Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 20


Saran Boye 20
Viral

No. 20

…………..Aiko ALLAH ya amsa masa, dan cikin amincinsa Yoohan na komawa gida bai rufa awa ɗaya ba wani irin barci mai daɗi da saka kwanciyar hankali yay awan gaba da shi. Sai ga Yoohan da ya kwanta tun kusan shida na yamma bai farkaba sai goma na safiyar washe gari.
Wannan al’amari ya bama Yoohan da su Papa mamaki, suka shiga masa tambaya akan yaya akai yay barci jiya?. Bai ɓoye musu komaiba ya basu labarin haɗuwarsa da mutumin da bai sani ba, bai kuma san inda zai sake samunsa ba a yanzun. Duk da sunji daɗin hakan sai suka nuna rashin damuwarsu da sanin wanene mutumin ko inda zasu samesa, saboda kawai sun fahimci musulmi ne. Yoohan ɗin kuma ya koma inda suka haɗu da mutumin har kusan sau huɗu bai samu koda mai kama da motarsaba ma balle shi ɗin. Haka ya haƙura badan yasoba ya koma makaranta.
Wannan shine dalilin samun sauƙi sosai daga matsalar Yoohan, ya koma yana barcinsa lafiya lau kamar kowa, sai dai lokaci-lokaci abin nasa kan buga, idan kuma ya juyo yana tsintar kansane cikin mawuyacin hali na baƙin rai da fushi da tsangwamar kansa. Dama gashi dalilin hakane sanadin maidashi mutum mara fara’a da son hayaniya.
To a yanzu gashi al’amarin nasa ya sake motsawa, duk da yakan jima baiyiba ma. Yau kwanakinsa uku kenan da dawowa ƙasar, amma ko barcin mintuna goma ya kasa ɗaukarsa. Yanda yake ganin rana haka yake ganin dare. Ya mugun fita hayyacinsa a kwana ukun nan, ya daina magana da kowa, abincima ya masa yajin aiki sai abinda ba’a rasaba yake ɗanci idan yaji yana neman halaka a banza.

★★★★

Cikin murya mai cike da lallashi papa ke kiran sunan Yoohan ta jikin Window da suke a tsaye shi da Madam Chioma. Duk da yana jinsu bai fasa wurgi da abinda duk yaci karo ba a ɗakin, har wani sashe na gilas ɗin dake zagaye da ɗakin ya tsage, dan ya jefa ƙarfe ne ya bigi gilas ɗin dake a matsayin bango ɗakin.
Sai da ya jigata dan kasan sannan ya zube a ƙara yana wani irin sauke ajiyar zuciya mai ƙarfin daban tsoro.. Duk da hankalinsu ya ɗan kwanta ganin yabar jefe-jefen basu daina kiran sunansa da roƙon ya buɗe musu ƙofarba cike da lallashi. Shi kuma yayi banza dasu tamkar baisan da zaman nasu a wajenba.
Papa ne ya tuna da extra keys ɗin sashen nasa, dan haka yabar wajen Window da sauri zuwa bedroom ɗinsa. Mintuna ƙalilan sai gashi ya dawo cike da farin cikin samo keys ɗin. Hakama Madam Chioma saboda daɗin da taji har kiss taima papa tare da rungumesa. Zagayawa sukayi domin buɗe ƙofar, sai dai kuma key ɗin yaƙi shiga alamar yabar wani key ɗin a ciki. Ransu duk a jagule suke bin ƙofar da kallo, madam Chioma har hawayenta sun dawo kwarara.
Solomon ne ya kawo shawarar bin ƙofar can baya dake sada mutum da ɗakin motsa jikinsa kai tsaye. Su ruɗewama ta sakasu mantawa da ƙofar. Da sauri suka zagaya tacan, cikin amincin ALLAH kuwa suna gwada key ɗin da suketa kokwanton ba nata bane sai gashi ya buɗe musu.
Har rige-rigen isa garesa kuwa sukeyi. Duk da yana jinsu bai motsa ba, sai da sukasha fama, dan Yoohan akwai taurin kai dama, da ƙyar ya yarda suka tadashi zuwa ɗakinsa. Madam Chioma da kanta ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi sosai. Kafin ta dawo inda papa ke rungume da shi yanata faman lallashinsa da masa magana mai daɗin gaske, wadda ko ba’a faɗaba da alama tana tasiri ga Yoohan ɗin.
Zama tai kusa dasu itama, ta miƙa hannu ta riƙo na Yoohan ɗin tana murmushin jin daɗin ganin ya nutsu,  matsawa tai jikinsa sosai zata rungumesa kamar yanda papa yay masa, sai ya ƙwace hannunsa ya miƙe zumbur. Cike da basar da abinda ya fahimci zatayin ya nufi toilet yana ɗingishi, dan da alama yaji ciwo a ƙafar tasa ne.
Duk binsa da kallo sukai ita da papa, yayinda ranta ya sosu sosai akan yanda Yoohan ɗin keyi mata a duk lokacin da ta nufi yimasa makamancin waɗan nan abubuwan. Tarasa dalilinsa na yimata hakan, ‘shi kodai ya fara tunanin…….’ sai kuma ta kasa ƙarasawa ta girgiza kanta alamar ba haka bane. Dariyar papa ta sakata saurin kallonsa. Ya ɗage mata gira da matsowa shi ya rungumeta yana faɗin, “Ɗanki fushi yakeyi dake yau, kinga yamaƙi yarda ki rungumesa. ni zo na rungumeki”.
Fuskarta a yatsine taɗan turesa, cike da salon yaudara ta matsa baya da juya masa keya irin maganarsa ta ƙara mata haushin nan. Shiko ya sake matsowa jikinta ya rungumeta ta baya yana dariya ƙasa-ƙasa. “Wasa nake miki Momyn Yoohan, shima nasan yanayin da yake cikine kawai ya sakashi aikata miki hakan”.
Duk da haushin da take ciki sai maganar papan taɗan sanyaya mata rai, dan ita ada tunaninta ba haka yake kawo mata ba. Juyowa tai idanunta cike da ƙwalla, muryarta na rawa tace, “Darling! Anya kuwa bazamu nema mutumin nan daya taɓa yimasa maganiba shekarun baya da suka wuce sannan muna farko-farkon zuwa Abuja?”.
Papa dake kallonta ya ɗan ɓata fuska yana nazarin maganarta, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya amsa mata. “Shawaranki mai ƙyaune momyn Yoohan, sai dai kuma a ina zamu samesa? Shi kansa Yoohan ɗin bana tunanin zaima iya ganesa idan ya gansa ai”.
Kafin ta samu damar bama papa amsa Yoohan ya fito daga toilet ɗaure da towel, dan duk zatonsa sun fita. Turus yaja ya tsaya yana kallonsu fuska a turɓune.
Ahankali madam Chioma ta sauke idanunta akan buɗaɗɗen jikin yaron nata dake ɗauke da wata lafiyayyar farar fata mai santsi da ɗaukar idanun mai kallonsa. Basai an faɗaba a kallo ɗaya zaka fahimci shi ɗin ya tashi cikin kulawar rayuwa da jin daɗi, dan sam babu alamar rama tattare da shi……
Jikinsa ya fara ja da baya yana ƙara tamke fuska, hakan yasa Mom saurin tashi tsaye har tana neman faɗuwa, da yarensu tace, “Ina zaka kuma yaro na? Kaga zo na shafa maka man ma da kaina idan bazaka iya b…..”
Kafin takai ƙarshen maganarta harya maida ƙifar bayin ya rufe, jingina yay a jikinta ya lumshe idanu zuciyarsa na ƙara ƙarfin bugu. Duk da yanda take buga ƙofar a hankali tana kiran sunansa bai motsa ba, sai ma wani haushi dake sake ziyartarsa. Sam bayason wannan halin da Mom take masa, a ganinsa bai daceba, yakamata tasan da ba yanzu bane, yanzu fa ya girma, shekararsa talatin har da biyu a duniya, miyasa bazata daina masa kallo kamar ɗan shekara goma ko ƙasa da hakaba?. bawai yana saka abinda take masan a wani mizani daban bane, dan yasan soyayyar da suke masa mai yawa ita da papa ne ya jawo hakan, amma ya kamata ta fahimci yanzu ya wuce ta dinga masa wasu abubuwan kanta tsaye ai……
A hankali ya buɗe kumburarrun idanunsa dake cike da barcin da baisan ranar yinsaba, ya sake lumshesu yana sauraren yanda Papa ke lallaɓa Mom akan su fita su bashi waje ya shirya, idan yaso saisu dawo daga baya.
Badan madam Chioma taso hakanba ta yarda suka fita ɗin ranta na mata ƙuna.

Yoohan najin sun fita shima ya fito, dan dama a gajiye yake da tsayuwar saboda ƙafarsa wani bala’in zogi take masa. Sai da ya leƙo ya tabbatar babu kowa sannan ya fito. Bai kalli ko inda Mirror ɗinsa yake ba balle ai tunanin shafa mai ya nufi wajen kayansa kawai. Dogon wando ash mai taushi da farar t-shirt data kama jikinsa ya saka. Ya taka zuwa gaban gadon yana cije baki, zama yay yana mai kallon ƙafarsa data ɗan kumbura dai-dai idon sawu. Hannu yasa ya taɓa wajen yana yamutsa fuska, duk da zafin da yaji haka ya daure ya kama ƙafar yaja da ƙarfi. Siririyar ƙarar azaba ya saki tare da sakin ƙafar itama.
Har rige-rigen shigowa ake tsakanin papa da Mom da Richard da yazo gidan yanzu babu jimawa. Sai Solomon da Miracle dake ƙoƙarin shigowa falon suma Joy biye dasu tare da masu aiki dake ɗauke da abincin Yoohan ɗin.
Yanda sukagansa a kan gadon ya saka hankalinsu sake tashi, suka zagayesa da tambayoyin yaya akai?. Duk da surutun nasu haushi yake sake bashi sai ya tashi zaune, ganin Rich tare da su ya sakashi miƙa masa ƙafarsa. Kallon ƙafar Richard yayi da ƙyau, kafin ya jawo stool ɗin mirror ya zauna yana tambayarsa garin yaya yaji ciwon?.
Bai tanka masa ba, dan haka Rich ɗin ya kama ƙafar kawai ya hau ja masa. “Jesus!!!” ya faɗa da muryar nan tasa mai amo data haɗu da damuwa a yanzun. Saurin zama Momy tai a kusa da shi ta amshe filon daya damƙe ta maye gurbin filon. Caraf kuwa ya kama hannunta ya damƙe cikin nasa da masifar ƙarfi, dan har sai da ta saki ƙara itama.
Yanda jikinsa ke rawa zufa na fito masa sai duk tausayinsa ya sake kamasu, Miracle tai saurin zama ɗaya gefensa tare da kwanciya a jikinsa tana hawaye. Sai da Rich ya tabbatar ƙafar tayi yanda ya kamata sannan ya barsa. Sai faman jera masa sorry sukeyi.
Duk da yaji mutum kwance a jikinsa bai motsaba sai da zafin ƙafar ya daina sosai, a lokacin ƙamshin turaren Miracle dana Momy suka tabbatar masa sune nanuƙe da shi. A hankali yasa hannu ya ɗaga Miracle dake lafe a jikin nasa, kafin itama Mom da tunda ta farga da Mira take zuba mata wani kallon ƙasan ido na gargaɗi, shi dai ya zare hannunsa daga cikin nata, jan jikinsa yay baya ya haye gadon sosai batare da yace uffanba duk da sannun da suketa faman yimasa har yanzun.
Cike da kulawa Rich ya basu shawarar ya kamata su fita abar Yoohan ɗin ya huta, dan ya kula da yanda Yoohan ya sake cika tamkar zai fashe, hakan kuma yanada nasaba da zamansu a ɗakin, dan shi ɗin shaidane akan yanda Yoohan yay mugun tsanar jin kowanne kalar motsi a kusa da shi idan har yana cikin wannan yanayin.
Papa da ya gamsu da shawarar Rich ɗin sai ya tarkatasu suka fice duk da uwar gayyar Mom bataso hakanba ita. Bin bayansu Richard yay shima dan yana buƙatar ɗakko wani abun da yake son gwadawa Yoohan ɗin ko zai aminta wannan karon yasha.

Yoohan na zaune yanda suka barshi idanu a lumshe Richard ya dawo ɗauke da ƙaramin tray mai ƙyau. Duk da Yoohan na jinsa bai buɗe idanu ba balle ya motsa, Rich ya jawo ƙaramin table glass dake gaban sofa zuwa gaba gadon. Trayn dake ɗauke da kwalbar barasa da kofuna biyu, sai ƙanƙara a wani bowl ya ɗaura a kai yana kallon Yoohan ɗin. “Mr-x!”. Ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe kwalbar barasan.
Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali batare da ya amsama Rich ɗinba. Rich ya ɗan murmusa, dan bai damu da rashin amsawarba, barasan ya zuba rabin kofi, ya ɗiba ƙanƙara ya zuba a ciki yana murmushi. Ɗagowa yay ya miƙama Yoohan dake kallonsa ta ƙasan ido kofin.
Ɗauke kai Yoohan yayi fuskarsa na nuna ƙarin ɓacin rai, dan yasan Rich ɗin yafi kowa sanin shi baya shan giya………..
“X-Man! inhar bazaka yarda na maka allurar da zata taimakeka kayi barci ba to ka daure kasha wannan, na tabbatar ita zata saka ka barcin koda na awa ɗaya ne. Kai fa likitane, kasan illar wannan matsalar da yanda take maida rayuwar mai fuskantarta a ƙarshe. Idan kana tunanin ƙin shan giya ne dan karta shiga maka rayuwar aiki yanzu ai ba’akan aikin kake ba, sannan don neman lafiyarka ne”.
Shiru kamar Yoohan bazai kulasa ba, dan har Rich ɗin ya fidda tsammanin samun kulawarma. Sai ya tsinkayi sautin tsakin Yoohan ɗin a hankali. Kallonsa Yoohan ɗin yake cikin ido da jajayen idanunsa dake a kumbure, murya a daƙile yace, “Rich! a wajenka ya kamata mutane su ƙara sanin halina akan idan nace bazanyi abuba bazan taɓa yinsa ɗinba, dan haka karka sake tunanin zansha barasa koda ba yau ba”.
Yanda yay maganar cikin kaushin murya ya saka Rich saurin cemasa “I’m very sorry”. Batare da Yoohan ɗin ya sake cewa komai ba ya maida idanunsa ya lumshe duk da yasan barcin ba ɗaukarsa zaiyi ba.

Haka suka cigaba da zama a cikin ɗakin shiru, Richard da ya sha barasar da Yoohan yaƙi sha har ya fara barci a gefen sa, shiko idanunsa biyu amma suna a lumshe. Lokaci-lokaci hawaye kan ziraro masa ta gefen ido. Yana sauraren yanda Momy da Papa keta faman zaryar leƙowa ɗakin, sai dai ɗauka suke ko Rich ɗin yaci nasara yasha giyar barci ya ɗaukesa, shiyyasa hankakinsu yaɗan kwanta suketa faman jin daɗin yanda duk shigowar da sukeyi suna samun Yoohan ɗinne a kwance.

Wajen misalin goma na dare Yoohan ya gaji da kwanciyar, tashi yay ya sauka daga gadon yana bin Rich dake barcinsa hankali kwance da kallo, bayi ya shiga ya watso ruwa. Bai jimaba ya fito sanye da bathrobe. a bakin gadon ya zauna tare da jingina da fuskar gadon. Ya kai hannu zai kashe fitilar gefen gadon idanunsa suka sauka akan farar envelope, cak ya tsaya yana kallon rubutun jiki, janyewa yay kamar zai share, sai kuma yasa hannu ya ɗauka tare da buɗewa ya zaro takardar dake a ciki.
Rubutun bashi da wani yawa sosai, amma a tsare yake gwanin sha’awa, sannan yanda aka tsara kalaman cikin rubutun da harshen turanci sunyi matuƙar jan hankalinsa har yana ɗan lumshe ido. Sai da ya maimaita takardar sau biyu sannan ya ninketa ya maida cikin envelope ɗin ya jawo drawer ya ajiyeta yana juya abinda ta ƙunsa a cikin ransa…….

________________________
*_SAUDIA_*

Duk da fushi da zuciyarsa keyi ga duk zuri’ar gidan tasu hakan bai hanashin jin ɗokin zuwan hajjo da Ahmad ba, dan baisan harda Nu’aymah a tafiyarba. shiri yay tsaf ya wuce airport domin tarbosu batare da ya saurari Adawiya da tace zata bishi ba, dan tana wanka ma ya siɗaɗe ya fice daga gidan.

Cikin sa’a kuwa yana isa airport ɗin jirginsu Nu’aymah na taɓa ƙasa. Lumshe idanu tayi tana karanto addu’oi da fatan cika alƙawarin da taima iyayenta akan kama kanta batare da wata fitina ta ɓullo ba. Hajjo na lura da duk motsinta, amma sai batace da ita komaiba har sukabi ayarin masu fita. Sanye take cikin wando blue na jeans da farar rigar fakistan da tsahonta yake har gwiwar ta, an ma rigar ado da blue ɗin duwatsu manya da ƙanana, sai farin veil da ta naɗa a kanta wanda ya sake fidda ƙuruciyarta da ƙyawun da ALLAH ya bata. Farar ƙafarta da kalar wandon ya haska tana sanye cikin blue ɗin takalmi da yay masifar mata ƙyau dan bata da babbar ƙafa sam. Sai ƙaramar jakarta itama dai blue ɗince.
Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tai lokacin da suke ƙoƙarin sakkowa daga jirgin, ta ɗan yamutse fuska tana sauke hannun a hankali da kai dubanta can ɗan nesa dasu. Wani irin bugawa ƙirjinta yayi saboda hango Abdallah dake tsaye jikin motarsa sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa ƙyau, ya ƙara ƙiba da ƙwarjini a idanun mai kallo kamar ba azumi ake ba. A take wata kasala ta saukar mata, tafiyarta ta sake raunana fiye da farko. Dan sai da Hajjo ta kama hannunta ta ida sauka da ita ma.
Abdallah da ya yunƙuro saboda hango Ahmad dake a gabansu da yay yaja ya tsaya cak lokacin da idanunsa suka sauka akan Nu’aymah da bai zato ko tsammaanin gani ba.. Wata irin hajijiya-hajijiya ya faraji tana neman ɗibarsa a wajen, ya kasa motsi balle ɗauke ido daga kallonta har suka ƙaraso inda yake.
Hajjo datai tamkar bataga halin da suka shiga ba ta mangare masa ƙeya tana faɗin, “Kurwata kur dan gidanku”. Firgigit yay da sauke nannauyan ajiyar zuciya, sai dai ya kasa ɗauke idanun nasa daga kan Nu’aymah da ta ɗauke kanta gefe tamkarma batasan da zamansa ba a wajen. Hannu yakai ya shafa inda Hajjo ta tallaresa kafin ya janye idanunsa da ƙyar ya maida kan hajjon data wani ƙyaɓe fusaka tana zuba masa harara.
“Yanzu dan ALLAH daga zuwanki mina miki zaki tallemin kai?”. Ya faɗa yana ɓata fuska da kallon Hajjon. Watsar dashi tai taƙi magana, saima hannun Nu’aymah data kamo suna shirin barin wajen.
Dariya Ahmad yayi, ya matsa ya rungume Abdallah, “Oh Yaya kaifa kai da Hajjo sai a slow, manta da batunta kayi tani da ƙanwarmu kawai”. Murmushi Abdallah yay tare da rungume Ahmad ɗin shima. Kafin su saki juna kowanne fuskarsa da murmushi jin daɗi. Abdallah ya sake kai dubansa ga Nu’aymah sannan ya kalli Ahmad.
Kai Ahmad ya ɗan jinjina yana murmushi, amma baice komaiba sai ƙyafta idanu da yayma Abdallahn. Ab ya kaɗa kansa kawai da nunama Ahmad hanya alamar suje to.

Nu’aymah da Hajjo na baya, yayinda Ab da Ahmad ke gaba. Hajjo ce kawai ke magana a motar Ahmad na tayata, dan mafi yawan maganar tata duk tsiya takema Abdallah, shi kuma Ahmad ɗin na karesa.
Abdallah kam rabin hankalin na’a tuƙi ne rabi akan Nu’aymah da a yanzuma ta ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. A haka suka iso madaidaicin gidan nasa mai ƙyau da tsari. Sai da ya faka motar inda ta dace kafin su fita shi da Ahmad, Ahmad ya buɗe na Hajjo, ya taimaka mata ta fito, Nu’aymah kuma ta buɗe da kanta ta fito tana kallon gidan dama anguwar gaba ɗaya, a baɗini kuwa zuciyarta har wani zallo take saboda ganin Yah Ab ɗinta, duk yanda tai tunanin zata daure sai ganinsa ya canja dukan ƙudirin nata lokaci guda. Sai dai kamar yanda ya fiske itama haka tai ƙoƙarin fiskewar.

Abdallah ne a gaba lokacin da zasu shiga gidan, Ahmad da Hajjo biye da shi, sai Nu’aymah a ƙarshe tana karanto duk addu’ar da tazo mata a baki domin samun sassauci daga abinda takeji akan ganin Abdallahn.
Falon tsaf yake ko ina a gyare, ga ƙamshi mai daɗi yana tashi da sanyin ac. Sallamar Abdallahn da karaɗin Hajjo ya saka Adawiya data cika da haushin tafiyar Abdallah batare da ta saniba ta fito. Sam idanunta basu kai a kan Nu’aymah ba, dan haka ta daka tsalle cike da ihun murna ta ɗane Hajjo, saurin riƙota Ahmad yayi yana faɗin, “Ke malama karki ƙarasata ki jamin tsiya wajen su Baba malam”. Sakin Hajjon tai tana dariya ta juyo ta rungume Ahmad ɗin shima tana tsale.
“Wannan matar taka bata da man kai sam Yah Abdallah ”. Ahmad ya faɗa yana janye Adawiya daga jikinsa. Murmushi yaƙe Abdallah yayi yana kama hannun Hajjo ya zaunar a kujera. Hakan yay dai-dai da ɗagowar Adawiya zataima hajjo magana idanunta suka faɗa akan Nu’aymah dake tsaye gefe tana kallonsu.
“What?!!!!” Adawiya ta faɗa da sauri tana waro idanu waje, a take ta sarƙe da yawu kuwa ta hau tari.
Karan farko Nu’aymah ta saki wani lallausan murmushi da har ya bayyana fararen haƙoranta waje, ta taho da wani irin ɗoki ta rungume Adawiya dake tari tamkar zata amayo harshenta.
Dakatawa Abdallah da Ahmad da suka miƙe saboda ƙwarewar Adawiyar sukai. Nu’aymah ta ƙanƙame Adawiya jikinta tana matso ƙwallar da suka taru mata a ido akan dalili biyu. Ganin Abdallah, da kuma kewar Adawiyan.
Da wani irin sauri Adawiya tasa hannu biyu ta tura Nu’aymah, jikinta na wani irin rawar tashin hankali…………✍

🤔Tofa, hajiya Adawiya yaya dai?🤗🚶🏻.

Barka da juma’a😍😘😍🤗

_______________________________

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA… SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply