Hausa Novels Sakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 26


Sakayyah 26
Viral

 

SAKAYAH

 

26

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

 

Isrnejg. Acan ɓangaren gidan Lamiɗo kuwa Ramadan ya fito daga Bedroom da gudu kai tsaye Bedroom din Mommy ya nufa afalo suka ci karo da Hajiya Bunayya wani irin kallo tabisa dashi dai-dai lokacin da Khausar ta fito sanye cikin riga da skirt na less ɗinkin ya zauna ɗas ajikinta kana ta sanya Blue Black hijabi mai Facemaks jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin turaren Oud Ma’aruf fuskarta ɗauke da simple Make-up.

Cak ta tsaya tare da kallon Hajiya Bunayya data tsirawa Ramadan idanu ganin tsayuwar Khausar yasa Hajiya Bunayya sakin murmushi tare da cewa.

“Ikon Allah Ramadan ƙafa tayi sauki sosai”.

Sai kuma ta juya tana cewa.

“Ki cewa Aysha ankawo kayan tazo ta gani ta zaɓa mana”.

Girgiza kai Khausar tayi tare da kallon Ramadan dake cewa.

“Addah Khausi ƙafana tayi sauƙi”.

Murmushi tayi tare da shafa kansa kana tace.

“Alhamdulillah Ramadan amma ka daina wannan gudun har yanzu ƙafanka baiyi ƙwari ba”.

Kai ya gyaɗa mata kana yabi bayanta zuwa Bedroom ɗin Mommy bakinsu ɗauke da sallama.

 

Ƙara sawa Ramadan yayi tare da faɗawa jikin Mommy kana yace.

“Mommy ƙafana yayi sauƙi badan Addah Khausi tace kar inyi gudu ba da nayi kin gani”.

Murmushi Mommy tayi tare da shafa kansa kana tace.

“Masha Allah mun godewa Allah, ka riƙa bi ahankali insha Allah zaiyi sauki”.

Khausar na murmushi tace.

“Mommy zanje gidan su Asma’u”.

Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

“Toh Allah ya kiyaye ki gaishe su amma kada ki daɗe Allah ya tsare”.

Kai ta gyaɗa kana ta fice.

 

Tare da Sallama ta ɗan tura ƙofar Falon.

Tana shiga Idanunta ya sauka akan M Jameel dake zaune kan 2 sitter murmushi ta sakar masa kana tace.

“Laa Yah Jameel”.

Murmushin ya maidamata tare da faɗin.

“A’a Lelewal kece yau agidanmu?”.

Kai ta gyaɗa kana tace.

“Eh mana Yah Jameel na kawowa Ummi ziyara ne kuma nayi kewar Asmeey”.

Wara ido yayi tare da cewa.

“Iyeee Lelewal wato wariya zaki nuna min ni bakiya kewata ba? Rabona dake tun randa kuka karkare makaranta fa”.

Rufe fuska tayi tare da cewa.

“Kai Yah Jameel nayi mana, duk makarantar ma nayi missing ɗinta da kowa nata”.

Murmushi yayi kana cikin yanayin fara’arsa yace.

“Yanzu naji bayani amman harda Modibbo kinyi kewarsa?”.

Da sauri ta tura baki tare da cewa.

“Kewar masu sona nayi banda maƙiyana”.

Dariya mai sauti yayi tare da cewa.

“Maƙiyi kuma, kai a’a kam Lelewal”.

Ita dai Khausar juyawa tayi ta kalli Ummi

kana tace.

“Ummi ina yini?”.

Cike da kulawa Ummi tace.

“Lafiya lau ya Ramadan da ƙafa?”.

Gyara zama Khausar tayi kana tace.

“Yaji sauƙi Ummi yanzu yana takawa ko ina”.

Atare suka ce Masha Allah Ubangiji Allah ya ƙara sauƙi”.

Murmushi tayi kana tace.

“Ameen”.

Kana suka ci-gaba da hira wanda duk mafi yawan hiran nasiyya M Jameel yake musu kan sukula da rayuwar duniya kana suka sance masu riƙe al’ƙawari tare da kare mutuncin su.

Ganin rana ya fara yasa Asma’u ta kalli Khausar tare da cewa.

“Khausy mushiga kichen muyi girki”.

Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa ta cire hijabinta tabi bayan Asma’u abakin ƙofar ta tsaya tare da juyawa falon kana cike da kulawa tace.

“Yah Jameel mai za’a dafa maka?”.

Murmushi yayi kana yace.

“Duk abinda kika dafa min Khausar ina so zanci”.

 

Jinjina kai tayi tare da sakar masa da murmushi kana tace.

“Toh shikenan Yah Jameel Insha Allah zanyi maka abinda zaka so da izinin Ubangiji”.

Khausar na shiga kichen suka fara aikin cikin nutsuwa da ƙwarewa Dambun shinkafa da yaji Vegetables suka Atake kichen ɗin ya gauraye da ƙamshi Warmers me kyau ta ɗauka ta zuba masa kana ta ɗauki Bowl ta haɗa masa Fruit Salat mai sanyi sannan ta ɗaura Ababban faranti ta fito.

 

Kallon M Jameel dake hira da Ummi tayi kana tace.

“Yah Jameel gashi na kawo maka”.

Wara ido yayi kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

“Wai Lelewal duka Ni kaɗai?”.

Kai ta gyaɗa masa kana tace.

“Eh aina Malamina ne yanzu ma zan gasa maka nama gashin tukunya”.

Jinjina kai yayi tare da cewa.

“Lallai Khausisi naji daɗina na dafa tudu biyu ga Malami sannan kuma yaya saura cikon tudun dafawa na uku”.

Murmushi tayi tare da zama gefensa kana tace.

“in sha Allah in akwai na huɗuma duk zaka taka Yaya Jameel”.

Yana sa Fruit Salat abakinsa ya lumshe Idanunsa kana ya kalli Khausar tare da cewa.

“Uhm Yummmy na daɗe bansha Fruit salat mai daɗi irin wannan ba Lelewal da alama dai na musamman ne”.

Asma’u data fito daga kichen ta wara ido kana tace.

“Kai Yah Jameel har nawa?”.

Kai ya jinjina mata tare da sanya dariya kana yace.

“Iyee sosai ma Asmeey nifa yau komai jinsa nake na daban, girkinma tun tuni yake cika min hanci da ƙamshi”.

Kallon yanda yake dariya Khausar tayi wanda har ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana idanunsa alumshe haskensa ya sake bayyana kana sajensa sunyi luf-luf suna sheƙi.

 

Ajiyar zuciya ta sauƙe still Fuskarta ɗauke da murmushi tace.

“Yah Jameel kaima yau na da banne kyawunka ya sake nunkuwa tamkar Balarabe”.

Bashir da Asma’u kuwa  haɗa baki sukayi wajen cewa.

“Wallahi kuwa Muma duk akwanakin nan haka muke kallonsa”.

Wara ido yayi still Yana Shan Fruit Salat ɗin yace.

“Uhm ko dai dan na kusa Aure ne yasa kuke kallon kyawuna”.

Saurin Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.

“Sai kace gobene auren.

Murmushi yayi tare da faɗin.

“Uyumm Ummina”.

 

Sai kuma ya maida Kallonsa kan Khausar tare da cewa.

“Lelewal zaman gida ya kusa ƙarewa ko?”.

Kai ta jinjina tare da cewa.

“Eh Yah Jameel Insha Allah result ɗin mu na fitowa za’a samomin Admission”.

Jinjina kai yayi tare da cewa.

“Masha Allah, haka muke fata, ku dai kiyaye ku tsare mutuncinku a duk inda kuka riski kanku”.

 

“Insha Allah Yah Jameel na maka alƙawari zan kasance fiye da hakan ma”.

 

Kallon Asma’u Ummi tayi tare da cewa.

“Kawo mana abincin muci”.

Kai Asma’u ta gyaɗa tare da miƙewa ta zuba musu ababban faranti Khausar kuwa drinks ta kwaso musu.

Kana suka zauna kallon Ummi M Jameel yayi tare da langwaɓar da kai kana yace.

“Ummi ya aka cire ni adangi gaskiya nima ajuye muci tare”.

Murmushi Khausar tayi tare da cewa.

“Toh Yah Jameel bari na zuba mana”.

Ta faɗa tare da juye nasa akan faranti kana suka zauna tare da sanya farantin Atsakiyarsu Ummi da Khausar na facin juna Asma’u da M Jameel na facing juna haka suka gama cin abincin cike da nishaɗi.

 

Suna gamawa ana kiran sallar Azahar M Jameel ya Miƙe tare da shiga toilet ya ɗaura alawala kana ya nufi masallaci Asma’u da Khausar kuwa wajen suka gyara tare da kwashe kwanukan suka kai kichen kana suka wuce Bedroom ɗin Asma’u suka ɗaura alwala tare da gabatar da sallah bayan sun idar suka fito zuwa falo.

 

Bayan an isar da salla.

M Jameel yana shigowa ya kalli Ummi dake zaune kan 2sitter kana yace.

“Toh Ummi zan tafi ina jin jikina aɗaɗɗaure tun jiya da daddare fa rabona da wanka ji nake kamar nayi wata banyi wanka ba”.

Cikin sauri Khausar ta miƙe tare da cewa.

“Yawwa Yah Jameel dan Allah ka sauƙeni agida Mommy tace kar in daɗe”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Toh Lelewal muje mana”.

Kai ta gyaɗa tare da riƙe hannun Asma’u kana suka fita.

 

Ummi kuwa haka nan ta tsinci kanta da ɗago kai ta zuba masa Ido batare da tace komai ba.

Ahankali ya kalli Ummi ganin shi take kallo yace.

“Ya dai Ummina?”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da girgiza masa kai kana tace.

“Bakomai ba zaka bari sai anjima ba?”

Girgiza kai yayi tare da cewa.

“Um-um Ummi ina so in tafi sauri nake”.

Cikin sanyin murya tace.

“Toh saurin me kake?”.

Langwaɓar da kai yayi kana yace.

“Toh Ummi banyi wanka bafa ba kuji na fara tsami ba?”.

Wara ido Asma’u tayi tare da sanya dariya kana tace.

“Ƙamshi dai kake Yah Jameel”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Gwara dai Inje inyi wanka”.

 

Dai-dai lokacin wayarsa ta hau ruri yana cirowa yaga Moddibo murmushi yayi tare da kallon Ummi kana yace.

“Kinga fa Moddibo na kira na yanzu zaice ko Breakfast baiyi ba yana jirana, haka yake dake cin abinci bai damesa ba idan bana nan sai yace yana jirana, yaita takura min da kira idan kuma ina nan yaƙi ci”.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

“Toh yanzu tafiya zaka yi?”.

Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

“Eh Ummi”.

Cikin sanyin murya tace.

“Toh ka kira Baban nawa yazo nan kuci abincin”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Ummi zan tafi Insha Allah da yamma zan zo musha hiran mu”.

Sai kuma ya matsa kusa da ita tare da ranƙwafawa kanta ya kai bakinsa dai-dai kunnenta kana yace.

“Ummi sai anjima da daddare zanzo insha Allah musha hiran mu sannan in faɗa miki matar da zan Aura da kuma matar da na zaɓawa A.J na”.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

“Toh shikenan Babana Allah ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya Ubangiji Allah yama SAKAYYAH da mafificin Aljanna”.

Murmushi yayi tare da durƙusawa agabanta cike da jin daɗin Addu’ar ta yace.

“Ameen Ummina Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

Ummi kuwa hannu ta sanya acikin sumar kansa tana shafawa kana tace.

“Allah ya rufa maka asiri duniya da lahira Allah yasa kagama da duniya lafiya Allah yasa Aljanna ce makomarka Allah ya tsareka da dukkan sharrin abinƙi Ubangiji ya raba ka da sharrin mai sharri”.

Tafin hannunta ya riƙe kana yace.

“Allah ya amsa addu’o’in ki Ummina, shiyasa nake da yaƙinin cewa duk abinda ya sameni, na tabbata ƙaddarar ce da  Ubangiji ya rubuta minne amma addu’ar ki ba zai taɓa bari wani mummunan abu yasame niba Nagode sai dai in daga Allah ne”.

Bashir daya shigo kuwa Ido ya zuba musu yana kallon yanda Ummi ke sanya masa albarka tare da adduo’i shi kuma yana Amsawa da Ameen.

Da sauri ya isa ya durƙusa gefen yayan nashi tare da cewa.

“Ayi addu’o’in damu”.

Murmushin Ummi tayi tare da shafa kansu,l.

Asma’u da Khausar kuwa tuni suka fita suna jira ganin shiru bai fito bane yasa Khausar leƙawa Falon kana tace.

“Yah Jameel baza mutafi ba. Mommyna fa tace kada in wuce Azahar”.

Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

“Gani nan zuwa Lelewal”.

Kai Khausar ta gyaɗa kana suka cigaba da hira da Asma’u.

M Jameel kuwa fita yayi har ya isa baranda sai kuma yayi baya tare da leƙawa falon kana yace.

“Ummi yau ba rakiya ne ko dan bamu zo da Babanki bane?”.

Ummi kuwata

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da Kallonsa kana tace.

“Na’am Jamilu”.

Langwaɓar da kai yayi kana yace.

“Ummi yau dai dan ban zo da Babanki ba ba rakiya”.

Murmushi tayi tare da faɗin.

“Toh muje in rakaka Babana”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Toh Nagode”.

Sannan suka fita afalon kai tsaye jikin motarsa ta nufa ta buɗe masa.

Murmushi yayi tare da shiga kana ya maida kallonsa kan Bashir tare da cewa.

“Bashir yau dai na ƙwace maka fadar ka”.

Murmushi Bashir yayi tare da kallon M Jameel kana yace.

“Ba komai Yah Jameel na bar maka lokacin kane ai”.

 

Ahankali Ummi ta tura Murfin motar tare da rufewa.

M Jameel kuwa Ido ya zubawa Ummi ta ɗan tsakanin glass din Motar batare daya jaba Itama Ummi Idanu ta zuba masa tare da juya masa hannun alamar ya dai?.

Sauƙe glass ɗin motar yayi tare da sanya babban yatsan sa acikin bakinsa yana ɗan ciza farcen a hankali.

Cikin tsare sa da ido tace.

“Ya dai?”.

Sauke glass ɗin motar yayi tare da zuba mata Ido.

Girgiza mata kai yayi still baice komai ba.

Matsawa jikin Glass din tayi kana tace.

“A’a wai meye haka?”.

Ƙasa cewa komai yayi still Idanunsa na kanta.

Sunkuyawa jikin Glass din Motar tayi kana tace.

“Ya dai?”.

Ahankali ya lumshe idanunsa tare da jan dogon numfashi kana ya fesar cikin rawan murya yace.

“Ban sani ba Ummi”.

Da mamaki tace.

“Baka sani ba kuma?”.

Kai ya gyaɗa mata still ya tsansa na bakinsa.

Cike da kulawa tace.

“Toh me kake so?”.

Juyawa yayi ya kalli faɗin ilahirin gidan nasu kana ya kalli Asma’u da Bashir  sai kuma ya dawo da Kallonsa kan Ummi kana yace.

“Ummi ku nake so”.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

“Kai ko Jameelu ba’a rabaka da zolaya”.

Ta faɗa tare da kallonsa tsakiyar idanunsa ga mmkinta sai taga still baiyi murmushi ba kamar yanda ya saba ba.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

“To ko dai ka manta wayar kane?”.

Hannu ya sanya tare da shafa aljihun gaban rigarsa still yatsansa na cikin bakinsa yana gyatsawa a hankali kana yace.

“Um-um Ummi ban manta wayata ba gashi a aljihuna”.

Cikin yanayin damuwa da jinƙai irin na mahaifa tace.

“Toh Meye ne?”.

Kanshi ya ɗaura a kan hannunta dake kan glass ɗin motar, tare da lumshe idanunsa kana ya janyo tafin hannunta ɗaya ya kife akan goshinsa tare da buɗe lumsassun idanunsa da suke sheƙi, shiru yayi kamar mai nazari.

Sai ya kuma lumshe idanu.

Khausar dake gefe tayi dariya tare da cewa.

“Kai Yah Jameel bisa dukkam alamu dai yau kam Shagwaɓa kake ji dashi?”.

Ahankali ya buɗe idanunsa dake lumshe batare daya juya ba kana cikin raunin murya yace.

“Uhm Lelewal baza ki gane ba”.

Murmushi tayi kana tace.

“Yah Jameel zan gane mana gashi yau Shagwaɓa kake yiwa Ummi”.

Ummi kuwa sun kuyowa kansa tayi sai taga ya kuma lumshe idanunsa yayi shiru Kamar mai tunani hannunta dake goshinsa ta ɗago tare da cewa.

“Menene? Shin wai meke damunka? Me kake son faɗa min mana?”.

Cikin sanyin murya yace.

“Ummi”.

Sai kuma yayi shiru.

 

Ahankali ya buɗe Murfin motar ya fito tare da jan hannunta suka nufi cikin falon kana ya kalli su Asma’u tare da cewa.

“Ku jirani”.

Da kallo Khausar, Asma’u da kuma Bashir suka bisu, amma babu wanda yace komai kowa da tunanin da yake Aransa.

Suna shiga falon ya zaunar da Ummi kan 1sitter kana ya durƙusa agabanta cikin raunin murya yace.

“Ummi ba abinda kikeso in miki?”.

Cikin raunin murya tace.

“Meyesa kake hakane, shin wai idan ina da ɓuƙatar abu, bani da kaina nake kiran ka in faɗa maka ba Jameelu?”.

Araunane ya kalleta tare da cewa.

“Ummi ki tuna dai! ba abinda kike so in miki kada damar ta wuceni fa Ummi? Ki tuna dai”.

Ya ƙare mgnar yana murza tafin hannunsa kan rumfa sawunta

Saurin Kallonsa tayi kana tace.

“Kamar ya damar ya wuce ka Jameelu?

Na faɗa maka bana ɓuƙatar komai”.

Cikin raunin murya yace.

“Toh bani wayar ki Ummi”.

Ahankali ta miƙa masa wayarta dake hannun kujeran karɓa yayi tare da shiga text messages ɗin ta, ya duba Alart gani yayi duka-dudu  kudin dake ciki baifi dubu ɗari biyu da hamsin da biyar ba.

Kallonta yayi kana yace.

“Ummi kina da buƙatar kuɗi”.

 

Girgiza kai tayi tare da cewa.

“Ga kuɗi kuma mai zanyi dasu?.

Me zanyi da kuɗi komai fa kai kakeyi min Jamilu”.

Girgiza kai yayi tare da zaro wayarsa acikin al’jihunsa Atake yayi charking balance tare da cewa.

“Nima bani ba kuɗi da yawa acikin account ɗina”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

“Ta yaya kuɗi zai zauna acikin account ɗin ka Jamilu nasan ka haka Allah yayi ka kana da yawan kyauta zaka bawa wannan ka bawa wancan”.

 

Girgiza kai yayi tare da cewa.

“Allah yabamu mu bayar Ummi”.

Jinjina kai tayi tare da cewa.

“Ameen”.

Atake ya Mata transfer million ɗaya zuwa account dinta.

Kana yace Ummi ga Million ɗaya na miki transfer”.

 

Cikin sauri ta kallesa kana tace.

“Me zanyi dasu Jameelu?”.

Hannunta ya damƙe acikin nasa kana yace.

“Ummi duk abinda kike so kiyi dashi, tunda kin ƙi ki faɗa min abinda kike buƙata ina ji kamar akwai nauyin da ban gama sauƙewa ba gani nake kamar kinada wata buƙatar”.

Ya ida maganar muryarsa na rawa sosai sai kuma ya kama gwiwoyinta da hannu kana ya kife kansa akan cinyarta.

 

Cikin sanyayyar murya mai cike da rauni yace.

“Ummi”.

Ummi kuwa cikin sanyin murya tace.

“Na’am”.

Still muryarsa na rawa yace.

“Idan akwai abinda na miki kiya femin”.

Cikin sauri ta kallesa kana tace.

“Wai Jameelu Meyesa kake yin haka ne?.

Wai meyesa?”.

Girgiza kai yayi tare da faɗin.

“Ai ɗa baya rasa laifin da yake yiwa Mahaifiyar sa, ko babu abinda na miki a yanzu, ai kin ɗauki nauyin cikina tsawon wata tara da kwanaki tara, kin sha wahalar naƙuda kafin ki haifeni, kinsha jidalin rainona, nayi miki kashi nayi miki fitsari na miki tumɓuɗi da amai, na hanaki bacci  a lokacin da kowa ke bacci

Ummi kiya femin domin wannan ma shine babban  abin neman yafiya ga iyaye, idan kuna akwai abinda na miki yayin kuruciya da girma da kuma yayin rarrafe wata ƙil har cizonki nayi yayin shayarwa dan Allah da Manzonsa duk ki yafe min, kiyi min aikin gafara”.

Ya ƙare mgnar cikin wani irin raunataccen muryar mai rawa.

Kai ta girgiza kana cikin raunin murya tace.

“Ba kayi min komai ba kuma na yafe maka duniya da lahira na yafe maka komai na raunin cewa ko da haihu da rainonka bayan haihuwa, duk na yafe maka shi tun kafin yau”.

Wasu irin tagwayen numfarfashi masu nauyi ya rinƙa sauƙe tare da cewa.

“Alhmadulillah Ummina ngd matuƙa.”

Ita kuwa Ummu cikin sarƙewan murya taci ga da cewa..

“Meyesa kake min irin wa’annan abubuwan bana sofa”.

 

Dariya yayi kana yace.

“Toh Ummi dan ɗa yanemi yafiyar Uwarsa sai yazama laifi?”.

Girgiza kai tayi tare da Kallonsa kana tace.

“Toh ni babu abinda ka min ka tashi mu tafi Allah yayi ma sakayya da mafifiyaciyar Al’jannah mai cike da ƙololuwa  ni’ima tashi muje in rakaka”.

Ta faɗa tare da miƙewa kana ta riƙe hannunsa kamar yaro haka suka fito kana ta buɗe masa murfin motar tace.

“Toh kashiga Allah yayi maka al’barka”.

Kai ya gyaɗa tare da shiga.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

“Toh kaje Ubangiji Allah ya maka albarka Allah ya tsareka Allah ya rufa maka asiri Ubangiji ya maka sakayya da mafi kyawun abin sakamako Allah yatsare min kai Allah Ubangiji ya Albarkanci rayuwar ka Allah ya azurtaka da arziki mai albarka da yara na gari”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Ummina”.

Ya ida maganar tare da zuba mata Ido.

Asma’u kuwa ita ma shiru tayi tare da zuba masa Idanu tana kallon yanda yake kallon Ummi.

 

Khausar kuwa Kallonsa tayi kana tace.

“Yah Jameel gaskiya zan tafi idan kai ba zaka tafi ba”.

Kallonta yayi kana yace.

“Toh mutafi Lelewal baki sani bane duk saurin da kikeyi nafi ki sauri fa bakisan inda zanje bane fa shiyasa”.

Tura baki tayi kana tace.

“Yah Jameel Ina zaka je”.

Murmushi yayi tare da kallon Asma’u da Bashir kana yace.

“Ku kula da kanku sannan ku riƙe kada ku manta da alƙawarin da kuka min ga amanar Ummi na kafin na dawo”.

Murmushi sukayi tare da gyaɗa masa kai kana suka ce.

“Insha Allah Yah Jameel Allah yatsare sai kadawo.

Murmushi kawai yayi tare da jan motar suka fita saida Ummi taga motar ya ɓacewa kallonta kafin ta sauƙe ajiyar zuciya ta koma cikin gida Asma’u da Bashir na biye da ita.

 

Acan mota kuwa Anutse M Jameel ke Driving kana ahankali ya juya ya kalli Khausar data tsirawa tiri idanu kana ya sauƙe numfashi daga zuciyarsa ya fara tunanin Maganar da zai mats kana cikin sanyin murya yace.

“Lelewal”.

Juyawa tayi ta kallesa tare da cewa.

“Na’am Yah Jameel”.

A hankali ya furzar da iska kana a hankali cikin tattausan lafazin yace.

“Inne mi alfarma awajen ki mana?”.

Anutse ta kallesa kana tace.

“Toh Malam Jameel Allah yabani ikon yin duk al’farman daka ke so awajena”.

Cikin jin daɗi ya buɗe idanunsa dake lumshe ya kalleta kana yace.

“Kinyi alƙawarin duk abinda nake nemi al’farmar zaki yimin?”.

Kai ta gyaɗa masa kana tana wasa da yatsun hannunta tace.

“Na sani malam Jameel baza ka sani yin haramtaccen abu ba sannan baza ka sani yin abinda yafi ƙarfi naba kuma kafi ƙarfin neman alfarma ko wani abu awajena ina hana ka saidai ka bani Umarni Yah Jameel faɗa min me kake so inyi maka? Kai tsaye bani umarnin kawai ni kuwa in cika maka umarninka da sauri”.

Jinjina kansa yayi still Yana driving Cike da nutsuwa kana yace.

“Alhamdulillah naji daɗin Lelewal Thanks”.

sai kuma yayi gyaran murya tare da juyowa ya kalleta, itama shi take kallo ganin yadda fuskarsa ta koma alamun daga can cikin ƙahon zuciyarsa abinda zai faɗa ɗin zai fito cikin yanayin neman al’farma cikin iyawa da ƙwarewa ya juya harshe zuwa sahihin Larabci mai cike da Kekkyawan lugga ya fara mgn da larabci yayinda itama Khausar ta  juya harshen zuwa larabcin.

 

Aƙalla sunyi magana daya ɗauki tsawon minti goma sha biyar, kafin suka koma magana da yaren Hausa Inda M Jameel ya ƙare maganar da cewa.

“Nagode Khausar Nagode Nagode Lelewal Ubangiji Allah ya miki albarka”.

 

Khausar kuwa cikin wata raunan’niyar murya tayi ƙasa da kanta yayin da ruwan hawaye suka cika kwarmin Idanunta kana tace.

“Ameen”.

Ahankali M Jameel ya cigaba da Driving kana Yana cigaba da yi mata nasiyya akan rayuwa.

Ahankali Khausar da Idanunta ke kan madubin side ɗin da take ta juya tare da kallon M Jameel kana tace.

“Yah Jameel kamar wannan motar binmu fa take”.

Kai ya gyaɗa mata kana cikin sanyin murya yace.

“Eh nima na lura da haka Khausar tun ɗazu ma”.

Jinjina kai tayi tare da cewa.

“Toh Yah Jameel ka rage gudu mugani mana muga kodai mudin suke bi”.

Kai ya gyaɗa tare da rage gudun still sai motar dake bayansu itama ta rage gudun.

Ahankali M Jameel ya cigaba da Driving yayin da still motar ke bin bayansu.

Suna isa wani babban super market M Jameel ya kalli Khausar da hankalinta ke kan motar kana yace.

“Bari mushiga cikin Super Market ɗin nan mugani idan ma mu suke bi ai zasu tsaya”.

Suna Parking suka fita tare da shiga cikin Super Market din M Jameel  ya ɗiba mata turaruka tare da Choculate da sweet da kuma Biscuits yana tsinta yana faɗa mata wasu kalamai da larabci, duk da dai ba ji nake amman yadda fuskarta ke nuna kalaman masu nauyi ne yake sanarmata.

Kana kamar kimanin minti talatin da shigarsu suka fito ga mamakinsu sai suka ga wannan motar ta faka agefen nasu kai tsaye suka shiga motar M Jameel ya mata key ita ma wannan motar sai akamata key aka tayar sunbi ta bayan motar idanun Khausar ya sauƙa akan  Motar tana kallon fuskar mutanen ciki, duk da nesa ne ta gane cewa mutanen ne da  ta gani Arugar Jauro Yaya sannan itace abakin makarantar su kana taga still Motar ta cigaba da binsu.

 

Lokaci ɗaya tsoro da damuwa ya shigeta cikin yanayin tsoro ta kalli M Jameel tare da cewa.

“Yah Jameel Motar nan mu take bi”.

Jinjina kai yayi tare da faɗin.

“Nima naga alama amma watakila arashi ake samu sunyi”.

Kai ta gyaɗa still zuciyarta na cigaba da bugawa da masifar ƙarfi suna cikin tafiya motar ta ɓacewa kallon su.

 

Anutse M Jameel ya Kalli Khausar kana yace.

“Kin gani kawai arashi ake samu may be suma zasu shiga Super Market ne sannan hanyar mu ɗaya shiyasa haka”.

Murmushin yaƙe Khausar tayi kana tace.

“Haka ne kam”.

Aranta kuwa cewa tayi to kodai mutanen sun gane ta ganeta ne shiyasa suke bibiyar rayuwarta wata ƙil ita suke son su kasheta kana ta raya dole idan ta koma dole ta faɗawa Mommy.

 

Anutse M Jameel ya juya tare da kallon Khausar data zurfafa cikin tunani kana yace.

“Lelewal muje mu gidan su Moddibo ki gaishe da Kakarmu”.

Da sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

“Gidansu Moddibo kuma?”.

Murmushi M Jameel yayi kana yace.

“Babu abinda zai miki Khausar”.

Girgiza kai tayi tare da cewa.

“Nikam ina tsoro Yah Jameel. Abu kaɗan ya fara masifa ko agidan mu ma faɗa yake min bare kuma naje gidansu”.

Cikin sanyin murya M Jameel yace.

“Nayi miki alƙawari ko hararanki ba zai yiba, Insha Allah bare kuma ya miki faɗa zai miki maraba, ki yarda dani”.

Kai ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.

“Toh shikenan”.

 

Suna isa gidan yayi Parking a coumpund din farkon kana ya fita cike da nutsuwa yake tafiya tana biye dashi a baya, a kuma dai-dai lokacin da Moddibo ke kokarin fitowa daga falonsa,  cikin sassarfa ya nufeshi.

Shi kuwa Modibbo wani irin sassayan numfashi ya fesar tare da tsaida idanunsa kan J ɗinsa.

Shi kuwa M Jameel murmushi mai cike da farin ciki yayi tare ƙara sawa wurin Modibbo rungume shi yayi da ƙarfi.

Wanda haka yasa shima Modibbo yayi masa wani irin amintaccen

runguma mai cike da son juna a tare suka sauƙe ajiyan zuciya cikin sanyin sauti  Modibbo yace.

“J nayi fushi da kai”.

Cikin sanyin Muryan M Jameel yace.

“Kada kayi fushi dani A.J idan kayi fushi da J ɗin ka dawa zaka sulhunta”.

Cikin sanyin Murya Moddibo yace.

“J ka tafi gidan Ummi ka barmu mu kadai agidan, sam gidan nan ba daɗi idan baka nan shiru baki ɗaya gidan bai mana daɗi ba”.

 

Murmushi M Jameel yayi kana a hankali yace.

“A.J Rungumeka da nayi alfarma nake nema awajenka.

Saboda muyi maganar sirri akwai baƙuwar da nazo da ita dan Allah dan darajar Annabi A.J ko hararanta kada kayi”.

Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da cewa.

“Ayyah A.J ka tayani cika al’ƙawarin dana ɗauka dan Allah kada ka tozar tamu ka tuna ba haushe yace baƙonka Annabin ka sannan Annabi Muhammad (S.A.W) yace duk wanda yayi imani da Allah da rana ta ƙarshe to ya girmama baƙon”.

Kai Moddibo ya jinjina kana yace.

“Toh J naji dama ya za’ayi na tozarta matar da J na zai aura har abada bazanyi hakaba?”.

Hararansa M Jameel yayi tare da faɗin.

“Kai dai kayi min al’ƙawari koma wacece ai zaka ganta”.

Kai kawai Moddibo ya gyaɗa.

Tare da cewa.

“Nayi al’ƙawari”.

Ahankali M Jameel ya sakeshi tare da matsawa.

Da sauri Moddibo ya ɗan yi gefe da kansa lokacin da idanunsa suka sauka akan Khausar da Idanunta ke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

 

Khausar kuwa cikin wata Sanyayyar murya mai cike da rauni ta kawar da kanta gefe tare da cewa.

“Ina yini”.

Kamar yanda ta kawar da kai gefe haka shima ya kawar tare da faɗin.

“Lafiya”.

Daga nan ya juya yayi gaba.

Khausar da M Jameel suka jera atare zuwa sashen Innayi bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga.

 

M Jameel kuwa cikin yanayin sa yace.

“Innayi ga baƙuwa na kawo miki ku gaisa”.

Daga cikin Innayi tayi murmushi tare da cewa.

“Sannun ku da zuwa ko dai matar ce ka kawo Min?”.

Murmushi mai sauti yayi kana yace.

“Ehahea lallai Innayi kenan ke dai ga tanan ku gaisa dama zan wuce da ita gida ne.

Kuma A.J nata kirana shiyasa nace bari na fara zuwa nasan idan bai ganni ba wataƙil hankalin sa bazai kwanta ba”.

 

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke kana yace.

“Hmmm Yayi maka kyau da kazo a gaggauce ai da sai ka ajiyeta kafin kazo”.

Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.

“Ai kawota nayi ta gaida Innayi kuma bamu gama tattaunawa da itaba”.

Taɓe baki Moddibo yayi ba tare da yace komai ba.

 

Khausar kuwa ahankali ta tsugunna tare da Gaishe da Innayi.

Kallonta Innayi tayi kana tace.

“A’a wannan ai kamar na ganeki kamar ƙawar Asma’u ko?”.

Kai Khausar ta gyaɗa tare da sakin murmushi kana tace.

“Eh nice Innayi”.

Jinjina kai Innayi tayi tare da cewa.

“Yasu mamanki?”.

Cike da nutsuwa Khausar tace.

“Duk suna lafiya”.

Ƙoƙarin miƙewa Innayi tayi kana tace.

“Bari akawo miki abin taɓawa”.

Cikin sauri Khausar ta girgiza kai tare da cewa.

“Nagode Innayi yanzu daga gidan Ummi nake ta cika min cika na da abinci”.

 

Saurin kallonta Moddibo yayi jin yanda take magana Anutse kamar ba ita ba baki ya taɓe tare da mgnar zuci.

“Ganta kamar gaske haka take da nitsuwa”.

M Jameel kuwa kallon Innayi yayi kana ya juyi ya kalli Khausar yace.

“Mu tafi ko”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Toh”.

kana tayi gaba M Jameel da Moddibo suka fito atare a hankali suke tafiya, a hankali lips ɗin M Jameel na motsawa alamun mgn yakeyiwa Modibbo, shi kuwa Modibbo kai kawai yake jinjina mishi tare da tsaresa da ido, a haka har suka isa bakin motar Moddibo da kanshi ya buɗe masa gaban motar ya shiga kana yace.

“Dan Allah kazo kada ka barni. Ni kaɗai sam bana jin daɗin gidan”.

Murmushi M Jameel yayi tare da yiwa motar key kana yace.

“A.J ka jika randa akace babu nifa?”.

Cikin sauri Moddibo ya rumtse idanunsa da karfi, sai kuma ya buɗe su da sauri ya kallesa tare da cewa.

“Jhhhh”.

Ya ja sunan a cikin maƙoshinsa.

Murmushi M Jameel yayi tare da jan motar,

Shi kuwa Modibbo hannunsa ya harɗe a ƙirji yana kallonsa har  suka tafi.

 

Kai tsaye unguwar su Khausar suka nufa suna tafe yana tsokanarta, a haka har suka isa yana isa yayi Parking ta fita tare da yi masa godiya kana tayi cikin gida.

 

M Jameel kuwa Anutse ya juya akalar motarsa kai tsaye gidansu ya nufa yana isa yayi Parking tare da fita kai tsaye sashen Abban sa ya nufa yan shiga sukayi ta hira har La’asar tayi, atare suka je masallaci suka gabatar da sallah kana bayan su. Idar ya fito ya nufi Sashen sa yashiga bai sake fita ba sai da akayi Maghariba kana ya nufi masallaci bai fito ba sai da aka Idar da Isha’i sannan yana dawowa ya nufi sashen Abbansa lokacin shima Abbah bai dade da dawowa daga masallaci ba.

Cikin lumshe ido yace.

“Abba zanje wajen Moddibo za muyi magana”.

Jinjina kai Abba yayi tare da cewa.

“Allah ya tsare amma idan dare yayi ka kwana a can bana son tafiyar daren nan, kasan duniyar nan babu gaskiya”.

Kai M Jameel ya gyaɗa kana ya fice yana murmushi.

Motarsa ya shiga da addu’a kana yayi Hong mai gadi ya buɗe masa ya hau kan titi yana maiyin murmushin, wayarsa ya zaro, whatsApp ya shiga kan number’n Moddibon ya kusa kai.

Cikin sakin murmushin yayi mishi voice ɗin 1 mitune And 33 second

Ba zato ba tsammani yaji an sako hannu daga bayansa an ɗaura masa bindiga akai kana cikin wata magautacciyar murya akace kana juyawa zan fasa maka ƙwaƙwalwar kai da sauri ya saki wayar tasa ta faɗa kan cinyarsa garin ta sule ɗin ne kuma yatsarsa ma nuniya tayi sending din voise ɗin nasa da sauri ya ƙara taka motar jin mutumin ya ɗana kunaman bindigar yana cewa.

“Maza mu tafi kada kayi min gardama dan ko motsi kayi zan fasa kanka…!

 

 

 

 

Dan-dan yanzufa aka fara labarin ku biyuni, da kekkyawar yaƙini da ƙarfin zuciya.

 

*By*

*GARKUWAN MARUBUTA*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply