Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 28


Sakon So 28
Viral

Wuraren magrib tabude kofanta tafito tana daure dawani pink towel a kirji rikeda Aneesarh datai bacci Kausar tagani dazata shiga dakinsu dasauri tace “inane dakinsu Aneesarh”? Kallonta Kausar tayi saikuma tamata pointing dakinsu Aneesa wucewa tayi tashiga Maman Aneesarh naciki tace “laaa tayi bacci” gyadamata kai tayi tana kallon wayan Maman Aneesarh dake kan gado, karban Aneesarh tayi ta kwantar da ita sannan ta tashi takalli Lujain dake kallon wayan tace “Ya akayi Lujain”? Ahankali tace “dan Allah na ari wayanki nakira Gwaggo na”? Dan murmushi tayi tace “to dauka kije ki kirata” wani kalan tsalle tayi cikeda farinciki tace “nagode Mom Aneesarh” daukan wayan tayi da gudu tafita tana saka number Gwaggo data haddace aciki tai dialing tabude kofan dakinta tashiga daidai wayan na ringing Gwaggo tadauka cikeda ihu yanda take waya tace “hello” dan murmushi Lujain tayi dayasa hawaye yataru akan idanunta murya chan kasa tace “Gwaggo” cikeda ihu Gwaggo tace “jama’a muryan Lulu nakeji”? Gyadamata kai Lujain tayi kaman jira take tawani kalan fashe da kuka itama Gwaggo fashewa tayi da kuka tace “wlh inda badan Babanki nina haifeshi ba da tuni na tsine mishi, tun Washegarin ranan da aka kaiki gidan miji naji ina baran iya rayuwa bakiba, ranan kasa bacci nayi nayi nayi da Babanki yakawoni gidanki yaki da asussuba kafin natashi yake fita baya kara dawowa sai dare bayan nai bacci, keto ya isa daina kukan hakanan kinji” gyadama Gwaggo kai tayi ahankali, murya chan kasa tace “Gwaggo dan Allah kizo kitafi dani gida” Gwaggo tace “namiki alkawari ko ana ha maza ha mata sainazo kafin satin nan yakare nadubaki kinji daina kukan kinashan maganin dana daddaka miki nasa miki a akwati”? Turobaki tayi ashagwabe tace “ni baram sha…..” daidai lokacin aka bude kofan dakin Abee ne yana tsaye sanye da kananun kaya riga da jean sun mishi wani kalan kyau sai kamshi yake ganinshi yasa dasauri tace “Gwaggo bye bye” takatse wayan dasauri tana zaro idanu, wani kalan kallo yamata tareda mikamata hannu alamun tabashi wayan, tashi tayi ahankali tazohar gabanshi sannan tabashi wayan yajuya yafita.

Koda akai magrib Abee zamanshi yayi a masallacin danjin ta’aleem da akeyi kan zamanta kewa da hakkoki mutane, saida aka gama tass malam yabada daman tambaya daga baya wani yadaga hannu hakan yasa Malam yace “yi tambayanka” dan sosa gemunshi yayi sannan yakalli Malam yace “Malam ni sonake nasan hukuncin tsofaffin dake auremana yammatan mu” duka jama’an masallacin juyowa sukayi suna kallonshi yahade rai banda Abee dake duba littafin hannunshi, Malam dake kallonshi yace “ban gane tambayanka ba yan samari” dan yatsine fuska Mandawari yayi yace “yanzu saikaga tsofaffi misali irinku malam na auren mata dakun haifesu kusan sau biyar mukuma yara mekukeso mu aura me atambayata dabaka ganeba”? Sai alokacin Abee yadago kanshi dan tambayan sounds so disrespectful to Malam dan Malam ba karamin mutum bane, shima Mandawari kyar idanunshi akan Abee, yanda yake kallon Abee yasa Abee ya gyara idanunshi akanshi, gyaran murya da Malam yayi a speaker yasa Mandawari ya janye idanunshi dagakan Abee dake kallonshi kyar yakalli Malam, Malam yace “shidai aure na farko Halas ne yan samari, dudda dai bansan mesa kayi irin wannan tambayan ba dan ba darasin mukeba amman dai abinda nasani shine wacce baraka iya aura ba aduniyan nan shine wacce take muharamman ka, idan kuma ana maganan Auren yara ne annabin mu Annabin Tsira Muhammad tsarki yatabba agareshi ya auri Yar yarinya Aisha kuma mu koyi mukedashi, jama’a atashi sahu” tashi sukayi akai salla ana idarwa Abee yafito dan yanada business meeting dazaiyi a zoom by 9, harya zo zaishige gida yaji ance “Yallabai” chak Abee ya tsaya saikuma yajuyo ahankali, Mandawari ne yataho tareda Olusay dayay hanyar gate nasu, jallabiya ce ajikinshi yakaraso gaban Abee hannu yamikamai yace “kasanni”? Wani kalan kallo Abee yamai tsaf yaganeshi from the first glance dayamai a mosque, hannu Abee yakawo zai bashi kaman jira Mandawari yake with so much disrespect and humiliation yajanye hannunshi yarugume hannunshi a kirji, hannunshi Abee yakalla daya kaimai su gaisa dake nan acikin thing air ahankali yaja hannunshi ya maida jikinshi yazubama Mandawari idanu, baisan mesaba jiyayi gabanshi yafadi amman daurewa yayi with so much courage yace “you took something that belongs to me Mr Imran, kuma na tabbata fada da kananun yara irinmu dazaka iya yara damu is not ur thing dan haka I come to tell you in peace ka saki babe dina daka daura lokacin da abin nan yasameku I wasn’t in Nigeria yanzu nadawo I want my woman back I want to marry her” wani kalan kallo Abee yamai saikuma yay folding hannunshi akirji yana kallonshi, Mandawari yace “yanzu ma nasameka ne namaka magana out of respect inba hakaba” anatse Abee yace “mezakayi”? Kallonshi Mandawari yayi yace “I will defame you! I will scatter everything you’ve ever stood for” dan murmushi Abee yayi iya lips nashi sannan yajuya yawuce anatse wani abu Mandawari yaji ya tsayamai awuya kaman yabishi ya chakamai wuka sai yanzu daya tsaya gaban Abee face to face kawai yaji yawani tsaneshi wani kalan mugun kishi nacinshi dan ko kadan mutumin doesn’t look old gashi he’s so handsome gashi so neat kayan dayake jikinshi tundaga kan slippers na kafanshi are designers, kamshin dayake koshi dayake takama yafi kowa using turare baikai Abee kamshi ba, wani kalan dunkule hannu yayi yadaki iska sannan yajuya yawuce gida, akan benci mai gadi yasami Olusay zaune Olusay na ganinshi yamike tsaye yace “Man nasanka to be stubborn tun muna yara, but idan kasan kazo anguwan nan ne to make trouble ni zan tattara nabarmaka gidanka, this man baida any business to do with you and yet you want to make trouble dashi akan mene ubanme yamaka eh” cikeda ihu Mandawari na tafarfasa yace “he stole my woman from me abinda Yamin kenan” cikin sauri Olusay yace “woman din dabaka taba cema kanaso ba or respond to her messages, this is not good Man, trust me this is not good at all” hannu Olusay yakai zai tabashi wani kalan bugemai hannu yayi yawuce ciki yana tafarfasa tsayawa Olusay yayi so worried Kodai yakira Mom yafada mata abinda ke faruwa ne amman yay haka Man will never forgive him, shi yasan Man always view her message dan shinema yafadamai about Lujain amman baitaba fadamai yana sonta ba saima wulakanci dakin kula yarinyar, saida wannan sex tape da news na aurenta ya yada social media shine fa tundaga ranan Mandawari yafara having sleepless night.
***

Falonsu yashiga da sallama chan kasa Musty yagani da Harun sunacin tuwo, Hajiya kadai yagaida yamusu mugun kallo yawuce sama, Hajiya tace “kudai kuna kokari da wannan abokin naku” tashi Musty yayi yace “cigaba daci Harun bari najawoshi ya sauko kasa” daidai Abee na zama gaban desk nashi Musty nashigowa ciki yace “waikai tunda kayi auren nan nakasa gane kanka” wani mugun kallo Abee yamai yace “I told you Musty, kasanni Musty banson aure let’s not even go there idan wata ne maybe I can even manage Auren na zauna not Auren little girl like this da dan karamin yaron saurayinta zai tareni this night yana threatening dina, what is all this rubbish what kind of mess kuka sani ciki haaa? At this stage some stupid small boy da aka haifa jiya jiya zaizo yatareni yanamin maganan banza can you imagine”? Yanda Abee ke magana zakasan he’s really pissed hakan yasa Musty yace “wait Imran I don’t understand me kake cewa? Waya tareka wani boyfriend kake magana”? Cikin dan ihu kadan Abee yace “her boyfriend dashine the reason behind abinda yasa taje toilet na maza mana taxauna tana kallon live video nashi Muhammad Mandawari” shiru Musty yayi yana kallon Abee dan shi dama dayashigo anguwan dazu Hamza ke fadamai sunyi neighbor wani footballer baima tsaya jin waye ba sabida Hajiya daketa kwalamai kira, one thing da Abee ya tsana to the core arayuwanshi is raini ya tsani raini da rashin kunya, dafe kanshi yayi saikuma yadago yace “how far about the tracking dasu Abdul keyi idan bazamu iyaba zan turama contact dina number a USA cus I can’t wait for all of this shit to be over narabu da yarinyar nan data shigo rayuwana tahanani kwanciyan hankali I am tired Musty I am tireddd” yay maganan yana kabar da keys na motanshi da wayanshi dake kan desk din kasa, dasauri Musty yazo yadafashi trying to calm him down yace “calm down Imran, fushinka is not good for you and kowa dake tareda kai, calm down please” dan ajiyan zuciya Abee yasauke ahankali Musty yace “what happen tell me” kaman Abee bazaiyi magana ba saikuma yafadamai komi shima Musty baci ranshi yayi yace “I don’t care koshi waye what gave him the gut dazai tare soja yanamai magana anyhow, lemme go and lock him up wlh sainai uselessing kafafuwan nan nashi na kwallo ” Musty yazo zai wuce dasauri Abee yarikeshi yace “common mu yarane dazamu biye musu, he’s just a child let him be please, is not easy karasa abinda kake so cikin dare daya to some extend I understand how bittered he’s” dasauri Musty yace “her grandmother told me baitaba kulata ba all this childish crush Lujain kemai” yatsine fuska Abee yayi yace “that’s non of my business, I’ve taken care of her, nasata a school da babu wanda zai bully nata, nayi securing waec nata and neco I am just waiting waiting for the whole thing to be over nagaji” yay maganan ahankali, murmushi Musty yamai yace “ya isa tashi muje falo muci tuwo tare” yatsine fuska Abee yayi yace “baran ci ba” Musty yace “Allah saikaci” badan yasoba yatashi yabishi suka fita falo tare, sai wajajen 11 sukabar gidan hakan yasa yarufe ko’ina yawuce sama ko dakin da Lujain keciki bai kalla ba.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply