Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 11


Sakon So 11
Viral

EPISODE 1️⃣1️⃣

Hannunta Baba yakama cikeda damuwan dazaka iya gani kwance kan fuskanshi yace “Gwaggo dan Allah ki zauna kiyi shiru maza suyi magana, haba mana Gwaggo” Abdulhadi shima cikeda damuwan yace “dan Allah Gwaggo, dan Allah” cikeda bacinrai Gwaggo tace “aini banmasan kamilin mutun bane haka ba babba kuma, nadauka irin yaran nanne dake tashen balaga masu kudi da rawan kai amman wannan kalleshi nutsaste kamili dashi” hannunta da Baba keja alamun ta zauna yasa ta zauna kan kujeran tace “nayi shiru yanzu amman wlh idan baku karbanma jikata hakkinta ba wlh zan bude bakina ehe” ta zauna tana goge kwalla, dan murmushi Musty yayi yataho wajensu anatse yace “dudda nasan kowa hankalinsa atashi yake gaisuwan musulinci wajibi ne dan haka Assalamu Alaykum” atare dukansu su Baba suka amsa, Musty yace “nasan meke tafe daku amman dan Allah alfarma nake nema inaso kafin ku yanke hukunci kokuyi wani abu zan muku bayanin komi dakuma asalin nuna muku video CCTV camera dake nan akowani lungu da saku na company mu” gyadamishi kai su Baba sukayi alamun tom, yace “ni sunana Mustapha nine babban abokin Imran gashichan aboki nane tun muna yara yan kanana” yanuna Abee daya maida kanshi kasa dukansu suka kalli Abee, Musty yace “ga kannenshi chan Hamza da Ibrahim wayan nan kuma abokanenshi ne, Imrana nada yara hudu, biyu sun rasu tareda matarshi da akazo har gida aka kashe” ahankali su Baffa sukace “Allah musu rahama” Musty yace “sai biyu yanzu keraye, namijin nada shekaru 22, macen 21, nasan kuna mamaki maisa nake fadamuku haka inaso kusan waye Imran ne, bawai sabida Abokina bane, tunda nake bantaba ganin mutum mai kiyaye dokokin Allah kaman Imran ba tun yana kankanin shi mutum ne kamili nutsastse mai amana, abinda kuma yafaru tsakaninshi da yarku was nothing daya wuce kaddara kokuma nace samin akasi akayi wannan shine kawai abinda zance bari na kunna muku CCTV camera footage na ranan dasukazo makarantan kugani Ibrahim zokasa” zuwa Ibraheem yayi gaban babban tV dake office din yamakala flash dinshi saiga video yafara daga inda sukazo makarantan tundaga waje har zuwa ciki da lokacin datace zatai fitsari anajin maganan dudda bada kyau yake fitaba aka nuna inda ta tsaya tana juye juye dan bata gane bayin ba saitabi corridor tahau gudu tana ciro su waya da chocholate har zuwa inda ta bangaje Abee Musty yace “inaso kusaka idanunku akan wan nan mutumin” bayan ta wuce tai kwana aka nuno Abee yayi hanyar office nashi ya murda akulle sai kuma yay hanyar bayi saiga mutumin yafito, saikuma aka shiga lokacin da Lujain tashiga bayin da gudu daganan babu komi kuma sabida babu camera a bayi, saiga Abee shima yazo yashiga, Gwaggo ta gyara zama idanunta kaman zasu fito su sauka kasa, saiga mutumin yazo ya soka waya yana video jin muryan mutane yatafi yabar wajen kusan 2min da shiganshi saiga Lujain tabude kofa ta tsaya sai gashi anyo ball da jakanta da wayan ta tsugunna ta dauka ta goya ta gyara riganta tana waige waige tawuce dahar yanda mutanen nan suka mata kwatace saiga Ibrooo yazo har bayin yashiga rikeda key sannan aka nuna musu duka video Lujain a factory da yanda tai Plate har lokacin databar company su sannan ya katse.

 

Anatse Musty yace “abu na farko danakeso kugane kuduba lokutan da abin yafaru idan fasikanci ko wani abu sukayi dan wanan lokacin yayi yagama? Sanan akanme yana mai kampanin nan gabaki daya bawai shida wani ba bazai kaita office nashi ba inda akwai daki, bayi dakomi aciki sai nan bayin kowa bayin ma’aikatanshi Iyye? Koma bayin kowa ne zai iya sa security idan wani abu zaiyi yace kar wanda yazo banda haka kuma bayin maza ne ita meya kaita bayin maza dudda nasan yaran makaranta babu abinda waya baya sasu suyi tunda harta bugeshi batama tsaya ta kalleshi ba balle bada hakuri, abu na karshe video dakuke gani idan kunada wayanda sukasan computer zasu iya gayamuku cewa anyi editing dinshi da yanda kofan ke jijjiga da muryan karan datakeyi duka kari ne, saikuma shi wanan mutum dakukaga yay video yaturama abokina messege kan yanaso abashi miliyan dari da kampanin nan koyayi releasing video shi yana tarayya da wata shi yasan baiyi abu hakaba yay blocking kaman yanda kukaji abin nan kwatsam haka muma muka jishi kwatsam, dan Allah dudda dai babu abinda kaddarace bayasawa amman babu amfanin cewa wannan keda laifi ko wanchan keda laifi, munsan sunan diyarku yabaci haka shima nashi yabaci amman dan Allah kuyakuri, dan Allah abu baiyi dadi ba ko kadan” binsu Baba Gwaggo tayi da idanu daya bayan daya kowa jikinshi yay sanyi dan babu karya amaganan su bawai wanan ba dukansu sun kalli Abee baiyi kama da wanda zai aikata hakaba dan zai iya haifan Lujain dinma kuma itama tafadi abinda yakaita bayin tun kafinma suji bakin na mutanen nan, tsaf abinda tafadi shi suka gani a video, babu atom of lie aciki, kumama idan akace za’ayi blame yarsu ce taje bayin maza ita takai kafanta, this is just a common mistake da kowa can make ganin yanda sukai shiru babu wanda ya furta abu yasa cikin kumfan baki Gwaggo tace “ohhh barakuce komi ba”? Dasauri Baba yace “Gwaggo dan Allah kiyi shiru kitashi mutafi gida kawai”. ”mtswwwwww” Gwaggo taja wani mugun tsaki ta mike tsaye batai wata wata ba ta jaye gyalenta data lullube Lujain dashi idanunta sunyi jajir fuskanta yay jaaaa sabida kuka jikinta dabare da jirwajen drinks fuskanta har kyallin dankon drinks yake tana kuka sosai tana wani kalan ajiyan zuciya tarike jikin kayanta gam da hannayen ta data dunkule kowa yabita da kallo adakin banda Abee da kanshi ke kasa, duk wani mai imani da zuciya yakalli Lujain saiyaji jikinshi yay sanyi, Gwaggo na rike da gyalen ta taka zuwa gaban table din da Abee ke zaune cikin ihu tace “kawani sauke kai kasa kaman sabon ango kalli jikana nace, dago kanta ta kalleta” ahankali Abee yadaga kanshi yadan kalli Gwaggo sannan gently yakalli direction din datake nunamai gabanshi na faduwa sauke idanunshi dasukai jaa yayi kan Lujain dake kuka sosai idanunta akasa yay shiru danji yayi zuciyanshi tai wani iri, komawa Gwaggo tayi wajen Baba ganin yana kallon Lujain din datace ta fizge paper da aka bama Lujain amakaranta tadawo ta ijiye gaban Abee tace “kaga yanda akama jikata wanka da lemu tundaga ka har kafa banda haka makarantan suka bamu takarda waisun koreta sabida fasika ce mugun iri zata bata musu sauran dalibai” fashewa Gwaggo tayi da kuka sosai daidai nan ta durkushe awajen ahankali Abee yasauke kanshi ganin yanda tsohuwar da akalla zata girmi Hajiyanshi da yan shekaru na kuka sosai agabanshi, Baba da Abdulhadi ne sukazo wajen da saurinsu zasu dagata tace “wlh kuka tabani zan daga muku nono awajen nan ku kayaleni kawai” tai maganan tana tashi takalli Abee da kanshi ke kasa sannan takalli Musty tace “kaga yarinyar nan dakake gani haka marainiya ce uwarta na nakuda kanta haifeta ta mutu agurguje akai operation aka cirota sabida wai tasha ruwan cikin wanda yamutu yarinyan nan dakuke gani saida tai kusan shekaru biyu acikin kwalban asibiti ni ke biyan komi ubanta wannan din nan dakuka gani” tanuna Baba dashima yasauke kanshi kasa tace “shi baida kudin biyan kudin kwalba duba sha biyar duk ranan duniya acirota daga kwalban wai mutafi gida, likita kuma yace ana cirota baifi tai awa ashirin da hudu ba zata mutu, mijina babansu mai kudin kauye ne daya mutu inada gado kap na saida gidaje na manya manya a binni guda hudu da shanaye na kauye haka na biya dubu sha biyar biyar na shekara biyu cur kafin acirota, nine komi na diyar nan tundaga zama a asibiti, abincinta, kayan sawanta da rainonta da komi ma, koda aka bani ita haka muka dawo gida yau lafiya gobe ciwo ko shigowa bayayi yadubata dan yanada wasu yaran lafiyayyu marasa ciwo, nikuma na nunamai zan iyama jikata mai ciwo gata tamafisu jin dadin duniya, saida yarinyar nan takai shekaru bakwai aduniya tafara makaranta” Gwaggo tashare idanu dan hawayen sinki tsayawa tace “bakuga yanzu tana shatara a SS2 ba bayan su Samira suna shekaru sha shidda sun zana jarabawan kare sakadire, amman ita har yanzu bata gamaba sabida ciwo, ni nasan wahalan danayi akan jikata nasan gumi rashin bacci rashin sukuni danasha akanta, har yau har gobe tunda tazo duniya bantaba baccin dare bantashi ba saita tadani, yau awayi gari sunanta yabaci kuce nai shiru koda akace zata mutu ban hakura akanta ba yanzu ne da lafiyanta kalau zan hakura nai shiru akanta wlh wlh Billahillazi La’ilaha Illahuwa bazata yuba ko laifinta ne ko laifinshi ne nidai nasan bakuyi fasikanci ba dan bangani alamu a jikinta ranan ina tareda ita data dawo daga makarantan ai kaima bakai kama da Babba mai lalata yaraba dan haka idan kunason zaman lpy abu dayan zan gayamaka shine ka auri jikata! Ka auri dan baran iya da raina da lafiya na inaji ina gani sunan jikata yabaci ba, tun yanzu a makarantan su kadai an mata wanka haka da koro uwa wacce aka kamata dumu dumu tana zina, ahanamini yarinya fita titi gudun kar adinga nunata wlh baran yarda ba, hanya dayace shine ka auri jikata!”

 

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply