Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 18


Saran Boye 18
Viral

Mo. 18

…………..Ran papa na zafi da ƙuna ya ajiye wayar, hakan da yay ya sake fahimtar da Madam Chioma cewar akwai damuwa.
“Lafiya Daddyn Yoohan?”. Ta faɗa da yarensu cike da zaƙuwa. Banza yay mata kamar bazai tankaba, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya sanar mata yanda sukayi da Yoohan ɗin. Itama abin ya sosa mata rai, amma saita bama mijin nata shawara akan ya barshi kawai. Karkuma su sake ɗaukar kowanne irin mataki akan yarinyar har sai Yoohan ɗin ya manta da zancen sannan.
Wannan shawarar ta masa daɗi sosai, harya kai ga jawota jikinsa ya rungume yana kissing ɗin wuyanta. Fakar idanunsa tai ta zuba masa harara tana yamutse fuska daɗan turesa daga jikinta irin kamar da wasa ɗin nan.
Shikuma yaƙi ya bari saima ƙara wuta yakeyi. “Darling!” ta faɗa tana fisge jikinta da ɗan fushi, ganin ya saketa kuma saita ƙyalƙyale da dariya tana miƙewa ta nufi ƙofa da gudu tana faɗin wai ta masa wayo. Miƙewa yay zai bita ta ida ficewa da gudu taja ƙofar ta rufesa a ciki.
Haɗe fuska tayi tamkar an aiko mata da saƙon wani ya mutu yanzun nan tana harar ƙofar. Jitake a ranta lokaci yayi da zata fitar da abinda ke ranta tsahon shekaru. Taja gajeren tsaki tana barin wajen ta nufi ƙasa inda take jiyo hayaniyar su Miracle dake casar rawa a falon sun ƙure kiɗan daya karaɗe gidan.

________________________
*_SAUDIA_*

Shirin Adawiya ya saka suka wuni cikin daɗin rai yau ita da Abdallah. Dan dakansa ya sakata tai musu girki kamar yanda tai masa alƙawarin yimasa irin girkin da Nu’aymah tafi iyawa kuma tafi so. Shiko ya biye mata harda binta kitchen sukai aikinma tare.
Bayan sun gama kuma ya jata ɗakinsa sukai wanka tare, dukda babu abinda yay mata irin na nuna soyayya ga ma’aurata ɗinnan hakan baisa ta damuba. acewarta ai yanzun aka fara wasan. Dan haka ta ƙara ƙaimi wajen saka masa sunan Nu’aymah akan duk abinda zasuyi.

Zuwa dare bayan tayi barci a ɗakinta shima yana nasa sai ya shiga dogon nazari akan shawarar Adawiyan. A yanda ya ƙiyasta zaiyi amfani da yarinyar wajen dawo da martabarsa ga Nu’aymah kamar yanda ta faɗa masa. Duk da yayi saurin ɗago dabararta nayin hakan game da sakko Nu’aymah a lamarinsu, sai yaga ai shima wata damace a hannunsa da zai dama ya yadda ƙwallon mangwaro kuma ya huta da ƙuda.
Dan haka ya kammala shirinsa tsaf game da yanda zai bida Adawiya akan Nu’aymah har haƙarsa ta cimma ruwa ya mallaki abar sonsa su gina rayuwar da yagama tsara musu tun asalin fara mallakar hankalinsa.
Da wannan ƙwarin gwiwar yay barci ranar. Washe gari kuwa tunkan ya tashi Adawiya harta shirya masa breakfast wai acewarta irin abincin da Nu’aymah tafi ƙauna kenan. Yakoyi farin ciki, a ƙasan ransa kuma yana mai mata kallon ƙuruciya da wauta. Zama yay yaci sosai ya ƙoshi, ya kuma taimaka mata suka gyara gidan sannan suka fita tare ya kaita makaranta kafin shima ya wuce tasa.

Ba ƙaramin farin ciki Maman Aaida tayi da labarin da Adawiya ta bataba. da kuma abinda ta gani da idonta na kawo Adawiya da Abdallah yayi school, rabonda hakan ta faru tun randa ta fara zuwa da kwanaki ukun da suka biyo baya. Daga haka yace ta cigaba da zuwa ai zata gane hanya. Sai gashi yau ya kawota da kansa cike da farin cikinsa.
Haka taita walwala a majaranta har lokacin tashi yayi. Abin mamaki kuma sai gashi ya sake dawowa ya ɗauketa. Suna isa gida kuma ya miƙa mata kwalin waya sabuwa fil harda sim card a ciki. Wani uban tsalle ta buga ta ɗaresa tana masa tagwayen kiss a wuyansa da fuska. Daga haka ya biye mata ya kwashi gara sanan ya sake wanka ya fice gidan ya barta da murnar waya.

Wani irin ji Adawiya tayi kanta na yawo a sama. Ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta cike da nishaɗi da yabama tunaninta da shirinta. ‘Yo ashe nice na zauna shashanci akanka Yah Ab, ashe kawai wata ƴar gajeriyar hanyar da zan bi da kai na samu nasarori a kanka bama nasara gudaba, amma na zauna ɓata hawayena da lokacina wajen tunani da baƙin rai. To yanzu kam saika shirya, dan Adawiya tayi alƙawari da alwashin sai kayi nadamar cin kashin dakai mata akan wata shasha Nu’aymah. Kaida Nu’aymah kuwa sai dai gani a hoto, dan lokaci zaizo da ko gaisuwar waya sai kun tsani kanku wajen dinga yinta balle ta zahiri. Ni Adawiya Mustapha Hashim Jibiya, ni kaɗaice matar da zata mallakeka a duniya da komai naka. Kuma Nu’aymah bazata taɓa samun wanda ko ya kama ƙafar matsayin Slippers ɗin wankan kaba Yah Ab. Dan saina sakata kuka da baƙin ciki kwatankwacin wanda ta sakani a baya saboda zazzafar ƙaunarka da begenka inhar niɗin jinin Fauza ce (Addah).

Tofa Adawiya anya baki ɗebo da zafiba kuwa🤔🤥🤐?.

___________________________________

Nu’aymah da batasanma Adawiya nayiba tana can durƙushe gaban Umm da Baba malam tana mai basu haƙuri akan ɓacin ran data assasa musu a safiyar jiya game da abinda ya faru. Dan jiya gaba ɗaya ƙin kulata Umm tayi. Baba malam kuma basu shigo gidaba sai gab da magriba. Yana zuwa yay alwala ya wuce massalaci ko Hajjo bai leƙaba. Bai kuma shigo gidanba sai goma saura kamar yanda ya saba. Zuwa lokacin kuma Nu’aymahr ta gama jigata da aman da taita kwarawa na ƙa’idar zuwan jininta hartasha magani tai barci.

Ƙinyin magana Baba malam yayi har sai da Umn ta gama yima Nu’aymah faɗa sosai akan shegen tsiwarta kamar zata daketa kafin ta koma nasiha kuma.
Bata bartaba har sai da taga tana sharar ƙwalla, dan Nu’aymah fa batason faɗa a rayuwarta, sai dai kuma babu yanda ta iya dan iyaye nagari suke saurin tsawatawa yaransu idan sun gansu akan dokin kuskure. Bayan Umm ta gama nata shima bana malam ya murje nasa idanun yay mata tas fiye da wanda Umm ɗin tai matama. Kafin shima daga baya ya koma nasihar da nuna mata illar rashin kunya ga ɗiya mace.
Tasha kuka da neman gafararsu sosai, dan har saida Muhammad ya sulale sashin hajjo ya sanar mata tazo ta ƙwaci Nu’aymah a hannunsu sannan suka barta. Duk da dai itama Hajjo ba ƙyaleta taiba sai da ta mata nasihar itama.

Haka Nu’aymah ta wuni ranar cikin halin ciwo da takaicin Yoohan da Guards ɗinsa da duk ta tattara laifin a kansu saboda faɗan da akai mata. Bata da riko sam idan akai mata abu. amma sai gashi yau Yoohan ɗin da tarkacensa sun kasa barin ranta harma washe gari da shima dai haka ta yini babu walwala saboda jinin nata.

Da haka kwanaki suka cigaba da  ƙara shurawa, baba malam yana cigaba da ƙoƙari neman hanyar haɗuwar Doctor da Nu’aymah batare da kowa ya saniba. Sai dai kuma har yanzu dai ba’a dace ba kam. Har gasu Yusrah sunyi nisa a zana jarabawarsu, wadda a dalilinta baba malm ya dakata da nemawa Nu’aymah makaranta. A cewarsu idan sun kammala sai a nema mata ita da Amal, tunda ita Yusrah zatabi Abdallah ne taje itama tayi nata karatun kamar adawiya.
Cikin wannan tsukun takardun da bawan ALLAH nan da har yanzu basusan ko wanene ba suka gama kammala. Daga na neman aiki harna karatun yaran daya buƙata. Haka suka tattarasu aka aika masa ta hanyar daya faɗa.
Kamar wasa kuwa sai ga saƙon ɗaukar aikin nata zuwa ɗaya bayan ɗaya. Hakama na masu shiga makaranta ba’a ƙulla sati uku ba ya turo da kammaluwar komai da makarantun da duk zasuje ɗin.
Wannan al’amari yayi masifar yima baba malam da duk ahalinsa daɗi. har takai ya shirya family meeting na musamman ya roƙa duk yaran da iyayensu akan su ware dare guda wajen mikama UBANGIJI addu’aoinsu na alkairi akan wannan bawan ALLAH da basusan wanene ba ɗan kuma wane yankine. Kowa ya aminta da wannan tukuyci, sunkuma ɗauki alwashi da ɗamnarar gudanarwa insha ALLAH.
Yanda Nu’aymah taga mahaifinta yana farin ciki da al’amarin ita bayanma ƙiyamullaili da tayi harda azumi ta tashi washe gari, dan a duniya babu abinda ke sakata nutsuwa da maɗaukakin farin ciki irin ganin iyayenta a farin ciki.

Kamar yanda Baba malam ya roƙama wannan bawan ALLAH addu’a ga iyalansa haka ya roƙama masa a massallaci, ya kuma roƙa masa a gidan marayun da alkairin yazam duk a kansune. Dan bayan wancan aiken duk ƙarshen wata sai an kawo mota guda ta kayan abinci gidan daga wannan mutumi da basusan ko waneneba. Wani abin mamakima harda yankakkun kaji lafiyayyu ake hado musu yanzun ko ɗanyen kifi ko jan nama.

______________
*_SAUDIA_*

Tunda Adawiya ta samu waya shikenanfa harka ta buɗe mata. Kullum cikin kiran ƴan uwanta takeyi suna shargallensu. duk da Nu’aymah bata da waya a hannu yanzu haka Adawiya ke addabama Umm kira akan ta bata. Kokuma wayar Amal ko Yusrah, kai harta hajjo kira take a haɗasu.
Duk hakan tanayinsane danta birge Yah Abdallah ya yarda da gaske tanason cika masa alƙawarinsa na maido Nu’aymah rayuwarsa. Shi kuma duk da yasan dalilin yin hakan bai taɓa nuna mata ya fahimta ɗinba. Haka ya cigaba da biye mata akan ƙuruciyarta da wauta. Sai dai yanajin farin cikin yanda yakejin muryar sahibarsa kullum sama da sau biyar a rana. Duk da har yanzu bai taɓa amsar wayar sunyi maganaba koda kuwa a gabansa ne Adawiya zatai fira da Nu’aymah.

A gefe kuma abinda Abdallah bai taɓa fahimtaba shine Adawiya ta daina shan maganin da yake bata. Duk sanda zai batan bata musawa wajen amsa, sai dai fa cikin dabara da wayon da ALLAH yay mata zata zirar dashi cikin riga tayi kamar tasha. Sai ta faki idanunsa ta watsa cikin wani abun da tasan idonsa bazai kaiba. A haka suka cigaba da shurawa ƴar shaƙuwar dake tsakaninsu kafin aure tana dawowa a dalilin saka Nu’aymah da sukayi a tsakkiyar lamarinsu.

★★★★★

A ranar da Adawiya ta fara kiransu a waya suka gaisa Nu’aymah tasha kuka a ɓoye, dan har Umm sai da ta gane tayi kuka. Dan haka ta jata a jikinta sosai cikin hikima taita lallashinta harta ware. Daga nan kullum Adawiya ta kirata bayan sun gama hirar da ƙyar take iya danne zuciyarta. Dan tunkan ai nisa ta fara fahimtar kamar da biyu Adawiya ke kiranta tana gasa mata magana a fakaice kan Abdallah.
Duk da ƙuruciya da yarinta dake tattare da ita hakan bai hanata zama ta harhaɗa wasu abubuwan cikin rantaba gameda abinda ya shuɗe na rayuwarta da Abdallah harma lalacewar aurensu da har yanzu an gaza gano musabbabin sa a gidan. Kuma har yanzu wasu basubar kallonta da tabon guduwaba a ranar auren nata. Yayinda sukeji a ransu rashin dawowar Ameer gareta butulcine da alhakin Abdallah.

A wayar da Adawiya takeyi da ita kowa yana kallonta a matsayin shakuwar da sukayice da ɗunbin soyayyar dake a tsakaninsu. Amma kuma a baɗini Nu’aymah ita kaɗai tasan mike faruwa tsakaninta da Adawiyar. Ta kuma shanye a ranta duk da yana damunta bata taɓa nunama kowa a fuskaba koda kuwa su Yusrah ne balle Umm.

★★★★

Rayuwa ta cigaba da shurawa, inda alkairin wannan bawan ALLAH keta sake faɗaɗa ga gidan marayunnan. Ga azumi nata gabatowa gamai yawancin kwana kuma. Kowa nata shirye-shirye da abinda ALLAH ya hore masa dan farantama iyalansa da bayin ALLAHn da basu da shi.
A gefe kuma babban gida irin na malamai su baba malam sunata shirye-shiryen tafsir da hidimar da suka shiryama marasa ƙarfi wanda suke jiran sakamakonsu a gurin UBANGIJI al’arshi.
Duk shekara su duka huɗun suna gudanar da wa’azi a mabanbanta garuruwan da suke rayuwa. Abba Mustapha dake tare da baba malam anan kano shine keyi anan masallacin ƙofar gidansu. Yayinda shi kuma baba malam keyi a massallacin gidan sarki duk shekarar duniya.
To a wannan shekararma sun kammala shirinsu tsaf daga gidajensu har gidan marayunsu. Ta wani ɓangaren kuma taimakone keta ɓullowa ta hanyoyi daban-daban zuwa gidan marayunsu. Amma duk da haka baba malam bai gazaba wajen tsayuwar daka akan tantance daga ina komai ya fito da ingancinsa ga lafiyar yaran da mutuncinsu.

Alhmdllh an shiga watan azumin ramadan cikin rahamar UBANGIJI da yardarsa. Kowanne musulmi na ƙwarai yana cike da murnar shigar wannan wata mai tarin falala dake zuwa mana a cikin watanni goma sha biyu na shekara sau ɗaya kacal ya wuce.
Randa aka kai azumi na goma Baba malam ya gama shirya maganar Umrah da Hajjo kanje a duk shekarar duniya idan wata ya raba. A ƙa’ida kuma takanje da yara biyune cikin ƴaƴan gidan. Namiji babba sai mace budurwa guda ɗaya. Sau ɗaya a wata shekara dasu Nu’aymah suka tada billi ita da Adawiya aka tafi dasu su biyu. Aiko Hajjo ta shawo wahala da su, tun daga lokacin ta rantse bazasu sake bintaba sai sunyi hankali. Sai dai idan wani zaije cikin iyayensu mata su bishi.
To a wannan karon koda Baba malam yay mata magana a mamakin kowa sai tace da Nu’aymah zataje. Babu wanda hakan bai bashi mamaki ba. Amma sai babu wanda yace wani abu tunda dama itake zaɓar abokin tafiyartata.
Amsar passport ɗinsu baba malam yay ya bama Ahmad yay musu komai su biyun, sai shi Ahmad ɗin da zaije a wannan karon tare da hajjon.
Haka kawai sai Nu’aymah ta tsinta kanta da rashin jin ɗokin zuwan, duk da kuwa tana matuƙar son rayuwa a ƙasar saudia saboda dalilan data ginu dasu a cikin rai game da ƙasar.
Ta samu hajjo a ɓoye ta roƙeta akan ta canja ta da ko Amal ko Yusrah, ita batason zuwa batajin daɗin jikinta. Harara Hajjo ta watsa mata tana taɓe baki. Batare da tace mata cikankiba a zancen ta ɗauke kanta ta maida ga lissafin atamfofin salla da ƴaƴanta kan siya mata danta rabama ƴan uwa da abokan arziki. To da yake bata dawowa sai a daren salla  sai yazam take rabasu kafin ta wuce.
“Hajjo dan ALLAH mana”. Nu’aymah ta faɗa cike da shagwaɓar data saba yima hajjon tana kwanciya mata a gefen kafaɗa.
Ture mata kai hajjo tayi tana faɗin, “K da ALLAH jacan shashasha, yo ko shi uban naki wama yake da suna (ba faɗafa zatai ba burgace sabida ɗan farine🤣) bai isa sakani ko hanani abinda nai niyyaba bareke haihuwar jiya jiya Zainabu. Dukfa take-takenku ina sane dasu. Yanzu bautar UBANGIJI ce ma baƙyason zuwa saboda Abdullahi nacan ko yaya? Ke koma ɗokin ganin ƴar uwarki da duk ta addabi kanta da ƙulafucinki a watannin nan baƙyayi? Ni na tausaya mukune dan kuga juna ke da ita shiyyasama na zaɓi tafiya dake. duk da nasan wahalarku da rashin arziƙi zaku jazamin acan kamar yanda kuka saba”.
Baki Nu’aymah ta sake kumburawa tana faɗin, “Ada kenan, sai akace miki kullum zama zamuyitayi jiya iyau Hajjo, yanzu fa munsan kanmu”.
Baki Hajjon ta riƙe tana ƙyaɓewa, “Oho to lallai sannu uwata Ɗaharatu, keni dalla tashimin a falo koma kizo na aikeki gidan marigayi malam Aminu kikai waɗannan zannuwan na marayun ƴaƴansu”.
“Ni wlhy hajjo bani da lafiya, ki aiki Amal kosu Muhammad ai basa azumi”.
“To wlhy ko zakiyi mushe a gidannan kece zaki aikarnan, kuma Umrah babu fashi sai kinjeta. Dan ALLAH idan kunga juna ke da Abdullahin ku babbaka juna saboda takaicin kanku da kukeji. Tunda shima ya zama babban hotiho ya ɗauki fushi da mutane shi mai zuciya. Toni namaga kuturu ƙarewa zuciyar banzarku da kuka gada wajen malam”.
Nu’aymah bata sake tankawaba, dan ita ɗaya tasan damuwar da take ciki da matsin da take fuskanta daga Adawiya akan Yah Abdallah ta waya. A ganinta suna a nesa da juna kenan inaga sun haɗu, tunda ta tabbata babu fashi a gidan zasu sauka. Tayi imani da ALLAH harta mutu son Yah Abdallah bazai bartaba, ƙilama shine zai zama ajalinta. Kafin ta san matsayin Yusrah da Adawiya a garesa tana fatan ko bayan shekara nawane idan ya gama fushin ya dawo gareta. Amma kuma zuwa yanzun ta haƙura koda sonsa zai halakata. Badan bazata iya zama dasu bane, sai dai kawai tanason tayi sadaukarwa a garesu dukda tasan ta fisu buƙatarsa.
Tanaji a jikinta inhar ta matsama kanta saita mallaki Yah Ab kamar yanda ta rayu da wannan burin a ranta to lallai zumincin gidansu da aka gina tunkan samuwarsu yana gab da tsinkewa ya tarwatse ta dalilinsu. Dan kuwa Adawiya da gaske take nuna mata zata iya yaƙi da kowa akan Yah Abdallah a yanzun har ita kanta Nu’aymah. Tana ƙaunar Adawiya har yanzu a ranta, duk da SARAN ƁOYEN da take mata batare da kowa ya saniba daga ita sai ALLAH. Wannan dalilan guda biyu kawai zaisa ta sakama ranta salama da haƙuri. Sai dai kuma haƙura da Abdallah yana nufin harta koma ga ALLAH bazatayi aureba. Shiyyasa ta duƙufa addu’ar ALLAH ma yasa kar a samu likitan da ake fatan ta silarsa ciwonta zai barta. Dan a yanzu bata buƙatar kowacce irin lafiya kuma, tafi buƙatar ta rayu a haka harmai kasancewa ta kasance a gareta. Idan da rabo zasu hadu da yah Ab ɗinta a gida mafi tsada shine Aljannah.
Da wannna tunani ta ɗauki aikan Hajjo ta fice bayan ta shiga bedroom ɗinta ta ɗakko hijjab dan akwai kayanta anan sashen hajjon.

*_ABUJA_*

“Wai nikam Khadijah mike damunkine haka kwanakin nan? Ina lura dake kullum walwalarki da farincikinki ƙara nisantar rayuwarki da mu’amularki sukeyi. Ko baki da lafiya ne?”.
Idanun Momyn Ab cike da ƙwalla take kallon mijin nata. Ta matso hawayen nata suka gangaro saman kumatunta tana girgiza masa kai.
Tausayintane ya sake kamashi, dan tsaf ya fahimci damuwar tata akan Abdallah ne da a yanzu ko kiranta a waya baya sonyi sai idan shine ya kirashi ya balbalesa da faɗa. “Khadijah!” ya sake kiran sunanta cike da taushin murya.
Kanta ta sake ɗagawa ta dubesa. Sai kuma ta duƙar tana fadin, “Na’am”.
“Mike damunki? Ki faɗamin dan ALLAH?”. Jin ya ambaci ALLAH ya sakata sake fashewa da kuka, cikin rawar harshe irin na mai kuka tace, “Abdallah ne, gaba ɗaya Abdallah yaƙi sauka daga fushin rashin Nu’aymah. Kuma nama lura yanzu fushin nasa duk a kaina ya tattarashi bansan miya saka ba?. Bayason kirana sam yanzun, sannan ƙiri-ƙiri yaki yazo ko sau ɗaya mu gansa. Idan wancan karon yana ganin baida iyali rashin zuwansa bai damemuba ai yanzu yana dasu, ita kanta tana buƙatar ganin nata iyayen ai Adawiyan. Kuma wancan karan a rana sai muyi waya sau uku hardama video call. Yanzu kam kaga inma bakai ka kirasa ka baniba sam ya manta dani?”. ta ƙare maganar da rushewa da kuka mai ban tausayi.
Jawota jikinsa yayi kasancewar darene sosai ansha aruwa. Dan sunama zaune ne sun kammala ƙiyamullaili suna jiran lokacin sahur ya ƙarasa su tashi yaran suma.
Bayanta ya rinƙa shafawa a hankali shima yana jin ɗacin hakan a maƙoshinsa. dan bama ita kaɗai Abdallah kema hakanba, kowama yana masa. Sai dai su da sauƙi saboda harkar business na shiga tsakaninsu akai-akai. Amma ko ranar sai da baba malam da kansa yay wannan ƙorafin na banza da kowa da Abdallah yayi tun tafiyarsa.
Baki ya buɗe a hankali yace………..✍

_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA… SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply