
“ba hanaki akayiba, amma kinsan idan Allura ta tono garma mune tushen fad’an ai, kinkuma san halin Abba da d’aukar zafi kamar baba k’arami”.
“tab, ta k’are musu dai suda suka takalo wlhy, jarababbu dangin masifa”.
“kina ciki kenan tunda kema dangin kine ai”.
Dariya muka Sanya nida munubiya.

*washe gari*

Tafiyar mu gidan mama Rabi bai yuwuba, saboda dawowar Abbanmu, da innarmu ta sanar masa a waya zamuje can muk’arasa Hutu sai yace a’a muyi hak’uri mu zauna, Dan akwai bak’in da zaiyi a k’arshen sati (weekend), kuma yanason dukkan yaran mukasance muna nan.
Innarmu tace shikenan.
Wannan dalilinne ya hanamu tafiya Hutu, dama ni ba so nakeba, Munubiya ce keta zakwad’in tafiyar.

Yau ta kasance alhamis, tunda safe muka tashi da himmar wanki nida Munubiya, ina sharar sashenmu Munubiya na fidda kayan wankin, yayinda Aryan da Aiyan keta tara mana ruwa daga fanfo zuwa banbu.
Ina gama sharar na wanke hannuna na k’arasa bakin fanfo inda Munubiya ke k’ok’arin jik’a kayan. zama nayi bisa d’an dakali da akayi wajen saboda irin hakan, wanki ko wanke-wanke da sauransu, waya nake latsawa ina nemo mana wak’a, dan muji dad’in wankin, maganar aunty khaleesa kawai mukji a kanmu tana fad’in,
“k! Munaya tashi kije ki gyaramin d’akinmu, akwai wani zanina nan ki d’akkosa ku wankemin”.
Banza namata ban d’agoba, sai Munubiya ce tace, “to aunty khaleesa”.
Shirun danayi ina kuma tamke fuska yasata gane nice munaya, Dan haka ta kalli Munubiya dahar tatafi, “k Munubiya!… dawo, bakece zakiyiba, k! Dan uwarku Munaya tashi kije kimin”.
Da sauri Munubiya tace, “Aunty khaleesa ai nice munaya, waccan Munubiya ce”.
Hararta tayi, “mai dani ‘yar iska to, ko kina tunanin ban ganeku nima d’in?”.
Banyi niyyar d’agowa ba, amma jin abinda tafad’a yasani sakin guntun murmushi, nasan k’arya takeyi tace tana ganemu kai tsaye, yanzu ma dan kawai na nunu halin nawane shiyyasa tagane nice, kawai tafad’ane dai, mai da kaina nayi nacigaba da abinda nakeyi…….
Wata ashar ta lailayo ta makamin, tareda zaburowa tamkar zata dakeni, dai dai nan sallamar innaro ta karad’e tsakar gidan. mu duka kallonta mukayi, nikam kallo d’aya namata na d’auke kaina, (dan nikam natsani kakarnan tamu) Munubiya da aunty khaleesa suka gaidata, nikam a d’age nace “ina kwana”.
“kin yima uwarki Ai’sha dan Ubanki”, cewar innaro ta na nunani da d’anyatsanta manuniya????, tacigaba da fad’in “ni zakima gaisuwa a haka? kamar wata sa’ar uwarki?, aiko Aisha da ubanki basu isa sumin gaisuwa hakaba balle ke haihuwar yanzun”.
Baki na la6e, ba tareda na kalleta ba natashi nahau wankin, Munubiya kuma tawuce danta gyarama su aunty khaleesa d’akinsu. abinda nayi na nuna halin ko in kula saiya kuma tunzura innaro, ta fara hayagaga da matse kwalla wai naci zarafinta.
Wannan yasaka matan gidanmu da yara fara fitowa d’ai-d’ai suna kallonmu (dan al’adar gidanmu ce hakan, da anji kaya-kaya kowa zaiyo waje yaganema idonsa abinda ke faruwa).
Dady ya k’araso da sauri yana fad’in “Inna miya farune haka da kuka? Keda waye?”.
“wannan shed’aniyar yarinyar mana” tayi maganar tana nunani “waini yarinyar nan zataima d’ibar albarka saboda uwarsu kullum tana aibantani a gurinsu, shiyyasa duk sun rainani….”
Baki bud’e nake kallon innaro da sherinta. wlhy wannan tsohuwar bazataga Annabi ba……..
Maganar Dady ta dawo dani daga mamakin innaro. Yace, “Munaya ce ko Munubiya? miya farune keda inna?”.
Dady yanada sauk’i, ba kamar Abbanmu da baba k’arami ba sun fishi zafi.
Nace, “dady Munaya ce. wlhy babu abinda namata, kawaifa daga shigowarta duk muka gaidata, shine kawai ta hau zagina wai ban gaidata da k’yauba…….”
“amma ai gaisuwar rashin tarbiya kikai mata”. ‘cewar Aunty khaleesa’.
Dady zaiyi magana Aunty Ramlah tace, “wlhy Dady ba haka bane, duk abinda yafaru akan idona yafaru, dan nafito zan d’iba ruwa a fanfo”.
Dakuwa Innaro ta mata, “kinci uwarki hadiza, kema ashe munafukace ban saniba, to ko hadizar ta haifama Ai’sha ne ke?”.
Fakar idon Dady aunty Ramlah tayi ta dallama innaro harara, sannan tace, “yo daga fad’ar gaskiya, nidai wlhy Dady abinda nagani nakuma ji kenan”.
Girgiza kai Dady yayi, sannan yace, “kiyi hak’uri Inna, Munaya tayi kuskure amma bazata sakeba. Munaya zoki bata hak’uri”.
Ban musaba nazo har gabanta nace tayi hak’uri, bata amsamin ba, saima hararata datayi kawai. nima saina bar wajen nakoma kan wankina.
Dady Yakama hannun innaro suka shiga falonsa, matan gidanmu duk suka bar wajen, basuso wasan yak’are a nanba, sunso ace cin mutuncin innaro yasauka har kan innarmu.
Innarmu dake tsaye daga k’ofar falonta tanajiyo abinda ke faruwa dukda katanga ta shiga tsakiya, ta girgiza kai kawai tana komawa ciki da fad’in ALLAH ya k’yauta.

Ina wanki ina zubda hawaye, sosai raina ya sosu yau akan abinda Innaro tamin, dukda bawai yaune karon farko da hakan ya faruba, sai dai na yau yamin zafi ainun, har inaji natsani zaman gidanmu, a fili na furta ALLAH kabamu miji muyi aurenmu mubar gidannan”.
Munubiya dabansan tazo wajenba naji ta amsa da Amin sweetheart, wlhy koni yanzu addu’ar danake mana kenan, sai dai banason mutafi mubar innarmu a wannan halin dasu Aryaan”.
“hakane Munu…, karki damu, insha ALLAH munayin aure d’auke innarmu zamuyi ko Abbah ya yarda kobai yardaba wlhy!!”. ‘ta k’arashe maganar a harzuk’e’.
Murmushi Munubiya tayi, dan tasan ran ‘yar uwar tata yakai k’ololuwar 6aci.
Har muka gama wankin innaro na gidan bata tafiba, bamusan uwarmi takeyiba. dayake girkin gwaggon Haleema nema ranar. ina tsaye a bayan flowers d’in d’akinmu ina goge glass d’in windows naga Abdul yafito d’aukeda tire an jera sabbin kuloli akai, nasan Abbanmu baya gari, dan haka nace, “Abdul wazaka kaima abinci haka?”.
Yace, “Aunty zan kaima innaro tana falon dady”.
Kai na jinjina masa kawai nace jeka, cigaba nayi da aikina ina fad’in “shidai munafurci ai dodone, maishi yakeci”.
Koda na koma ciki sai nake bama Munubiya labari, innarmu dake bayanmu bamu saniba tace, “to ina ruwankine wai Munaya?, nifa banason gutsiri tsoma wlhy, wai sai yaushene zaku daina jamin fitina a gidanan ne?”.
A sanyaye mukace kiyi hak’uri innarmu“.
Batace komaiba tashige d’akinta, muduka da kallon tausayi muka bita, dukda tasan ita ake tauyema hak’i amma bata ta6a nuna itace mara laifi, kullum ta amince itace a k’asan kamar yanda kowa ke kallonta agidan.
https://2gnblog.blogspot.com/

?????

Washe gari Abbah yadawo da yamma, duk munyi murnar ganinsa, shima kuma hakan take a garesa.
Sai da daddare suka tara iyayenmu mata meeting shida Dady da baba k’arami.
Abbanmu yay gyaran murya sannan yace, “dama wani abune yasaka muka taraku, maganace akan yaranmu mata, Ramlah da khaleesa da Rahaima da Hauwa’u kowa yasan sun fida mazajen aure harma an tsaida bikinsu nanda bayan salla”.
Duk suka amsa da eh.
“yauwa to Alhmdllh, yanzu munada sauran yara ‘yan mata agidanan ak’alla su 8, kuma duk kusan Kansu d’ayane, dukda su Ramlah sun girmemusu, to wani uzirine yataso na tilas zamu had’awa auren wasunsu danasu khaleesa. shin ko akwai wad’anda a cikinsu sukeda tsayayye? domin a fiddasu?”.
Da sauri maman safara’u tace, “Safara’u nadashi, dan harma yanason turo iyayensa, amma nace ta dakatar dashi sai angama na yayyensu”.
“to Alhmdllhi, sai kuma wa?”.
Umma Ruk’ayya ma tace, “Fiddausi tanada tsayayye itama”.
“masha ALLAH, to bayansu fa?”.
“mamansu yaa hameed tace, “ai inaga sukenan kam Abban Hameed”.
“yanzu su 6 kenan suka rage? to dama Alhaji halliru d’an majalissar datta6ai, nasan duk kunsan abokinane shak’ik’i? to shine yanemi alfarmar nemama ‘ya’yansa maza biyu auren biyu daga cikin ‘ya’yana, d’aya d’ansane na cikinsa, d’aya kuma d’an yayarsane tarasu tabari yacigaba da rik’onsa. to harga ALLAH nasan yaransa sunada tarbiyya dan haka na amince, amma dukda haka saida nasake dogon bincike akan yaran saboda yaron yanzu ka haifeshine baka haifi halinsa ba, to Alhmdllh suma basuda wata matsala, dan haka mun yanke magana dashi akan suzo saisu za6a acikinsu, wannan shine dalilin dayasa muka taraku kenan”.

Hummm yaufa anzo da Sabon al’amari a gidan namu, nanafa iyayenmu mata suka hau tsugunne-tsugunne, kowa burinta ace d’iyarta aka za6a, harma da iyayensu safara’u dakeda mijin a hannu, ganin sunji gidan maik’one kowacce tafara k’ok’arin gani da fatan ‘yarta ta kasance acikin gidan, aiko sai shirye-shirye kowa keyi a asirce, aka fara gyara ‘ya’ya.
Mudai a 6angarenmu babu abinda innarmu kemana, hasalima inda taji maganar anan ta barta, komu bata sanarma ba, sai abakin Fauziyya mukejin komai.
Yanda ake shirye-shiryen bak’i takowanne 6angare saika d’auka ‘ya’ya. Shugaban k’asane zasuzo, ni abinma mamaki yabani dan kowanne d’aki da nasu shirin, dayake kowane d’aki akwai budurwa d’aya, mu 8ne, su shida kowanne d’aki 1 kenan, saimu mu biyu a d’akinmu, ‘ya’yan abbanmu mu 4 kenan, na baba k’arami 2 na Dady 2, gashi biyu za’a za6a acikinmu amma saika d’auka mu duka za’a za6a saboda shirye-shiryen da iyayenmu keyi.

Ranar Asabar (Saturday) kenan takama zasuzo, dan haka muduka ‘yan Matan 8 baba k’arami yace muhad’u muyi girkin tarbarsu.
Ni Munaya, Munubiya, Safara’u, Fauziyya, Haleematu, Fiddausi, Zarah, Siyama.
A kitchen d’in 6angarenmu muke girkin, dukda dai iyayenmu sun d’an saka mana hannu wajen tsara kalolin abincin daya dace a tanada. Ni abunma haushi yabani, yanda naga ‘yan uwana NATA rawar kai, sai wani k’alk’ale-k’alk’ale akema abinci da drinks na gargajiya damuka had’a.
A raina nace Kodai sune iyayen cin tsiya, ai bazasuci ko quarter d’in abincinnan ba, wannanma ai almabazzaranci ne wlhy, mutun biyu kawai amma anmusu abinci wajen kala 6, banda kuma kayan ciye-ciye irinsu snakes da nau’in nama da aka sarrafa zuwa daban-daban. haka dai muka gama aka kai falon baba k’arami aka shirya, sannan kowa takoma 6angarensu danta kimtsa……..???

Anan ne za’ayi kece rainin????????????

Guys kumuje zuwa??????

One luv????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing??_*

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce????_*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply