Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 21


Saran Boye 21
Viral

o. 21

……………..“Adawiya!!” hajjo ta faɗa a ɗan tsawace. Yayinda Ahmad da Abdallah ma sukai wani zallon mamakin abinda Adawiya tayi suma.
Kallonsu tai a firgice idanunta na tara ƙwallar takaici da jin zafin ganin abinda batai zato ko tsammani ba. Ta buɗe baki zatai magana a zafafe sai kuma ta tuna abinda ta nema mantawa. Saurin sauke numfashi tayi tana fashewa da kuka, tare da juyawa ta kalli Nu’aymah dake tsaye dafe da kujerar data taimaketa ta hanata faɗuwa lokacin da Adawiyar ta turata.
“Nayi fushi wlhy Aymah, yanzu dama dake za’azo amma kikaƙi sanarmin saboda ke yanzu kinma daina sona?”. Adawiya ta faɗa cike da makirci da waskewa.
Ajiyar zuciya Abdallah da Ahmad suka sauke, dan duk zatonsu Adawiya da gaske da faɗa tayi abinda tayi. Hajjo dai bata motsa ba, amma ta kafesu da kallo su duka huɗun tana nazarin kowa.
Jin abinda Adawiya tace ne ya saka Nu’aymah sakin murmushi, dan tsaf ta fahimci Adawiya canja hanya tayi, inkuwa hakane ai itama tanada wayonta, dan wani abun ma sai dai ta koyama Adawiyar duk da kuwa ta girmeta da wasu wattani. Sake tahowa tai da ɗan gudunta ta rungume Adawiya tana faɗin, “Afuwan habibiya, surprise nai niyyar miki shiyyasa na hana kowa faɗa miki”.
Leɓe Adawiya ta cije dan ta juyama su Hajjo bayane, itama cike da ɗacin zuciya ta rungume Nu’aymahn tana magana cikin kuka, “ALLAH saina hukunta ki tunda kika sani kuka”. Nu’aymah tai dariya hawaye na sakko mata itama, ta ɗago Adawiyan daga jikinta tana durƙusawa gabanta da riƙe kunnuwanta, “Afuwan hassanata, kaina bisa wuya Please”.
Karan farko Adawiya ta saki dariya, itama sai ta durƙusa kamar yanda tayi sunama juna kallon ido cikin ido, Nu’aymah murmushi takeyi, Adawiya kam ta haɗe fuska ganin su hajjo basa ganinta. “Kin haƙura kenan?” Nu’aymah ta faɗa tana wani ɗage ma Adawiyar gira ɗaya da sakin mata lallausan murmushin da yay mata tsaye a maƙoshi.
Kasa magana Adawiya dake mata kallon tsantsar takaici da haushi tayi, sai kawai ta rungumeta a jikinta tana gyaɗa kai……..
Gyaran Murya Yah Ahmad yay yana faɗin, “Kunga malamai ya isheku haka, ku barmu mu ƙarasa ƴar yunwar azuminmu da sauran yawu a baki dan ALLAH, idan akasha ruwa komaima sai kuyi zamu tayaku da sulhu”.
“Faɗa musu dai”. Abdallah ya faɗa a wani irin yanayi yana komawa kusa da hajjo ya zauna. Ƙaramar dariya Hajjo tayi kawai tana ɗauke kanta, sai kuma ta kalli Abdallah tana faɗin, “Kaga Audillahi kaini ɗakina na huta kaji, bazan iya luguden laɓɓa ba da azumina a baki”.
Fuskarsa ƙawace da murmushi ya miƙe tare da taimakama hajjon itama ta tashi. Har ɗakin da zata zauna ya rakata, tana zama Nu’aymah na shigowa itama. Duk kallonta sukai shi da Hajjon, ta ajiye jakarta tana zama a kujerar dake a ɗakin ƙwaya ɗaya tal, batare data kalli Abdallah ba tace, “Yah Ab! Ina yini?”. Kallonta yay a karon farko suka haɗa ido, sai ta ɗauke nata gefe tana komawa jikin kujerar ta jingina.
“Kunzo lafiya?”. Ya amsa mata shima cike da basarwa, dan haka kawai yanzu yakejin zafin abinda ta aikata a ranar ɗaurin aurensu. Ƙin sake tanka masa tayi, hajjo kuwa tamayi kamar bata a ɗakin.
Ƙofa ya nufa dan kai Ahmad nasa masaukin yana faɗin, “Ki taso ki koma ɗakin Adawiya, ita hajjo sai ta zauna anan…”. Kafinma ya rufe baki cikin sauri tace, “A’a zan zauna anan tare da Hajjon”.
Da ga Hajjo har Abdallah kallonta sukai, amma saita ɗauke kanta tana ɓata fuska danma kar Hajjon tace dole sai taje. Shima har zai sake magana sai kuma ya fasa ya fita kawai.

“Miyasa bazakije can ɗinba? Bayan ƴar uwarki na cike da ɗokin ganinki?”. Hajjo ta faɗa bayan ficewar Abdallah.
Nu’aymah dake ƙoƙarin cire kayan jikinta tace, “Babu komai Hajjo, nafison kawai na zauna da ke kodan himma akan ibadar da mukazoyi, sannan nifa ma ittiqafin zan shiga insha ALLAH”.
Murmusawa Hajjo tayi kawai tana ɗauke kanta batare da ta sake cema Nu’aymah komai ba, itama Nu’aymahn sai ta shige bayi abinta batare data jira amsar hajjon ba.

★★★

“Kuturun ubancan kayyasa! Yanzu wane algungumine mai wannan shirya tafiyar a gidanmu?”. Adawiya daketa faman zagaye ɗakinta ita kaɗai ta faɗa tana cizar laɓe kamar zata hudashi. Ganin babu mai bata amsa ta rarumo waya ta fara neman maman Aaida. Bugu biyu kuwa ta ɗaga. Harta fara tsokanarta Adawiyan ta katseta da faɗin, “Maman Aaida yanzu ba lokacin wasa bane, ko kinsan sister ɗin nan nawa da zata auri Yah Ab da, ta biyo kakarmu sunzo Umrah tare?”.
Da ƙarfi Maman Aaida tace, “Na shiga uku, da gaske dan ALLAH?”. Adawiya da ranta ya ƙara dugunzuma tace, “Wlhy kuwa. Bama zuwan nata bane tashin hankalina Maman Aaida, kinga kuwa yanda Yah Ab duk ya susuce, gashi kakarmu ɗin nan shegen sa idone da ita wlhy”.
“Tab, lallai aiki ya samemu, dan kuwa wlhy mukai sanya to ki tabbatar nanda wata ɗaya ko sati biyu ma mijinku zai koma na mata uku….”
“ALLAH ya kiyaye” Adawiya tai saurin katse Maman Aaida hawaye na ziraro mata a idanu. Takaicin maganganun maman Aaida ya sakata katse kiranma gaba ɗaya tai wurgi da wayar kan gado.
Abdallah dake ƙoƙarin shigowa ɗakin yace, “Lafiyarki kuwa kike wurgi da waya? Kamar ba kuɗi akasa aka saya ba!”. Da sauri tasaka hannu ta share hawayenta, kafin ta nufesa ta rungume da ƙarfi. Saurin tureta yay yana faɗin, “Haba Adawiya, shin wai kina mantawa muna azumi ne? Duk hanyar da zaki raunanama mutum azumi kin santa”.
“Kayi haƙuri Yah Ab, wlhy ɗokin zuwan Nu’aymah ne ya sakani yin hakan”.
“Umyim! Kina ɗokin zuwan natane kika barta tafiya ɗakin da Hajjo zata zauna ta sauka”. Kamar zatai kuka ta kallesa, acan ƙasan ranta kuma tamkar ana babbaka wuta, cikin shagwaɓa tace, “Damafa jira nake kazo na kawo maka ƙararta ALLAH, nayi-nayi tazo mu zauna anan taƙi, wai batason shiga haƙƙinmu”.
Kafeta yay da idanu kamar mai nazarinta, sai kuma ya ɗauke kawai yana ƙaɗa kansa ya fice batare daya bata amsa ba.
Harara ta raka bayansa da shi harya fice, taja gajeren tsaki, ‘Wlhy tunda aka munafunceni sai yarinyarnan ta gwammaci kiɗa da karatu a gidan nan, ni kama ƙaramin haske akan dawowarta ɗakin nan Yah Ab, dan wannan itace babar damar da zan riƙe wajen tarwatsa zuciyarta, saina maidata mahaukaciyar gaske idan da ƙaramin haukane a kan nata mtsoww!! Aikin banza kawai’.

Oho, ita Nu’aymah ma batasan tanayiba, dan bata sake leƙo falonba har lokacin shan ruwa ya ƙarasa, itama Adawiya bata shiga inda sukeba ta maƙale akan shirya kayan shan ruwa takeyi. Duk da kuwa ba ita ta girkaba. Fita Abdallah yay ya musu order ɗin komai daya dace, dan yasan Adawiya bazata iyaba ita kaɗai tunda sunada yawa. Bai kuma kamata asa Nu’aymah shiga kitchen ba daga zuwansu.
Aikin da Adawiya tayi kawai shine shirya abincin a tsakkiyar falo, wanda saida Abdallah ma ya tayata suka tsara komai a inda ya dace.

Koda aka kira salla ruwa da dabino kawai suka ɗanci, sannan suka gabatar da sallar magriba. Daga hajjo har Nu’aymah basu zaƙeba akan abincin, sukai zamansu gefe suna tsumayen tayi daga Adawiya. Itako hankalinta ma baya garesu, tana can tana ƙullama zuciyarta abinda zata aikata a wajen shan ruwan idan an zauna danta cusama Nu’aymah takaici. Shiyyasa ta fara ƙoƙarin shiryama Abdallah nashi tunkafin su shigo.
“A’a Hajjo ya naga baku fara buɗa bakin ba?”. Abdallah da ke ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon sosai ya faɗa idonsa akan Nu’aymah dake danna waya. Wando da rigane marasa nauyi a jikinta, sanin basu kaɗai bane ya sakata ɗoro hijjab a sama wanda yaje mata har gwiwa.
Murmushi hajjo dake kallon Adawiya cike da nazari tayi, sai kuma ta maida kallonta ga Abdallahn tana faɗin, “Ku muke jira mana, dan zaifi daɗin ci ai”. Cike da jin daɗi ya kama hannunta ya sumbata, kafin ya zauna kusa da ita yana gaisheta da mata barka da shan ruwa. Nu’aymah dake a ɗayan gefen Hajjo itama tace, “Barkanku da shan ruwa”. Ahmad dake ƙoƙarin zama kusa da Abdallah ne kawai ya amsa, sai hajjo data ƙwace wayar tana harararta da faɗin, “Sai yanzu kika san damu?”.
“Waini miyasama na biyoki?”. Nu’aymah ta faɗa cikin haushin amshe mata waya tana tura baki cike da shagwaɓa. Hajjo da Ahmad sukai dariya, hajjo tace, “Tambayi kanki mana, ja’ira kawai”.
Adawiya da abun sam bai burgetaba, ta kalli Abdallah da gaba ɗaya hankalinsa akan Nu’aymah yake.  Haushine ya sake turniƙeta, murya a cinkushe tace, “Yah Ab ga abincinka”. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. “Gasu hajjo da suke baƙi baki haɗa musuba sai ni da ko shigowa banyiba……..?”
Katseshi Hajjo tai da faɗin, “Kaga barta, ai abincinma so nake a haɗesa a babban tray mu haɗu tare mu sami ladan juna”.
‘Tabɗi jan’ Adawiya ta faɗa a ranta tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki, a fili kuwa sai ta kafe Abdallah da ido a zatonta ko zaice wani abu. Duk da ya ganta sarai baice uffanba, saima ɗauke kansa yay abinsa.
Hajjo da duk take lura da motsin kowa tace, “Zainabu zuba abincin, ki haɗe da wanda Adawiya ta zuba duk a haɗu kowa ya saka hannunsa”.
Murmushi Nu’aymah tayi a karon farko, ta gyara zamanta tana faɗin, “Angama Hajjaju uwar masu gida, uwar gida ran gidan malam Hashimu ɗan jibiya”.
Sosai Abdallah, Ahmad da Hajjo suka sanya dariya da kirarin na Nu’aymah. Hajjo ta ranƙwasheta akai tana faɗin, “Ja’ira”. Adawiya kam wani baƙin cikine ya kumeta a rai, harta kasa daurewa ta miƙe.
Abdallah yace, “K kuma ina zaki?”. Da ƙyar ta iya haɗiye kukanta tace, “Zan ɗakko abune a kitchen”. Bata jira amsarsa ba tai gaba.
Wani shegen murmushi Hajjo da Nu’aymah suka saki, wanda kowa da manufar nasa.

Hawaye sosai Adawiya tayi a kitchen, sai dai gudun kar wani ya biyota yasata saurin wanke fuskarta ta ɗakko ruwa ta fito.
Koda ta dawo babu wanda ya tanka mata, saima ƙoƙarin kai abinci suke a cikinsu. Yayinda Abdallah duk Motsin Nu’aymah na gunada ne a idonsa. Itama Nu’aymahr dai hankalinta na a kansa. Sai dai tana ƙoƙarin fuskewa ita babu mai ganeta.

A haka dai suka kammala buɗa bakin, yayinda kowa yaci komai dai-dai misalin da bazai cutu ba. Duk da akwai gajiya tattare dasu haka suka rarrafa zuwa massallaci sukai isha’i da asham. Kafin su dawo kowa ya nema makwanci.
Abin mamaki sai ga Adawiya tayi shiri ta tafi kwana ɗakin Abdallah.

(😂ta wajena Adawiya gara ki dage ki samu kan, gaskiya fa, dan naga su o’e anzo saudia da shirin Snatching mijin mutane.😎🙄🚶🏻)

_______________________________
*_NIGERIA_*

“Wai tunanin mi kiketayi ne haka da zurfi Darling? indai akan Yoohan ne na samo mana mafita”.
Da sauri Momy ta juyo tana kallon papa da ke maganar da yarensu, bakinta har ɗan rawa yake wajen tambayarsa wace irin mafita ya samo?.
Sai da ya rungumeta kafin yace, “Mu lallaɓashi ya auri Miracle kawai”. A wani irin zumbur ta miƙe zaune tamkar wadda maciji ya sara. Ta nuna Papa da yatsa tana faɗin, “Kasan mi kake faɗ kuwa Darling? duka-duka shekarar Yoohan ɗin nawa da kake maganar yay aure? Indama son Miracle ɗin yake to da sauƙi, amma kana ganin yanda yake mata a gidan nan ai ko”.
Tsuru papa yay yana kallon yanda matar tasa ke masifa kamar zata haɗiye harshenta, sai da takai ayar zancenta tana wani huci sannan yay saurin jawota jikinsa yana girgiza kansa. “Ki fahimceni mana, idan Yoohan yay aure matarsa zata dinga ɗebe masa kewa a duk lokacin da ya shiga irin wannan damuwar, kum…….”
“Kaga nifa bani da lokacin wannan maganar, ka barni barci nakeji”. Ta faɗa ranta a ɓace da ƙwace jikinta taje gefen gadon ta kwanta. Da kallo kawai ya iya binta har na tsahon lokaci, kafin shima ya kwanta ɗin yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. A cikin ransa kuwa ya ƙudiri aniyar lallaɓata ita da Yoohan ɗin har sai sun amince da ƙudirinsa.

*_WASHE GARI_* safiyar lahadi, tunda safe jama’ar gidan suka shiga hada-hadar shirin fita church, dan papa ma tun da sauran duhun safiya ya fice shi.
Rich daya fito wanka ya kai dubansa ga Yoohan dake zaune kan sofa, ƙafafunsa miƙe akan table, ya jingina bayansa kansa na kallon sama. Duk da idanunsa a lumshe suke ya tabbatar ba barci yake ba.
“Doctor ya kamata ka tashi kai shiri mu shiga church ko? Idan mun fito sai mu ɗan zaga gari danni yau da yamma zan koma Lagos”.
Shiru Yoohan bai motsaba, duk da kuwa sarai yanajin Rich ɗin. Sai da ya ɓata wasu mintuna kafin ya buɗe idanunsa da sukai wani irin kumburowa, fatarsu tayi jaa sosai alamar jin barci tattare da shi, hakama fuskar tayi jajur sosai abin tausayi. Miƙewa yay batare da yayi magana ba, ya wuce toilet yana ɗan ɗingisa ƙafarsa da bata gama sakiba, sai dai hakan kuma sai ya bama tafiyar tasa wani style daban kamar mai tafiyar izza.
Baija dogon lokaciba ya fito ɗaure da towel ruwan gwaiduwar ƙwai. Babu kowa a ɗakin dan Richard ya gama shirinsa ya fice. Ya ƙarasa gaban mirror, shafe jikinsa yay da mai da kayan ƙamshi tamkar yanda ya saba, kafin ya nufi wajen kayansa. Fararen suit ya ɗakko yana ɗan yamutsa fuska da kallonsu. Sai kuma yabar wajen dasu zuwa gaban gado. Tsaf ya shirya a cikin suit ɗin da sukai masifar zama masa a jiki, tare da fiddo surarsa mai jan hankalin mata dama mazan kansu. Necktie ɗin ya ɗauka a hannu tare da jacket ɗin suit ɗin, dan shi kam har yanzu ɗaura tie na masa wahala. Gaban mirror ya sake komawa ya feshe kansa da kalolin designers ɗin turarurrukansa, kafin ya ɗau sarƙa ɗaya a cikin sarƙoƙinsa na Cross da taji zallar diamond tanata ɗaukar idanu ya saka. Ya ɗauki agogo ya ɗaura tare ɗan wani abin hannu na gayu ya ɗaura a ɗayan hannun, ya kuma manna ɗan kunnensa a kunne ɗaya. Yayi ƙyau sosai, duk da kuwa fuskar a turɓune take matuƙa. Amma yanda yau ya gyara kansa da sajensa sai yay ɗas da shi kamar ka suresa ga gudu.

Tun fara sakkowarsa daga benen Mom da Rich, Solomon dake a falon duk suka zuba masa idanu, sake ɗaure fuska yayi yana ƙarasa sakkowa. Saurin tararsa Solomon yay da kofin coffee daketa turiri akan tray, yace, “Good Morning sir”. Kansa kawai ya ɗaga masa yana gyaɗa kai, tare da ɗaukar coffee ɗin ya nufi Mom da ta tsatstsaresa da idanu tun sakkowar tasa, sai dai fuskarta sam babu walwala. Tayi ƙyau sosai abinta tamkar zata gasar sarauniyar ƙyau. Necktie ɗin hannunsa ya miƙa mata batare da yayi magana ba, saima kofin coffee ɗinsa da yakai baki yana curɓa kamar bayaso.
Tsaye ta miƙe, duk da ya fita tsaho, amma da yake tana kan tudun dining ne saita samu damar kaiwa wuyansa cikin sauƙi. Ɗaura masa tie ɗin tayi, tare da amsar jacket ɗin ta koma bayansa. Hannunsa guda ya miƙa mata ta saka masa, ya sake miƙa ɗayan ma ta saka, sannan ta zagayo gabansa tana gyara masa da ƙyau.
Ta ɗan saki murmushi tana masa wani narkakken kallo, kafin takai hannunta saman fuskarsa ta shafa kwantaccen sajensa dayin magana ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa. Ɗanja baya yay yana zame hannunta, murya a cinkushe yace, “Thanks Mom”.
Kafin ta samu damar yin magana ƙannensa dake fitowa cikin nasu gayun suma suka shiga gaishesa ɗaya bayan ɗaya. Hannu kawai yake iya ɗaga musu yana cigaba da shan coffee ɗinsa cike da basarwa.
Ganin yanda Mira ke binsa da wani shu’umin kallone ya sakashi miƙama Solomon kofin duk da bai ƙarasa ba, batare da yayima kowa magana ba ya nufi hanyar fita abinsa cike da takun nutsuwa da ƙasaita sai kace wani jinin mulki.
Dukansu baya suka take masa, yayinda Gebrail yay saurin kaiwa inda yake yana riƙo hannunsa. Batare daya kallesaba yace, “What happend?”. Murmushi Gebrail yayi yana susar kai, cikin ɗan in ina yace, “Brother Yoohan kuɗi nakeso Please”.
Yoohan baice komaiba, ya zare hannunsa daga cikin na Gebrail ɗin, ƙarasawa yay jikin motar da yaga Rich tsaye yana waya. Da sauri ɗaya a cikin Guards ɗinsa ya buɗe masa yana gaishesa. Hannu kawai ya ɗaga mar ya shige. Richard ma shiga yay ta ɗayan gefen, Solomon da driver ma suka shiga. Cike da ɗoki Gebrail da yasan matsalarsa ta yanke ya shiga motarsa shima tare da su Mira da taso bin motar Yoohan ɗin. Sai dai ganin Rich datai tunanin ba a gidan ya kwanaba da, ya sakata haƙura ta shiga ta Gebrail ɗin ita da joy.

Motocin na gama fita a gidan Yoohan ya zaro wayarsa dake cikin aljihu, transfer ɗin kuɗi masu yawa yayma Gebrail tamkar baisan ciwonsu ba, kafin ya ajiye wayar gefensa ya maida kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa.
Har motocin suka tsaya a katafaran church ɗin da papa ke riƙe da shi Yoohan bai motsaba, duk da kuwa Rich na masa bayani ne akan wata harkar business ɗinsu da sukeyi tare.
Katafaren church ne mai girman gaske, wanda akaima gini na ƙawa da ɗaukar hankali, dan a gaba ɗaya gaban church ɗin da idanuna ke iya gani anyisane da zalkar glass. Yayinda akasa ƙaton tambarin Cross da akayisa da golden ɗin abu. Tun a farkon shigowar titin zaka faracin karo da muryar papa dake lecture. Gaba ɗaya titin wajen sun kashesa babu maibi saboda motocin da duk akai parking masu tarin yawa. Securitys ɗin church ɗin da sauri suka shiga bama motsocin su Yoohan ɗin hanya cike da tsantsar girmamawa. Sai da sukai parking a waje na musamman da aka tanada domin motocin nasu dama sannan aka shiga buɗe musu suna fitowa.
Yoohan ne ƙarshen fita, dan sai da ya gama jan ajinsa kafin ya ziro sandarsa ta gayu sannan ya fito gaba ɗayansa. Gebrail da tun a hanya yaga alert yay saurin ƙarasowa ya rungumesa yana godiya. Baice dashi komaiba sai shafa masa baya da yay kaɗan.
Yanda securitys ke basu kariya da tsantsar kulawa sai ka ɗauka dajin sambisa zasu shiga🤥🙄, suna zagaye dasu har ta ƙofar da take ta musamman domin iyalan papan kawai da shi. Tanan suka shiga cikin church ɗin dake a cike maƙil da mabiya kamar zai fashe.
Duk suka zuba musu idanu suna miƙewar girmamawa a garesu cike da sha’awa da ƙauna. Sai da suk suka ɗaga musu hannu banda Yoohan da ko kallon basu ishesa ba sannan suka ƙarasa wajen zamansu na musamman dake a gaba duk suka zauna.
Papa dake a gaban wani glass mai ƙyau da aka ƙawata da golden ga abin magana kusan huɗu a jiki yay murmushi yana ma iyalan nasa barka da zuwa, kafin ya cigaba da zubo bayani cikin kwakwazo da karaɗin da aka san fastoci da shi, ko haɗiyar yawu bayayi😕.
A hankali sai hayaniyar ta fara takurama Yoohan, duk da kuwa tunda ya zauna yana jingine ne da kujera idanunsa a lumshe kamar mai barci. Siririn tsaki yaja yana yamutsa fuska. Ya shafa kunnensa na dama dake manne da Bluetooth yana cizar lip. Sai kuma ya buɗe ido da motsawa zai miƙe Rich yay saurin riƙe masa hannu. Ransa a ɓace ya kallesa, sai dai baice komaiba.
“Please ka daure” Rich ya faɗa cike da marairaicewa dan kar Yoohan ɗin ya bijire. Siririn tsaki ya kuma ja kaɗan ya maida kansa ya sake kwantarwa ya rufe idanu.

Kusan awa guda Yoohan nata sake daurewa duk da kansa ya fara masa wani azababben ciwo. Kiran daya sake shigowa a wayarsa ne a karo na babu a dadi ya sakashi yamutsa fuska, duk kiran da ake masa bai amsa ko guda ɗaya ba, amma yanzu sai yaji buƙatar amsawar. Miƙewa yay zai fice Rich yay saurin sake riƙosa. Nuni yay masa da Bluetooth ɗin kunnensa batare da yayi maganaba. Hakanne ya saka Rich sakinsa yana gyaɗa kai.
Sama-sama ya amsa mutumin dake gaishesa, kafin yay shiru yana sauraren bayaninsa da magiyar da yake masa akan buƙatar mutanen da kimarsu ta wuce ace Yoohan ɗin yaƙi buƙatarsu.
Ajiyar zuciya Yoohan ɗin ya sauke a karon farko, batare da ya amsaba ya yanke kiran kawai. Wayarsa ya ciro yay ɗan typing ya tura abinda shi kaɗai ya sani. Mintuna uku ba’a rufaba saiga reply an naido masa. Buɗewa yay ya gani, batare da yayi maganaba ya maida wayar aljihu yana ɗan dube-dube kamar mai neman wani abu. Sai kuma ya sake zaro wayar ya sake yin wani abun.
Yanzu kam ya kai tsahon mintuna biyar yana jiran reply ɗin kafin a turo masa. Shiru yay yana ɗan kallon wayar kamar mai nazari, kafin ya gyaɗa kansa da nufar inda motocinsu suke da wasu a cikin guards ɗinsa tsaye a wajen.
Batare da yayi maganaba ya miƙama drivernsa hannu da masa nunin ya bashi key. Kamar driver zaiyi magana sai kuma ya haɗiyeta da sauri ganin kallon da Yoohan ɗin ya zuba masa. Saurin bashi key ɗin yayi, shi kuma ya buɗe motar da kansa ya shiga mazaunin driver yay mata key tare da yin reverse ya bar wajen securitys nata risina masa cike da girmamawa………….✍

To ɗan dabe ina zuwa kuma🤥🤐?.

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA… SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply