Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 8


Sakon So 8
Viral

Baki gayen dake video yakama daga waje yana kallon yanda kofan ke jijjiga kaman ana wani abu jin muryan yarinyan na nishi, jin mutane na zuwa wajen dasauri yaciro wayanshi daga cikin bayin yawuce abinshi yana maida wayan aljihu yama ma’aikatan dazasu wuce maganan yace “sannun ku” yawuce suka wuce corridor abinsu yalabe wani lungu dan yaga fitowarsu.

 

Ganin yanda take ihu ta kulle idanunta gam da bakinta gashi takare kofan gabaki dayanta da kibanta balle yama fice abinshi yasa cikeda daka tsawa yace “Ke!” Har cikin kwakwalwanta taji tsawan daya daka mata hakan yasa tarufe bakinta gum sannan tafara bude idanunta kadan kadan ta makale jikin kofan kaman zata manne awajen zuciyanta na bugu ba kakkautawa tasauke idanunta ahankali kan fuskan Abee, ganin yanda tayi kaman tana shirin sakin fitsari yasa yace “open the door kifita” bakinta har rawa yake sosai danta bala’in tsorace tace “ban…….ban…..iy……iyaba” ganin dukta tsorace kawai ta manne kyam akofan yasa anatse yace “step away” gyadamai kai tayi sannan tamatsa ahankali bude kofan yayi fuska adaure batare daya kalli fuskanta ba yace “out” da bala’in sauri tafice daga bayin jakanta da chocholate da wayanta dake kife akasan bayin yakalla hartasa hannu zata bude kofan bayin tafita yasake dakamata tsawa yace “kee!” Juyowa tayi azabure suna hada ido tasauke idanunta kasa jikinta yadauki bari takasa koda daga kafa tai tafiya ball yayi da jakanta daga cikin bayin tareda wayan duka ko ajikinshi dasauri ta tsugunna tadauki jakan tadauki wayan ta jefa cikin jakan ta mike batamasan halin da wayan keciki ba kawai jikinta bari yake fitowa tayi tana waige waige bama tasan ta ina tabiyo tazo wajen ba sai gyara riganta take tafara tafiya tafita daga corridor hanyan bayin wasu ma’aikata ne su biyu mace da namiji suka ganta sukace “what are you doing here student”? Tsuri tayi bamatasan mezatace ba macen dake kallonta tai dariya tace “hala ta bace ne, come” kaman jira take dasauri tai wajen macen murmushi tamata ganin duk ta tsorace tace “don’t be scared kowa da kikagani awajen nan ranan farkon zuwanshi saiya bace acikin company nan, just take that stairs zai kaiki direct kasa though naga Mr Hamza na shirin tafiya daku Factory” Gyadamata kai tayi zata wuce matan tace “what’s your name”? Juyowa Lujain tayi takalleta saikuma tanuna kanta ahankali tace “ni”? Gyadamata kai tayi ahankali tace “Lujain” murmushi matan tace “you have a very very beautiful eyes” Gyadamata kai tayi tajuya da sauri sauri tai stairs mutumin yace “kedai Kiyawa kinada son mutane” murmushi tayi tace “she just reminded me of myself danake yarinya haka nataso inada kiba sosai but kasan banbancin mu?” Da sauri ya girgiza mata kai suka cigaba da tafiya tace “she’s so beautiful nikuma I was fat and ugly” dariya sukayi yace “common don’t say that wlh kinada kyau sosai ke kinganki ne” murmushi tayi tace “yanzu danai girma ne nakuma dakaina nai kyau, amman this girl nada kyau kam sosai Masha Allah kaman ka saceta” murmushi yayi yace “ni duk idanunta sukafi burgeni” dariya dukansu sukayi suka shige office nasu.

Tana kaiwa Anty su tace “ina kikaje? Anje bayi ba’a ganki ba”? Kaman zatai kuka tana haki tace “I got lost dazani bayin sainaje na sama” mugun kallo teacher su tamata ba’a kara cemata komiba suka wuce factory din, sun zagaya factory tass bata taba sanin haka ake kera plate din tangaran dasukecin abinci ba sai yau, aka nuna musu tana daga cikin wayanda ma aka zaba tai practicing tayi plate aka bata kyautanshi daganan suka tafi show room kaman ta kwashe komi takaima Gwaggo takeji sai wajajen 1 sukabar wajen saida taga sun fita sannan hankalinta ya kwanta, abakin layinsu school bus yasauketa.
*****

Tsayawa yayi abayin yabi kasan bayin da kallo yanda chocolate suke akasan wait ma what in the first place takeyi a Gent’s restroom?? Dan tsaki yayi daidai Ibro dayasake kira kan yazo bayi direct yakawomai key yashigo ganin Yayanshi dayayi acikin bayi tsaye ga chocolate akasa yana kallo yasa yakarasa gaban bayin da sauri yace “lpy Yaya Imran” juyowa yayi yakalleshi dasauri Ibro yazaro ido yace “what happen to kayanka Ya Imran”? Hannunshi kawai Abee yasa ya karbe key office nashi dake kan hannun Ibro batare daya amsashi ba yawuce yafita daga bayin yay kofa harya bude batare daya juyoba yace “call Hamza tell him I will not be able to see those school people” yana maganan yawuce office nashi yabude yashiga wani kalan lafiyayyen office ne babban gaske gaban wani daki yaje direct yabude lafiyayyen bedroom ne ciki da gado dakomi bayin dake dakin yashiga wanka yayi da ruwa kai zafi yana fitowa yadauki wani sabon suit ash yasaka sannan yadauki makullin motanshi yawuce yafita.
Stairs yayi daidai mutumin nan yafito daga office girgizakai yayi ganin Abee ya chanza kaya saikuma ahankali yakoma cikin office ya zauna yana jinjina lamarin nan azuciyanshi.

 

Koda aka sauketa da kafa takarasa gidansu bude gate tayi tashiga Mama ne a tsakar gida da Abida suna gyaran shinkafa duk suka bita da kallo ahankali tace “sannu da aiki Mama” fitowa Gwaggo tayi daga bangarenta tace “makiran matan nan ina zata amsa gaisuwanki taho diyata tun dazu nake zuwa kofar gida na leka ko kin fara dawowa amman baki dawoba zonan diyar Gwaggo” Gwaggo tabude mata hannu dasauri tana murmushi tawani fada jikin Gwaggo ahankali tace “Gwaggo yunwa” sakinta Gwaggo tayi tace “tuni namiki abinci dakaina dakuma na wanchan Matar ubanki data kawo saida na dandana dan intabbatar ba guba tunda gashi har yanzu ina raye ba guba muje daki” daki suka shiga saikuma tafito ta kalli Abida tace “kin fasa shan furan dakikacemin zakisha ne tijararriya”? Dasauri Abida ta tashi Mama ta tabe baki batace komiba dan yasan dazaran tace wani abu Gwaggo zata hada karya da gaskiya yau yau din nan ta tara yaranta kaf takai karanta.

 

Tana shiga dakin taga Lujain zaune akasa ko takalmin makaranta bata cireba Gwaggo tacika mata abinci agaba kusan kala takwas, Mama dama fried rice tayi da salad da chicked, Gwaggo takara soyamata wani Kazan daban cikin kula, ta dafamata kwai guda hudu, sai katon flask din tea, ga buredi saikuma taliya ga fanta da coke gakuma fura datake rabawa bama Abida tayi cikin kofi tace “ungo” karba tayi tana kallon cikin kazan dake cikin kula gaban Laujain data faracin abincin ga Kazan Gwaggo badai dadi da zaki ba tanajin kafizabo ahankali tace “Gwaggo nima kaza” dan zaro idanu Gwaggo tayi takalli Lujain data batarai Gwaggo tace “fisabilillahi Abida ni dai bansan kokin maida Lulu kishiyarki bane amman tsakani ga Allah kemafa dazu kin shigo nabaki Kazan nan sannan kinci na wajen uwarki yanzu na jikata ne baraki bari taci ba” turo baki Abida tayi tace “ai nima jikankice” ihu Gwaggo tayi tace “daman nace ke ba jikata bace ni Safara’u amman ai wannan bata da uwa keko ga uwarki chan awaje tana aiki sai shegen bakin zuciya” daure fuska Abida tayi tamike zata fita Lujain tadauki katon cinya tace “uhm” juyowa Abida tayi ganin Lujain nabata tazo ta amsa tajuya bako godiya Gwaggo tace “kobaki gode ba Allah dai yabata lada kinga banbancin rainona da rainon uwarki ko, diyata akwai kirki da farar zuciya kuko zukatanku uwa an shafa bakin fenti irin na gyatumarku” daidai nan Lujain ta tashi tana gaytsa ahankali Gwaggo takalli abincin dudda bata cinye komi ba amman tarage sosai tawuce tashiga bedroom nasu kayan makarantan tacire tashiga bayi wanka tayi tafito daure da towel tasa hijabi tai salla sannan tafito falo ganin bataga Gwaggo ba yasa tadauko jakanta taciro wayan Ya Samira ta kunna wayan batai komiba amman screen din ya tsage faduwa gabanta yayi ahankali ta tashi tana rike da wayan tafito da towel din nan tawuce side dinsu bataga Mama awaje ba hakan yasa yasan tana kitchen dakinsu Ya Samira tashiga tana zuwa ta ijiye mata wayan akan kayanta sannan tafito tadawo daki Gwagho da fitowa ta daga nan daki kenan tace “barakizo kihuta ba kinsan anjima kadan zaku islamiya ko

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply