Hausa Novels Raina Kama Book 1 Hausa Novel

Raina Kama Book 1 Page 8


Raina Kama Book 1 Page 8
Viral

??8?

…….Hidimar biki ta kankama gadan-gadan, dan har bak’in nesa sun fara isowa, a ranar alhamis aka gudanar da sister’s and brother’s day Wanda mune k’annensu muka shirya musu da yayinmu maza. da farko a tsakar gidan innaro aka shirya, saboda su Abba bazasu barmu mu saka kid’aba a gidanmu, gashi mun gayyato k’awayenmu ne, sai abokan su yaa Nasser danasu Anas. daga baya kuma sai muka canja shawara saboda samun wani fili damukayi can k’asan layinmu, filin a zagaye yake da katanga an saka gate. Tunda safe suka fara shirye-shiryen gyara wajen, kasancewar sai 4pm za’a fara, mudai makaranta muka tafi nida fauziyya da Munubiya, dan munada lectures, amma sauran duk k’in zuwa sukayi, barema su Siyama amare.
Around 3pm muka dawo gida, yauma kam da alama wasu bak’in sun iso, dan gidan Yakuma cika da yara da ‘Yar hayaniya.
Mun tarrar innarmu tana d’akin abbanmu, dan haka mukayi wanka muka fara shirin tafiya wajen taron, ko abinci bamu nemaba, dagani har munubiya mun iya makeup, kasancewar mama Rabi’a tasakamu wajen koya muda Ayusher lokacin damuka gama secondary, a d’an tsakanin kafin fitowar results d’inmu, taga damuyi zaman banza gamma muje mukoya wata ‘Yar sana’ar, tunda bamusan inda rayuwa zata kaimuba. Ko gama shiryawa bamuyiba Rahma tashigo kiranmu inji su Aunty Rahaima, dan mune zamu musu kwalliya.

Mun tarar dasu duk sunyi wanka dama mu suke jira, zaman musu kwalliyar mukayi, ni nafarama Aunty Hauwa’u, yayinda Munubiya takema aunty Ramlah.
Kiran Ayusher yashigo wayar munu…., ta d’aga tana fad’in “kin isone?”.
Bansan mitace mataba daga can, naji tace, “kizo muna 6angaren su Aunty Ramlah”.
Babu dad’ewa saiga Ayusher itama, ta gaggada su Aunty’s d’in, sannan muma tabamu hannu muka gaggaisa cikina musabaha.
“lah dear nifa harna fidda ran zakizo ALLAH”.
Ayusher tace “kibari kawai, wancan jarabbaben ne yasakani aiki, tuwo mama tayi da rana, kinsan kuma bayaci shi, shinefa ya tsareni wai saina masa sakwara, harfa nayi shirin tahowa”.
“uhm ai lamarin yaa marwan saishi, matarsa dai taga banu wlhy, shi anya ma yata6a budurwa kuwa?”.
Dariya duk muka sanya a d’akin, aunty Hauwa’u tace, “ai marwan akwai miskilanci wlhy shima, nifa zan iya cewa mun ta6a magana dashi kuwa?”.
Ayusher tace, “yo aunty ai wannan kowama haka yake masa, komu muka gaidashi sai yaso yake amsawa, kullum mama cikin masa fad’a take amma abanza wlhy?”.
Nann dai hira Yakoma kan yaa Marwan da mutane masu muskilanci irinsa, Munubiya ce mai kareshi, (dama ita suna d’an d’asawa, nice dai kamar muna ganin hanjin juna dashi danma ina tsoronsa ).
Kasan cewar mu uku ne sai kwalliyar tai sauri, dan danan muka kammala, nida munubiya mukayi tamu muma, simple makeup mukayi, amma komai iri d’aya, dama haka mukeyi, komai namu kullmun iri d’ayane.
Munyi k’yau, 6angarenmu muka koma mukayi shiri cikin blue d’in skirt da pink d’in Riga kamar yanda aka tsara sai veil shima blue.
Na jujjuya ina kallon kaina a mirror, “kai jama’a nikam bazan iya fita hakaba gaskiya”.
Ayusher dake kwance tana danna wata tad’ago ta kalleni, “kai amma kuma wlhy kayan sun miki k’yau, kinganki kuwa? dan ALLAH ki barsu, kiyi rolling veil naki kawai”.
“kai ba munaya kad’aibafa, nima bazan iyaba, after dress zan d’ora wlhy”.
Dariya Ayusher tayi, ta tashi zaune tana ajiye wayar, “waiku miyasa k’auyawane sister’s, naga a ke6antaccen waje za’ayi?”.
“amma kuma dai ai akwai maza kema kin sani”.
“to alaranmiya, Ku saka, amma kafin Ku saka d’in nidai kuzo miyi hotuna”.
Gaskiya koni nasan munyi k’yau, kasancewar mud’in fararene, kalolin duk sai suka kar6i jikinmu blue & pink. Wanda bai saniba saiya ce mu ‘yan uku ne har Ayusher, dan muna matuk’ar kama da juna, sai dai Ayusher tafimu haske da d’an jiki.
Sai da mukad’anyi hotuna sannan muka fito. Innarmu tace kunyi k’yau, amma dan ALLAH kar inji wani yayi abinda za’ace gashi-gashi, Ku kama kanku da mutuncinku kunga dai acikin anguwane, idon kowa akanku yake”.
Mukace to innarmu insha ALLAH. mun fita tana binmu da addu’a.

A k’afa muka taka har wajen taron, tunkan mu k’arasa muke jiyo tashin kid’a. wajen dank’am yake da ‘yanmata da samari, k’awayen amare da namu muma, sai ‘yan uwa kuma da abokan su yaa Nasser, dama shi ya Hameed bai gayyaci kowaba, yace ya bar mana mu k’anne (shidama ba auren farko bane).
Tunda muka shigo akai mana caa da idanu, wasu tsantsar kamarmu ce tajawo hankalinsu kanmu, wasukuma burgesu mukayi, wasu kuma gulmarmu sukeyi da zaginmu, to dama shi taro ya gaji hakan, ballemu da ake ganinmu k’ask’antattu agidanmu, kamar kowama yafimu komai.
Amare suma duk sunyi k’yau cikin tasu shigar ta Riga da wando pink gaba d’aya, sai suka d’aure k’ugunsu da blue d’in belt, suka d’aura jacket blue.
Snacks ne kawai akad’anci a wajen da drinks, sai pictures da’aka d’auka da video, ‘yan mata sunata casar rawarsu da samari, mudai muna daga gefe zaune muna shan kallo. mun rarraba gifts d’in damuka tanada, bawani Abu bane masu tsada. silifas d’in wankane sai brush, MacLean, soson wanka da sabulu d’ad’d’aya aciki, gifts d’in nan mun shiryashine kawai dan tsokana dama. gabda magriba taro yatashi lfy, kowa ya kama gabansa. muma gida muka koma.

 

?????

Washe garima saida mukaje makaranta, sai dai 11:30 muka fito lecture, ALLAH ya taimakemu muka samu taxi da wuri.
Sanda muka dawo har ‘yan jere sun dawo, kowa dangin mamarsa sukaje jerensa, shiyyasa mukaji tsitt babu gutsiri tsoma.
Muna dawowa ko wanka bamu tsaya yiba mukaci abinci muka tafi shagon auntynmu data koyar damu makeup domin yin k’unshi da saloons.
Cikin farin ciki ta tarbemu, dan mun rabu da ita cikin mutunci bayan mun iya aiki, Aunty salamah batada damuwa, inkaga tana maka fad’a to baka fahimtar abinda take koyar dakai ne, kwazon damuka nuna alokacin yasa takeji damu over. Tana kiranmu ‘yan ukun ta.
K’unshi aka mana mai k’yau da gyaran kai, (dan d’aurema k’arya gindi irinnan aunty salamah harda mana gyaran jiki??, wai tanaso muma musamo mazajen aure??).
Kowa ya gammu yasan munyi k’yau sosai.

Amakare mukaje gida, dan mun tarar amare nata jiranmu mu musu kwalliya, ‘yan gidanmu harsun fara k’ananun magana, wai wulak’ancine yasa muka fita ai, kuma muna kallon lokaci yana k’urewa mukak’i dawowa. hakan da innarmu taji yasata kiranmu tana mana fad’a, hak’uri muka bata dacewa gamunan a hanya.
Masifa mukaitayi nida Ayusher, munubiya na bamu hak’uri, wlhy badan innarmu ba da bazanyi kwalliyar nanba yau.
Babu zancen mu huta muka hau musu kwalliyar. aikam ranar k’in fita wajen kamun nayi da akayi a tsakar gidanmu, kwanciyata nayi, innarmu taitamin fad’a kuwa.??

Washe garin asabar d’aurin aure, dakam gidanmu yacika tab, 6angarenmu dai da sauk’in mutane, sai mama Rabi’a kawai da matan abokan Abbanmu.
K’arfe goma aka d’auro auren yaa Hameed da amaryarsa, sai yaa Nasser shima da yaa Shafi’u.
Na ‘yan matan kuwa sai k’arfe 1:30pm. K’ofar gidanmu yacika dank’am da jama’a ta ko’ina, ‘yan siyasa tawagar senator halliru da abokan su Sa’eed, hakama mijin aunty Rahaima d’an siyasane, dan haka harda governor a mahalarta taron d’aurin auren.
Har aka gama d’aura aurarrakin ina d’akinmu kwance, ko wanka banyiba, garama munubiya da Feena da Ayusher su duk sunyi, amma suna d’akin basu fitaba, sai balkisu k’awarmu da itama tazo mana.
Hira suketayi, nikam dai ina kwance kaina namin ciwo.
Gidanmu babu masaka tsinke, tako ina jama’ane, amare ansha k’yau, su siyama baki har k’anne an auri ‘ya’yan sanata, hakama iyayensu sai burga sukeyi, ranar munga gasar dressing wajen iyayenmu mata kam, kowacce so take ace itace uwar amarya datafi kowa fita.
Innarmu kam babu ruwanta, shiga d’aya tayi ta atanfar da Abbanmu yamusu Na fitar biki, sai da yamma ta canja da less.
Aranar kowaccensu tayi yini. Baza’a kai amareba sai washe gari, saboda anason agudanar da dinner waje d’aya, amma an kawo nasu yaa Shafi’u sudai.
Yau d’inma dai mune muka musu kwalliyar su dukansu, kafin k’arfe 8pm afara kwasar mutane zuwa wajen daza’a gudanar da dinner d’in.
Gurin yayi k’yau sosai, yayinda aka shirya ma amare da anguna hi table.

Sai dai kuma wata sabuwa, ba duk angunan bane suka halarci wajen dinner d’in, nan fa aka fara ‘yan gulmace-gulmace tsakanin dangin iyayenmu mata, tuni labari harya kai kunnuwan iyayenmu mata dasuke zaune a gida.
Amaren da babu angunansu sunsha kuka, wad’anda kuma dama sukasan angunan nasu ustazaine bazasu zoba basu damuba.
Haka dai aka gudanar da dinner d’in zukatan wasu babu dad’i, tunkan agama ma wasu sukaita tafiya gida abinsu. K’arfe 11 aka tashi.
A wajen dinner kam nayo saurayi mai suna Fu’aad, hakama munubiya da Ayusher dun sunyi, Fu’aad k’yak’yk’yawa dashi masha ALLAH, duk da dai bawani sake masa nayiba ya burgeni.
Su Ayusher sunata tsokanata, nidai ban kula suba.
Washe gari da safe kuwa saida abin yazama fad’a, wai ankama wasu suna gulma akan rashin zuwan sauran anguna, kuma dangin momy Hadiza ne, aikam sosai aka zuba rikici, har saida abbanmu ya tsawatar.
Aranar aka shirya kai amare, dole sai dai a rarrabu, tun la’asar aka fara kawo motoci, baba k’aramine yabada shawarar ahad’a tafiyar kawai gaba d’aya, su aunty Hauwa’u suma su siyama rakiya, sannan suma haka.
Haka kuwa yayima wasu iyayenmu mata dad’i, dan kobabu komai saji yanda gidan kowacce ya kasance.

mun fara kai su Siyama da Zarah, wad’anda babu alamun kuka a idanunsu, gidajensu jere da juna, sunyi k’yau masha ALLAH, kayan gado dai duksu Abba sukayi, kuma kud’insu d’aya, saidai kowa da za6insa, kayan kitchen ne kowa uwarsa tayi da sauran tarkace, ananne kowa ya ware ido dan aga kwazon uwar mutum, nidai agareni babu makusa, gidansu Zarah duk yayi.
Mun ajiyesu tareda k’awayensu, mukuma muka tafi kai sauran.
Daga Nan sai gidan aunty Rahaima, itama masha ALLAHU wlhy, saidai mak’iyi, gidanta yayi k’yau, sai dai tanada kishiya.
Saikuma gidan aunty khaleesa, itama dai d’in zamm zamm wlhy, daga nan sai aunty Ramlah, wlhy itama yayi d’as, itama tanada kishiya. Aunty Hauwa’u ce k’arshe dan itace babba, itama gidanta yayi k’yau sosai.
Nidai aganina babu wadda mahaifiyarta batayi k’ok’ari ba wlhy, amma hakan bai hana sauran gumtso gulmarmakiba aka taho da ita.

Kasancewar duk babu Inda muka zauna aka taho gida da wuri, harzamu wuce Fu’aad daya d’akkomu yace bari yashiga Birnin gayu plaza damu.
Nace a’a muwuce gida kawai, kar aga kowa yadawo mu bandamu, gashi lokacin har 8:30pm ya wuce.
Ayusher ce tace indai bazamu dad’eba ashiga, saimuce muna gidajen su siyama mu, mun zauna jiran anguna.
Kamar dai nace a’a amma nayi shiru, saboda naji munubiya da feena suma sun bada goyon bayan mu Shiga, sannan Fu’aad yace bazamu dad’eba.
Ya kalleni murya k’asa-k’asa yace, “ginbiya bakice komaiba?”.
Murya a sanyaye nace, “indai bazamu wuce 1hour ba muje”.
“insha ALLAHU my luv bazama mu kaiba”.
A kasalance Na d’aga masa kai saboda agajiye make ti6is.
Haka yashiga wajen nidai zuciyata Na dukan uku-uku daban San Na miyeba.

Munshiga cikin plaza d’in, bansan takamaimai miyasa Fu’aad yace mushigo wajenba, tunda dai bawani abin ci ake saidawa a wajenba.
Mun shiga 6angaren kayan kwalliya, yace kowa yaza6i abinda yakeso.
Nidai nace masa a’a mun Gode.
6ata fuska yayi yana hararata, ya maida kallonsa gasu munubiya dake tsaye “please dan ALLAH karku biye mata, kuje Ku d’auka”.
Badan suma sunasoba suka amsa da to.
Ya kalleni yana fad’in “mujeto ni na d’ebar miki”. bance masa komaiba nabi bayansa ganin kamar yayi fushi, wayarsa aka kira, ya zaro daga aljihu, saida yad’an saci kallona yaga hankalina baya kansa sannan ya d’aga, murya k’asa-k’asa tamkar mai gulma yace, “nagama aikina”.
Dawowa yayi wajena bayan ya katse wayar, da kansa yake za6ar mini duk abinda yadace.

Su munubiya ma sunacan suna d’auka, kamar ance munubiya ta bar wajen saita zagaya tabaya, a dai-dai wannan lokacinne shikuma yake tunkarowa shida wasu matasan samari guda biyu, da alama yana zagayene kowani abun daban. tafiya yake cikeda nutsuwa da sarauta, sai sautin takunsa dakakeji, tunkan su iso gareta k’amshin turarensa ya iso.
Waige-waige munubiya tafara, tanason tuno mai wannan k’amshin. bata ankaraba saijinta tayi tatafi suuuu santsi ya kwasheta.
Shi mutumne mai yawan tausayi da taimako, da sauri yayo kanta kafin taje k’asan, Dan yasan fad’uwarta a wajen babban had’arine, yakai hannu zai rik’eta itakuma ALLAH yabata ikon dafe wasu tarin baskets dake wajen. Cikin runtse ido da sauke ajiyar zuciya ta furta “Alhmdllh”.
Janyewa yayi daga rankwatowar dayay kanta tamkar zai rungumeta, batareda yace uffanba yafar wajen.
Muduka akan idonmu komai ya faru, wad’anda suke tare dashine sukaima munubiya sannu, mukuma muka k’araso da sauri gareta muna tanbayarta babudai wata damuwa ko?.
“babu komai Alhmdllh”. ‘tafad’a tana gyara tsayuwarta’.
Nace, “kunga kuzo mu tafi hakanan, wlhy inajin tsoron agane bama gidansu siyama”.
Duk suka amsa da gsky mu tafi, da k’yar muka yarda mukaje wajen biyan kud’in. yabiya sannan muka tafi.
ALLAH ya taimakemu ba’a mana fad’aba.
Duk cikinmu babu Wanda yakuma maida hankali akan abinda yafaru a birnin gayu plaza, saidai abin yakasa barin raina, kamar zuciyata tana cikin fargaba, amma bansan ta miyeba, ita kanta Munubiya wani sukuku nake ganinta, bandai tanbayeta ba Na share.
Washe gari Monday, muka tashi da shirin makaranta, saida muka gama gyara gidan tsaf sannan muka tafi harsu Ayusher, dayake lectures d’inmu Na yau sai 1:30pm ne. yauma sauran ‘yan uwanmu bakowa yaje school d’inba ma har fauziyya.
Tun muna tsaye abakin titi muna jiran taxi naga wasu tsirarun mutane nabinmu da kallo. ban kawo komai arainaba muka samu taxi.
Driver ma yana tuk’i yana kallonmu ta madubi, sainaga kuma ya kalli takardar dake saman cinyarsa. d’an fara tsarguwa nayi, amma saina dake ina zaton irin dirobobin nanne masu shegen kallon tsiya.
Da muka sauka cikin makaranta ma bata sauya zaniba, kallonmu akeyi har ana nunamu, wasu da jaridu a hannu wasu kuma waya.
Munubiya tace, “Manaya bakiga abinda ke faruwaba tundaga fitowarmu gida zuwa nan ne?”.
“nagani wlhy Munubiya, bansan miyakawo wannan kallon k’urilla d’inba, dama bakiga kallon da direban can yake manaba ni da ke harya saukemu, ko sanda muke sallama dasu Ayusher idonsa Na kanmu kyam kuma yana kallon wata jarida dake cinyarsa”.
Muduka kallon jikin junanmu mukeyi, babu wanda shigarsa tazama aibu acikinmu, sannan bama tareda wani abin kallo,
Hannun juna muka kama muka cigaba da tafiya cikin tsantseni da nazartar kallonda ‘yan uwanmu d’alibai suke mana.
Tunda muka shigo cikin class sai duk aka zubo mana idanu, kuma anata k’us-k’us. yanzu kam hankalinmu yatashi sosai, wai mike faruwane? saikace yau mutane suka fara ganinmu? shin yaune muka fara shigowa makaranta?.
Bamu da mai bamu amsar tanbayarmu, muka nufi Bilkisu dake zaune itama tazubo mana idanu, ga jarida agabanta, kamar yanda muka gani wajen sauran ‘yan department d’inmu, wasu narik’e da jaridu wasu wayoyi, sunyi group group kuma suna k’us-k’us.
Da sauri Na k’arasa zan d’auki jaridar gaban Bilkisu amma saitayi saurin d’aukewa…………???

Babbar magana, shin mike faruwane? kallonmi jama’a kema su Munubiya? Sannan mi ake kallo a jikin jaridar da wayoyin kuma???????.

Nasan masu karatu ma wannan amsar suke son sani??

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*??????
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing??_*

 

*_HASKE WRITERS ASSO…??_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_

 

*_?RAINA KAMA……!!?_*
_{Kaga gayya}_

 

*_Bilyn Abdull ce????_*

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply