Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 30


Raina Kama Book 1 Page 30
Viral

??3?0?

………………Da sallama ciki-ciki ya shigo, nayi saurin maida zip d’in rigata sama nafasa cirewa, a sace ya kalleni yawuce bakin gadon ya zaune tareda dafe kansa.
Kallonsa nayi Na kauda idona nima, kusan mintuna 3 kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa. d’agowa yayi yakuma kallona, kamar an masa dole yake maganar cikeda k’asaita, “k! Wai bazakima Momma magana ba kikoma d’akinki?”.
Kamar bazanyi maganaba saikuma nayi batare da Na kallesaba, “inaga kaine yakamata kamata maganar ai, dan nima zanfi son haka, duk nabi Na takura zama da Namiji d’aki d’aya”.
Banza yamin bai sake tankawa ba, saima yamik’e yana jan k’aramin tsaki, nikam Na ta6e baki a zuciyata ina fad’in ka iya fad’ar R kafin kamin mazurai.
Baima san ina yiba, yaje wajen wardrobe d’insa ya d’auki kayan barci yanufi bathroom.
Murmushi kawai nayi, danni rayuwar mutuminnan mamaki take bani, ina dad’i kabi ka k’untata kanka irin haka? baka hira da kowa, baka dariya, shifa ko kallo inba labaraiba ban ta6a ganin yanayiba, hakama wak’a banta6a jin yana jiba, koranar dana duba wayarsa karatun Qur’an kawai nagani da Tafseer. nakai dubana gawata ‘Yar kanta dakecan gefe a bedroom d’in nasa, mafi yawanci littatafan addini ne awajen, sai English Novels. (To yayi karatun addinine? tunda naji Momma tace anan India ya girma??). Wata zuciya tacemin su India basuda musulmai ne?. “hakane kumafa” nafad’a a fili ina mik’ewa.
Ganinaima bara nacire kayana kafin yafito, daya fito saina shiga nima.
Har ga ALLAH banyi tunanin fitowarsa ba yanzun, dan haka hankalina kwance na zuge zip d’in rigar, na cireta gaba d’aya, shima sket d’in nayi k’asa dashi yafad’i k’asa.
Juyowarnan da zanyi da nufin d’aukar towel dana ajiye saman akwatina sai kawai naga mutum tsaye a k’ofar bathroom, hannunsa rik’eda k’aramin towel yayi tsaye yana kallona.
Bansan Na kwalla k’araba wlhy, Na rarumi towel d’in nayi saurin kare jikina, ALLAH ma yaso k’ofar a rufe take, dan dawuya su Aunty Mimi sujini.
K’arata tadawo dashi daga sumar tsayen dayayi, yawani kauda kansa cikeda basarwa yana ta6e baki, saikuma yaja guntun tsaki yaje bakin gadon ya zauna yana cigaba da goge fuskarsa, dan har yayi shirin barcinsa a ciki.

Jinayi tamkar na makesa, d’an rainin hankali yagama kalleni zai wani miskile fuska asfa baiga abin kalloba. hijjabin sallata na janyo Na saka, sannan nawuce bayi ina hararsa.
Ina shiga yamik’e yana wani munafukin murmushi, abin salla ya shinfid’a ya kabbara shafa’i da wutiri.
Nadad’e abayin nak’i fitowa, saida nabar jin motsinsa duka sannan Na fito, dayake nayi shirina a bayin nima, nazata ya kwanta, amma saina iskeshi zaune a kujerar dake gefen kantar littatafan nan ya bud’e laptop yana danne-danne, gefensa kofine yanata turiri, da alama coffee ne aciki.
Yad’an juyamin baya kad’an, dan haka cikin sand’a Na rufe k’ofar, nakuma tako a hankali har zuwa wajen sofa Na kwanta, duk zatona baya ganina, Ashe yana kallon duk abinda nakeyi ta gefen idonsa.
A ransa yace munafunci. cigaba yay da aikinsa hankaki kwance, bai bar wajenba har kusan 1:30pm, maimakon ya kwanta sainaga yashiga bayi ya d’auro alwala.
Nima har time d’in barci yakasa d’aukata, maganar Momma tanata min yawo a zuciyata, tunanin ta inda zan taimaki Galadima kawai nakeyi.
Ina kallonsa ya kabbara salla. saida yay kusan raka’a 6 yanayi yana sallamewa, daganan ya d’auki alku’ani yafara karatu k’asa-k’asa.
Masha ALLAH nafad’a a raina, danjin yanda muryarsa ke fita cikin karatun littafi mai tsarki, gashi yana fidda kowane harafi cikin tsantseni da kwarewa. Tun ina saurarensa har wani barci mai dad’i ya saceni, bansan lokacin daya kammala ba yazo ya kwanta.

Muduka makara mukayi sallar asuba yau, dan haka shima yau a gida yayi.
Bayan ya idar waya ya d’auka naga yayi kira.
Bayan an d’aga daga can sukayi gaisuwa, jin ya tambayi ya Nigeria Na gane da ‘yan can yake wayar. yacigaba da fad’in.
“Nuren naga ka turomin hotonsa, shin a inane yake haka?”.
Bansan mi akace masaba daga can, naga dai yayi kwafa, sai yace “ya maganar Minister? dan nagansa wajen d’urin aurena, ban kuma yi zaton zai zoba”.
Canma aka kuma yin wata maganar.
Zamansa yagyara, yakuma jingina da bangon, dayake yana kan abin salla har yanzun. “kayi k’ok’ari Nuren, yanzu abinda nakeso dakai shine, akwai yarinyarsa d’inan datake karatu a nan jami’ar Abuja, inason a sacemin ita k’arshen watannan, yanzu ka saka ana bibiyarmin komai nata, Shikuma Alhaji Balala driver n sa zaku d’aukemin, dan bincikena ya ganomin shekarunsa 30 dawani Abu yana masa aiki, kuma randa su Alhaji balala sukayi zama da Abie shine ya kaisa masarautar mu, inada tabbacin zai San wani Abu koda kad’anne, kuyi aikinku da kulawa Nuren, banason asami matsala kamar wancan time d’in, gobe kashiga birnin gayu plaza kuyi zama Na musamman da Saleem akan maganar CCTV camera data daina aiki randa abinnan ya faru, ni naso Na zauna dashi, amma kaga Momma tamatsa akan dawowata”.
bayan nacan yagama magana.
Yace “ok babu damuwa, zan turo maka number yarinyar, saiku bibiyeta tanan. sai anjima, ka gaidamin Mom d’ina”.
Koda ya ajiye wayar saiya koma gado ya kwanta abinsa, nikam ina zaune sai cud’awa da kwancewa nakeyi, ban fahimci wayar tasaba gaba d’aya, shin wanene kuma NUREN!? shikuma miye alak’arsa da Galadima kuma?.
Tabbas aikina bazai yuwuba saina San wanene NUREN, wane kuma aiki yakema Galadima a sirrence, su waye wad’annan mutanen biyu daya ambata Minister da Alhaji balala? suna cikin wancan case d’in Na Abie ne? kokuwa tasu dabance?.
Kwanciya ta na juya yanda zanji dad’in tunanin da k’yau, saikuma naga ai ba sanin waye Nuren bane matsalata yanzu, kamata yayi nafara sanin shi kansa Galadima d’in da rayuwarsa, na tuna maganar Momma da tece “shi mutumne dabashi da yadda”. Mutum mara yarda kuwa yanada wuyar sha’ani, kad’an na juyo na kallesa, idonsa a rufe yake, amma ban yarda barci yakeba, na janye idona nima na maida lumshe, barcine mai nauyi ya kwasheni, harya fita bamma saniba inata barci, babu kuma Wanda yazo ya tadani.
Sai around 11:30 na tashi, wani masifar ciwo kaina yakemin, haka dai na tak’ark’ara nayi wanka, nagyara d’akin sannan na sako k’asa, gidan shiru tamkar babu kowa, sai television daketa aiki, zama nayi bisa kujera dafe da kaina.
“ranki ya dad’e lafiya dai?”.
Bud’e idona nayi a hankali, sai naga jakadiya ce, namata murmushi tareda yunk’urin tashi zaune, “wlhy kaina ke ciwo jakadiya, halanma ke kad’aice ma a gidan?”.
“subahanalla, sannu ranki ya dad’e, bara na samo miki abinci saikisha magani, eh ni kad’aice ranki ya dad’e su Sauban sun tafi makaranta. Gimbiya Mimi kuma tana asibiti itama, taga kina barcine shiyyasa tahana a tadaki”.
Nace “ALLAH sarki”.
Wucewa tayi zuwa kitchen, babu dad’ewa saigata tadawo da tire, a gabana ta ajiye tana fad’in “gashi ranki ya dad’e, kici saikisha magani kafin Magajin gari yadawo saikuje asibiti”.
Kallonta nayi da mamaki, “jakadiya waye magajin gari kuma?”.
Tayi ‘Yar dariya, “ranki ya dad’e ina nufin mai gidanki, ai magajin gari nake cemasa”.
Murmushi nayi ina girgiza kai kawai, na had’a tea nasha, sannan nasha maganin, anan falon na kuma kwantawa, barci yakuma kwasheni.
Jakadiya na zaune tana gadina.
Da sallama ya shigo, jakadiya ta amsa tareda mik’ewa da sauri ta kar6i kayan hannunsa tana masa sannu da zuwa, yad’an saki fuska yana amsawa. d’aya acikin kujerun ya zauna, sai lokacin idonsa ya sauka kaina…..
maganar da jakadiya take masa ce yasakashi janye ido daga kaina ya maida kanta.
“ranka ya dad’e akai kayan samane?”.
“no jakadiya kibari zan hau dasu, ai sunmiki nauyi, ita wannan mike damunta tayi barci anan?”. ‘yay maganar yana maido idonsa kaina’.
“kanta ke ciwo ranka ya dad’e, amma tasha magani ma, shine barcin ya kwashe a wajen”.
Ido yad’an tsuramin, kafin ya cije lips d’insa kad’an.
Jakadiya tajuya zuwa kitchen, babu dad’ewa tadawo da ruwa ta ajiye masa.
Sannu yamata sannan yad’auka yana sha, itakuma tabar wajen.
Kofin da yasha ruwan ya ajiye, ya maida kansa jikin kujerar ya jingina kansa, tareda maida k’afarsa d’aya kan d’aya, lumshe idonsa yayi, ta k’asan ido yake kallona, tsawon lokaci yana a haka, yayinda nikuma nake barci bansan yana yibama.
Kamar an tasheni saina bud’e idona a hankali, dashi na fara tozali, dan haka namik’e zaune da sauri, tareda warware d’an kwalina na yafa, dan gown d’in material ce a jikina, gashi irin mai santsinan, kuma rigar takamani sosai, a raina nace dukma yagama kalleni, wama yasan tun yaushe yake anan?.

Duk abinda nakeyi yana kallona, sometimes yarinyar nan takan bashi dariya, a d’an zaman dayayi da ita yalura tanada kunya, saidai batason raini, bakuma tada tsoro ko kad’an, ganin ina Neman mik’ewa saiya bud’e idonsa.
Harna fara tafiya saina juyo, danjin kamar ana kallona. idonsa a kaina, amma saiya wani basar tareda janyewa.
Kaina kawai na girgiza, harzan cigaba da tafiya saina tuna nemanfa kusanci nake dashi domin cika alk’awarin Momma da zanyi, baya na dawo nakoma na zauna, muryata a sanyaye nace, “sannu da dawowa”.
Sosai na bashi mamaki, dan haka ya kalleni da k’yau, kamar zaiyi magana saikuma ya fasa, kusan minti 1 dawasu Second’s sannan yace “mike damunki kika kwanta anan?”.
“kainane ke ciwo amma yama daina”. maganar dayayice tabani mamaki.
Mik’ewa yayi yana fad’in “ba gulma tasaki k’inyin barci jiyaba, dole ai kitashi da ciwon kai”.
Galala nabishi da kallo, kai wannan guy d’in yafara bani tsoro, dama yasan banyi barciba jiya kenan? Anya guy d’innan baya gani har hanji??? nabishi da kallo yayinda yake taka step d’in benen cikeda izza, hanunsa d’aukeda ledojin daya kwashe a falon, saida ya 6acema ganina sannan na sauke ajiyar zuciya.

https://2gnblog.blogspot.com/

?*?*?*?*?*?*?

https://2gnblog.blogspot.com/
*_Nigeria_*

Tun bayan zuwanmu sallama da tafiyarmu ‘yan gidanmu sai suka dainama innarmu magana, musamman yanda sukaga anata fita da abubuwan dana bari a baiwa mutane, innarmu ko’a kwalar rigarta itakam, bata damu da rashin mata maganar dasukeba, harkokin gabanta kawai takeyi hankali kwance.
Innaro kam kud’in da Galadima yabata suka sakata d’agama innarmu k’afa, ko gaidata tayi cikin salama take amsa mata, a jiya harda siyoma su Aryaan sllifas, wai taganine a hanya sun mata k’yau ta siya musu, murmushi kawai innarmu tayi damata godiya ta kar6a.
Wannan k’yauta tasaka mamansu yaa Hameed kasa hak’uri taita sakin habaici, daga nan sauran matan gidanmu suka d’auka suma, innarmu saita saka karatun alkur’ani ma a waya tashige d’aki tarufe kanta.
Har sukaci suka tsire dan kansu sukayi shiru.
Kusan k’arfe hud’u na gamma saiga Zarah wujiga-wujiga tashigo gidan, ga ciki yafito masha ALLAH, Innarmu dake tsakar gida tana wankin kwanuka tayi saurin cewa “zarah lafiya?”.
Jikin innamu tafad’a ta fashe da kuka, “innarsu 2 ki taimakeni zai kasheni, wlhy bani na d’auka masa kud’iba, narantse da ALLAH……..”
Tuni ‘yan gidanmu duk sun fito, danjin kururuwar Zarah, mamansu yaa hameed tazo ta janyeta daga jikin innarmu, “k mahaukaciyar inace dabazaki nutsu kisan wazaki fad’ama matsalarki bane?”..
Oho ita Zarah ba wannan bane matsalarta a yanzun, takuma fad’awa jikin mamansun tana kuka da rantsuwar ba ita ta d’auki kud’iba.
Ganin tana neman yage musu zani a kasuwa sai mamansu tajata suka shige d’aki.
Wata dariyar gatsatsa maman Safara’u tayi, tareda ta6e baki tana kallon Gwaggon Haleematu dake k’usa da ita “to anfara da bismillah kenan? Wata 6 an koro yarinya da duka?……
Caraf Momy Hadiza ta k’ar6e “yo mai kashi a gindi ai baya toshe hanci yace makwafcinsa na wari, kidai iya bakinki tunda kema kinkai gidan wani”.
“can a bakinki, nakai kuwa, kuma tawa zama daram babu yaji balle nik’a gari, tunda ba auren hange-hange da tauye hak’in wasu namata ba, ai bama saikin zak’eba, munsan mai kaza a aljihu dama baya jimirin Asss!, indai nice kinga tafiyata, kiyi da wani ba niba”.
Tamkar Momy Hadiza zata daki maman Safara’u haka ta hayayyak’o mata, wannan hayaniya ce tafara jawo kunnen makwafta gidanmu, saiga innaro tamkar an jehota, ta shiga tambayar ba’asin hayaniyar, dansu Abbanmu duk suna wajen aiki.
Duk shiru sukai mata, sai innarmu Ce da maman Fauziyya suke fad’a mata abinda yafaru.
d’akin mamansu yaa hameed tashige domin jiyo ba’asin dawowar Zarah n.

Itadai innarmu jikinta duk yayi sanyi, wannan zamanin ko aurar da yaranka mata kayi tsugunne bata k’are makaba, dan sai ALLAH yabasu mazaje na garin dazasu iya hak’urin zama da juna, aurene tunkan ayisa zakaga angama kwashe masa albarka wajen buruka da bidi’oin biki, ga iyaye yanzu gaba d’aya hankalinsu Yakoma ga d’irkama ‘ya’yansu kayan mata kawai ba koya musu dabarun zaman aurenba, sun manta kayan mata basu kad’ai bane ma’aurata ke buk’ata a zaman aure, sudai sukan kawo wata nutsuwane da kuma dank’o cikin rayuwar auren, gaba d’aya yanzu zakiga gidajen auren Malam bahaushe sun canja, wuyarta dai akai yarinya miji ya kauda mata budurcine, wata biyu yayi yawa kwarnafinsa ya kwanta saiya fara Neman makusarta, gakuma yaran basuda wata dabara dazatasa su taka tsantsan ga zamantakewar, har yakai an sami sassaucin cin zarafi daga mazajen nasu, to an nuna musu kayan mata sune kawai jigon aure da hangar mallakar mijin kansa, to ALLAH ka zaunar mana dasu lafiya dai agidajensu.

Nace amin innarmu??????

????

Kusan minti 10 da shigarsa saina tashi nabi bayansa, waya nakeson ya aramin nayi kiran su innarmu Susan mun sauka lafiya.
Saida nai sallama yabani izinin shiga sannan, saman sofa na iskeshi zaune yana latsa waya, da alama waya yagama ko zaiyi.
Zama nayi a kujerar da yake karatu takusa da kanta, na kwantar da murya cikin sigar ladab nace “yalla6ai ka aramin waya dan ALLAH nayi kiran innarmu da Munubiya”.
Biris yay dani, sai zuwa can yad’ago ido ya kalleni, ya motsa baki zaiyi magana amma jin kai ya hanashi, saiyay shiru kuma yacigaba da latsa wayar, saida yamula dan kansa sannan yajawo ledar daya shigo da ita, wata k’aramar pink d’in souvenirs bag yamik’o min batareda yace uffanba.
Tasowa nayi zuwa gabansa zan kar6a, hanun bag d’in k’aramine, dan haka hanunmu ya had’u waje d’aya, ni da shi kowa saida yaji shock, yay saurin janye hannunsa, yayinda bag d’in tayi k’asa zata fad’i yay saurin kuma k’ok’arin tarewa kamar yanda nima nakawo hannun hagguna da sauri. Sai kawai na damk’e hannunsa kanmu ya gwaru waje d’aya.
Kowanne dafe kansa yayi da sauri, yayinda hanun damarsa dana hagguna suke tallafe da juna mun tare bag d’in karta fad’i.
Na kallesa tamkar zanyi kuka, dan wlhy naji zafi, kansa kamar kwakwa?.
Hararata yayi yana fad’in “k wane irin kaine dake haka?”.
Haushi saiya kamani, shi baiga nasaba sai nawa, na matso kwallar dasuka cikamin idona, cikin turo baki nace “kana niyyar fasan kai, shine zaka maida abun kaina?”.
Hanunsa daya dafe kai yasaka ya d’an bugi bakina, “k kinma rainani wlhy”.
K’asa na durk’ushe kawai nasaki masa kuka. ya waro ido da mamaki yana kallona, wannan d’an abin dayamin shine na kuka? yarinyar nan akwai rainin hankali fa”.
Ganin abin nawa azimunne saiya mik’e tsaye, tareda d’iremin wayarsa bisa cinyata ya shige bathroom.
Yana shiga nama bayansa gwalo, dama duk cikin takune, sonake kawai nagano lagwansa. goshina nad’an shafa dan gaskiya naji zafi, saima naji wajen kamar yafara kumbura.
Ban tashi a wajen ba nashiga loda numbar innarmu, amma tak’i shiga, saina saka ta Munubiya, itama tak’i tafiya, nad’an ja tsuka, ina kuma shafa goshin, kamar wasa wajen sai rad’ad’i yakemin, ina cikin mulmulawa da matse baki yafito, kallona yad’anyi kamar zai basar saikuma ya kasa, ya k’arasa jikin wardrobe d’insa yana bud’ewa, “har yanzu goshin zafi yake?”.
Kamar zanyi kuka nace, “eh wlhy ”.
Daina abinda yakeyi yayi yajuyo yana kallona, saikuma ya maida drowan yarufe yanufe inda nake zaune. A gabana ya d’urk’usa, k’amshin sabulun wankan ya daki hancina, hannunsa na haggu ya d’aura bisa kaina, ya d’aura na damar akan goshina, sanyin damshin ruwan da taushin hannunsa suka ratsa goshina, a hankali yafara mulmula goshin, nafara matse baki ina rik’e hannunsa, dan wlhy akwai zafi, “please kabarsa dan ALLAH, wlhy akwai zafi fa”, bai saurareniba, duk rik’e masa hannun danake saida ya mulmulamin sosai sannan yamik’e yana hararata da ta6e baki, “halan kekam kina jaririya ba’a miki wankan jegoba?”.
Baki na tunzuro masa, nace “ka kira innarmu ka tambayeta mana, ni ina zan sani”.
Batareda ya shiryaba ya murmusa yana barin wajen. Kayansa ya d’auka yakoma bayi danya sanya.
Nikuma saina mik’e nakoma kan sofa d’in ina bud’e bag d’in d’azun. kwalin wayane mai k’yau, wani dad’i ya kamani, amma saboda jan aji saina maida na ajiye gefena, nacigaba da danna kiran su innarmu.
A haka yafito ya sameni, yana sanye cikin Brown d’in wando da Navy blue t-shirts mai gajeren hannu, ya tsuke k’ugunsa, bai kalleniba yawuce wajen wani kwando mai k’yau da aka zuba sandunan wasan Golf a ciki??, guda biyu ya ciro, sannan ya tako inda nake yana fad’in “bani wayata idan kin gama”.
Fuska na marairaice nace “ALLAH kagani bamma yiba, tak’i shigama”.
Wayar ya kar6a ya duma number, bakinsa ya d’an ta6e “k bak’auyar inace dazaki kira number a haka? ko nan k’asarkice?”.
Tunawa nai da saina saka + ashe, nace “oh namanta saina saka + wlhy”.
Aljihu ya saka wayar, “saiki bari sai wani time d’in kuma, yanzu sauri nake ana jirana”.
Da sauri nace “zan bika please, wlhy gidan shiru babu dad’i”.
Yana fesa turare yace, “ba yauba, baga jakadiya nan a gidanba, yanzu kuma Khumar zai d’akko khaleel a school ai”.
Shiru nayi bance komaiba, saiya juyo ya kalleni, ganin na kwa6e fuska cikin damuwa saikuma yaji wani iri, juyawa yayi yagara kwalar rigarsa, kafin yaje drowan gefen gadonsa ya d’akko wasu album na pictures har hud’u, saman cinyata ya ajiye batareda yace uffanba, yakwashi sandunansa yakama hanyar fita, batareda ya juyoba yace “wad’annan kayan nakine ki duba”.
Kafin nabasa amsa harya fice abinsa.
Kaina na girgiza ina ta6e baki, a fili nace, “Alaramma mara R ALLAH ya gyarakama Momma kai dai”. (Kifad’a a gabansa mana yarinya. ????).

_______________,,___________,,,______

Da sauri mamansu yaa Hameed ta kwa6e bakin Zarah alamar tayi shiru, saboda shigowar innaro, innaro bata kulaba, dan haka ta zauna a kujerar falon idonta akan Zarah, ganin yanda duk jikinta shatin duka, “kekauwa zara’u miya sameki haka? Ga ciki?”.
Harara mamansu yaa hameed taketa zubama Zarah, amma ina bata kulaba, ta share kwallar fuskarta tana fad’in “innaro wai kud’i ya ajiye a gidan jiya, shinefa yaduba yau bai ganiba, ina kitchen yashigo yana tambayata wai kona canja musu wajene? shine nace bammasan yashigo da kud’i gidan ba bare harna canja musu waje, ko rufe baki bai bari nayiba ya fallamin mari, nikuma naji zafi namasa ALLAH ya Isa, shinefa kawai yacire belt d’in jikinsa yahau buguna, wlhy da k’yar nagudo na fito, nasan idan nashiga gidan Siyama zai iya bina har can, tunda gidan d’an uwansane, dak’yar nasamu napep a anguwar nataho gida”.
Innaro tarik’e ha6a tana fad’in “oh ni marwanatu jikar Falalu, yanzu shi Sa’eedunne yamiki haka da hankalinsa? toke kin tabbata baki d’aukar masa kud’iba?”.
“wlhy innaro ban d’auka ba, kinji na rantse miki, shi dama halinsane haka?, indai ransa ya6aci ko kika masa kuskure sai dai kawai kiji mari, wlhy zuwana gidannan tun bankai satiba yake marina idan namasa Abu, yaune harda duka, gashi ko kad’an bashida hak’uri, Abu kad’an yagani saiyayi tsogumi, idan kuma kin masa na kirki bazai yaba mikiba, dawuya kimabasa Abu sau 10 bai kushe 8 a cikiba, 2 kuma bawai zai nuna yaji dad’i baneba??”.
“kai amma wannan yaro anyi wulak’antaccen yaro, yoshi dama dukan mata yake akasa nabashi jikata? Bari su Auwalun suzo, koti zansa su kaishi, sai an kwatar miki hak’inki,”.
“nidai babu wani court k innaro, kawai akirasa amasa bayani a sasantamu nakoma d’akina, inason mijina wlhy”.
“enyeee! A lallai zara’u kinkai kuwa, nikike fad’ama kina son mijinki? to dan ubanki auwalu saiku tashi ki koma yanzu, idan yagadama anjima akiramu jana’izar gawarki”. fuuu tafito tana sababi, kayaya tunta da maimaita maganar da Zarah tafad’a mata yasaka ‘yan gidanmu fahimta komai, wasu dad’i har tsakar kansu, (yo dama gidanmu kowa bawani son d’an uwansa yakeba, salon munafurcine kawai da bariki na tsoffin mata).

‘Daki Momy Hadiza tashige takira Siyama danjin k’arin bayani, anan Siyaman ke sanar mata wai dama ba wannan ne karon farko da Sa’eed d’in yay Complain Zarah na d’auka masa kud’i ba”.
Momy Hadiza ta rabga salati tana fad’in “k ‘yarnan da gaske?”.
“wlhy kuwa Momy, yanzu haka ma gashi anan gidanmu suna maganar da Sulaiman”.
“to ALLAH ya k’yauta, ni dama auren ya mutu ki zauna daga ke saike, danni bama na k’aunar wannan had’in gambizar family d’in, komai yaro yamaka ido nakai”.
“yo nifa Momy wlhy yanzu haka bama magana da Zarah, daga ranar mun had’u da ita a gidan sunan Hanan k’anwarsu, toni shine ya kaini da kansa, itakuma Ashe bashi yakawitaba, shine ta tambayeni miyasa ban biya mata mun taho tareba? Nace mata ai shine yakawoni, itama nazata Sa’eed d’inne zai kawota, shinefa taketa faman fushi da gaba dani”.
“eye, kice tafara miki hassada kawai saboda taga mijinki tafi kulawa dake? to wlhy bance ki d’aga mata k’afaba, karma kituna da ubanki da ubanta ciki d’aya suka fito”.
“insha ALLAHU Momy bazan raga mataba”.
“yauwa ‘yar albarka. Yanzu yamaganar kud’in damukayi ranar? kinsan fa bikin nata tahowa?”.
“zan aiko miki Momy, wai Momy da gaske Munaya bata Nigeria? ”.
Tsaki Momy Hadiza taja, cikin bak’in ciki tace “haka dai iyayenta sukace, mudai bamuda tabbas tunda ba’a gabanmu jirgin yatashiba, anzo dai mana sallamar munafunci itada wannan miskilallen mijin nata”.
“aikam Momy indai da sunzo d’in to da gaskefa sun tafin, dan Sulaiman yacemin yaga Galadima a airport shekaranjiya da sister d’inan watawa, shikuma yaje raka babansune zaiyi tafiya”.
“suyita tafiyar mana, kema dan sakaraice ai, yo mi mijin nata yafi naki? Amma kod’an Honeymoon d’in nan da ake zuwa ke kin kasa sakashi ya kaiki”.
“lallai momyn nan, shikenan tunda laifina kike gani, nidai zan kiraki anjima, yanzu jirana suke nakai musu abinci”. ‘bata jira cewarta ba ta yanke wayar’.
Takaici yakuma kama Momy Hadiza, saitaja tsaki, amma saboda munafurci saita nufi d’akin mamansu yaa Hameed jiyo abinda ya maido Zarah gida. (Fuska biyu????).

*******************

Hotunan na ajiye nafara bud’e wayar, woow irinfa wayarsa ce komai da komai, saidai tawa pink ce, gakuma extra condom na wayar har kala uku, kai gsky wayar tayi babu k’arya, layin dana gani a ciki na d’auka na saka sannan na jona charge saboda d’oki, sauran ledojin nahau bud’ewa, duk kayan sawane k’ananu marasa nauyi, kuma bamasu fidda tairaiciba, zan iya sakasu gaban kowa, a raina nace Ashe Galadima yanada kirki haka?, saida nagama had’a kayan waje d’aya sannan na haye gadonsa da yaune karon farko zan haushi, nawani 6ararraje ina kallon hotunan, wasu hotunan abin dariya wlhy, dan wasu yana yarone k’arami, wani a makaranta, wani awajen wasan yara, wani a masarautarsu, wani tareda mom, wani da aunty mimi da sauban, duk inda suke da Abie saida nayi kuka, dan abie duk yana kwancene, k’alilanne yakeda lafiya sannan. wasu kam ya zube wayoyi yanata had’e-had’en abubuwa na wasan yara??.
Kallon hotunan ne suka d’aukemin hankali har wani lokaci dasu Sauban suka dawo, bamma san sun dawoba saida Samha tahawo saman.
Zama tayi tanamin bayanin wasu mutanen jikin hotunan muna dariya, bamu sakkoba saida Sauban ya hawo yakiramu.

******

Sai bayan isha’i suka dawo shida aunty mimi.
Ina d’aki zaune har sannan ina kallon pictures d’in ya shigo, d’ago kaina nayi na kalleshi tareda amsa masa sallamar. Namasa sannu da zuwa.
Ciki-ciki ya amsa yana zubewa bakin gadon, d’an kwanciya yayi kusan minti 10 kafin yamik’e yashiga bathroom, kusan 1hour sannan yafito maybe su yalla6ai an sauke nauyine (????).

Yau saida na jirasa harya idar da shafa’i da wutirinsa, dan magana nakeson muyi, ganin ya idar ya zauna latsa wayane nace “dan ALLAH yalla6ai in tambayeka?”.
Batareda ya d’agoba yace “uhmm”.
Zamana na gyara cikin nutsuwa nace, “shin tunda Abie yafara jiyya anta6a masa maganin gargajiya ko amaida hankali ga addu’oi haka?”.
Yanzun kam d’ago ido yayi ya kalleni, dama tunda nafara maganar ya dakata daga latsa wayar.
“lips d’insa yad’an cije, kamar zaiyi magana saikuma yay shiru.
Nace “kayi hak’uri idan nashiga hurumin daba nawaba”.
Nanma shiru yamin, saida yaja wasu mintuna kafin ya ajiye wayar yagyara zamansa, cikin alamun bak’in ciki yace, “duk an gwada masa, saidai gaskiya bakamar yanda aka maida hankali gana asibitinba, saboda anriga da an sanar mana Allurar gubace aka masa, amma muna k’ok’arin sakashi a sallalolinmu na farilla dana nafila. Kullum addu’oinmu akansa yake”.
Ajiyar zuciya na sauke, nace “ALLAH yabashi lafiya, yakawo mana iyaka, yakuma bashi ikon cinye jarabawar nan”.
“amin yafad’a a la66ansa”.

Dagani harshi babu Wanda yasake magana har muka kwanta, saidai yauma banyi isashen barciba, inata cud’awa da kwancewa, har gabannin asubahi kafin barcin ya saceni………………???

_To Alhmddlh my sweet fans, zamu dakata anan kenan, saikuma ALLAH yakaimu bayan salla darai da lafiya, zanbar wannan a matsayin *RAINA KAMA….. PART ONE* yanda zamu tafi a tsare kawai, basai mundawo ba kuma mushiga tunanin inama aka tsaya? Ina kuma za’a tashi, a *RAINA KAMA PART TWO* zamuga yanda Munaya zata taimaki Galadima kamar yanda Momma ta buk’ata, shin zai bata had’in kaima Kuwa? domin kunji Momma dai tace bashida yarda? ya matsayin auren Zarah? Muftahu yaya zata kasance idan Galadima ya cafkoshi? shin Munaya tanada wani fikra ne game da ciwon Abie?. wannan amsoshin duk suna cikin *RAINA KAMA PART TWO* da zaizo bayan sallah insha ALLAHU my guys, one Luv??????????????????_

_tabbas banida bakin godiya a gareku, saboda addu’oi da mahaifina ke samu agareku, Comments naku suna matuk’ar sakani a farinciki sosai, ngd ALLAH yabar zuminci, duk inda masoyin wannan buk yake yasaka aransa yana can k’ark’ashin zuciyar Bilyn Abdull.??????????????????????????????????????._

_ga azumi zamu shiga, ‘yan uwana dan ALLAH mu maida hankalinmu ga ibada, sadaka da k’autatama marasa k’arfi, marayu,, k’autata mu’amullarmu da jama’a dayin amfani da abinda malamai zasu fad’akar damu, karya zam kullum muna wahalar zuwa tafseer amma bamu d’aukar komai, da bayan salla yawuce munkuma koma kan munanan ayukanmu, karmu manta irin wannan watan saikuma mai rabon gani, sau 1 tak yake zuwa mana akowacce shekara, wani yawuce agaresa kenan har Abadan, zata iya yuwuwa nice ma??, zata iya yuwa kece ‘Yar uwa??????, zata iya yuwa kaine d’an uwa??????. dan ALLAH mu gyara please & please, muyi amfani da damarmu kafin ta kufce mana, (kullu nafsin za’ikatul maut, kowane rai saiya d’and’ani mutuwa, ubangiji bai turo maka date d’in da rundunar mala’iku zasuzo d’aukar rayin nakaba,?? mutuwa bata kwankwasa k’ofa, batada wata alamar yanda zatazo ta riskeka, kana tafiya ne, ko kana barci, ko kana salla, ko zaune, ko kana hira, ko kana aikata wani sa6o, ko kana wani abin alkairi??, ya ALLAH ka d’auki ruhinmu muna masu imani agareka da tsoranka, ALLAH ka gafarta mana, kamana maganin abinda muka Sani da wandama bamu saniba._
_ina rok’on dukkan Wanda na 6atamawa a yayin wannan rubutun ko kafin shima dan ALLAH Ya gafarceni, nidai na yafema kowa._??????

*_duk masoyina na gaskiya Dan ALLAH inason yasakani a ddu’arsa ta cikin azuminnan koda sau d’ayane, idan munada Rabon haihuwa adunaya nida mijina ALLAH ka azurtamu da samu masu albarka cikin sauk’i da rahamar ubangijin talikai, idan ba alkairi bace agaremu ALLAH kasamana hak’uri da juriyar azuciyata??????, ALLAH kayaye mana dukkan damuwarmu baki d’aya._*??????
Dan ALLAH ko sau 1 yane kar’a manta dani??????

Amin afuwa zan rage groups saboda yawan groups d’in suna cimin data wlhy, idan nayi sub na wata d’aya ko sati bata yimin take k’arewa????.
Ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, ALLAH yasa munada rabon sake had’uwa a bayan salla, ALLAH ka kar6i ibadunmu baki d’aya. yabamu juriya da hak’urin ibadar dake tunkaromu nanda kwana 1????.

Happy Ramadan Advance????????????????????

Binyn Ku Ce dai????

Writer???
*Abdul-maleek bobo!!*
*Auren k’addara ko biyayya!?*
*Ban saketa ba!!*
*Ciki da gaskiya…!!*
*Karayar arzeek’i!!*
*k’anwar uwace ko kishiyar uwa!?*
*Kukan krciya…!!*
*Ni da Aminiyata!!*
*Nawaff!!*
*Rashin Sani!!*
*Raina kama…..!!*
*Sabon Al-amaree!!*
*Sanadin bikin salla!!*
*Siyasa ko k’abilanci!?*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
*_Typing??_*

*_Haske writer’s asso…._*??

*_?RAINA KAMA……?_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*????

____________________________

*_Dolene page d’in farko yazama sadaukarwa agareki MAMAN JUNIOR??, ALLAH ya gafarta miki, ya raya abinda kika bari, ALLAH ya k’addara bazakiga k’arshen wannan littafiba. (Masoyan Raina kama kusaka wannan baiwa a addu’arku, ta rasu cikin azumi, kusanma k’arshe, member ce a group d’in raina kama, ALLAY ya yafe mata??????._*

_INA fata kunyi salla lafiya gaba d’ayanku, ALLAH ya kar6i ibadunmu. Ya yafe mana, yasa kar6a66iyar ibada mukayi??????._
Sai dai banci naman salla ba sosai, gashi banida d’inkin dallah????????.

______________________________

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply