Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 42


Sakon So 42
Viral

EPISODE 4️⃣2️⃣
Wuraren 2 suka fito daga saloon din an gyaramata gashinta anyi stretching anyi parking sai kanshi yake an gyaramata kumbunanta, kallonta Anty Binta tayi tace “kin iyashan Popsicle”? Gyadamata kai tayi dasauri tace “eh” murmushi Anty Binta tayi tace “sweet tooth, muje nasaya miki” wani shago suka shiga tasaya mata sannan tasayama su Kausar sannan suka fito suka shiga mota suka dawo gida kusan tare itada Musty suka iso gidan parking yayi yafito daidai itama tafito haka Lujain murmushi yayi ganin Lujain yace “wifey ina kika kaima Imran mata”? Dan dariya Anty Binta tayi tace “saloon nakaita kitsonta duksun warware shine mukaje aka kawance kan gabadaya aka gyara” murmushi yayi ahankali Lujain da adan kunyace ta lallai tana sunnar dakai tace “ina yini” murmushi yayi yana kallonta yace “lafiya lau Lujain je daki zan magana da Anty taki gatanan zuwa” gyadamai kai tayi tawuce yakalli Anty Binta yamata alamu data shigo cikin mota shigowa tayi shima yashiga tace “Husby wai ina kaje I mean mekaje yu da Doctor Ya Imran”? Dan shiru yayi yace “Dr is the only person that can help us at this point yadawo kaman family” yayi dan shiru saikuma yasa hannunshi acikin aljihun gaban riganshi yaciro wani tablet kwaya daya rak yabama Anty Binta kallon kwayan maganin tayi tace “what is this”? Dan shiru Musty yayi ahankali yace “ke kanwar Imran ne bai kamata ina fadamiki sirrin yayanki ba but you are the only help danake dashi” shiru yakarayi ahankali yace “Wifey inaso Imran ya sad…..” saikuma yadanyi shiru kafin ahankali yace “I want Imran yay consummating aurenshi da Lujain!” Dawani kalan sauri Anty Binta ta kalleshi gyadamata kai yayi yace “that’s the only way dazamu iya saving this marriage inhar abu ya shiga tsakaninsu nasan bazai taba sakinta ba” yay dan shiru saikuma ahankali yace “after dogon explanation da magana Dr shi yabani wannan kwayan maganin daya tal dakike gani shima yace aure will help Imran sosai he needs a woman, he’s a full grown up middle age healthy man yana neman 14yrs ba mace kenan karyazo ya haukace” cikeda dan tsoro Anty Binta tace “to mene maganin zai sashi”? Ahankali Musty yace “I don’t know wlh exactly but nasan dai zai tadamai da sha’awa ne dabazai iya bearing ba baya neman matan banza dan haka dole yaje wajen matanshi ta sunna this is just my saying oo Dr bai fadamin takamaimen abinda maganin yake ba, but yace to avoid kar Imrana ya zargi kowa abashi maganin around 7 dan 3hrs maganin yake dauka kafin yay taking effects, kinga around magrib zaki samai a shayi dazai sha anan falo ko” gyadamai kai Anty Binta tayi saikuma tace “yaya zamuyi da mutanen gidanmu Lujain is v……..” saikuma takasa karasa maganan, dasauri Musty yace “shima is under my control duka yaran gidan nan kap hatta Maman Aneesarh kwasansu zamuyi zance zan kaisu cinema, Hajiya kadai za’a bari agidan akasa, around 9 zamu tafi idan yaso dagachan zan ce musu yau kowa agidana zai kwana dama duk basu zo sabon gidanmu ba cus banson situation dazasusan something happen tsakanin Imran da Lujain” dasauri Anty Binta ta gyadamai kai zuciyanta na bugawa hannunta yarike yace “we got this babe, I am helping my best friend and you are helping your brother, we are saving the most stubborn man dana sani aduniyan nan” atare dukansu sukai murmushi, ahankali Anty Binta tace “I wish I can have a friend like you Husby” murmushi yayi yace “I am nothing wlh wish to have a friend like your brother Imran not me” murmushi tayi tashige jikinsu tace “Allah yabamu lada and May this plan be successful” murya chan kasa yace “Ameen baby hold this magani well nasan anything 4 ko 5 zai dawo gida I will be with him har dakinshi baran bari yay any rubutu ba balle yamata saki zamuje magrib bazan bari yazauna ba zamu dawo da sumin cin abinci that’s when you will bring the tea a two cups kibashi mai magani kibani empty mara magani” gyadamai kai tayi ahankali yace “sauka muje ciki namusu announcing cinema thing din fa ticket din nan tayani kwasa agaba” kwashe ticket din tayi suka fito suna shiga falo kowa na falo banda Lujain dataje sama Musty yace “tantadaaaaa yau munada all family movie night, Ibro tell ur wife to get ready around 8:30 9 zamu tafi dukanmu Hajiya ne kawai bazataje ba nasani” hannu Hajiya tadaga tace “aikam inani ina zuwa wani kallo da idanun nan danake fama dasu” dariya akayi Kausar tace “Second Dad thank u wlh dama mun dade ba’a fita damu ba” Anty Binta tace “theater gabaki daya ya karba mana sai ashirya” sosai sukaji dadin zancen da rabon dasuyi having fun haka tun kafin kaddaran da yafada kan babansu, zama Musty yayi yace “kubani abinci wlh yunwa nikeji Hajiya”, Hajiya tace “Binta bama mijinki abinci”.

 

Wuraren 5 Abee yashigo gidan parking yayi yabude kofa yafito he’s so happy yau jinshi yake sakat abinda ke kanshi ya sauka maida kofan yayi yarufe yawuce ciki, afalo yasami kowa yakalli Abdallah ya wurgamai car key yace “jeka kawo abubuwan cikin mota is for you guys” gaidashi kowa yayi da kai ya amsa ya gaida Hajiya sannan yawuce sama binshi Musty yayi dasauri yana shiga cikin dakinshi shima Musty na binshi ciki yace “Ya Meeting din”? “Fine” ya amsa yana shiga cikin closet saikuma yafito yawuce cikin bathroom kwanciya kan gadonshi Musty yayi yana daddanna waya yadade cikin bathroom sannan yafito bayan yayi wanka daure da bathrobe yawuce closet nashi nan ma yadade ciki shiryawa yayi cikin jean black dawata maroon t-shirt sai kamshi yake zubawa yay wani kalan kyau dake shiga ido, Musty yanunamai abincin da aka kawo a tray yatsine fuska yayi yace “I will eat later” Musty yace “waikai me abinci yama I am sure tun safe bakaci komiba” hararanshi yayi yakalli agogon bango yace “tashi muje mosque” tashi Musty yayi suka fice tare ana magrib Musty yatasashi agaba suka dawo gida afalo suka zauna Anty Binta tawuce kitchen maida kofan kitchen din tayi tarufe tazuba musu shayi a cup sannan ta balle maganin tajefa a cup na Abee nan da nan maganin ya narke cokali tasa takara juyawa sannan tasa a tray tadauki tray tafito tana tafiya ahankali Gaban Abee taje tadauki cup nashi tadauramai akaramin coffee table dake gefenshi tace “Ya Imran ga shayin ka” murya chan kasa yace “thanks” sannan tawuce gaban Musty ta ijiyemai nashi cup din a coffee table dake gabanshi sannan tawuce tace “bari muje mu shirya” gyadamata kai yayi, Hajiya tace “kaji wai cinema zasuje Imrana, Mustafa da asaran kudi hall gabaki daya ya kama musu” dan dariya Musty yayi yace “Hajiya inada wasu kannai ko yara sama dasu ne, ba asaran kudi bane let them go out today and have fun” tabe baki Abee yayi yadauki tea shi yakai baki batare daya sa bakinshi a zancen ba, tass ya shanye tea Kausar tasauko sanye dawata doguwan Riga na abaya black tai kyau tazo gaban Abee tace “Abee kayan nan sunyi” kallonta Abee yayi ahankali yace “yes” murmushi tayi tajuya takoma sama daidai ana kiran isha’i tashi Abee yayi lokacin Ibraheem yashigo gidan shima ya shirya tsaf da matanshi da yaranshi biyu akunyace matanshi ta gaida Abee da katon cikinta haihuwa yau ko gobe amsawa yayi batare daya kalleta ba yamikama yaran hannu alamun sallama sakamai hannun sukayi sukace “Abeeeee” tareda rungumeshi daukansu yayi tareda dan murmushi yace “how are you”? Dasauri Babban Muhammad yace “Abee the coco pops u bought for us has finished” gyadamusu kai yayi yace “okay” karamin yace “Abee second Dad is taking us to cinema will you go with us too”? Girgiza musu kai yayi anatse yace “Abee has some work but I promise to go next time” murmushi yaran sukayi sukace “okay” murmushi kowa na falon yayi harda Hajiya Musty aranshi yace “I can’t wait Lujain ta haifomaka little baby Kausar tai kanwa ko kani” kaman Abee yaji abinda yace kallonshi yayi suka hada ido ya sauke yaran kasa dan suje wajen Hajiya yace “let’s go” ficewa sukayi dukansu harda su Abdallah da Hamza dasuka shirya suma duk sunyi kyau.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply