Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 32


Sakon So 32
Viral

Fita yayi daga dakin yawuce gym dinshi dake compound din dayake all kayanshi na workout na wajen saisa baimaje sama dan chanza suit na jikinshi ba.

Kallon Binta datai zamanta anan kusada Hajiya tayi tace “tashi kije ki kiramini yarinyar nan munaji muna gani barinta zamuyi ta kashe kanta” tashi Anty Binta tayi ahankali tawuce sama tun kafin takai wajen dakinta taga kulan abincin agaban kofanta tsugunnawa Anty Binta tayi tabude kulan ganin kotaba abincin batayi ba yasa ta murza kofan zata bude taji kofan arufe ita abinma dariya yabata tace “ohhh sabida kada asakici abinci shine kika rufe kofan ko, to Hajiya na kiranki” tashi Lujain tayi ahankali tana rike cikinta tawuce bayi dan batamaso tanajin maganan Anty Binta, maida kofan bayin tayi tarufe ta tsugunna awajen ita kanta mamaki take mahaukacin yunwa takeji bana wasaba tunda uwarta ta haifeta bata tabajin yunwa irin wanda takeji yau din nan ba, amman ita wlh saita daina cin abinci sabida ta rame Mandawari yakara sonta sosai.

Anty tadade tsaye awajen ganin taki bude kofan yasa tajuya takoma kasa Hajiya tace “ina take”? Ganin yanda Hajiya ta damu yasa tace “Hajiya karki damu zataci abincin yanzun nan” cikeda damuwa Hajiya tace “dan Allah Binta koma wajenta ki tabbata taci, hankalina bazai taba kwanciya ba ace yarinya na wajena takicin abinci awani dalili ita ba azumi ba sai bama kai yunwa, yooo ita kibar har guda nawa ke gareta bandama shirme irin na yarintar Lujain, kiba kyau ne azamanin mu idan kinada kiba ba kowani kalan mutun nema zaizo neman aurenki ba sai masu kudi sabida ansan Kinacin abinci mai kyau gidanku babu yunwa ke Yar gata ce, azamaninmu da zaran an ganki mara kiba ramammiya cewa ake gidanku da yunwa baku samun abinci kuci, ni wannan zamanin nema naga gayu ake da siranta kiga yarinya kaman zaka hure da iskan bakinka tafadi wai shine gayu, to wlh bada niba, ni baran miki karyaba Binta ranan da mahaifin Lujain yakawota nan gidan da daddare dana fara daura idanuna akanta abinda nafara cewa shine Masha Allahu yarinya bulbul da ita son kowa kin wanda yarasa akan mene takeson bata kanta, ita batasan rama bazai mata kyau ba, sotake iyayenta suganta ace bamu bata abinci yarsu dukta tsotse jesama idan bataci abinci ba kizo kifadamin dan saina saba mata daga ita har Imran da akacemai taki cin abinci yakama hanya yay gaba abinshi” ganin yanda Hajiya tabata rai yasa Anty Binta tace “a’a Hajiya ai baimakai hakaba zataci ma bari naje” Hajiya tace “kada mata shayi ki tafin mata dashi” kitchen Anty Binta tawuce tahada mata tea a babban flask tadauko a tray da cup tawuce sama gaban dakinta taje ajiye tray tayi akasa tai knocking tareda murza kofan amman har lokacin a kulle at this point Anty Binta jitayi itama ta damu sosai, bubbuga kofan tayi hakan yasa Maman Aneesarh dake daki tafito tace “Ya Binta lafiya” dan murmushi Anty Binta tayi da idanu tamata alamu data koma daki kar Hajiya taji hakan yasa takoma daki itakuma Anty Binta tawuce dakinta dan dauko waya dauka tayi tafito Hajiya dake kasa tace “taci kuwa”? Dasauri tace “eh Hajiya taci” gaban dakin Lujain taje takira number Ya Imran dan shine spare keys ke hannunshi amman har wayan ya katse bai daga ba kusan 3 miss calls tamai bai dagaba sake fitowa Maman Aneesarh tayi jin yanda Anty Binta ke knocking kofarta tazo har wajen tace “Anty Binta wai menene”? Abincin dake gaban dakin tanuna mata tace “Lujain refuse to eat she wants to loose weight kuma yunwa takeji kaman ba gobe” kallon abincin Maman Aneesarh tayi tace “harwani kiban dazata rage takedashi tanadai so tama kanta wani illan kin fadama Ya Imran” cikeda damuwa Anty Binta tace “kema kin sanshi ko kulamu baiyiba danake gayamusu” Kausar da tun dazu tadawo daga school tana bacci bude kofa tayi tafito daga bakin kofa ta tsaya tace “ni wlh dukkan hanani bacci, ku barta mana Anty Binta maybe cikin nan nata yakoma flat kaman nawa” tai maganan tana dariya dakuwa daga Anty Binta har Maman Aneesarh suka mata daidainan Abee yashigo saman kallo yabisu dashi daki Kausar tawuce dasauri Dan babu hula akanta tace “welcome Abee” wani kallo yama Maman Aneesarh da Anty Binta strictly yace “I don’t wanna see any one of you anan” sadaf sadaf kowa yawuce Abee yace “it’s time for magrib” duk dakunan su suka shiga, yace “Fateema” dasauri Anty Binta tafito tadawo har gabanshi anatse tace “na’am Yaya” strictly yace “call your husband kiwuce kitafi gidanki” dan murmushi tayi tace “to Ya Imran” wucewa yayi yashige dakinshi batare daya kalli kofar dakin Lujain ba, wanka yayi yafito ya shirya cikin wasu fararen shadda riga da wando dayawani kalan haskashi yasaka, Wandon as usual iya idon sahu rigan kuma jumper babu aiki ajiki hannun rigan yakamashi hakan yanuna murdaden hannunshi irin full nan dinnan turare ya feffesa jin an tada salla yasa yasaka slippers yafito dasauri yasauka kasa a compound yaga Hamza da Abdallah na alwala shigowansu kenan wucesu yayi yawuce yafita suma suka biyoshi abaya, sai bayan isha’i yafito daga masallacin yana tafiya ahankali Mandawari dake tsaye gaban gidanshi tunda Abee yafito daga masallaci yake kallonshi tunda yake in his life baitaba ganin mutumin da he feels so insecure about ba kaman Abee, tundaga kai har kafa yake binshi da kallo yakasa ganin makusa, gashin kanshi dana gemunshi baki sidik shida yake yaro shine ma yakeda yan furfura akai, tundaga nan kofar gidanshi yana iyajin hadadden kamshin da Abee keyi, hada idanu sukai da Abee daya kalleshi sau daya ya daukekai dasauri shima yadauke kai yana tsaki yace zaiga kaman na damu dashine, kaman daga sama yaji muryan Olusay yace “are you scared kar babe dinka tafara son mijinta danni wlh mutumin nan yafi mini kai kyau sau dubu, just look at a matured classic cool guy dan Allah ga naira, kai kaga shaddan jikinshi kakosan shaddan Oman ne wannan special edition din nan just guda 10 ne aduniya gabaki daya nidakai ba munje siya ba but bamu samuba thats what he is wearing, Mandawari a word of advice this guy no even send you so back off” dawani kalan sauri Mandawari yajuyo azuciye chakumeshi yayi hakan yasa Olusay yadaga hannuwanshi sama alamun yay surrender sannan yamai alamu da idanu kan ana kallonsu masu fitowa daga mosque sakinshi yayi yawuce cikin gidanshi yashige fuuuuu.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply