Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 18


Sakon So 18
Viral

Zaunarda ita Anty Binta tayi akan gado itada Amina sosai take kuka tana kwabe baki kaman yanda yara ke kuka Anty Binta dake kallonta da yanda takeyi kawai fadomata maganan mijinta yadingayi a zuciya she looks so cute, cute sosai yanda takeyi gashi yanda takeda kiba da yaran kumatunta keyi yayi soo adorable kaman kasaceta kagudu she looks kaman Yar baby Yar yarinya hakanan kawai taji Allah yasanya mata son yarinyar azuciya and idan Abee zaizo yasota she will be so soo happy wlh, zama Anty Binta tayi kusada ita tace “dan Allah ya isa hakanan Lujain kiyakuri” makema Anty Binta kafada tayi tana tabe baki cikin kuka tace “ni gidanmu zani wajen Gwaggo na” murmushi dukansu biyun sukayi Amina tace “to yanzu kidaina kuka kinga tunda babanki yayi fushi yanzu baraki iya komawa ba kibari gobe saimu maidaki gida” rage kukan tasomayi tana kallon Amina dake magana ahankali tace “da gaske zaku kaini wajen Gwaggo na gobe”? Gyadamata kai daga Amina har Anty Binta sukayi atare daidai su Sajida da Zainab na shigowa da kulolin abinci da tray na drinks suka bita da kallo kaman yanda itama ke kallonsu still hawaye nafita daga idanunta amman ba kuka takeba gashin idanunta sun jike sharkab, suna ijiyewa suka fita Anty Binta tace “zakici abinci? Ga abincin ki nan ankawo miki” murya chan kasa tanabin abincin da kallo tace “tea zansha da bread” tashi Anty Binta tayi tace “bari naje nakawo miki” daidai lokacin Sajida tashigo da flask da gwangwanin madara da Milo da chokali da karamin mug da bread Anty Binta tace “yauwa ga kayan tea nan bari nahada miki” karba tayi Sajida tawuce tafita Anty Binta nan da nan tahada mata tea akaramin cup tadaura akaramin tray takawo mata saman gado tabata karba tayi ahankali tana kallon fuskan Anty Binta saikuma takalli tea yanda yake tururi Anty Binta tace “oohh zafi bakishan tea tafashashe haka”? Gyadamata kai tayi ahankali hakan yasa Anty Binta tashiga juya tea ahankali take sauke ijiyan zuciyan kuka saida Anty Binta ta dandana tea jin zata iyasha yasa tamika mata karba tayi takai bakinta ta dandana jitayi yafi na Gwaggo dadi kaman bada milon da aka sabayi aka mata anan ba bread din Anty Binta ta dauka tana kokarin budewa taciro mata slice Lujain tamika mata cup din ahankali tace “Anty akaramin” daga Anty Binta har Amina kallonta sukayi ayanda kadai yarinyar take orobo Masha Allah sunsan bakaramin abinci takeci ba da murmushi Anty Binta tamata shima tasha tareda bread cup uku tasha na tea sannan tace takoshi yunkurin sauka tafara daga kan gadon har lokacin bata daina ijiyan zuciya na kuka ba Anty Binta tace “ina zaki”? Kaman zatai kuka tace “wanka zanyi kayan nan na cizona” wanan karan Amina saida dariya ya kufce mata Anty Binta kuma ta murmusa tace “to ga bathroom naki nan kije kiyi” gyadamusu kai tayi tawuce ciki duk suka bita da kallo suna kallon uban tulin gashinta kodan family su basuda gashine oho jitayi kaman ta deba ta sammata, tashi sukayi Amina ta tayata daukan flask din itakuma Anty Binta tadau cup da tray suka fitada shi suka rufo mata kofa, kowa har yashige dakinshi though bawai anyi bacci bane but babu wanda ke falo ijiye komi sukai a kitchen suka fito Hajiya suka gani tsaye gaban dakinta dake nan kasa tace “taci abincin kuwa”? Anty Binta tace “shayi kawai tasha Hajiya” kallon Amina Hajiya tayi tace “ke ina mijin naki” dariya tayi tace “wlh Hajiya ni baraki kadani natafi yauba kwana zanyi sai gobe zan koma” hararanta Hajiya tayi tace “ai shikenan, saida safenku” “saida safe Hajiya” har Hajiya tashiga daki saikuma tajuyo daidai sun zauna a falo zasu kunna kallo Hajiya tace “Binta” dasauri Binta tadaga kanta tace “naam Hajiya” cikeda damuwa tace “dan Allah kiduba mini Yar mutane kafin ku kwanta dan nasan Imrana ba dubata zaiyi ba” murmushi Anty Binta tayi tace “tom yanzu ma wanka tashiga Hajiya saisa muka dan zauna anan mubata wuri” gyadamusu kai tayi tawuce ciki dan ita bata jure hawa benen nan sabida kafafu saitafi wata bata haura sama ba.

Tadade tana kallon bayin komi daban da bayinsu dansu normal shower ne, kasa amfani da shower tayi, da kyar ta iya bude pampon shikuma ruwan sanyi ne aciki duk yanda zatai tayi takasa hakan yasa tabude wani sabon towel fari kal data gani abayin tadaura tafito tana tafiya ahankali tana kalle kalle dakin, bakin gadon taje tazauna ahankali dudda sunce zasu kaita gida gobe but hakanan taji wani sabon kuka yazomata data tuna auren da aka mata yasa take awan nan gidan dabatasan kowa ba, babu wani abu dake mata dadi aduniya, bata taba tunanin zatai aure yanzu ba ita dake ganin zabga zabgan yayunta agida basuyi aure ba, wai itane matan aure matan wani tayi kukan jin kanta na sarawa yasa ta tsagaita da kukan hakanan tareda jingina kanta da bangon gado wani kalan gyangyadi ne yafara dibanta har baccin yay nasaran kwasheta ahaka wuyanta ya bankare.

 

Ganin Shadaya har darabi yasa Anty Binta takashe kallon tace “zomuje mu duba Amarya saimu je mu kwanta” kashe wutan falon sukayi sukai sama, sallama sukayi jin shiru yasa Anty Binta tabude kofan ahankali zaune suka ganta daga ita sai towel babu dan kwali akanta wuyanta Ya karkace tana bacci awahale Amina tace “laaaaaa” gaban gadon Anty Amina tayi takira sunanta. “Lujain, Lujain” amman shiru dan ita tanada nauyin bacci idanba itane ta tashi ba saikai da gaske zaka iya tadata, Anty Binta tace “ko kayan bacci bata sakaba baccin ya kwasheta” Amina tace “gajiya ne da uban kukan datashi gyaramata kwanciyan kawai” gyaramata kwanciya Anty Binta tayi hakan yasa tasake sauke ijiyan zuciyan kuka Anty Binta tadan kalleta sanan taja bargo tarufa mata tareda rage gudun AC dakin sannan takashe wutan dakin sukaja mata kofa sannan suka wuce dakinka.

“Don’t forget cinta, shanta, lafiyanta, suturanta her well-being is now on you, not any of your family members ko Hajiya, I know you saisa nake fadin hakan, it doesn’t matter ko kanason auren ko bakaso anriga an daura, make sure ka kiyaye hakkokin that girl Imran, she’s in that house because of you, so kaji tsoron Allah and remember Allah na yafe kowani laifi banda hakkin wani bazanzo kafara this phase at the wrong foot her” dan gajeren tsaki yayi gama karanta messege din da Musty yatura mai ijiye wayan yayi yana kallon magungunan shi dake gabanshi kwashesu yayi yaja drawer yazuba su all this while baya sha yanzu ma bazai faraba duk maganin sa bacci hakan zai taimakamai da migraine but no kusan 12 yakai yana aiki a desktop nashi komi anatse yakeyi sannan ya kashe komi yamike yawuce gado kwanciya yayi tareda addu’a yaja bargo dudda bayajin bacci but he’s trying to fall asleep.

Wuraren 3:00 cikin bacci tace “Yunwaa” ahankali tasake cewa “yunwaaaa” jin shiru yasa dakarfi tace “Gwaggo yunwaaaaaa” jin yanda dakinta ya amsa maganan sabida yanda tai dakarfi yasa tabude idanunta rasss ganin duhu still adakin babu hasken torchlight na Gwaggo yasa ta tuna bata gidansu yau, gadon datake kai tashiga tattabawa hartakai karshen gadon bataji alamun mutum akaiba wani kalan mugun tsorone yasauka akan zuciyanta tunda ta taso tai wayau yaune rana na farko datake ganinta adaki ita kadai bata kwana da kowaba she’s always with Gwaggo ga ko’ina tsit babu ko minshari irin na Gwaggo dake fadi wani kalan tsinkewa zuciyanta yashigayi ko za’a kasheta batasan ina switch yakeba dazata danna taga haske ba balle kuma waya, tashi tayi lips dinta har rawa suke ta jingina da bangon gado tana kwalalo idanu tana bin ko’ina da kallo gani tayi kaman akwai wasu abubuwa da yawa kan carpet na dakin hakan yasa ta kara Gwalalo idanu ganin abubuwan na motsi suna kusada ita yasa tawani kwala uban ihu tsakar daren nan. “Wayyooo Gwaggooo, Gwaggo kizo akwai aljanu agidan nan wlh gasunan Gwaggo suna tahowa kusadani, wayyooo Allah na nashiga uku na bani, Aljanuuuu” tai maganan takai hannunta tadaura akan idanunta ganin kaman kwara daya yahayo kan gadon nan daidai nan aka bude kofar dakinta tareda kunna wutan dakin hakan yasa haske ya gauraye dakin, Abee ne tsaye gaban dakin sanye dawata faran jallabiya batare daya rufe boturan wuyanba da alamu da sauri yafito dan mana iya hango kwantaccen gashin kirjinshi, ganin yanda take ihu tana kiramusu Gwaggo kaman zata tadamusu da gida sama sabida ihu yasa yace “Ke!”

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply