Hausa Novels Sakayyah Book 3

Sakayyah Book 3 Page 2


Sakayyah Book 3 Page 2
Viral

Ajere-Ajere motocinsu suka fara shiga harabar gidan Innayi. Moddibo kuwa sassayan numfashi ya fesar a hankali ransa cike da mamakin, shin meyesa Abban Jameel yace su sau?a anan duk da yasan cewa ba wasu wadatattun ?akuna bane a gidan, kasancewar daga ?akin Innayi sai Side ?in sa dake da 2 bedroom sai single room a bakin ?ofar falon, yace wa Abba su sau?a a hotel daya musu booking Amma yace a’a ya?i masa musu ne, saboda bai san mai ya shirya ba duk da yafi tunanin Abba yace hakane ko sai sunci abinci kafin su tafi Masau?insu.

Akuma dai-dai lokacin motocinsu sukayi Parking a farfajiyar gidan.
Daga can waje kuma cikin sassarfa Haiydar da Bashir suka nufo gidan wanda har sun dauki hanyar komawa gida kasancewar sun jira su basu zoba sai kuma suka hango motocin su.

Acan harabar cikin gida kuwa cike da matsanancin mamaki da al’ajabi Moddibo ke bin baki ?aya ilahirin gidan da kallo wanda aka tsara shi yayi masifar kyau wasu dan ?ara dan ?aran Side ne akayi su guda biyu wa ?an da kusan komai nasu irin nasa ne sai dai basu da wadatan flowers kamar nashi cikin fesar da numfashi da mamakin dake kwance saman fuskarsa ya ziro ?afarsa na dama kafin ahankali ya gama fito da gangar jikinsa daga motar, hannunsa na ri?e cikin na Khausar still Idanunsa na bin harabar gidan da kallo.
Akuma dai-dai lokacin Idanunsa suka sau?a kan Abban Jameel, Lami?o da Malam Ahmad suna sau?a daga kan barandar ?aya daga cikin Sabon Side biyu da aka gina still da mamaki ya maida kallonsa kan Innayi data fito daga Motar da suke.
Murmushi Innayi tayi ganin kallon mamakin da yake bin gidan dashi kana tace.
“Bismillah ku shiga side ?inka”.
Kallon yaushe akayi wannan ginin yayi mata, fahimtar kallon da yake mata yasa ta jinjina masa kai tare da cewa.
“Tun kwanaki ai aka fara ginin saboda sanin cewa zamu zo Auren su Jameel, kana lokaci zuwa lokaci zamu bu?aci zuwa nan tunda ni da kai dai ba zamu manta garin Membila ba”.
Sanyayyar ajiyar zuciya ya sau?e kana yayi murmushin gefen baki sosai yaji da?in hakan saboda bawai ya tsani garin Membila bane saboda ya samu nasa garin, kawai dai Membila ta fita a ransa ne saboda rasa amininsa, Amman duk da haka yasan gari Membila garine wanda yake da tarihi arayuwarsa yana jin Membila na cikin garin da yake tamkar tsagin jikinsa, ya sani bazai manta garin arayuwarsa ba, ko ina yaje a duniya watara zata fa?o masa arai kuma dole zai bu?aci jin yana son zuwa cikin garin.

Anutse Didi ta fito kana Lalla Khadijah, Lalla Hafsat, Sai Rahama tana fita ta nufi gefen Khausar fuskarta ?auke da murmushi tace.
“Woww Lalla Khausar haka garinku yake da?i?,Masha Allah kina jin weather Mai da?i haka Masha Allah i like it”.
Murmushi Khausar tayi kana ta gya?a mata kai da fa?in.
“Aikuwa zaki sha sanyi”.
Idanu Rahama ta lumshe sai kuma ta bu?e tace.
“Aikam akwai sanyi kam, duk da muma A Morocco ana mana sanyi but time to time ne amma bai kai wannan ba sanyin nan daban ne”.
Ta ?arashe maganar tana ?an?ame jikinta waje ?aya jin yanda sanyi ke ratsata.

Kallon Khausar dake ?an lumshe idanu Didi tayi kana ta maida kallonta kan Moddibo cike da kulawa tace.
“Aleeyu ku shiga ciki yarinyar ta gaji da zaman motar nan ”.
Kai ta gya?a Tare da cewa.
“Toh”.
Sai kuma ya dam?e hannun Khausar cikin nasa tare da ?an janyota jikinsa suka nufi Side ?in sa.

Gaba Innayi tayi tana mai cewa.
“Didi, Lalla Khadijah Lalla Hafsat Bismillah”.
Kai suka gya?a tare da bin bayanta suka nufi ?aya daga cikin Side ?in.
Akuma dai-dai lokacin Ummi ta fito daga Side ?in fuskarta ?auke da farin ciki da mamakin ganinsu tace.
“Masha Allah sannunku da zuwa, sai yanzu kuka iso, da naji ku shiru-shiru har nake cewa barin tafi wata ?il zaku kai dare”.
Ta ida maganar tare da rungumar Didi itama Didi rungumeta tayi tana cewa.
“Masha Allah fatan mun sameku lafiya”.
Kai Ummi ta gya?a tare da ri?o hannun Lalla Hafsat tace.
“Alhamdullah. Bismillah mu shiga daga ciki”.
Cike da farin ciki suka bi bayanta…

Abban Jameel kuwa shi yayi wa Abualeey, Waziri, Galadima, Baffan Zakariyya, Dr Jameel Zakariyya jagora zuwa Side ?in da suka fito ko wanne yana ?auke da 3bedroom manya,-manya wanda aka shirya su da kaya na alfarma da kawa ?aya daga cikin ?akunan Dr Jameel, Zakariyya da Ibraahim ne aciki.
Sai kuma na biyun Abualeey ne da Waziri, Sai kuma Baffan Zakariyya, Galadima.
Acan Side ?in su Ummi kuwa Didi da Rahama ta nunawa ?akin farko inda zasu zauna kana bedroom ?in gaba ta kai Lalla Khadijah, Lalla Hafsat,da Niyna.
Sai da ko wannensu yayi wanka kana suka canza kaya zuwa mai ?an nauyi amma ba can ba saboda yanayin sanyin garin kafin suka gabatar da sallolin suka ?an huta tare da ta?a hira sai kuma suka fito Falo Ummi da kanta tayi musu iso zuwa dining.
Didi na murmushi ta sha?i sanyayyar Iskar garin da kuma wanda bishiyoyi da flowers ?in gidan ke ka?awa tace.
“Kai Alhamdulillah Masha Allah weather garin nan akwai da?i ”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Aikam sai dai akwai sanyi”.
Sai kuma tayi serving ?in su da lifiyayyan abinci iri iri na alfarma da suka musu.
Akuma dai-dai lokacin Haiydar da Bashir suka shigo bayan sun fito daga ?angaren su Abualeey Haiydar na bin Falon da kallo yace.
“Ummi ina Addah Khausy?”.
?an Murmushi Ummi tayi tare da fa?in.
“Tana side ?in Moddibo”.
Cikin sassarfa ya juya da niyyar fita sai kuma yayi saurin juyawa ya kalli Didi cikin girmama ya ?an rusunar da kanshi yace.
“Ayyah Didi kuyi ha?uri na manta bamu gaisa ba ina yininku fatan kunzo lafiya?”.
Dariya tayi tare da fa?in.
“A’ lafiya lau anyi kewar ?ar uwa ko?”.
Dariya yayi tare da kama hannun Bashir da yake gaida su daga nan suka ficewa kai tsaye Side ?in Moddibo suka nufa.

Acan Side ?in Mazan ma haka ya kasance Abban Jameel da kansa yagabatar musu da abinci na alfarma da girmamawa sosai Abualeey suka jinjina mutunci da karramawarsu…

Haiydar da Bashir kuwa tun daga kan step ?in Side ?in Moddibo suke ?walawa Khausar kira suna cewa.
“Addah Khausy! Addah Khausy!!, Addah, Khausy!!!”.
A kuma dai-dai lokacin Khausar da Moddibo ne tsaye Dining hannunsa na cikin nata cikin taushi ya ran?ofa kanta tare da sassauta murya yace.
“Me zaki ci?”.
Kanta ta langwa?ar tare da tsirawa jerin abincin dake dining ?in ido lumshe idanunta tayi tare da fara bu?e womers ?in cikin yanayin jin sanyi ta motsa la??anta tare da cewa.
“Ga nan tuwo miyan kuka kasa min ka?an zanci ”.
Ajiyar zuciya ya sau?e tare da fa?in.
“Masha Allah zauna toh bari na zuba miki”.
Da dan sauri ta juya jin Bashir da Haiydar na cewa Addah Khausy Addah Khausy hannunta dake cikin nasa ta janye ta juya cikin sassarfa ta nufi ?ofan anufinta tayi gudu.
Da wani irin sauri Moddibo ya ri?o tsintsiyar hannunta yace.
“Kiyi ha?uri Minha na tuba dan Allah kada kiyi gudu”.
?an ware idanunta tayi tare da fa?in.
“Su Bashir da Haiydar ne fa”.
Kafin ta ?arasa suka ?ara so cikin falon tare da rungumeta shima Bashir cikin sauri ya rungumeta ta gefen Haiydar.
Murmushi Moddibo yayi tare da har?e hannunsa a?irji yana kallonsu da tattausan murmushi bisa kekkyawar fuskarsa.

Khausar kuwa kallon Bashir tayi tare da cewa.
„Bashir ina Asma’u?”.
Murmushi yayi kana yace.
“Ba tazo ba wai ita kunya Amarya baza ta zo ba”.
Dariya mai tauri ta sanya tare da fa?in.
“Don Allah yanzu baza tazo ba haka zata min kenan?”.
Kai ya gya?a tare da cewa.
“Wallahi fa ta?i zuwa tun safe ta?i zuwa ayi shara da ita wai Ummi tayi ha?uri”.
Dariya Khausar ta sanya tace.
“Lallai dai kam”.
Haiydar kuma hannunshi yasa cikin nata.
Cikin mamaki ta kamo hannun tare da kallon faratunsa hararansa tayi tare da cewa.
“Me haka zaka wani tare farce kamar mace?”.
Cikin lingwa?ar da kai yace.
“Na gaza koyan yanke wa nefa, Mommy kuma tace in dai bazan koyaba bazata yanke minba”.
Murmushi tayi tare dasa hannunta ?aya ta dungure ?eyarsa tare da cewa.
“Shine daga isowata zaka ha?ani da aikin yankewa”
Ta ?areshe mgnar tana jawosu suka zauna bisa kujerun Dinnin table ?in.
Moddibo kuwa a kujerar dake fuskantar Khausar ?in ya zauna, yana maiyi mata wani arin amintaccen kallo ya fahimci akwai tsananin sha?uwa da so tsakaninta da Haiydar duk da yawan fa?an da suke a da.
Anan sukaci abinci tare.
Kana sukayi ta hira kiran sallan Magrib ne yasa duk mazan sunka tafi masallaci.
Kana basu dawoba saida sukayi sallan Isha sannan suka dawo nan kuma suka sake dasa sabon hira.
Hakama Abban Jameel dasu Abualeey.
Suma su Didi da Ummi haka ta kasance a wurinsu.

Misalin sha ?aya su Lami?o suka yiwa su Abualeey saida safe kana suka tafi.
Su kuma duk sukayi shirin bacci suka kwanta.

Ummi dake tare da Malam Ahmad ta nufi sashen Khausar tana fa?in.
“Bari in je in jawo su Haiydar dan na lura su yau in zasu samu a nan zasu kwana”.
Kai ya jinjina mata tare da jingina jikin motarsu ya tsaya jiran fitowarta.

Ummi na shiga ta kalli Haiydar dake zaune gefen Khausar tace.
“Ku tasa mu tafi”.
Da sauri Khausar ta mi?e tare da cewa.
“Toh Ummi bari in ?auko mayafina mu tafi”.
Juyawa Ummi tayi jin Moddibo na cewa.
“Ina zaki je?”.
Idanunta ta narkar kana tace.
“Zanje gida mana”.
Yana tsuke fuska yace.
“Da Izinin wa?”.
Murmushi Ummi tayi tare da kallon Haiydar da Bashir tace.
“Haiydar kuzo mu tafi dare yayi mu barsu su huta”.
Saurin kallon Ummi Khausar tayi tace.
“Ayyah Ummi dan Allah ku jirani ya za’a kuma ace bazan jeba don Allah kayi ha?uri”.
“Da Izinin wa?”.
Ya maimaita tambayar yana mai tsuke fuska.
Kamar za tayi kuka tace.
“Da Izinin ka mana”.
Kai tsaye yace.
“Toh ban bada Izini ba”.
Ummi kam hannun Haiydar da Bashir taja suka fice.

Sai da suka sau?e Haiydar agida kafin suka wuce.

Haiydar na shiga Falon Momy ya shiga da sauri ya zauna gabanta kan lallausan Darduma da take bisa alamu shafi da witri tayi.
yayin da ta jingina kanta jikin kushin cike da matsanancin farin ciki yace.
“Momy”.
Cikin tsira nasa ido ta gyara zamanta tare da cewa.
“Na’am”.
Murmushin fuskarsa ya fa?a?a tare da fa?in.
“Kin ga yanda Addah Khausy ta dawo kuwa Momy?”.
Kai Momy ta girgiza kana tace.
“A’a ya ta dawo?”.
Zama ya gyara yace.
“Wallahi idan kika ganta zakice Balarabiya ce Masha Allah Subhanallah, tayi wani irin fari mai masifar kyau farinta har wani ?elli takeyi”.
?an ware idanu Momy tayi tare da fa?in.
“Allah ko?”.
Kai ya gya?a yace.
“Wallahi fa”.
Daga nan suka cigaba da hira.

Acan ?angaren su Moddibo kuwa cikin tura baki Khausar tace.
“Haka kawai ahanani zuwa gidan mu yanzu Fisabilillahi muna ?asa ?aya gari ?aya ace bazan ga Momyna ba?”.
Kansa ya ?aura bisa kafa?arsa yace.
“Na isa? Ai ban isa in hana ki ganin Momyn kiba? waya isa ya raba uwa da ?a? ban isa in ra Baki da Momy ba.
Kawai dai nima bana so ara bani da ?ana akusa dani ne shiyasa”.
Cunno baki tayi tana kallonsa cike da shagwa?a hanci ya lakace mata kana ya cigaba da cewa.
“Kuma ina so ki huta nasan in kunje hira zaku tayi baza ki huta ba kiyi ha?uri ki kwanta kiyi bacci ki huta gobe da kaina zan kai ki muje mu gaida Momy”.
Ajiyar zuciya ta sau?e tare da cewa.
“Da sassafe”.
Kai ya gya?a cikin tabbatar wa yace.
“In sha Allah in dai mun karya”.
Lallausan murmushi ta sakar mishi tare da ri?e tafin hannunsa tace.
“Toh shikenan”.
Bedroom suka wuce sosai tsarin ?akin yayi kyau komai yayi yanda ake bu?ata kana agyare tsaf-tsaf sai tashin ?amshin roomfteshner yake, zama tayi kan gadon tare da jingina kanta da jikin gadon.
Moddibo kuwa gefenta ya zauna yana ?an matsa mata ?afafun yace.
“Kinga tafiyar nan da akayi mai ?an tsawo sai nake ga kamar ?afarki ta kumbura”.
Idanunta dake lumshe ta ?an bu?e ta kalli ?afan sai kuma ta gya?a masa kai tace.
“Eh dama Ni haka nake in dai na ?anyi tafiya mai tsawo amota Normal haka yake min, zuwa safiya zaka ga ya watse”.
Ajiyar zuciya ya sau?e tare da fa?in.
“Kuma ahaka kike so ki tafi kije ki zauna ba kiyi bacci ba”.
Ya ?are maganar yana jan yatsun ?afar tata tare da ?an mammatsa mata su, sassayan numfashi ta fesar tare da muskutawa, da sauri ya ?an tallabota tare da gyara mata kwanciyar saboda ganin duk ta sake alamun bacci mai nauyi takeji.
Ahaka ya cigaba dayi mata massage suna hira jefi-jefi har bacci ya ?auketa.
janyota jikinsa yayi ya ha?a hannunsa waje ?aya ya tofa musu addu’a ajikinsa ya fara shafawa kana ya shafa mata.

Washe gari bayan sun kammala breakfast da duk wani abu da za suyi Kai tsaye sashen su Didi suka shiga bakinsu ?auke da sallama suka shiga bayan sun gaigaisa Moddibo ya kalli Didi tare da cewa.
“Didi zamu je wurin Momy”.
Kai Didi ta gya?a kana tace
“Ok sai munzo muma yanzu Ummin Jameel zata zo mu taho tare”.
Kai ya gya?a yana ?an matsa hannun Khausar yace.
“Toh shikenan sai kun zo”.
Daga nan suka mi?e suka fito da kansa ya shiga mazaunin driver, kana ta shiga gefen mai zaman banza, cikin nitsuwa yaja suka tafi anutse yake driving yana Jin wani yanayi na daban.

Titinan garin ya zubawa ido lokaci ?aya kuma tunanin J ?insa ya fa?o masa sai kuma yake tuna Lokuta da dama Idan yana tu?i J na gefensa ko kuma J na tu?i shi yana gefensa jikinsa ne yayi sanyi, tafin hannunta ya ri?o tare da mannawa kan cikinta yayi shiru kwayar idanunsa na tsats-tsafo da ruwan hawaye.
Tuni ta fahimci yanayin da yake ciki cikin sanyi da rauni tace.
“Allah ya ji?an Yah Jameel Allah ya mishi Rahma Allah ya gafarta masa”
Araunane yace.
“Ameen Ya Allah Minha”.
Tana matsa hannunsa dake cikin nata tace.
“Yah Jameel yanzu baya bu?atar kukan nu addu’ar mu yake bu?ata”.
Cikin ?o?arin hana hawayen sa zuba yace.
“Nima haka nakeso ina ta ?o?arin hana zuciyata da Idanuna kuka akan J sai dai muyi ta mishi addu’a Amman wasu lokutan ina gaza hana kaina hawaye a kanshi saboda nayi rashine da har yau ban samu madadinsa ba”.
Cikin tausasawa tace.
“Na sani Yah Mu’allim to Amman Allah ya fimu sonshi, kuma dama shi ya bamu shi dan haka addu’a kawai zamuyi ya mishi”.
Cikin sanyi yace.
“In sha Allah za muyi masa”.

A kuma Dai-dai lokacin mai gadi ya bu?e musu gate ?in gidan Lami?o Parking yayi kana suka fita da sauri ta nufi harabar gidan da nufin gudu,
saurin ri?o hannunta yayi cikin tsira mata idanu ya langwa?ar da kai yace.
“Kar kiyi gudu mana wai ke bakya jin tsoron ki fa?ine”.
Kai ta ta gya?a tace.
“Toh ai sauri nake inje inga Momy”.
Sake langwa?ar da kai yayi yace.
“Ai zaki ganta Minha ba sai kinyi gudu ba tun da gaki cikin gidan”.
Ko gama rufe baki baiyi ba ta hango Raudat ri?e da Comb da kifiya bisa alamu kitso zata tafi.
Da sassarfa ta nufeta tana kiranta,
Ita kuwa Raudat jin muryar Adda Khausy tane yasa ta ?ago kanta aiko ganinta ne yasa ta buga tsalle cike da matsanancin farin ciki tace.
“Addah Khausy”.
Da wani irin sauri Khausar ta janye hannunta dake cikin nasa ta ruga da gudu.
Atsorace ya sanya tafin hannunsa biyu ya dafe kansa kana ya motsa la??ansa tare da fa?in.
“Ya Salam ki daina gudun nan”.
Ina bata saurareshi ba da gudu ta rungume Raudat Raudat kuwa tsalle ta ri?a yi ajikinta tana cewa.
“Oyoyo! Oyoyo Addah Khausy!, Mommy Addah Khausy!! Tazo Addah Khausy!!!,Oyoyo”.
Cike da matsanancin farin ciki Khausar ta ?aga ta sama ta ri?a juyawa da ita a tsakiyar gida wanda hakan ne yasa baki ?aya mutanen gida suka san cewa Khausar tazo.

Dai-dai lokacin kuma Haiydar ya fito daga ?akinsa.
Da gudu Sulaiman ma ya fito daga sashen Hajiya Bunayya atare suka rungumeta suna fa?in.
“Oyoyo Addah Khausy ”.
Khausar kuwa cike da matsanancin farin ciki take jujjuyawa atsakiyarsu ruggume da Raudat tsam a jikinta.

Jin sowarsunw yasa Momy dake zaune falonta ta mi?e da sauri ta fito jin sautin muryansu na tashi cak ta tsaya ta ri?e ?afan Falon tare da tsirawa Khausar idanu tana kallonta cike da so, ?auna, bege, kewa irin na uwa da yarta.

Khausar kuwa sai juyawa take dasu tana ?yal?yala dariya sai kuma tayi saurin sake su ta nufi Momy tana gudu tare da fa?in.
“Oyoyo Momyna”.
Runtse idanunsa yayi sai kuma ya ?an ?aga saitin muryansa yace.
“Dan Allah Momy kice mata ta daina gudun nan zata yiwa kanta Illah fa”.
Murmushi Momy tayi tare da kallon Khausar kallo ?aya ta mata ta fahimci tana da ciki wanda har ya ?an tasa ga wani irin kyau da tayi sai ?elli take zubawa ga ?an cikinta daya turo gwanin kyau ya zauna a jikinta cib da cib sai ?ugunta da ya ?ara fa?i.
Cikin sauri da bege Minti ta rungumeta asanda ta isa gareta sau kuna tace.
“Ke meyesa bakya girmane. Khausar wannan guje-guje har yanzu baki barshi ba”.
Murmushi tayi tare da sake Momy sai kuma ta sake rungumeta kana ta sake ta ta kuma sake rungumeta ?an turata Momy tayi tare da fa?in.
“Ni matsa ahanya Bismillah Moddibo shigo”.
Sai alokacin Haiydar ya mi?awa Moddibo hannu kana yace.
“Yah Moddibo Bismillah mu shiga”.
Kai Moddibo ya gya?a suka shiga bayan sun zauna a falo Momy da kanta ta kawo musu Drinks da Snacks da ruwa ta ajiye musu agabansu.

Raudat kam cike da farin ciki ta kwanta kan Khausar tana ta nu?ur?usata,
ahankali Moddibo ya ri?o tafin hannunta yace.
“Kiyi ha?uri Aunty Raudiy adaina danne Adda Khausy kar aji mata ciwo”.
Cikin jin da?i Momy ta kawar da kanta jin yanda yake mata magana cike da kulawa sai kuma ta mi?e tace.
“Bismillah kusha ruwa bari nazo ”.
Ta ?arashe maganar tana fita kai tsaye bedroom ?in ta ta wuce.

Acan ?angaren Hajiya Bunayya kuwa a dai-dai lokacin zaune take aruwan zafi idanu ta tsirawa ruwan tana kallon ?ananun tsutsotsin farare masu jajayen kai wanda ga duk kan alamu sune suke addabar ta da jarabar ?ai?ayi wanda zuwa yanzu tsakaninta dubaranta da gabanta ya wawake tuni sun fafeta ta kashin ta da gabanta ya ha?e saboda masifar ?ai?ayi da yanda suke cinta taje asibiti har ta gode Allah abanza kana ta kira matar data ha?a su da Boka Gillaw.
Taje ta fa?awa Boka Gillaw ga abinda yake faruwa yace wannan sakamakon aikin su suke girba babu abinda zai iya kada su sake kiransa, dama shi ya gaya musu idan bu?ata ta biya su biya ku?i idan kuma bai biya ba shikenan suji da kansu.
Matar ta tambaye shi mai zai basu amma yace babu abinda zai basu wannan Sakayyar sune babu wanda ya isa ya kawar da Sakayyar zunubansu ne ya sauka akan su Babu ruwansa suji da kansu shima yaji da kansa.

Tuno wa?anan maganganun ne yasa ta fashe da marayan kuka mai cike da nadama mara amfani, tana cikin kukan ta jiyo sautin muryoyi ana cewa Oyoyo Addah Khausy ahankali ta juye ruwan tana kallon tsutsotsin masu masifar gudu da ?ai?ayi dole sai ta shiga ruwan ?umin ne take ?an jin sau?i.

Tana fitowa daga Bathroom ?in ta zaune gefen Amina dake kwance kan gadon wacce ta rame ta zama wata halitta daban kamar ?warangwal tana nan tamkar wacce babu numfashi ajikinta kuka ta fashe dashi tare da cewa.
“Amina kinga Sakayyar abinda mukayi ko. Ubangiji ya kama mu tun a duniya Allah ya kamu da Sakayyar tarin zunubanmu Amina ya zamuyi?”.
Araunane Amina ta ?ago kanta cikin muryanta da baki ?aya ya koma na wata halitta ta kalleta duk ta disashe baki ?aya kamanninta da siffofinta ya fara zama na maciji ne ko menene dai ho da kyar ta bu?e bakinta tace.
“Umma munemi gafarar wa’anda muka cutar tun kafin dare ya mana ”.
Cikin rauni da zubda hawaye Hajiya Bunayya tace.
“Dole ma mune mi gafarsu su yafe mana nasani wannan Sakayyar abinda nata yiwa wannan baiwar Allah ne, da abinda nayi wa ?arta da kuma yanda nayi ta zubar mata da ciki sannan nasa aka kashe Ramadan yanzu shine Allah ya jarabceni da wannan abin”.
Kuka sosai Amina ta fashe dashi tana ji kamar adawo mata da lokacin baya ta gyara kuskurenta.
Ita ma Hajiya Bunayya kuka ta fashe dashi Asiya ce ta shigo ta zauna gefen su ta shiga rera kuka cikin rauni da tausayinsu tace.
“Umma ku nemi gafarar Momyn Khausar da Khausar duk wanda ku kasan kun cutar kunemi gafarar su Allah gafururrur rahim ne shima zai yafe muku sai kuma ku nemi gafarar Allah akan shirka da kuka yi Allah ya yafe muku ”.
Cikin raunin Murya da shesh-she?a Amina ta gya?a mata kai tare da fa?in.
“In sha Allah zamu nema amma Addah Asiya ki taya mu basu ha?uri ”.
Kai Asiya ta gya?a tare da cewa.
„In sha Allah yanzu ma mukayi waya da Samira Sani take cemin itama jiya baki ?aya Momyn ta kwana tayi tana ta ihu acikin gida gaba ?aya tazama kamar mahaukaciya, ita tana jin tsoro yanzu zata dawo nan ma”.
Atsorace Hajiya Bunayya ta dafe kuncinta tace.
“Yau sun shiga ukunsy Hajiya Lami fa ta haukacene”.
Cikin sanyi da zubda hawaye Asiya tace.
“Haka dai alamu suka nuna Umma Allah ya yaye muku ya dubeku da idon Rahama”.
Cikin rauni da tarin tsoro Hajiya Bunayya tace.
“Ameen”.
Amina kam sai hawaye take tana nadama da danasanin abinda ta aikata.

Acan Falon Momyn kuwa bayan Moddibo yasha ruwa kana yaci Snacks da Drinks Momy ta fito suka gaisa bayan sun gaisa ta kallesa da kulawa tace.
“Ina su Didi kuma?”.
Sake sunkuyar da kansa yayi tare da cewa.
“Momy su Didi suna gida amma sunce zasu ?an fito zuwa azahar, sannan zasu fara ta gidan su Ummu kafin suzo”.
Dai-dai lokacin kuma Asma’u ta shigo Falon bakinta ?auke da sallama kasancewar Haiydar ya kirata ya sanar mata Khausar tazo gida.
Khausar na ganinta ta mi?e da tsalle kana ta ha?a da gudu suka rungume juna da Asma’u suka fara juyawa atsakiyaar Falon.
Cikin tsuke fuska Moddibo ya kalli Asma’u tare da fa?in.
“Asmau me haka ki sake ta?”.
Ahankali Asma’u ta sunkuyar da kanta ?asa sai kuma ta saki Khausar ta tsugunna gefen Moddibo cike da ladabi tace.
“Yah Moddibo sannu da zuwa Ina yini”.
“Lafiya”.
Ya fa?a yana ?an sake Fuskara sai kuma yace.
“Ke baki ga yanayin yanda ?awar taki take bane kike mata irin wannan rungumar?”.
Dariyar dake cinta ta danne ganin yanda Khausar ta Cunno baki kana tace.
“Yah Moddibo ayi ha?uri”.
Yana murmushi yace.
“In sha Allah yanzu dai akiyaye”.
Kai ta gya?a tare da mi?ewa ta ri?e hannun Khausar suka nufi bedroom ?in ta.
Ganin haka yasa ya mi?e tare da cewa.
“Momy bari in fita dan su Dr Jameel na jirana zamuje gida Abban Jameel ”.
Mommy na gyara mayafinta tace.
“Ayyah ai nima Jameel ?in nan ina so akawo minshi in ganshi Haiydar yata bani labarinsa”.
Cike da girmamawa yace.
“In sha Allahu Momy za’a kawo miki shi”.
Murmushi tayi tare da fa?in.
“Toh ka gaishe su”.
Amsawa yayi kana ya fita.

A dai-dai lokacin kuma Didi, Lalla Khadijah, Lalla Hafsat, Suna gidan Ummin Jameel duk sun gaisa da ?an Uwanta wanda suka fara taruwa saboda bikin bayan sun gama suka fito zuwa gidansu Momyn Khausar.

Suna shiga Falon dai-dai lokacin Asma’u da Khausar na kitchen Khausar har mamakin kanta take saboda ?osai da kunun gya?an da taci da safe, kana yanzu kuma Asma’u da kanta ta tu?a mata tuwan Semovita da miyar ?anyen ku?ewa a?aramin dining Dake kitchen ?in suke zaune.
Khausar kam ta kasa daina mamakin kanta yanda take cin tuwon sosai kallon Asma’u da itama tayi wani irin kyau na ban mamaki tayi ta fito a asalin amarya tace.
“Wallahi Asma’u har mamakin kaina na keyi rabona da abinci hakafa nafi wata hu?u”.
Murmushi Asma’u tayi tare da cewa.
“Ikon Allah baby ?an albarka yasan yazo garinsu kenan”.
Murmushi Khausar tayi tare da sunkuyar da kanta ta ?an kalli cikin,
dai-dai lokacin kuma suka jiyo sallamarsu Didi sun shigo gidan cikin wani irin…

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply