Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 27


Saran Boye 27
Viral

No. 27

…………Zubewa Yoohan yayi a saman gadon tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa biyu, sai kuma ya ɗan naushi gadon da faɗin, “Noooo!!!”. Da ƙarfi kamar mai magana da wani.
Tashi yay zaune zumbur yana huci, so yake abinda ya faru yabar ransa, amma tamkar ana ƙara kusanto masa da hotonsa ne a zuciya. Da ya rufe ido babu abinda yake gani sai yana kissing ɗin yarinyar da ko sunanta baima sani ba. Miƙewa yay daga gadon ya shiga toilet ɗin dake cikin ɗakin, ko takalman dake ƙafarsa bai cireba balle kuma kaya, ya ƙarasa gaban shower ya tsaya, tare da kai hannu ya murza makunnar da ƙarfi, tamkar itace tai masa laifi.
Shaaa!!! Ruwa ya fara sauka masa bisa gyararren gashinsa yana gangarowa fuska. Lokacin da ya gangara cikin jikinsa ya wani saki sassanyar ajiyar zuwa tare da lumshe idanunsa ya dafe bangon da hannunsa duk biyu. A haka ruwan ya cigaba da sauka a kansa, kafin wani dogon lokaci ya gama jiƙewa sharkaf. Sai da yay kusan mintuna ashirin a haka sannan ya kashe shower ɗin yana sauke numfashi a jajjere, kafin ya ƙarasa saman toilet sit ya zauna yana mai riƙe kansa da hannu biyu….

_______________________

Duk yanda Nu’aymah taso sakewa a sashen Addah ta kasa hakan. Gani take kamar kowa yasan abinda ya faru tsakaninta da Yoohan. Kamar an tsikareta ta miƙe daga zaunen da take kusa da Kubrah. Dukansu da kallo suka bita har suna rige-rigen tambayarta lafiya.
Sai da taɗan saci kallon Addah da tai banza dasu kafin ta amsa musu cike da in-ina. “Um…..u…. Zanje su Aunty Zulfah na jirana”. Bata jira amsar su ba tai wuf ta nufi ficewa da ga falon tamkar zata kifa dan sauri.
Karo suka kusan ci da Malam ƙarami da ke shigowa. Tai saurin komawa da baya tana faɗin, “Yi haƙuri Yaya, bansan ka taho ba”.
Murmushi ya mata da cewa, “Karki damu Aymah. Ashe dama kina nan naje nemanki wajen Umm”. Ɗan kallonsa tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ya sake faɗaɗa murmushin sa, “Dama ba wani abu bane, baƙon da kika ganmu tare a sashen Hajjo ne ya bada barka da salla a baki. Shine naje kai miki na Iske baƙya nan. Amma na bama Umm ta ajiye miki”.
Tunda ya ambaci baƙo gabanta ya sake tsananta faɗuwa. Ta tsaresa da manyan idanunta dake wani mar-mar na rashin gaskiya. Sai kuma ta ɗan juya ta kalli sashen da su Addah suke. Su dukansu hankalinsu na wajen. Sai taji hankalinta ya sake tashi. Tai saurin faɗin, “Ni banaso Yaya”.
Kafin yayi magana ta fice da gudu daga falon. Shi malam ƙarami ma dariya abin nata ya bashi. Hakama su Hajarah. Dan haka suka shiga ƙyalƙyala dariya banda Kubrah da tai shiru tana kallon wani waje daban.
Hajarah ce ta fara farga da yanayin Kubrah, dan haka ta tsagaita da tata dariyar tana faɗin, Aunty Kubrah ALLAH dama nasan ba ciwon kai Nu’aymah keyiba. Inagafa sabon siriki ta samo ma su Addah shine duk take a ruɗan nan”.
Uffan Kubrah batacema Hajarah ba. Sai ma mikewa tai ta bar falon tana wani ɗan murmushin da su duka basu fahimci ma’anarsa ba……

Nidai nace, “Humm”.

“K lafiya? Kika shigoma mutane tamkar wadda aka koro!”. Umm ta faɗa a tsawace tana kallon Nu’aymah data shigo falon a guje.
Duƙar da kai tayi ƙasa tana ƙoƙarin haɗiye kukan da ke son zubo mata. Cikin rawar murya tace  “Umm babu komai fa, zanje toilet ne”. Bata jira amsar kowa ba a cikinsu ta shige ɗakinta da sauri.
Dariya su Aunty Zulfah sukayi, sai dai banda Umm da tabi Nu’aymahn da ido dan sam bata yarda da abinda ta faɗa ba.

Tana shiga toilet ɗin ta maida ƙofar ta rufe harda murza key. Jingina tayi da ƙofar ta fashe da kuka maiban tausayi. A ranta tana faɗin yaya zatai da wannan abin kunya da takaici da mutumin nan ya aikata a gareta? Ita namiji yayma kiss, namijinma kafiri da baya bautama ALLAH. Baisan idan ya saɓama UBANGIJI ba ya nema gafara. Baisan haramci ba baisan halacci ba, balle yasan hukuncinsu. Bakinda bai taɓa ambaton ALLAH ba sai shan giya da zina, bakin dake ambaton wanin ALLAH (Shirka) shine yau akan nata. ‘ALLAH ya isa bazan taɓa yafe makaba’. Ta faɗa a fili tana sake rushewa da kuka. ‘Na shiga uku ni Zainab, ni………’
“Nu’aymah!”. Muryar Umm ta hanata ƙarasawa. Saurin toshe bakinta tayi dan kar Umm taji shashshekar kukanta.
“Nu’aymah wai baƙya jinane?”.
Umm ta sake faɗa tana matsowa jikin bayin.
Da sauri Nu’aymah tai gyaran murya. Kafin ta miƙe da sauri gaban tap ta fara wanke fuskarta, kallo ɗaya taima mirror tasan idan Umm ta ganta a haka akwai matsala, to amma kuma bata da wani ikon ko dabarar yin wanka tunda yanzu nan tayi sa. Towel tasa ta tsane fuskar tata sannan ta buɗe ƙofar a hankali ta fito.
Haɗa ido sukai da Umm da ke a tsaye tana jiran fitowar tata. Tai saurin kauda idanunta zuwa ƙasa da faɗin, “Umm yi haƙuri, ALLAH toilet ne”.
“Toilet ko kuka?”.
Da sauri ta ɗago ta kalli Umm ɗin. Muryarta na rawa tace, “Umm toilet ne ALLAH”.
“Toilet ɗin ki kai ma kuka kenan?”.
Baki taɗan tura gaba, “To Umm gudawa fa ce”.
“Mtsoww! K dai bansan randa zaki bar wannan shashancin ba wlhy. Idan gudawan ne bazaki iya zuwa ki amshi magani ba”.
“Kiyi haƙuri Umm”.
Juyawa Umm tayi ta fice batare data tanka mataba. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya tanabin mahaifiyar tata da kallo. Ta tabbatar yau da tasan mita aikata da saita fasa mata baki. Dan Umm tana da zafi idan aka ƙureta, sam bata ƙaunar halin banza.
Duk da tana buƙatar kaɗaici haka ta daure ta sake gyara fuskarta sannan ta fito falon. Dan bata fatan wani ya gano halin da take ciki. Musamman ma Umm data kasance mace mai saurin fahimta akan rashin gaskiyar yaranta. Ba komai ya jawo hakanba kuwa sai saka musu ido da takeyi a duk motsinsu kwarai da gaske. (Iyaye ya kamata mu kasance haka. muzama kowanne motsin yaranmu nakan idanunmu da zukatanmu kodan gudin yin tufƙa da warwara akan tarbiyyarsu. ALLAH ya kare mana su dai damu baki ɗaya).
Tana zama aunty Rafi’a tace, “Hummm! Aymah ina kika samo wannan turaren mai shegen daɗi haka?”.
Gaban Nu’aymah yay mugun faɗuwa. Ta ɗago da dauri tana kallon aunty Rafi’a. Sai taga har Umm ma ashe kallonta take tamkar yanda su Aunty Zulfah duk suka xuba mata idanu. Ta buɗe baki zatai magana su Nanah suka shigo cikin uhun sallama.
Wata muguwar ajiyar zuciya Nu’aymah ta sauke a ɓoye. Tare da saurin miƙewa zumbur ta nufi su Nanah ta rungume.

Zuwan su Nanah gidan ne ya shashantar da maganar turare. Amma ga Umm sam abin yaƙi barin ranta. Dan sai da tai duk dabarar da uwa ta gari ya dace tayi wajen shaƙar ƙamshin a jikin Nu’aymah. Ta kuma jisa, ta tabbatar duk gidan kuma batasan kowa da wannan ƙamshin ba. Amma sai bataima Nu’aymah maganar ba. Dan tuni su Nanah sun janyeta ma sun fice su da su Amal daga gidan.
____________________

Ya jima zaune matuƙa akan toilet sit kafin ya miƙe ya fara zame jiƙaƙƙun kayan jikinsa. Wanka yayo, ya fito sanye da Bathrobe fara mai ɗan tsaho. Dan ta wuce gwiwarsa kaɗan. Towel ƙarami ya riƙo a hannu ya fito yana goge fuskarsa da sumarsa.
Kallo ɗaya yayma Solomon daya kasa haƙuri ya dawo ɗakin duk da korar da yay masa ya ɗauke kansa. Kan Solo a ƙasa yace, “Kamin afuwa Sir, bazan iya nutsuwa ba bayan kai kana cikin wani hali”.
Yanzun ma uffan baice masa ba. Ya dai gitta ta gabansa ya wuce zuwa gaban kujeru biyu dake a ɗakin. Zama yay cikin ɗaya ya ɗora ƙafafunsa saman table ɗin dake a gabansu tare da naɗe towel ɗin hannunsa saman kansa ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe idanu.
Shi dai Solomon na tsaye yana cigaba da kallonsa cike da damuwa. A can ƙasan ransa kuwa zargine fal ciki akan su baba malam. Gani yake kamar yau rashin bin Yoohan cikin gidan yasa aka cutar da shi……..
“Ina buƙatar coffee”. Ya katsema Solomon tunaninsa cikin yin magana a daƙile.
Da sauri Solo ya dawo hankalinsa. Ya amsa da “Okay sir” yana matsawa inda telephone ɗin ɗakin take yay kira domin yin order ɗin coffee ɗin da Yoohan ya buƙata.
Ba’afi mintuna uku zuwa huɗu ba kuwa sai ga cikin ma’aikatan yay knocking. Solomon ne ya je ya buɗe ya amso. Ya dawo inda Yoohan ɗin ke zaune ido a lumshe ya ajiye tray ɗin ƙasa dan ya ɗaura ƙafarsa akan table ɗin. Saida ya tsiyaya masa, tare da saka sukari ƙwara ɗaya kamar yanda yasan Yoohan na buƙata sannan ya miƙa masa.
“Gashi Sir” ya faɗa da yarensu.
Buɗe ido Yoohan yay a hankali. Sunyi jajur alamar baya cikin nutsuwarsa. Baice komaiba ya amsa tare da yima Solomon alamar yaje. Badan Solo yaso hakanba ya fito yana waigensa. A falo ya maƙale dan bazai iya zuwa ko inaba yabar Yoohan ɗin a haka, kodan gudun ɓacin rai mai tsanani da zai iya fuskanta a gurin madam Chioma da Papa.

Yoohan da baisan Solomon bai fitaba ya fara shan coffee ɗin a hankali zuciyarsa na cigaba da kai kawo akan abubuwa masu yawan gaske. A haka ya shanye ya sake zubama kansa. Yanzu kam ko sugan ma bai sakaba a haka ya sha kayansa. Koda ya gama kuma nan ya cigaba da zama har tsahon lokaci.
Zuwa can kuma tamkar wanda aka mintsina sai ya miƙe, duk da rigar wanka ce a jikinsa bai damu ba, a haka ya buɗe ƙofar ya fice bayan ya zura Slippers. Tsaye yayi yana kallon Solo dake gyangyaɗi a falo, kansa ya ɗan girgiza ya nufi ƙofa batare da yayi magana ba.
Can ya fita harabar hotel ɗin da ko ina ke ƙwanyar da haske, mutane nata kai kawo tamkar ba dare ba. Mafi yawansu mazane dake shigowa da mata. Wasu kuma matan su kaɗai ke shigowa alamar masu jiran nasu suna ciki su. Wasu mazan kuma su kaɗai ne suma, dan wasu matafiyane ba sheɗancin ne ya shigo dasu ba.
Watsar da komai yay dan shi baya matsama kansa shiga hurumin da banasa ba. Can wajen kujerun da aka tanada dan hutawa ya nufa. Babu mutane sosai a wajen, dan haka ya samu ɗaya ya zauna, tare da sake tsunduma cikin abinda ke masa kai kawo a zuciya da ruhi tun ɗazun.
A cikin tunanin nasa ne hankalinsa ya fara karkata ga abinda na kusa da shi ke saurare a wayarsa. Duk da ya saka ƙarar can ƙasa sosai hakan bai hana Yoohan ji ba saboda dare ya fara nisa. Wajen da suke kuma wajene da sam babu hayaniya, dan hotel ɗin dama bana ku bayi bane, na manya ne masu ji da ƴan canji, inda aka ginasa ma kawai ya isa baka amsa.
Lecture ce da ga bakin Sheikh Fantami yake saurara. Kasancewar da turanci ne sai komai yake shiga kunnen Yoohan raɗam. Buɗe idanu yay a hankali ya kai dubansa ga mai sauraren wa’azin. Matashin saurayine tamkarsa, sai dai kallo ɗaya zakai masa kasan kaga ustaz. yayi shiru a wajen tamkar baisan da motsin kowaba yanata sauraren wa’azin sa.
Tsintar kansa yay shima da sake nutsuwa sosai yana saurare. ya shagala sosai da sauraren wa’azin nan mutumin ya miƙe, batare da yayi tunanin wani na tayasa ji ba ya kashe tare da barin wajen ya koma ciki dan ya kwanta ya huta.
Ko kaɗan Yoohan baiso hakan ba, dan anzo wata gaɓa da duk mai sauraren wa’azin zai so jin ƙarshensa. Bin mutumin yayi da kallo harya ɓacema ganinsa. Ji yay tamkar ya bisa ya roƙe ya basa ya ƙarasa ji. Dan jikinsa wani irin tsuma ya keyi, gashi duk ya mimmiƙe masa. Komai ya sake birkice masa, duk yanda yake tunanin tasirin mafarkinsa da maganganun Nu’aymah sai lecture ɗin nan daya saurara ta sake faɗaɗa rauninsa zuwa ƙololuwar rikicewar tunani da gushewar wani duhu daya fahimci ya jima a cikinsa. Tunanin bin bayan mutumin ya sakashi kallon agogon hannunsa, ya ɗan waro idanu waje dan bai ankaraba sai yaga agogo ya nuna ƙarfe ɗaya saura.
Sake maida idanunsa yay ya lumshe tamkar baiga mi agogon ya nuna masa ba. Sai ajiyar zuciya daya dinga saukewa a jajjere.
A haka Solomon daya sake shiga ɗakin nemansa bai gansaba ya fito a rikice nemansa ya iske sa. Duk da wayar dake a hannunsa da alama ta nuna wanine akan layin sai da ya sauke ajiyar zuciya .
“Ashe kana anan sir?!”. Solo yay maganar yana sake sauke numfashin ruɗanin da yake ciki na rashin ganin nasa da farko.
Yoohan da tun isowar Solomon wajen yana kallonsa ta ƙasan ido ya buɗe idanunsa ya watsa masa wani shegen kallo mai cike da gargaɗi…..
“I’m sorry sir. Madam ce”.
Kafesa da ido sosai yayi, duk da kuwa yasan Momy Solomon ɗin ke nufi. Bai amshi wayarba, bai kumace komaiba ya miƙe yabar wajen. Solo dake binsa da kallo yay saurin bin bayansa hankali a tashe.
Koda suka koma ɗakin bai gajiya ba sai da ya sake maimaita masa maganar amsar wayar sannan ya miƙa masa hannu alamar ya bashi. Yana amsar wayar ya nunama Solo toilet da hannu.
Duk da bai fahimcesa ba haka ya nufi toilet ɗin dan ya duba. Shi kuma ya ɗora wayar saman kunnensa muryarsa mai amo da kauri ɗin nan ta fara fidda sauti. “Hello Mom”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi madam Chioma ta sauke da ga can, kafin cikin ƙasa da murya sosai tace, “My boy!”.
“Humyim”.
Ya faɗa a hankali cikin maƙoshi.
Murmushi mai sauti ta sake da ga can tana mai ƙanƙame filo a ƙirjinta da lumshe idanu. Cikin sake narke murya tace, “Mike damunka?”.
Shiru yay na wasu sakanni. kafin ya furzar da ɗan huci yana sauke idanunsa da ga table ɗin. “Ba komai Mom, bakiyi barci ba?”.
Sake narke murya tayi kamar zatai kuka. Tace, “My Boy tunaninka ya hanani barci. Kai kasan muna tsananin buƙatar ganinka tare da mu ni da papan ku dama ƙannenka gaba ɗaya. Amma duk da ɗokin dawowarka da mukeyi wannan karon, bayan tsahon sati biyu da ka ɗauka bakanan shine kai wucewarka wani gari batare da ka fara sauka Abuja mun ganka ba”.
“Am so sorry Mom”. Ya faɗa a taƙaice kawai.
Matse filo ta sakeyi sosai a ƙirjinta. Dan ji take jininta na wani masifar yamutsawa tamkar zaiyi tsartuwa ya fito. Kafin ta samu damar sake magana ta sake tsinkayar muryar Yoohan na faɗin, “Mom goodnight, zan kwanta”. Ƙitt ya yanke wayar.
“My b……” tai yunƙurin faɗa sai kuma taji ƙitt. Da sauri ta ciro wayar daga kunnenta ta kalla. A take fuskarta tai masifar tsukewa hawaye na taruwa mata cikin idanu. Filo ta sake jawowa zata ƙanƙame papa ya shigo ɗakin nata.
“Wai lafiya kika maƙale anan bayan inata jiranki a can?”.
Wani irin takaici da baƙin ciki ne ya kumeta a zuciya. Ta ɗan hararesa a kaikaice tana maijin wani irin zafinsa da ɗaci a ranta. Amma a zahiri sai tai ɗan murmushi da cewa, “Ka bari kawai. Solomon ne ya kirani wai yaga kamar John a damuwa. Shine fa nasa ya haɗamu dan wayoyinsa duk basa tafiya. Amma yaron nan sai ya amsa ni sama-sama. daga ƙarshe ma ya yanke wayar”.
Ƴar dariya Papa dake hawowa gadon yayi. ya jata jikinsa ya rungume yana faɗin, “Kema kinsan halin yaronki ai. Minene zai ɓata miki rai a ciki. Maybe yana buƙatar hutawa ne shiyyasa ya kashe”.
Kafin ta samu damar basa amsa ya haɗe bakinsu waje guda. Duk yanda taso ta ƙwace kanta ya hanata wannan damar. Dan dama inhar ALLAH ya bashi sa’a a kanta baya wasa da damarsa. Saboda duk lokacin da zai buƙaci kasancewa da ita sai sunsha uwar rigima, wani lokacinma ƙarfi yake nuna mata ya samu nutsuwa. Yakan rasa miyasa take masa hakan tunda shi dai yasan auren soyayysa sukayi. ada can kuma sam bata masa wannan halin sai a shekarun nan da bazasu gaza goma zuwa sha ɗaya ba.
To komadai minene yau ya moreta da ƙyau. Daga ƙarshe ya koma lallashinta sabida kuka da take masa tamkar wanda yay mata fyaɗe. Da ƙyar ya samu kuwa tai shiru sukai barci duk da shi ya rigatayi kafin itama ya sacetan.

Yoohan kam koda ya yanke wayar sai yay jifa da ita saman kujerar dake gefensa. ya sake maida kansa jikin kujerar ya lumshe idanunsa tamkar ɗazun.
A haka Solomon da ya kammala tattare kayan da Yoohan ɗin ya baza a toilet ya fito ya samesa. Baiyi magana ba, ya lallaɓa kawai ya ɗauki wayarsa ya fice da ga ɗakin. Duk da Yoohan najinsa bai motsaba, haka ya cigaba da zama a wajen har tsahon lokacin da shima kansa baisan ya kai ba, dan barci ne mai nauyi ya kwashesa a wajen, tare da faɗawa cikin nannauyan mafarki maiban tsoro da al’ajabi a garesa.
Gabannin asuba ya farka a firgice, da ƙyar ya iya motsa wuyansa da ya ƙage, cikin dauriya da jarumta ya shiga jujjuyasa yana matse fuska saboda zafi. Sai da yaji ya ɗan sake masa sannan ya miƙe tsaye yana sauke tagwayen ajiyar zuya. Duk da a zuciyarsa yayi mamakin barcin da yay a zaune na kusan awa huɗu sai baiyi magana ba ya taka a hankali zuwa gaban Window. Idanu ya rufe zai fara addu’a kamar yanda sukeyi a addininsu sai kuma yay saurin buɗewa. Hannu ya saka ya buɗe Window ɗin. Sassanyar iskar asubahi ta feso masa, tare da ƙwala kiran sallar farko da ga wani massallaci da alamu suka nuna yana gab da hotel ɗine ko kuma a cikin hotel ɗinma yake . Wani wawan numfashi ya sauke tare da lumshe idanunsa. Haka kawai sai ya tsinci kansa a wani irin nishaɗa na musamman…………..✍

 

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply