Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 7


Raina Kama Book 1 Page 7
Viral

????7?

…….Yau ake saka ran ganin wata, dan haka kowane gida zaka iya jiyo kamshin miya dana nama, harma da kayan snacks.
Muma agidanmu kusan hakanne ta kasance, dan kowanne 6angare sunata hidimarsu, yau ko bud’a baki bakowa yasamu zaman yinsa ba.
Muma muna namu 6angare muna taya innarmu ayyukanta, dayake kowa yana miyarsane, da safe ahad’u ayi tuwo da masa da shinkafa, haka muke had’a kalolin abinci iri-iri saboda yawan jama’a da gidanmu kan tara a ranar salla, abokan yayunmu maza, abokan su abbanmu dawasu dangin iyayenmu mata.
Har wajen 10 munata aiki, sai kuma a lokacinne mukaji ana sanar da ganin wata.
Nannafa yara suka shiga murna gobe salla, Muma kanmu manyan murnar mukeyi. badan mun kammala aikiba muka kwanta.

Washe gari tun kiran sallar farko aka tadamu muka fara aiki, sai wajen 7am muka samu kanmu, a gurguje muka fara wanka da shirin tafiya idi, duk shekara dama ‘yan gidanmu a masallacin da sarki yake salla muma mukeyi.
A gurguje duk mukaita fitowa saboda horn da yayyenmu suketa mana, yara an d’urasu a school bos d’insu Na makaranta, yayinda mukuma muka rarrabu a motar yayinmu datasu Abba dasuka bayar, tunda bakowa keda motarna acikin yayyen namu.
Dagani har Munubiya cikin shigarmu muke iri d’aya tamkar yanda muka saba a koda yaushe, dai-dai da kwalliyama iri d’ayace a fuskarmu, komai namu mukayishi iri d’ayane, wannan yasaka ake gaza banbancemu akoda yaushe.

Mun Isa filin idi, inda muka taddashi dank’am da jama’a maza da mata, wasu harda iyalansu, kamar yanda muma muka taho baki d’aya harsu innarmu, mu mata muna 6angaren mata, yayinda mazan sukayi nasu 6angare.
Khud’ubar da aka gabatar tazamo mana mai ratsa jiki da 6argo, Malam yayita cikin tsantsar larabci, yayinda wani malamin ya fassara acikin harshen Hausa, saboda marasa jin larabcin irinsu o e??.
Daga nan aka gudanar da sallar idi kamar yanda addini ya koyar.
Had’a kan yaran muka shigayi gudin karsuyi wani waje, sai dai hakan bata samuba, dan annemi Kamal da Haneep an rasa, nannafa muka shiga bulayin nemansu, duk mun rikice, gashi baba k’arami da Abbah sai fad’a suke wai sakacinmu ne.
Tamkar zan kifa haka nake tafiya da sassarfa ina kalle-kalle. ban ankaraba naji naci karo da Abu, tunkan inkai idona kansa k’amshin turarensa yabigi hancina. da sauri na ware manyan idanuna bisa kamilalliyar fuskarsa dake d’aure babu alamar yasan miyema dariya, janye idona nayi cikin fargaba da fad’awa kogin tunani, inban mantaba irin wannan k’amshin naji a asibiti wajen Wanda aka kira galadima a wacan ranar da feena batada lafiya.
Cikin yanayin tantama Na maida idona nad’an saci kallonsa…
Tsaye yake kyam tamkar dutshin da aka dasa waje d’aya, idonsa akan wayarsa dake k’asa a tarwatse, Wanda inada tabbacin karon damukacine yasaka wayar fad’uwa.
A rikice nace “ya Salam” tareda duk’usawa nafara harhad’a wayar.
A hankali ya durk’usa kamar yanda nima nayi, ya d’ora hannunsa akan wayar dana ke k’ok’arin sakama battery ya zareta daga cikin hannuna. bugun zuciyata yak’aru saboda tsoro gashi yak’i cewa uffan, nasan nice da laifi, kafin Na ankara ya sake d’oramin wayar bisa hannuna yamik’e yabar wajen.
Sororo nabisa da kallon mamaki da al’ajabi, sanye yake cikin farar shadda k’al, wando da riga harda malun-malun, ya murza hularnan da ake kira Minister bak’a a kansa, takalminsa da agogonsa duk bak’ak’e, duk da bawani k’are masa kallo nayiba fuska da fuska nasan tabbas yayi k’yau, kayan sun maidashi wani babban mutum. Ajiyar zuciya Na sauke saboda ya 6acema ganina, nabi wayar daya barni da ita a hannu da kallo, tomi yake nufi da hakan?.
Banida mai bani amsa, dan haka nacigaba da had’a wayar, sai alokacin Na lura da sim card d’insa dake kan wayar yacire d’azun lokacin daya kar6a kenan.
Jujjuya wayar nashigayi cikin tafin hannuna, wayace mai azabar k’yau ga k’amshin turarensa ya manne jikin wayar tamkar itama ana fesa matane. ‘Yar tsagewane tayi kad’an daga gefe, amma daga hakan ni banga wata matsalaba, kenan yana nufin koyaya waya ta tsage a hannunsa tatashi aiki a garesa?. Nanma babu mai bani amsata. Cikin mak’oshi Na furta to wanene wannan d’in shikuma?”.

“Galadima!”. ‘naji wata murya tafad’a abayana’.

Cikin hanzari najuyon dan inga mai bani amsar tawa. wayam naga babu kowa, sai alamar gittawar mutum mai jajayen kaya.
Goshina Na dafe inamai runtse idanuna, cikeda mamaki nace, “kenan shine wanda yabama feena jini? Galadima!”.
Nafad’a cikin bud’e idanuna inabin inda yabi da kallo tamkar zan sake ganinsa, a hankali nakuma furta _“Galadima!”_.

“galadima kuma?”.
Najiyo muryar Safara’u a bayana, da sauri a cusa wayar cikin hijjabina Na mik’e, kallonta nayi cikin basarwa nace, “ya angansu ne”.
Tace “eh mana an gansu tun d’azun, saikuma aka koma nemanki, miya faru naji kina kiran sunan galadima?”.
d’an guntun tsaki naja “naji wasu ‘yan matane suna fad’in wai INA zasuga Galadima, tunda ance yazo sallar idi. shine nikuma nake maimaita sunan Galadiman saboda takaicinsu”.
Dariya Safara’u tayi, ke ‘Yar uwa karkiga laifinsu wlhy, koni zan sameshi saina bar Sadeeq wlhy, yanzu fa Nima ake nunaminshi, dama haka yahad’u? Wayyo ALLAH yau naga tsantsar gwanzartakar sarauta ajikin bawan ALLAH nan, tafiyarsama kawai abin kalloce, inaga kuma yayi magana?, kai ALLAH yakai damo ga harawa…… kedai kawai……..
Baki kawai Na ta6e, batareda nagamajin k’arshen zancen nataba nayi gaba abuna da mamakinta a raina, wai zata iya Barin sadeeq?, saikace ba’akan sadeeq d’in bane akaso cin zarafina da innarmu, amma yanzu saboda taga Wanda ya fishi bakinta yake furta haka.
Da gudu Safara’u tabiyoni. Kusan a tare muka k’arasa Inda motarmu ta tsaya, yaa hameed yafara zagina akan INA kuma naje Na tsaya?, hak’uri nabashi muka Shiga mota kawai, dan nasan shima d’in masifafene kamar su abbanmu.
Amotar ana fira amma ni tunanina yanakan had’uwarmu da Galadima ta yau, ga mamakin wayarsa daya bari yatafi a hannuna batareda yace min uffanba, kai wannan Bawa yanaji da k’asaita da mulki.
Har muka Isa gida bakina bai iya furta komaiba acikin hirar tasu. Mun tatar su innarmu ma harsun huta su, yara kan summa fara cin abinci.
Ban zauna faloba kamar yanda munubiya tayi, saina zarce bedroom d’inmu Na 6oye wayar sannan nacire hijjab d’ina nashiga bathroom Na wanke hannuna gudun kar wani yaji k’amshin turaren saina dawo falon.
Tuni gidanmu ya kacame da hayaniya, munubiya tazubo mana masa da fankasu zamu faraci Ayusher da Feena suka shigo da gudu, juna muka rungume muna murnar ganinsu, Yaa Fadeel & yaa Marwan suma suka shigo, sai mama Rabi’a dake take musu baya tana rik’e da hannun Ahmad.
Nan muma muka kacame da farin cikin ganin ‘yan uwanmu wad’anda bamuda kamarsu, innarmu ta baje mana abinci da kayayyaki da dama dansu duk ta tanadesu, sai makwafta dasuke gaisawar arzik’i suma duk tabada ankakkai musu.
Bamusan hidimar da kowa keyi anasa 6angarenba, mudai namu muka sani.
Ayusher takawo bakinta saitin kunnena, ahankali ta rad’amin sweet sis…. Wlhy k’amshin turaren Galadima kikeyi, kinsan har abada bazan mance k’amshi nan ba”.
Cikin dakiya Na d’ago kai Na kalleta tareda balla mata harara, “Ayusher wlhy ki kiyayeni, a’a k’amshin turaren sarki kikaji bana Galadima ba k’arewa”.
dariya ta sanya harda rik’e ciki, nikuma Na tashi Na canja waje ina mamakin Ayusher mai gani har hanji, duk dawanke hannuna danayi sosai amma ace wai har yanzun anajin k’amshin turaren?, kai shikam wannan dawane mayen turare yake aiki haka?”.
Wajen 12 muka fito domin zuwa kallon sarki dazai wice yima governor barka da salla.
A wannan karan tafiyarmu daban data ‘yan gidanmu, dan mafi yawancinsu duk sun fice gidajen kakanninsu, tacan masu ra’ayin zuwan suma zasuje.
Mukuwa mudasu yaa marwan muka tafi.
Acikin gari duk inda ka kalla jama’a ne keta kai kawo, musamman yara da ‘yanmata da samari, kowa yaci kwalliya ta kece raini da garari (yo dama ai ance ba’a za6ar budurwa ran salla, saboda duk k’azantar mutum ranar saika sameshi cikin tsafta da gayu??).
Dukda akwai rana hakan bai hanamu jeruwaba domin kallon wucewar mai martaba sarkinmu da jama’arsa.
Masu busa algaita da kid’an taushine suka fara wucewa, sai kuma ga tawagar sarki Na biye.
tawagar saiki Na wucewa sai ta Galadima, kamar yanda mukaji wasu gungun samari Na fad’ar cewa ga Galadima nan.
Kowa yasan dama tsarin haka yake, daga sarki sai shi.
‘Daga idanuna nayin donson sake ganinsa a karo na biyu. yanzu kam ya canja shigarsa zuwa milk coulor d’in janfa da wando Na lallausan yadi, Wanda aka k’awatashi da d’inkin surfani Na ainahin gidan masu sarauta, ya d’ora Brown Na alk’yabba mai kwalliyar Milk Color, hakama rawaninsa daya zagaye fuskarsa ya kasance milk ne, takalmansa heir cover masu lankwasa daga gaba irinna sarauta, sukuma Brown. yanzun kam fuskarsa d’auke take da k’asaitaccen murmushi mai kama da anmasa dole, hannunsa d’aya dayake d’agama mutane yana d’aureda farin agogon azurfa, sai zabba biyu a yatsunsa Na tsakkiya Wanda nake k’yautata zaton azurfane suma.
Nanfa su Ayusher suka fara d’aukarsa hotonsa a wayoyinsu.
Tsaki naja ina hararsu, “mtsoww wahalallu kawai, dama kanku kuka d’auka yafi Ku k’are wajen d’ura hotunan Wanda baisanma da zamankuba a wayarku”.
Kafin cikin su Ayusher wata tabani amsa, wasu ‘yan mata dake kusadamu d’aya ta kar6e da fad’in “k ‘yan mata kama kanki, kodai kema son nasa ne yakaiki ga kishinsa?”.
Wata wawuyar harara Na buga mata, “kekuma shasha waya sako bakinki?, kajimin ballagaza kawai, uwarmiye abin so a jikinsa dahar ya isa ayi kishinsa? Ke dai dabakisan inda ke miki k’aik’ayiba ita dakon wahala, dan nakula ke amatanma suffar mata maza ALLAH yayiki….”
Gaba d’aya suka taso min da masifa tamkar zasu cinyeni d’anya itada k’awayenta..
Yaa marwan dake zaune saman mota a bayanmu duk yana saurarenmu yad’ago kai ya kalleni, yasan tabas Munaya ce, baya buk’atar k’arin bayani kuma ko tambayar wacece ita, tunda Na nuna halin nawa, yace, “K munaya zoki shige mota”.
Nasan halinsa sarai baya wasa damu, cikin tunzura baki gaba nazo nashige motar Na zauna, amma saina bar k’ofar abud’e k’afafuna awaje, banida buk’atar cigaba da kallon kuma, dan haka nabud’e data nashiga chart kawai ina cika ina batsewa masifa nacin raina, gashi kuma an hanani amayar da’ita,. sai antayama yaa Marwan harara nakeyi ta gefen ido baima San inayiba, gaba d’ayama sainaji dama banzo kallon hawanba.

Koda muka bar nan ba gida muka komaba, yawo yaa Marwan yaytayi damu gidajen dangin babansu, bamune muka dawo gidaba sai magriba, kowa yayi ti6is da gajiya.
Mun tarar innarmu da mama Rabi’a sunata shan hirarsu ta zuminci.
Sai kusan 10 suka bar gidan.

????

Washe gari muma agidansu mama Rabu’a muka yini har innarmu, koda yakema fitarmu mukayi nida Munubiya, Feena, Ayusher, mukabar su mama agida dasu Aryaan.
Yauma mun zaga gari sosai, dan Ayusher takira mana wani saurayinta yazo ya kwashemu, yauma munje munga hawan sarki da la’asar, saidai yau babu Galadima a tawagar, hakan bai dameniba, dan nama manta da lamarinsa ni.

Kwanaki kusan biyar zuwa 7 munashan shagalin salla, munsha yawo tamkar bamuda mafad’i mudasu Ayusher, sai Fauziyya dakan bimu wani lokacin idan basu fitaba da mamarsu suma.
‘Yan matan gidanmu kowa sabgar gabansa yayi, rana d’ayane muka fita gaba d’aya domin gaida danginsu Abbanmu da Innaro takafa ta tsare akan sai munje wai su Anty Ramla sunyo musu sallamar aure.

Kwanaki 10 cif dagama bikin salla muka koma makaranta.
Haka rayuwa tacigaba da shud’ayawa, yayinda ‘yan gidanmu keta shirin bikin ‘ya’yansu, shiri akeyi babu kama hannun yaro, kowa burinsa ace ‘ya’yan d’akinsa sune Star’s, kuma sunfi kowa komai.
Sati uku kacal bikin yarage, an kawo lefe daga gidan senator halliru, akwatina 24, siyama 12 Zarah 12.
Humm ai ranar munsha kallo Na al’ajabi wajen mamansu yaa Hameed da momy Hadiza, habaici da gugar zana da burga, kowa yashashi, har dai abin yak’ure mamansu haleematu da maman Safara’u suka tanka musu, kafin kice mi gida yagama kacamewa da hayaniya, kowa yana ya6ama kowa magana, saida suka gama cin zarafin junansu sannan sukayi shiru bisa tsawatarwar baba k’arami, dayake yana gida a lokacin.
An bar maganarne kawai amma badan ta k’areba, mudai a 6angarenmu ma innarmu hana kowa fitowa tayi, dayake weekend ne.
Suma sauran duk an kawo nasu lefan, Aunty Rahaima, Ramlah, Hauwa’u sai aunty khaleesa, suma dai Alhmdllh, komai sai dai mak’iyi, duk da basukai nasu siyama ba gaskiya. a wannan karonma dai saida akayi ‘yan gulmace-gulmace a gidanmu, amma basu bari tafito sarariba.
Suma su yaa Hameed aka kai nasu lefan gidajen matan dazasu aura shida Ya shafi’u da yaa Nasser. suma iyayenmu sunyi k’ok’ari wajen had’a musu lefen girma, ankai kuma kowa Na sambarka.
Tun bayan gama kai lefe gidanmu yakuma d’inkewa da k’us-k’us na gutsiri tsomar gidan yawa, kowa yana gulmar kowa akan aga wace rawa zaka taka, su 5 masu aurar da ‘ya’yan.
Mamansu yaa hameed zata aurar da 3, yaa hameed, aunty khaleesa da Zarah.
Sai maman Haleematu zata aurar da aunty Hauwa’u.
Sai Momy Hadiza zata aurar da Siyama da aunty Raihan.
Mama Ruk’ayya kuma zata aurar da yaa Shafi’u da yaa Naseer.
Maman Safara’u kuma Aunty Ramlah.
Innarmu da maman Fauziyya ne kawai bazasu aurar da kowa ba, dan haka suka zama ‘yan kallo, sai idan mazajensu sun saka su acikin shawarane………….???

 

 

 

 

*_Ya Rabbi ka gafarta iyayenmu??????_*
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

_________________________

_Happy marriage life *SANNA S MATAZU* ALLAH ya sanya alkairi da albarka a wannan aure, yabaku zaman lafiya na har Abadan da zuria d’ayyiba, bad’i muzo cin rangam??????????????????????._

__________________________

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply