Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 29


Sakon So 29
Viral

 

Around 1 tafarka daga bacci sabida mugun yunwan datakeji rabonta dacin abinci tun lunch dataci a school shima ba sosai ba taci, yanda Mandawari yagaya mata tacika kiba taje tarage kiba kafin takulashi yadameta tayi alkawarin zata rage kiba, barata dingacin abinci sosai ba, kulolin abincin da aka kawomata jiya da daddare takalla amman taki zuwa wajen, kife cikinta tayi ahankali tanajin yanda cikin ke sokanta amman tadaure tana lumshe idanu, ganin yaki denawa yasa ta tashi tadauki bottle water tabude tasha sosai sannan takara kwanciya tana shafa cikinta da hannunta dake cizonta cikin wani kalan murya tace “wayyooo cikina wauyooo” juyi kawai take akan gado sai wajajen 3:00 bacci yay awon gaba da ita, 4:30 Abee yafito, tada kowa yayi saida yatada Kausar yace “jeki tashi yarinyar nan” gyadamai kai Kausar tayi tawuce tafita shima Abee yafita yasauka kasa.

Bude kofan dakinta Kausar tayi takarasa gaban gadon tana mamakin yanda koda yaushe tana daure da towel bubbuga gadon tayi hakan yasa tabude idanunta ahankali Kausar dake kallonta tace “Abee yace kitashi kiyi salla” tashi tayi ahankali ta zauna itakuma Kausar tawuce tafita daga dakin, mikewa tayi ahankali tashiga bayi wanka tayo tafito tai salla sannan ta tashi tashiga saka kaya tana tunanin yau jumma’a zata huta, kayan makarantan ta tasaka batare datasa safa ko hulaba tafito sai kamshin turarukan data fesa take masu bala’in dadi, gaban dakin Kausar taje tadade tsaye sannan tabude kofan ahankali tashiga ciki Kausar dake saka dogon Riga tajuyo dasauri takalleta ta tace “mehaka kika shigo mini daki” girgiza matakai Lujain tayi saikuma ta taho cikin dakin zuwa gabanta ahankali tace “mesa kika tsaneni baki sona”? Tai maganan tana kallon fuskan Kausar hararanta Kausar tayi takarasa saka riganta tajuya tadauki dan kunne tasa ahankali Lujain tace “eh mesa” juyowa Kausar tayi dasauri tace “kinason ki sani, to sabida ke sunan Babana Abee yabaci aduniya, because of you mahaifina is suffering, bayan komi laifinki ne, kene kikazo kampanin shi amman ba’a duba hakaba sannan aka kuma kakabamai Auren ki akanshi sabida mugunta irin naku da yan gidan ku” hawaye ne yazubo daga idanun Lujain dasauri tasa hannunta ta goge takalli Kausar tace “kinsan mesa naketa son miki magana sabida ke kadai nagani agidan nan datake nan kaman matsayin yayyuna su Ya Samira, kin dauka I am happy with all this ne, kaman zan mutu nakeji, nima nagaji nagaji dakomi” saikuma tafashe da kuka wani iri Kausar taji dan tanada bala’in tausayi dauke kanta tayi tace “nidai me kikazo mini adaki mekikeso” hannunta Lujain tasa tashare hawayen fuskanta tass tace “sonake kiduba min recipes na rage kiba awayanki kibani narubuta inaso narage kiba ne” dan kallonta Kausar tayi ganin yanda take kallonta yasa Kausar tace “kiba halitta ce, haka Allah ya yiki maisa kikeson wahalar da kanki”? Girgiza kai tayi tace “nidai dan Allah kidubamini inda inada waya bazanma zo wajenki ba” bala’in tausayi tabama Kausar wayanta tadauka tashiga google tamata browsing sannan tabata wayan da memo da byro tace “write it down” zama tayi abakin gadonta tashiga kwafewa da saurinta Kausar duk tana shiryawa tana kallonta komesa takeson rage kiba oho kuma kiban yamata kyau sosai da chubby kumatunta yanzu idan tarage kiba tai muni fa oho itadai baruwanta, gama rubutawa tayi tamike tsaye tana ijiyemata wayan akan gado tai murmushi sosai dayasa Kausar ta tsareta da idanu sabida yanda dimples dinta ke lotsawa tace “thank you Kausar” sannan tawuce tafita, dakinta takoma tadauko jakanta da hijab tashiga saukowa lokacin babu kowa a falo jakan ta ijiye akan kujera sannan takalli kitchen dinsu datagani abude tawuce tashiga ciki Anty Binta datagani tsaye tana aiki yasa tai murmushi tabi kitchen din da kallo ganin yanda tahadu tace “good morning” murmushi Arty Binta tayi tace “kin tashi lpy Lujain mekikazo yi a kitchen”? Dasauri tai wajen Anty Binta paper tanuna mata tace “weight loss smoothie zan hada” kallonta Anty Binta tayi tace “kewayace miki kirage kiba so kike Gwaggon ki taganki tace bamu baki abinci” murmushi tayi batace komiba Anty Binta tace “ai shikenan fruits duka na fridge ga blender anan” dasauri tai fridge, celery tadauko, da green apple, cucumber dakuma ginger tahada tai blending Anty Binta sai kallonta take one thing datagani is tanada tsafta kaganta zaka dauka bata iya komiba amman ta iya danta yayyanka abinta tasa a blender ta blending Anty Binta dakanta tabata bottle mai kyau da straw tajuye aciki tace “Allah bada sa’a nidai banga me zaki rage ba” dan turo baki tayi tace “flat tummy da fats” dan hararanta Anty Binta tayi tai murmushi takai bittle na baki tazuko tasha taba tabe baki ko kadan baimata dadi ba amman sabida yanda takeso ta burge Mandawari rufe ido tayi ta shanye tass sannan tawanke giran da blender dasauran kwanukan wajen Anty Binta tace “debi chips naki kije dinning kici” girgiza mata kai tayi tace “a’a ni nakoshi” wani kalan kallo Anty Binta tamata tace “Lujain what’s all this kaman wacce tai wani mafarkin abu yunwa kikeso kifara hora kanki dashi sokike naje nafadama Ya Imran abinda kikeyi”? Dasauri Lujain ta girgiza kai tace “to zanci Anty please karki fadama kowa” tai maganan tana daukan plate chips kadan tadeba tasa kwai ma kadan kaman ba Lujain ba Anty Binta tace “tea fa” girgizamata kai tayi tace “idan nadawo shi zan sha” a kitchen din tazauna kan kujera taci abincin tass sannan tawanke plate ta taya Anty Binta kwaso kula tafito dasu falo Hajiya sai murmushi take tana samata albarka afalo duk akaci abinci banda Abee dabai dawobama yana gym dinshi ita tana kitchen wajen Anty Binta, Kausar ne tashigo kitchen din tace “Uncle Hamza yace kizo mutafi yau shizai kaiki school” wanke hannunta tayi tace “Bye Anty” bye Anty Binta tamata tana murmushi sanan tawuce tafita zama afalo tayi tasa safa da takalmin makaranta sannan tasaka hijab tagoya jakanta tafita itada Kausar dake daddanna wayanta motan Uncle Hamza suka shiga, motar mai kyau benz amman ba tinted bace, murmushi yama Lujain yace “Amaryan Ya Imran” sauke kanta tayi kasa bata sake cewa komiba suka fito, tsaye taga Mandawari a kofar gidanshi yauma yana sanye da wani rigan jearsay da gajeren wando, hada idanu sukayi ga mamakinta wani dan karamin murmushi yasakin mata batasan lokacin dataji wani farin ciki ya lullubeta ba, hannu yadaga mata alamun bye bakaramin mamaki tayi ba noke kanta tayi batare datamai bye ba, ita suka fara ijiyewa a school sannan yawuce yatafi da Kausar school.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply