Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 3


Saran Boye 3
Viral

No. 3

……………Sama-sama takejin motsin mutane na matsota, sai dai bata fahimtar maganar da sukeyi balle ta ɗauki muryar kowa. Ta dafe kanta dake tsananin juya mata tare da jingina jikinta da bangon daya raba gidan nasu da massallaci. A hakanma dai bata tsiraba, garin cigaba da mata hajijiya yakeyi. Tai ƙasa zata zame ta faɗi aka riƙota. Ƙoƙarin buɗe ido take taga wanene? amma ta kasa saboda nauyin da sukai mata, haka ta sake jiki ga koma wanene ya riƙeta sosai, kafin ya fara janta suna takawa a tare batare da tasan ina suka dosa ba.
Tabbas taji an sakata a mota an kwantar, amma daga haka bata sake sanin komai dake faruwaba a duniyar, dan barci mai nauyin gaske yayi awan gaba da ita…….

★★

A ɓangaren Abdallah kam yata jiran Nu’aymah ta buɗe data amma sai yaji shiru, sai kusan 12 yaga tazo online ɗin, yay mata magana sai dai ta buɗe saƙon amma bata amsashi ba. Hakan yaso sosa ransa, amma kuma daya tuna ƙuruciya na bala’in ɗawainiya da Nu’aymah sai ya watsar da abin yay kwanciyarsa, a cewarsa ai daga dai gone idan ALLAH ya kaimu duk wani zagaye-zagaye ya ƙare kuma, tunda ta zama tasa. Da wannan tunanin yay barcinsa batare da ya sake bi takan wayarba ma.

______________________________

A firgice ta farka jikinta jiƙe sharkaf da gumi. Baba malam dake saman abin salla ya kalleta da mamaki, sai kuma ya ajiye Al-Qur’anin hannunsa ya miƙe zuwa gareta. Zama yay kusa da ita ya rungumeta dan ya kula sam bata cikin hayyacinta, da alama kuma wani mafarkin tayi mara daɗi. Sai da sukaja kusan mintuna huɗu a haka ya tabbatar numfashinta ya dawo dai-dai sannan ya ɗagota ya bata ruwa ta sha. Sai da tasha kamar rabi ta miƙa masa sauran tana sauke ajiyar zuciya. “Jannat! lafiya kuwa?”. Ya faɗa yana share mata gumin goshinta.
Umm taɗan dafe kanta tana kallon mijin nata, “Abban Nu’aymah mafarki nayi wlhy, kuma akan Nu’aymah ne. Inaga bara naje na dubata a ɗakinsu” tai maganar tana ƙoƙarin sauka ƙasa.
Saurin riƙota yay da faɗin, “Ah ah Jannat”. Kallonsa tai tamkar zata fasa kuka, muryarta a sanyaye tace, “Inaji a jikina Nu’aymah tana cikin damuwa  Abbansu”. Murmushi yayi daɗan girgiza kansa. ya kamata ya maida ya kwantar tare da duƙawa ya sumbaci goshinta. “Nasan maganganunta na ɗazun da kika saka a ranki yasa kikejin kamar bata da lafiya, ki kwantar da hankalinki Jannat, ƙuruciyace kawai ke ɗawainiya da Nu’aymah, idan bamu ƙarfafata ba karmu yarda taga gazawarmu muma, kiyi haƙuri kimata addu’a kinji”.
Kanta ta ɗaga masa tana haɗiye kukan da ya cika mata idanu, sai kuma tai ɗan murmushi domin ƙoƙarin danne abinda ke azalzalar ranta har yanzun. Kanta ya cigaba da shafawa a hankali da tofa mata addu’a har barci ya sake kwasheta. Ya sauke numfashi a hankali da sake sumbatar goshinta sannan ya miƙe ya koma inda yake da.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

____________________________

WASHE GARI

Tun kiran sallar farko wasu daga jama’ar gidan da makusantansu suka tashi aka fara ƙaƙainiyar ɗaura abinci. Hajjo data kwana da haushin Nu’aymah da batazo kirantaba ta nufi sashensu Nu’aymahn tana faɗa akan yau sai taci ƙaniyarta duk da ranar aurenta ce.
Masu kai kawon fita can waje inda aka ɗaura girki sunata gaisheta, amma amsawa take sama-sam dan a ƙule take, tana nufar ɗakinsu Nu’aymah. Babu wanda ya tashi a cikinsu, dan mafi yawansu basuyi barici da wuriba, Hajjo ta kunna fitilar ɗakin tana kiran sunan Nu’aymah. “K Zainabu! Zainabu kina inane wai?”.
Amal ce ta fara farkawa saboda bata da nauyin barci sam, ta tashi zaune da ƙyar tana murje idanunta da faɗin, “Kai Hajjo! Kinzo mu kin tadamu da kwakwazonki wlhy”. “Ubanki Lurwanu ne ke kwakazo, mara kunyar banza”. Tura baki Amal tai tana komawa ta kwanta dan taji haushi Hajjo ta faɗi sunan Abbansu.
“K ni tashi dan gidanku ki faɗamin ina Zainabu take?”.
“Ba tana sashenki ba” Amal ta faɗa tana juya ma Hajjo Baya. “K Safiya banson lalata, dan gidanku tana sashena zanzo nan nemanta ne?”.
“ALLAH Hajjo tana sashenki, bayan ta dawo muka faɗa mata kina nemanta shine ta tafi can”. Nanah data tashi yanzu itama ta faɗa cikin muryar barci.
Hajjo tace, “To sai dai idan tana ɗakin uwarta ko kuma wajen Fauza. Dan nidai ban gantaba, Adawiya ce kawai ta kwana a ɗakina”. Nanah tace, “To sai dai idan tana sashen Addah, dan ɗakin Umm su Mom ne suka kwana, nasan kuma Nu’aymah bazataje cikinsu ta kwanta ba Hajjo”.
“To bara na dubata wajen Fauzan, kuma saiku tashi kuyi salla tunda lokaci yayi”. “To” kawai Nanah tace. Amal kuwa bata sake maganaba har Hajjo ta fita.

Hajjo na fita Umm na shigowa, tadasu ta shiga yi dan su Nanah ma komawa sukai suka kwanta ganin Hajjo ta fita. Sai raba idanu Umm keyi a tsakaninsu nason ganin Nu’aymah, sai dai sam babu ita a cikinsu. Kafin ta samu damar tambaya Hajjo ta sake shigowa Addah biye da ita a baya.
Cikin girmamawa Umm ta rissina tana gaida Hajjo. A taƙaice ta amsa mata da tambayarta ko Nu’aymah a ɗakinta ta kwana ne?. Gaban Umm yay masifar faɗuwa, ta girgiza kanta da haɗiye yawu da ƙyar. “A’a Hajjo ba can ta kwanaba”.
“Yau mun shiga uku”. Cewar Addah tana ida shigowa ɗakin sosai. “Ku batare kuka kwana da Nu’aymahr ba ne wai?”.
Yusrah tace, “A’a Addah, batare muka kwana da itaba, bayan kin haɗa mata ruwan turare kin fita suka shigo ita da Adawiya, to na faɗa mata dai ga ruwa can kin haɗa mata ta shiga ta amsa da to. Sai dai tana shiga bata jimaba ta fito ta fice daga nan, ni dai har barci ya ɗaukeni bata dawo ba, kuma kusan nice ƙarshen barci”.
Tashin hankaline ƙarara ya bayyana a fuskar Umm dasu Addah, basu tsaya jan zancenba suka fito daga ɗakin domin neman Nu’aymah a sauran sassan gidan ko taje wani ɓangaren ta kwana.

Ɓangaren Momy mahaifiyar Abdallah suka fara shiga tace rabonta da Nu’aymah tun a wajen Walima, amma bara a duba kotazo ta shiga ɗakin su Amal bata saniba. Sun duba ɗakinsu Amal babu kowa sai ƙannen Amal ɗin biyu dake barci. Sauran ɗakunan kuma duk akwai baƙi da wahala ace ta shiga can, amma duk da haka sai da suka shishshiga suma. Amma babu ko mai alamarta.
Sun koma sashen Abba Musbahu nanma dai matarsa Ammi da Ummah sunce basuga Nu’aymah ba, an kuma shiga ɗakin su Yusrah da ƴammatan sashen yayun su Nu’aymahr nanma babu ita, sai su kaɗaine da sauran ƴammata sa’anninsu na gidan da baƙi. Sake dawowa sukai Sashen Addah aka duba ko ina nanma dai babu ita, suka koma sashen Hajjo nanma haka. Zuwa yanzu kam hankalin kowa ya fara tashi, dan ko sallar Asuba wasu sun kasa samun nutsuwar yinta.
Duk da ba’a tunaninta a sashen samarin gidan haka dai aka shiga canma ko za’a dace. amma kuma bata nan. Yanzu kam dai kowa ya tabbatar Nu’aymah bata gidan, samarin gidan dasu Baba malam duk sun dawo massallaci suma an haɗu anata taraddadi, sai sake tambayar su Yusrah da akasan suna tare akeyi da Adawiya data dage take rusar kuka tamkar ranta zai fita.
Gari ya waye tangaran, waɗanda basuyi sallaba suka samu sukaje suka yiyyyi batare da hankalinsu na tare da suba. Umm kam tama kasa magana sai ajiyar zuciya da taje faman sauke a jajjere. Shi kansa Baba Malam binsu kawai yake da kallo. Hajjo tuni ta fara kuka itakam. Ango Abdallah kam nasa tashin hankalin ai ba’ama magana, danshi ya dage sai sake bin ɗakunan gidan yake lungu da saƙo yana dubawa.

Kamar wasa saiga ƙarfe 11am ta buga babu Nu’aymah babu mai kama da ita, saima cin karo da akayi da takarda a jikin Windown ɗakinsu an ajiye. Sai kayanta ƙwara huɗu da alamu suka nuna jehosu akayi ta Windown maybe.
Nanah ce taga takardan, dan haka ta nufi inda su Baba malam ke tsaye da sauran ƴan uwansa ta miƙa musu da faɗa musu inda ta gani. Abban Adawiya ne ya amsa takardan daga hannun Nanah, ya buɗe yana gyara tsayuwarsa. Duk idanu su Baba malam suka zuba masa da ƙaguwar sonjin minene a ciki.

Assalamu alaikum iyayena.

Kuyi haƙuri da abinda zaku wayi gari da shi daga taskar kuskurena, wlhy yanzu bana son Yah Abdallah akwai wanda zuciyata keso. Nasan babu wanda zan faɗamawa a cikinku ya fahimceni balle akai ga yarda, amma wlhy ina masifar son Ameer fiye da yanda kuke zato da tsammani. Banason na wahalar daku wajen ɗauramin aure da Yah Abdallah nazo kuma na zama sanadin ɓata zuminci da aka gina tunkan samuwarmu daga baya, shiyyasa na zaɓi bin Ameer mu gudu, shi kuma ku aura masa wata a cikin ƴan uwana. Na muku alƙawarin idan komai ya lafa zan dawo gareku ku ɗaura mani aure da masoyina Ameer. Ina fatan bazakuyi fushi dani ba dan ALLAH 🙏🏻😭.
Na barku lafiya.
Daga ɗiyarku Zainab Sooraj Hashim (Nu’aymah).

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

____________________________

Tsit wajen yayi babu wanda ya iya ko ƙwaƙwaran motsi, Baba malam sai faman kaɗa kai yake kawai zuciyarsa na kaikawo.
Hajjo ce ta ƙaraso wajen ganinsu cirko-cirko. “Lafiya? Na ganku cirko-cirko? Ko anji labarin inda take ne?”.
Duk kasa bata amsa sukayi, hakan yasa ranta ɓaci ta daka musu tsawa. “Wai kuna cikin hankalinku kuwa? Ina magana kunmin shiru kai ɗan Malam” ta ƙare maganar idonta akan Baba Malam (Abban Nu’aymah) dan bata faɗar sunansa saboda shine na fari, sai dai tace ɗan Malam.
“Kiyi haƙuri Innah, da kanta ta gudu”. “Ban gane da kanta ta gudu ba? Kana haukane?”. Kasa amsa mata yayi, dan shi kaɗai yasan kalar tashin hankalin da yake ciki a halin yanzun.
Abba Musbahu ne yace, “Innah inaga muje ciki, wannan ba maganar nan baceba”.  Zata sake magana ya kama hannunta suka nufi sashenta tacan baya inda falon mahaifinsu yake. Bin bayansu su Abban Abdallah sukayi, Baba Malam dai bai iya motsawa ba har tsahon wasu mintuna kafin ya bisu.

Bayan haɗuwar duk wanda ya kamata a falon, Abba Musbahu ya sake maimaita abinda ke a rubuce a takarda, wadda Nu’aymah ta ajiye kamar yanda kowa yaji.
“Kai wannan zancen ban yarda da shiba, ina Zainabu taga wayon wani yin wannan iya shegen? Wanene ma Amiru yake ko uwarwa? Tunda muke a gidan nan waya taɓa ganin Zainabu da saurayi ma?”. Hajjo tai magana ranta a ɓace.
Shiru falon yayi, dan kowa yasan maganar Hajjo gaskiyace, babu wanda zaice ya taɓa ganin Nu’aymah da saurayi bayan Abdallah, dan Nu’aymah yarinyace mai shegen tsiwa da rashin tsoro, ko cewa akai ana sonta kai tsaye take faɗin an mata miji a gidansu. Bama ta yarda saurayi yay zuwa biyu wajenta……..
“Ina magana kowa yayi shiru, wlhy ni dai ban yardaba, sai dai idan wani munafukine ya sacemin jikata”. Hajjo ta faɗa tana fashewa da kuka.
Baba Malam ne ya kalli Hajjon zuciyarsa na masa zogi, yace, “Innah karki saurin kareta, kinsanfa yaran yanzun ka haifesune amma baka haifi halinsu ba, mudai fara bincikar ƴan uwanta ƙila wani acikinsu yasan Ameer ɗin”.
Girgiza kai Abdallah yayi shima cike da damuwa, “Baba ALLAH koni ban yarda wannan takardar Nu’aymah ce ta rubutata ba, mu dai bincika gaskiya”.
Baba Malam yace, “Abdallah batun ba ita ta rubutaba kam bazai yuwuba, dan wannan rubutun natane, kuma da bakinta a jiya da daddare ta samemu da batun ita a fasa wannan aure ta fasa, bayan mun lallasheta ni da mahaifiyarta ta tafi sai gashi ta sake dawowa daga baya, sannan muna tare da Rudwan, sai dai nasan ganina tare da shi yasa batace komaiba ta gaidasa ta fita. Kaga kenan a lokacin ta silale tabar gidan?”.
Addah tai saurin faɗin, “A’a dan ALLAH Yaya karmu yanke hukunci, mudai bincika ɗin ta bakin Abdallah”.
“Humm” kawai Baba malam ya faɗa zuciyarsa na ƙuna, dukda shima dai wani gefe na zuciyarsa nata masa wasiwasi akan al’amarin.

Yaran gidan duk aka tattaro, sa’anninta su Amal da yayunsu mata harma da ƙannensu mazan da matan. Ɗaya bayan ɗaya aka tambayesu ko sunsan Nu’aymah nada wani saurayi?.
Mafi yawancinsu sunce basu saniba, sai ƙalilan da sukace sun taɓa ganinta kusan sau huɗu da wani saurayi baƙi. Sai dai takance Yah Abdallah ne yake aikosa wajenta.
Da mamaki Abdallah yace, “Ni kuma? Kai gaskiya a’a. Wlhy tunda nake ban taɓa aiko wani wajen Nu’aymah ba sai Ahmad kawai, gashi nan kuma zaune tare damu. danni ko abokaina da yawansu basusan Nu’aymah a ido ba”.
Sosai abin ya sake ɗaure kan kowa a wajen. Adawiya dake sharɓar kuka tace, “Tabbas akwai wani Ameer dake zuwa wajenta, amma acewarsa shiɗin abokin Yah Ab ne, kuma ko jiyama ai yazo wajen walima”.
Duk kallonta sukai. Abdallah yay saurin faɗin, “Wlhy kamar yanda na faɗa ban taɓa aiko kowa wajen Nu’aymah ba, amma k Adawiya zaki iya ganesa ne?”.
Kanta ta ɗaga musu tana sheshshekar kuka.

Hajjo tace, “Nifa gaskiya har yanzu ban yardaba sai naji ta bakin Zainabu, ko naga wata shaida da zata tabbatarmin da cewar guduwa tai da kanta. Kowafa yasan yanda Zainabu keson Abdallahi a gidan nan tunma bata san kantaba, bata tashi nuna mana bata sonshiba sai daren da za’a ɗaura mata aure da shi. Waye ya kawo wannan takardar? A ina kuma ya ganta?”.
Nanah tace, “Hajjo nice na kawo, abayan Windown ɗakinsu na gani an ajiye, kuma harda kayantama a ƙasa”.
“Muje na gani”. Cewar Hajjo tana miƙewa. Sauranma duk tashi sukai suka bita. Kamar yanda Amal ta faɗa haka suka taras, hardama ƙarfen zif ɗin akwati da alamu ya nuna ɓallewa yay wajen rufewa ko buɗewa.
Maigadin gidan baba malam yasa aka kira masa, aka tambayesa ko yaga fitar Nu’aymah a gidan?. Yace shikam bai ganiba, dan tun sha ɗaya da kwata ya rufe gate ma, kuma babu wanda ya sake shiga da fita.
Omar ne ya bada shawarar a duba ta ƙaramin gate na massallaci to. Babu musu akabi shawararsa, da yake yau da asuba ta babban gate duk su baba malam suka fita massallaci sai ga sayin takalma an gani dana akwati. Ƙaramin sayi na mace, sai babba da alama ta nuna takalman mazane, sai sayin jan akwati dake biye da sayin takalman har wajen massallaci, sai dai kasancewar akwai kwalta a titin layin sai ba’aga inda sayin ya tsaya ko ya nufa ba.
Sun dawo cikin gida ana taraddadai saiga wani yaro riƙe da wayar Nu’aymah acewarsa cikin filawoyin massallaci ya gani.
Amsar wayar Abba Musbahu yayi aka hau dubawa bayan anba Adawiya ta cire lock ɗin dan ita kaɗai ta sani. Ana buɗewa a kan WhatsApp aka samu wayarma, cikin kuma inbox ɗin wani datai saving da suna (Sweet Ameer). Scrolling saƙwanin Abba Musbahu yayi ya koma har can farko ya fara karantawa.
Gaba ɗaya hirarrakine tsakanin Nu’aymah da Ameer kuma ta soyayya harma da alƙawarin auren juna kota halin ƙaƙa. Har zuwa saƙon ƙarshe-ƙarshe da duk ya zam na ƙulla yanda zasu gudu ita da shi.
Zuwa yanzunkan kowa jikinsa yayi sanyi, Umm da baba malam sai faman haɗiyar zuciya suke na ɓacin rai, duk da zuciyar Umm sam taƙi gaskata gaskiyar wannan al’amari, dan tafi kowa sanin wacece ɗiyar tata da halayyarta harma da tarbiyyar data bata. Babu abinda Nu’aymah ke ɓoye mata a rayuwa, dai-dai da hira idan tayi ita da Abdallah saita sameta har ɗaki ta bata labari, daga ƙarshe-ƙarshen nan nema take ƙwaɓarta dan kartaje bayan sunyi aure tace zata cigaba dayin hakan. Abinda ya tsoratata a zancen shine sunan Ameer, dan lallai kusan sau huɗu Nu’aymah na kawo abu tace Yah Abdallah ya aiko mata ta hannun abokinsa Ameer, kuma gaba ɗaya saƙwanin har gida yake zuwa ya sameta ya bata. To gashi kuma shi Abdallah yace baida abokima Ameer ɗin balle ya aikosa wajenta. ‘Innalillahi wa’inna ilairraji’un. Mike shirin faruwa da ɗiyarta ne haka? Ya ALLAH ka bayyana abinda ke ɓoye akan wannan al’amari dai cikin sauƙi’. Wannan sambatun Umm keta famanyi a cikin ranta zuciyarta na mata zafi da ɗaci. Yayinda ɓacin ran da take gani shimfiɗe a fuskar mijinta ke sake tada mata hankali.

A yanzu kowa ya yarda Nu’aymah guduwa tayi, sai dai Hajjo dai bata daina faɗin cewar tana wasiwasiba, dan da cataima sai dai idan Ameer wani abu yayma Nu’aymah harta bishi. Babu wanda yabi takan zancenta dan suna ganin akwai ruɗun tsufa tattare da ita.
Ana cikin wannan taraddadi Abdallah yaci karo da saƙon Nu’aymah a wayarsa wanda baisan da shiba. Danshi tunda yay mata magana yaga bata bashi amsaba ya jiya wayar bai sake bi takantaba, tunda da safe kuma an tashi da tashin hankalin rashintane.

Assalamu alika.

“Yah Ab kayi haƙuri karkaga ban maka adalciba, kasan shi so tsuntsune, gobe ya tashi kan wannan ne ya koma kan wancan. Tabbas na soka a baya kamar babu wasu maza a duniya sai kai kaɗai. Kaima kasan akwai ƙuruciya a kaina a lokacin, shiyyasa sam na kasance bansan Zaɓin daya dace dani. Yanzu kam idanuna sun buɗe ras, zuciyata ta samo zaɓinta. Nasan kozan shekara faɗama iyayenmu bana sonka yanzu bazasu yardaba, bakuma zasu fahimceniba sai sun aura min kai, shiyyasa na zaɓi guduwa, idan komai ya lafa saina dawo a auramin zaɓina. Kaima dan ALLAH ka nema dai-dai kai ka aura kaji. Na barka lafiya Yayana, ina fatan bazaka zauna jirana ba, kuma bazakayi fushiba.

Ƙanwarka Nu’aymah Sooraj Hashim.

Cikin matsanancin fushi Abdallah yay wurgi da wayar hawaye na sulalo masa saman kumatu masu masifar zafi, jikinsa sai rawa yake na ɓacin rai. Dama shi haka yake bai iya fushi ba.
Duk kansa samarin sukayi suna tambayar lafiya?. Kansa ya dafe yana cigaba da kukansa kamar wani yaro ƙarami. yace, “Wlhy ina sonta, amma miyasa Nu’aymah zatamin haka? Minene aibuna dan ina ƙaunarta. Wlhy bazan iya auren kowaba sai ita”.
A tsawace Baba malam ya miƙe yana faɗin, “Dole ne kuwa ka auri watanta a yau ɗin nan Abdallah, ita bata isa kunyatamu ba, bayan mun tara mutane. Inaso daga yau, daga yanzu ka manta da Nu’aymah a cikin zuciyarka har abada kamar yanda nima na manta da ita matsayin ɗiyar cikina”.
Cike da tashin hankali kowa yake kallonsa a falon, dan kowa yasan dama Baba malam yanada zuciya, sannan kaifi ɗaya ne shi, idan yace A dolene A ɗin za’abi, idan yace A’a shima dolene abi…………✍

Wannanfa shi ake kira da gaba kura baya sayaƙi😥. Nu’aymah kizo ki bamu gaskiya batu ko masan ina matsalar take ne?.😭

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

 

*_Typing📲_*

*_SARAN ƁOYE!!_*

 

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

Free page😋

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply