Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 6


Raina Kama Book 1 Page 6
Viral

??6?

…….Bamusan abinda yafaruba, mukaji ‘yan gidanmu suna k’ananun magana da safe, wai girkin jiya na dare da mamansu yaa hameed tayi sai asararsa akayi, girkin yay d’anye yak’i dahuwa, kuma a gas tayi girkin bare ace iccen yabata matsala, gashi kuma normal gas d’in yake aiki.
Muna cikin yima su Aiyaan shirin school muka fara jiyo hayaniya, sai da muka gama musu shirin sannan muka fito, cirko-cirko muka iske ‘yan gidanmu, yayinda mamansu yaa hameed keta zabga masifa. tana fad’ama abbanmu wai mune muka mata kwari shiyyasa jiya abinci yay mata d’anye danta hanamu abinci, kuma gashi yanzuma tasaka doya amai tak’i soyuwa.
Ni dariyama taso bani wlhy, wai mune muka mata kwari, to miye kwarinne ma datake magana a kai? danni bamma sanshiba…..
Maganar Abbanmu ta katsemin tunanina.
“ ‘Yan biyuna kuzo nan naji kunji”.
K’arasowa mukayi kusada abbanmu harsu Aiyaan, ya kallemu cikeda kulawa, “haba ‘yan albarka mike faruwa haka?”.
Cikeda rashin fahimta nace, “Abba a ina?”.
“haba twins d’in Abba, bakuji mi mamanku take fad’aba? abinci yamata d’anye jiya da yau”.
“amma Abba Dan abinci yayi d’anye kuma sai ace mune? Kagafa jiya munama asibiti bamuci abincin dareba agida, darana ma mama hanamu tayi tace innarmu tatafi da kasonmu asibiti, haka muka dawo muka iske su Aryaan sunajin yunwa, sai Munubiya Ce tamana girki, kuma tayi takai mana wani asibitin, ni wlhy Abba bammasan wani kwari dasuke maganaba akai, wannan ai canfine, tunkuma zamanin da aka barsa”.
“canfin uwarki, kujimin munafukar yarinya, inbakune kukayi muguntarba uwarwaye yayi, to wlhy ahir d’inku, ba ‘yan biyu ba ko ‘yan gomane ni ubanku zanci a gidannan…….”
Afusace Abba yace, “to ai gani, saikizo kici ko, ai gaskiyama yarinyarnan tafad’a, wannan canfine kawai, dan abinci yayi d’anye saikuma a fassarashi dawani Abu daban, haba Dan ALLAH, saikace wata mara ilimin addini? Karna sake jin wannan maganar, inba hakaba rankowa zai 6acine a gidannan”.
Yana gama fad’a yabar wajen. muma ganin haka muka tasa su Aiyaan gaba muka koma 6angarenmu. duk da nakasa fassara mi mama ke fad’i hakan yamun dad’i, koba komai dai ai ALLAH yamana sakayya da hanamu abinci datayi muda wad’anan k’ananun yaran da basu da alhakin kowa.
Yanzuma munubiya Ce ta dafo mana indomi mukaci, sanan ta zubama su Aiyaan a kulolinsu Na makaranta, suna tafiya muma mukayi shirin tafiya School.
Bamu tsaya jiran sauranba mukayi gaba saboda zamu biya ta asibiti, kuma munsan acikinsu babu mai binmu, harmun fita saiga Fauziyya tabiyomu, itama zataje taduba feena d’in.
Alhmdllh munma tarar an sallamesu sunata shirin tafiya gida, mukaima feena sannu, ta amsa tana fara’a da tambayarmu ya makaranta?. mukace gatanan zamu tafi.
Bamufi mintuna 30 ba muka fito, Fadeel ya d’aukesu, mukuma muka wuce school.

A mota Munubiya take bama Fauziyya labarin ganin Galadima damukayi jiya a asibiti, ko sau d’aya ban saka musu bakiba har muka sauka.

 

?????

A wannan karon har mamansu yaa hameed tagama girkinta Na kwana biyu asarar abinci akaitayi, Dan kullum d’anye yake mata. hakan yasa taita sakin habaici agidan itada muk’arrabanta irinsu momy hadiza,.
Maman Fauziyya ta sanar ma innarmu komai tun randa taje duba feena agidan mama Rabi’a, Dan haka Innarmu tayi kunnen uwar shegu dasu, tamkarma batasan da ita sukeba balle ta nuna tama fahimci zancen nasu.
Innaro ma tazo tayi tata tsiyar San rai, tabi duk ta zagemu dacin mutuncin innarmu, koma fitowa innarmu hanamu yi tayi, har Innaro tagama tafice. Matan gida najin dad’i.

??????

Haka rayuwar tacigaba da tafiya, yau da gobe kayan ALLAH har gashi azumi ya rage saura kwanaki uku kacal a fara, Dan haka musulmai NATA shirin tarbar wannan wata mai tarin albarka da falala.
Kasuwanni sun cushe saboda yawan hada-hada, duk da ‘yan kasuwa sunyi taiyar tasu ta k’arama abinci kud’i, maimakon su sassauto bayin ALLAH su sami sauk’i (ALLAH ka shirya ‘yan kasuwarmu subar wannan hali dai).

A 6angaren gidanmu ma iyayenmu maza duk sunyi shirin, Dan dukkan wani abun buk’ata an tanadeshi, sai abinda ba’a rasaba dazai iya lalacewa idan an ajiye, wannan anbarsa yayunmu maza su ringayo cefanensa kullum kamar yanda aka saba.
Itama Innaro an ajiye mata dukkan abinda zata buk’ata, dukda kullum daga gidanmu ake kaimata abinci, safe yamma da dare, kuma dolene kowane 6angare sai sunkai nasu.
Muma a 6angarnmu munyi dukkan namu shirin, dukda abin zai had’e mana da zuwa makaranta, hakan yasa nake tausaya mana, gashi ana tsula rana mai zafi kuma.
Alhmdllh yau ta kasance Alhamis, kuma yaune ake saka ran ganin wata atashi da azumi washe garin juma’a.
Har zuwa 9pm kunnen kowa naga redio da talabijin, jira kawai Muke muji sanarwa daga sarkin musulmai. sai wajen 9:30pm sanan aka Sanar da ganin wata, duk wani Muslim yana cikeda d’okin fara azumin watan Ramadan da zamu Shiga goma ta marmari (inji hausawa??).
Tun alokacin duk muka d’auki niyya, kasancewar girkin innarmu ne tayi shirin tafiya d’akin Abbanmu, muma tace mu kashe TV muje mu kwanta kar atadamu da asuba kuma muzo muna k’unk’uni.
Badan mun soba muka kashe mukaje mukai shirin barci muka kwanta da addu’ar abakunanmu.

Aiko da asuba dak’yar innarmu ta iya tashinmu mukai sahur, tea kawai muka shama, dama mu bama sahur da abinci nida munubiya, garama ita wani lokacin takan had’a da kunu ko fura.
Bamu kwantaba saida akayi sallar asubahi, still kwanciya muka kumayi, sai 8 innarmu ta tadamu, kasancewar yau saima 10 mukeda lecture, kuma zamu fito 12 ne.

Tunkan aje da nisa azumin yafara garani, dak’yar Na daure aka kammala lecture muka fito, amma badan Na fahimci komaiba nidai yau.
Su Munubiya sai dariya suke mini wai Raguwa, nidai ban kulasuba, Burina kawai naga mun Isa gida Na kwanta.
Tunda muka dawo school nazube a falo k’asan carpet, ban sake Sanin duniyar danake cikiba saida munubiya ta tadani nayi salla, Ashe harsu Aryaan sun sako masallacima inata barci, sallarma dak’yar nayita atsaye, INA kammalawa nakuma kwanciya.
“oh ni Aisha, wai Munaya mikikeson maida kankine? yanzu azumin kikema langa6e haka? saikace yau kika fara azumi a rayuwarki?”.
“ALLAH innarmu bazaki ganeba, nidai ALLAH yasa akira salla da wuri”.
Munubiya dasu Aiyaan suka sakamin dariya. “Aunty yanzufa k’arfe 2 ma, sauran kusan awa 5 dawani Abu asha ruwa”. ‘Aryaan yafad’a yana dariya’.
Harara Na Dalla masa INA fad’in “ALLAH inbaka rife wannan bakin naka mai gajerarrun hak’oraba zaka dakune, Dan k’aniyarka kaiba yanzu kagama lodama cikinka abinciba?”.
Aunty nimafa Dan innarmu bata tadamu baneba kawai, amma insha ALLAHU gobe zamuyi ko Aiyaan?”.
cikin zumud’i Aiyaan yace, “eh mana, muma zamuyi bro”.
“kuma wlhy yaro bai Isa karyashiba, garama karku d’auka”.
Munubiya tamik’e tana dariya, “imm innarmu bara kiga naje nafara rage aikin, miza’ayi?”.
“ki fere doya kafin Na fito, Munaya tashi maza kuje, kekuma ki gyara kayan miya”.
“wayyo innarmu ki tausaya min mana”.
“mukuma mu kashe kanmu tunda bama azumin ko?”. ‘cikeda gatse tayi maganar’.
“a’a innarmu, bara naje kodaga zaune sainayi”.
“kimayi daga kwance, raguwar banza kawai, ai mijinki yashiga uku, wataran sai yadawo aiki baki gama abinciba”.
Baki Na tura gaba sannan nafita.

Mun rage aiki sosai kafin la’asar, sai bayan sallar la’asar d’in ‘yan Matan gidanmu suka shishshigo kitchen d’in kamar yanda aka saba, dama duk shekara gaba d’aya muke had’uwa a kitchen d’in 6angarenmu ayi abincin bud’a Baki, saidai saboda munada yawa akanyi time table saboda a rarrabu kowa da ranar da Zai taya mai aikin ranar.

Da yake aikin yawane dandanan muka kammala kafin 6, a can tsakar gida aka shinfid’a manyan tabarmi bayan an tsaftace wajen, duk azumi gaba d’aya muke had’uwa asha ruwa dama anan, kafin matar ya hameed ta rasu har itama anan suke zuwa suyi bud’a Baki.
Bayan mun had’u mun gama shirya komai kowa yanufi 6angarensu ya watsa ruwa kafin akira salla, dolene kaga jama’ar gidanmu aranar mu burgeka, babu fad’a babu hantarar juna, (yo kowa azumi yagama cin k’aniyarsa????).
Kasan cewar babu wuta ya kamal yazuba fetur a Gen… Ya tada, kowa yayi wanka saiyayi shirinsa da alwala yadawo tsakar gida ana jiran kiran salla, yara dabasuyi azumi baneba suketa shargallensu a tsakar gidan.
Yanda na zube a tabarman tamkar mara kashi yasaka yaa Shafi’u fad’in “kai kekam anyi raguwar yarinya wlhy, nasan dai Munaya Ce, Dan Munubiya tafiki jarumta”.
Dariya wad’anda ke wajen sukayi, yaa Naseer yace, “gaskiya mijinki yaga banu, yo idan yayi wasa dai bazai dinga cin abincin bud’a bakiba a gidansa”.
Cikin dariya Aunty Hauwa’u ke fad’in “sai ya d’auka mata ‘Yar aiki ai”.
Caraf maman Safara’u ta amshe zance… “yo basai idan mai halin d’aukar ‘Yar aikin bane, ana fama da masarar tuwo da shinkafa a jajibo mai aiki?”.
Gurin tsit yayi kamar ruwa ya cinyemu, da alama kowa baiji dad’in furucin Na maman safara’u ba, sai mamansu yaa hameed ce tayi dariya itada momy Hadiza.
Ganin abin zai koma cin zarafin juna sai maman fauziyya ta d’ako wani zance, daga nan aka koma hirar d’inkin salla. babu dad’ewa ma aka kira sallar magriba, cikeda d’oki kowa yafara k’ok’arin cin dabino. tab aini kam bandani, tuni Na d’ebi ruwa mai sanyi nafara sha, Dan shine babban burina. a gida mukayi jam’i, baba k’arami yajamana limanci. da ganan kuma kowa ya maida hankalinsa wajen bud’a baki, harda su hajiya innaro??, tayi kane-kane ita masu gidan ‘ya’ya??, koda wasa dagamu har innarmu babu Wanda yashiga sabgarta gudun gwalasa, har aka gama lafiya muka gabatar da sallar isha’i da asham. daga nan aka d’an ta6a hira kowa yahad’a kan ‘ya’yansa zuwa 6angarensa.

haka muka cigaba da gudanar da ibadar azumin watan ramadan, tun ina ragwan taka harna fara daurewa, an gama goman farko aka shiga ta biyu (goma ta wuya?? ).
Gaskiya nad’an wahaltu a tsakanin, ga makaranta ga aikin gidanmu dabaya k’arewa, ko wanke-wankema ya isheka, dukda had’uwa akeyi anayi kuwa.
Azumi yana 13 aka kawo kayan sallarmu, an bajesu tsakar gida kowa ya za6a, kala uku-uku ne dama duk shekara, atanfa, shadda, les, saikuma iyayenmu mata su k’ara mana gwargwadon abinda ALLAH ya hore musu.
Munada telolinnmu masu mana d’inki iya ‘yan gidanmu kawai, shiyyasa bamuda matsala. Washe gari kuwa sukazo suka gwadamu, kowa aka saka sunansa ajikin kayansa da style d’in data za6a.
Innarmu ma sun saya mana itada mama Rabi’a, dan tunma kan azumi an kammala mana d’unkunanmu mudasu feena, (innarmu tana business itada mama Rabi’a) shiyyasa duk wani abun kwalliya Na ‘yan mata bama rasashi, duk da dai ‘yan gidanmu suna mana d’agawar sun fimu komai, saboda danginsu masu kud’ine, suna ganin kayansu sunfi namu tsada. hakan baita6a damunmu ba, dan aganina duk sutura sunanta sutura, yawan kud’in nawani bai d’ad’ani da k’asaba, to barema Munubiya da babu ruwanta.
Ana cikin haka muka shiga goman k’arshe Na azumi (goma ta d’okin sallah????).
Ranar wata weekend yayyanmu maza suka kwashemu domin za6o takalma da sauran tarkace Na kwalliya, dama duk ankai yaran suma kowa ya za6o, mu matasan ‘yan matan muka rage dakuma yayyenmu su Aunty khaleesa.
Plaza ce babba mai k’yau da burgewa, kayansu Na manyane, amma yayyenmu dayake sunaso mufito suka kaimu can, sa6anin da da ake kaimu kasuwa kamar sauran yaran, su aunty khaleesa ne kawai ake kawowa nan saboda sune manyan ‘yan mata, to yanzu muma mun shigo layi????.
Sosai muka rikice da tsarin wajen, takalmane ‘yan waje wad’anda duk inda kayi taku sai an kalleka ansan kagama Isa. Harda bags, kayan makeup, turarurruka da dogayen ruguna irinsu Arabia’s gowns, gyalilla da kayan ‘yan kunne, kananun Maya Na garari Na mata da maza, kai inaga babu abinda zakazo Baja sameshi awannan PLAZA d’inba kam”.
Lallai an narka dukiya a wannan waje, ko plazan wanene? oho. munga dai sunan plaza d’in *BIRNIN GAYU!!*
“Lallai kuwa taci sunanta birnin gayu”. ‘ cewar Anty Ramlah’.
Haleematu tace, “wlhy wannan ace plaza d’in mijinace to bazan maimaita kaya sau uku ba, hakama waya duk wata za a dinga canjamin”.
Dariya tabamu, dan haka muka shiga darawa kuwa. kowa yad’auki abunda yakeso gwargwadon iko, yayyanmu suka biya da kud’in dasu Abba suka basu, sannan suka cika mana danasu kud’in, kowa yafito cikin farin ciki muna jera musu godiya, mun d’auki picture’s sosai awajen kuwa. muna tafiya a mota nake cewa yaa Anas dan ALLAH wai Plaza d’in waye wannan?”.
“ai plaza d’in ta babban kwaroce k’anwata, plaza d’in *GALADIMA* ce”.
shiru nai kamar banjishiba, danjin sunan wanda ya ambata, inada tabbacin kuma wannan mai girman kan tsiyar yake nufi kenan, yayinda ‘yan uwana suka rud’e da firar galadiman.
d’an tsaki naja nace, “ashema Na mai shegen girman kai d’innan ne”.
Kusan atare sukace ke a ina kika sanshi? dahar kikasan yanada girman kai”.
Shiru namusu, sai Munubiya ce tashiga basu labarinsa da had’uwar damukayi a asibiti da shi, aikam duk sai sukabi suka rikice, harda masu fatan yazame musu mijin aure.
bansan miyasa duk hirar tasu ta k’untataniba, tabani haushi, saina maida hankalina ga kallace-kallacen jama’ar daketa kai kawo akan titi.
Har mukaje gida suna hirar Galadima sudasu yaa hameed dake basu labarin halayen kirki Na Galadima d’in, wai kuma bashida girman kai kamar yanda Na fad’a, kawai dai dan ban fahimcesa bane nima.
Nidai jinsu kawai nakeyi, amma badan Na yarda baida girman kai ba, tunda da idona Nagani ba labari aka baniba.??ehe

Innarmu tayi mamakin wad’annan kanya, dan haka takasa hak’uri, har 6angaren samarin gidanmu taje tamusu godiya da fad’an d’awainiyar tayi yawa ai, ga hidimar biki Na tunkarosu.
Sunji dad’i sosai akan hakan da innarmu tayi, koba dad’i kowa yayi aikairi yanaso anuna jindad’i kuma amasa godiya.
Sukace tayi hak’uri, ai k’annensu ne, idan basu mana ba wazai mana, da samari suzo suna mana hidima su lalata mana rayuwa ai garasu sumana su kare mutuncinmu.
Sosai innarmu ma taji dad’in furicinsu, dan hakan ya nuna cewa su basu d’auki halayen iyayensu mataba Na raba d’aya biyu.

Salla nata gabatomu, yayinda aka fara ‘yan kimtse-kimtse Na shirin bikin sallar, masallatai nata rufe tafseer, hakama gidajen redio dana talabijin…………..???

*Kusaka yayan mahaifiyata a addu’arku, ALLAH yamasa rasuwa ranar alhamis??????, ALLAH ya gafarta masa, ya raya abinda yabari.*

_Bansan makaranta Raina kama…. kunada yawa hakaba wlhy, nazata ki rabin group bazaku kaiba????, gashi yacika wasu basu sami wajeba kuma._

 

Na gaisheku k’yauta, ina fatan duk kuna cikin k’oshin lafiya kuda iyalanku???????.

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*.??????
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply