Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 32


Saran Boye 32
Viral

No. 32

…………Tun isowarsu asibitin aka fara bama Nu’aymah dake a sume taimakon gaggawa. Sai dai harsu baba malam suka isa asibitin bata farfaɗo ba. Hakan sai ya sake ɗaga hankalinsu. musamman ma Hajjo dake ta faman sharɓar hawaye. Cike da kulawa baba malam ya zauna kusa da ita duk da kunyar ɗan fari dake tsakaninsu. Murya a tausashe da nuna ɗunbin kulawa da ladabi ya fara lallashinta da faɗa mata kalamai masu taushi da nutsuwa irin na masu ilimi. Ya nuna mata koda rasa Nu’aymah sukayi su zama masu haƙuri da godema ALLAH. Dan lokacin da ya basu ita baiyi shawara da suba. A yansu kuwa idan ya karɓeta ya fisu bukatarta ne.
Haka ya cigaba da mata nasiha harta samu nutsuwa tai shiru. Abba Musbahu yazo gabanta ya durƙusa tare da saka handkherchief ya share mata hawayen.
Ana haka Doctor ya fito daga ɗakin da aka sanya Nu’aymahn. Ya buƙaci ganin ɗaya daga cikinsu cikin nuna girmamawa a garesu. Abban Abdallah da Abban su Adawiya ne suka bisa office. Dan baba malam ya nuna kawaicin nasa da ya saba kamar ko yaushe. Amma zuciyarsa cike take da tsoro da rauni. Yana ta dai ƙoƙarin danneta ne da ambaton ALLAH wajen ƙarfafa imaninsa.

A office ɗin likita kuwa ya nutsu ne wajen rubuce-rubuce a wata takarda kafin ya maida hankalinsa gasu Abbah.
“ALLAH ya gafarta malam zan fara da muku albishir ɗin farfaɗowarta. Sai dai kuma kamar yanda kuka sani raunin dake a cikin ƙwaƙwalwarta shine ya motsa mata. Kuma gaskiya a bincikenmu yarinyarnan tana matuƙar buƙatar son ganin babban likita. Idan ba hakaba a koda yaushe zata iya fuskantar gogewar komai na ƙwaƙwalwar ta. saboda tana ƙara girma ciwon na daɗa faɗi. Musamman ma daya kasance kamar tana sakama kanta abubuwa masu nauyi a cikin rai. A duk kuma lokacin data shiga ƙunci ciwon na mata kuɗa a cikin kanta, ba dan ma tana samun kulawa da kuma addu’oi ba da gaskiya bana zaton yarinyarnan zata kai wannan shekarun batare data tsinci kanta a ciwon hauka ba. Duk da komai na ALLAH ne, babu wani bawa daya isa canja ƙaddarar wani bawa daga yanda tazo a littafinsa. Amma a wannan karon ayi himmar sadata da likitan daya dace da matsalarta, munan taimako kawai muke bata na dakatar da raɗaɗin a gareta a lokacin daya taso. Amma matsalarta sake hauhawa takeyi gaskiya”.
Su Abba da duk jikinsu yay sanyi sukaima Doctor godiya sosai. Tare da tabbatar masa insha ALLAHU a wannan karon zasuyi abinda ya dace.
Yaji daɗin hakan sosai. Ya sake ɗan musu wasu bayanan da suka dace akan yanayin kula da Nu’aymahn kafin ALLAH yasa a dace da samun Doctor ɗin daya faɗa. Dan ya basu note dazai taimaka musu samun ganin makusancin likitan da lokaci-lokaci yake shigowa cikin kano. Baya kuma duba marasa lafiya a ko ina sai a General hospital. Dan haka ya basu abinda zai taimaka musu ganawa da wata likita dake aiki a General hospital ɗin, wadda yake da tabbatacin ta hanyarta zasu iya ganin Doctorn.
Godiya sukai masa sosai, sannan suka fito. Sai dai basu ma su baba malam bayanin komaiba, a ƙoƙarinsu nason yin wani hoɓɓasa akan jinin yayan nasu da a kullum hidimarsa ke ƙarewa a kan su da nasu iyalin. Suma wannan karon sunason nuna tasu bajintar akan ɗaya daga cikin jininsa guda biyu da ALLAH ya bashi.

________★★

Ganin lokacin sallar la’adar ya gabato Yoohan ya buƙaci kaɗaicewa dan ya huta. Hakanne ya saka papa fita ya barsa shima ya nufi ɗakin da aka kama masa.
Yoohan ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana miƙewa. Zuwa yay ya sakama ƙofar ɗakin key. Kafin ya nufi bayi yayo alwala kamar yanda baba malam ya koya masa. Duk da zuciyarsa na kwaɗayin zuwa massallaci yay salla cikin jam’i kamar yanda suka gabatar ɗazun a massallacin juma’a haka ya haƙura ya daure yin tasa shi kaɗai a cikin ɗakin kamar yanda aka koyar da shi.
Bayan ya idar da sallar a tsanake yay addu’a gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa. Waya ya jawo yay kiran baba malam. Cikin sa’a kuwa bugu biyu aka ɗaka. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke wadda har baba malam ya jiyota.
“Banyi zaton zaka ɗagaminba Uncle. Nazata zakayi fushi dani bisa kuskuren papa”.
Baba malam da fitowarsa kenan daga massallacin cikin asibiti sun idar da salla kiran ya shigo masa yay sassanyan murmushi, ƙaunar Yoohan ɗin da ƙyawawan ɗabi’unsa na sake dulmiyasa a ƙaunar yaron. Cikin kulawa yace, “Haba Yahya! Mizaisa nayi fushi da kai? Ai koshi bazanyi fushi da shiba dan ya fini gaskiya. Da farko ina fatan dai ka gabatar da sallar la’asar. Na biyu kuma ina fatan babu wata matsala tsakaninka da mahaifinka a dalilin ganinka da yay a wajena?”.
Lumshe idanu Yoohan yay a hankali yana jingina bayansa da kujera, cikin so da ƙaunar baba malam dake ratsashi shima yace, “Alhamdulillahi Uncle. Yanzun nan na idar da salla, sai dai banje massallaci ba, ina fatan hakan ba laifi baneba. Dan nayi hakanne saboda ahalina, banason su fahimci ni musulmi ne tun yanzu dan zasubi hanyoyi da dama wajen kaini ƙasa. Amma idan na sami wadataccen ilimin addini musulinci duk ta inda suka ɓullo zan kare kaina”.
Baba malam dake murmushi ya sauke ajiyar zuciya. “Tunaninka mai ƙyau ne Yahya. Sai dai salla cikin jam’i tanada matuƙar muhimmanci, dan haka kar kayi sakaci da samun ladan dake cikin jam’i kaji”.
“Zan kiyaye Uncle”.
“Alhamdulillahi haka ake so. Mahaifinka fa?”.
“Karka damu da shi Uncle. haka yake da zafi, amma da an fahimtar da shi yanada saurin fahimta. Munyi magana da shi ya kuma fahimceni, kafin ma ya wuce zai shigo wajenka yacemin”.
Hakan ya bama baba malam mamaki matuƙa. Amma sai bai nunama Yoohan ba ya amsa masa kawai. Sannan sukai sallama.

Lokacin da Yoohan ke waya da baba malam a can papa ma yana ɗakinsa suna waya da Uncles ɗin Yoohan ɗin su Uncle Godwin. Ba akan komai suke wayarba sai akan baba malam. Kamar yanda papa ya girgiza da ganin Yoohan da farko haka suma suka girgiza dajin Yoohan a wajen baba malam. amma daga baya sai bayanin da Yoohan yayma papa ɗin yaɗan sanyaya musu rai.
Uncle Mike yay wata dariyar mugunta yana faɗin, “Wannan ɗan nakafa shegen kansane, inaga akwai aikin da yakema turawan nan ta ƙarƙashin ƙasa shiyyasa kullum bai damuwa da lamarin kowa sai wannan aikin nasa. A da ba ƙaramin haushi yake baniba akan hakan, amma jin wannan maganar ta yau sai naji ƙaunarsa da son haɗa tafiya da shi. Sai dai matsalar ɗaya ce yaron yanada taurin kai, nasan bazai taɓa yarda musan cikinsa gaba ɗaya ba. Amma ni a ganina mizai hana muma muyi namu aikin akan wannan hausa man ɗin, dan fa multi millions ne. Kawai dai baya nunawa ne”.
Papa ya kwashe da wata dariya, kafin yace, “Mike! tunaninmu ɗaya, dan haka ku bari sai na shigo Abuja mu tattauna da ƙyau. Yanzu dai matakin farko zanbi shawarar Yoohan zanje har gida na bashi haƙuri. Daga haka na ƙulla alaƙa mai ƙarfi da shi. Sauran bayani kuma sai mun zauna a tebirin shawara”.
Duk sunyi na’am da hakan suma. Dan haka yay musu sallama ya kashe wayar cike da zumuɗi a ransa. Kaɗan-kaɗan sai ya ƙyalƙyale da dariya. Dan gaba ɗaya zuciyarsa ta gama tsara masa yanda komai zai kasance.

______________★★

Bayan Baba malam sun shiga sun duba Nu’aymah dake barci suka bar Hajjo da Abba Musbahu a asibitin. Koda suka iso gidan sai su Umm suka shirya su kuma suka tafi duba Nu’aymah. Wanka yayi ya zauna a falonsa yaci abincin da Umm ta shirya masa kafin su wuce. Abincin kawai yake ci a zahiri, sai dai zuciyarsa sam bata tare da duniyar mutane. Yayi zurfi matuƙa gaya a tunanin Pastor Goshpower (Papa). Ba komai ya kaisa ga tunaninba kuwa sai mamakin dama Papa nada babban ɗa a duniya kamar Yoohan? Ga shi dai a zahiri akwai kamanni tsakaninsu, sai dai baisan miyasa zuciyarsa ke kawo masa wani al’amari mai kama da kokwanto a cikin zuciyaba. Musamman da zuciyar tasa ke tariyo masa wani shuɗaɗɗen al’amari daya faru a shekarun baya tsakaninsa da Papan.
Haka yayta saƙawa da kwancewa har lokaci yaja bai farga ba. Sai da Abban Abdallah ya shigo dubasa sannan ya fahimci yayi zurfi sosai a tunani ashe. Alwala yayi suka fice massallaci dan lokacin sallar magriba ya gabato
Suna fitowa su Umm na dawowa gidan. tambayar jikin Nu’aymah sukayi. Suka sanar musu har yanzu tana barci, batama san sunje ba balle tahowarsu.
Baba malam yabi Umm da kallo harta shige. tausayinta mai tsanani ne ke sake shigarsa. Tanada haƙuri da kawaici matuƙa, shiyyasa yake tsananin ƙaunarta fiye da zaton mai hasashe. Yanzu haka inba shi daya gama sanin kayarsa ciki da bai ba bazaka taɓa fahimtar tanada damuwa ba a fuskarta. Ta dake ta shanye komai, baka ganin komai akan fuskarta sai tsananin jarumta da tarin haƙuri da juriya.
Haka ya tafi massallaci da wannan tunanin na Umm.

Bayan idar da sallar isha’i suna shirin zaman karatu kamar yanda suka saba ɗaya daga cikin ƴan agajin massallacin ya shigo ya sanar masa cewar yayi baƙi.
Jimm yayi alamar tunanin baƙi daga ina a wannan lokacin? Bai gama kaiwa ƙarshe ba ya hango Yoohan dake ƙoƙarin shigowa massallacin. Bai tashi ba, sai ya jira harya ƙaraso inda suke. Yoohan da kallo ɗaya zakai masa ka fahimci damuwa da rashin walwalarsa kamar ko yaushe ya ɗan bama na kusa da shi hannu sukai musabaha kafin ya ƙarasa inda baba malam ɗin yake. Cike da girmamawa ya risina ya gaishesa. Amma sai baba malam ɗin ya kamo hannunsa cikin nasa sukai musabaha kamar kowa. Cike da jin nauyi Yoohan yay masa bayanin tare yake da baƙi, wannan ya saka baba malam miƙewa bayan ya bama ɗalibansa haƙuri ya barsu da Abbansu Abdallah shi kuma suka fito.
Duk da dai yayi mamakin ganin papa ne sai baice komaiba. Da kansa yay musu iso gidan saukar baƙinsu. Sannan ya kira Umm ta bada abinda ke akwai a gidan cikin su Omar wani ya kawo.
Papa dake ta waya tun ɗazun ya ajiye yana kallon baba malam da murmushi, shima bai gazaba wajen maida masa murtani. A ƙasan ransa kuwa yana neman tsarin ALLAH da ga kowanne irin sharri papan ke tare da shi ko yake shirin ƙullawa. Duk da shi mutum ne mai ƙyautatama mutane zato zuciyarsa ta kasa ƙyautata zaton akan papa, dan shi shaidane akan sanin papa bayahude ne na gaske, sai dai bai saniba ko yanzu ya canja daga yanda ya sanshi a da ɗin.
Hannu ya bashi suka gaisa, hakan yay dai-dai da shigowar Omar ɗauke da basket da Umm ta shiryo abincin motsa baki. Sai da ya gaida Papan, suka gaisa da Yoohan da alamar sanayya tsakaninsu sannan ya fice. Papa ya gyara zamansa yana wani ɗan basarwa, fuskarsa da murmushi har yanzu ya duba baba malam da faɗin, “Kayi haƙuri da kuskurena na ɗazun, ina fatan zaka dubesa akan rashin sani na aikata. Bansan alaƙarka da yarona mai daraja bace irin haka sai bayan mun barka ne yaymin bayanin da har na fahimta, ina fatan zakamin afuwa”.
Sosai mamaki ya kama baba malam, dan duk zatonsa Yoohan ya ma mahaifinsa bayanin ya musulunta ne. dan haka ya ɗan dubi Yoohan ɗin. Da sauri Yoohan ya girgiza masa kai yanda papa bazai fahimtaba, hakanne ya saka baba malam fahimtar akwai abinda Yoohan ya sanarma mahaifinsa daban kenan. Sai kawai ya murmusa abinsa ya fuskanci papan shima.
“Karka damu komai ya wuce. Dama kuma ni ban ɗaukesa wani abuba. A inda ya faru anan na zubar da shi, nima ina fatan kaimin afuwa ka kuma fahimci alkairine ya haɗani da Yahya ba sharriba. Sanin shi wanene kuma bazaisa na taɓa cutar da shi ba insha ALLAHU. Saɓanin dake tsakanina da kai kuma bana fatan ya zama sanadin ɓata alaƙata da shi, dan sanin kai ne mahaifinsa bazai canja komai ba daga yanda na ɗaukesa a raina”.
“Naji daɗin haka, na kuma gode sosai da wannan girmamawa”. Papa ya faɗa yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushin mugunta.
Daga haka dai suka ɗan taɓa hirar da bawani tsaho taiba, shi dai ma Yoohan ba saka musu baki ya keba, yama maida dukkan hankalinsa ne ga wayarsa kamar baya falon. Kusan awarsu ɗaya da rabi sukai masa sallama suka fito inda su Solomon suke. Sai da baba malam yaga barin motocinsu anguwar sannan ya shiga cikin gida ransa taf da wasiwasi akan wannan ziyara ta Pastor Goshpower, amma sai ya bar abinsa a zuciya bai faɗama kowa ba, ya ma maida hankalinsa wajen kwantarma matarsa hankali akan damuwar ciwan ɗiyarsu.

WASHE GARI.

Washe gari papa ya matsa akan sai Yoohan ya bisa sun koma Abuja. Badan yaso hakanba ya amince zai bisa, dan dama yau ɗinne zai kammala abinda ya kawosa kanon. Yaso komawa wajen baba malam dansu tattauna game da neman iliminsa amma papa ya tsare ko ina ya hanashi matsawa ko nan da can. Asibiti ma binsa yay sukaje tare, ya kuma zauna a office ɗinsa har sai da ya kammala komai suka fito.
Da ga asibitin airport suka tafi kai tsaye, sai da jirginsu ya ɗaga sannan guards ɗinsa suka ɗauki hanya suma a motocin.

Baba malam na asibiti wajen duba jikin Nu’aymah da jikinta Alhmdllh saƙo ya shigo masa. Buɗewa yay ya duba ganin Yoohan ne. Murmushi baba malam yayi saboda ganin abinda saƙon ya ƙunsa, a ransa kuwa yana tsananin tausayi da ƙaunar Yoohan, insha ALLAH yayi alƙawarin zai taimaki yaron nan har ya zama HASKEn da zai zama HASKE ga waɗansu.
Ajiye wayar yay ya maida hankali ga Nu’aymah da Hajjo take lallaɓawa taci abinci amma sai shagwaɓa take ita ta ƙoshi. Ya ɗan murmusa tare da kamo hannunta cikin nashi. “Mamana daure kici ko kaɗanne kinji, inba hakaba fa kinsan Doctor yace allura zai miki, idan kuma kin fison allurar to sai a kirashi kawai”.
Da sauri ta shiga girgiza kanta idanunta cike da ƙwalla. “Abba dan ALLAH a’a banaso”.
“To ki daure kici abincin sai kisha magani ki kwanta ki huta. Kinga kince dama kanki na ciwo har yanzu, Doctor kuma yace kina buƙatar hutune sosai”.
Kanta ta sake jinjina masa. Hajjo da batace musu komaiba ta miƙama baba malam abincin. Babu musu ya amsa ya fara bata da kansa. Batafi spoon huɗu ba su Ahmad suka shigo ɗakin bayan sunyi sallama an basu izini. Ba Nu’aymah kawai ba hatta Hajjo da baba malam da ɗunbin mamaki suke kallon wanda ya shigo tare da su Ahmad ɗin. Ba kowa bane face Nasir jikan yayar Hajjo.
Babu kunya idonsa fes akan Nu’aymah da mamakin ganin nasa ya sakata masa kallo mai nisan zango. Hajjo ce ta katse su da faɗin, “Naseru yaushe a gari? Inji maƙi baƙo?”.
Goshinsa yaɗan sosa najin kunyar kallon da baba malam ke masa. Kafin yace, “Hajjo yanzun nan muka iso”.
“Kuka iso? To kai da wa kuma?”.
Kansa tsaye yace, “Rufaidah”.
Baba malam da tun gaisuwar daya amsa musu baice komai ba sai yanzu yace, “Lafiya dai ko Naser? Yau ka tuna damu a duniya”.
“Ayi haƙuri Kawu, ni ɗin mai laifine kam, mun tahone saboda ga biki nata gabatowa, ganin mun sami hutun makaranta mu duka sai kawai nace bara mu taho maɗan huta ai”.
“Oh to masha ALLAHU, ALLAH yayi jagora to”.
A tare suka amsa da amin. Nu’aymah dai bata tanka ba, tama ɗauke kanta tamkar batasan mi akeyiba. Sai da Naser ya tambayeta yaya jikin sannan ta gaidashi batare data kallesanba yanzun ma. Shiko yanata so su sake haɗa ido ko zaiji ɗan sanyi a ransa da ruhinsa.
Miƙewa baba malam yayi yana faɗin, “To ni bara naje gida hajjo, dan ina saka ran zuwan wasu baƙi ɗan anjima kaɗan idan ALLAH ya kaimu. Idan sun wuce insha ALLAHU zan dawo muji ko zasu bamu sallama, banason zama asibitin nan sam”.
Amsa masa hajjo tayi tare da binsa da addu’a. Nu’aymah ma ma dasu Ahmad sukai masa sallama ya fice. Hajjo ce ta sake cigaba da bama Aymah abincin, badan yana mata daɗi ba take amsa, sai dai mayataccen kallon da Naser ke mata duk ya sake takureta matuƙa, sannan ya tuno mata da wasu shuɗaɗɗun abubuwa dake tdakaninsu a lokacin ƙuruciyarta, hakan yasa taketa cuno baki gaba da ɓata fuska duk da ƙasan ranta cike yake da mamakin ganin nasa ya dawo bayan barinsu na tsahon shekaru da yayi akanta.
Idan bata manta ba shekara kusan takwas kenan rabonsa da kano. Dan tunda tace masa ita Yah Abdallah ne zaɓinta yay zuciya saboda goyon baya da Hajjo ta bama Abdallah a wancan lokacin. Anyi bukukuwa kashi-kashi a gidansu shi kaɗai ne baya zuwa sam.
Ta ɗan sake satar kallonsa da jijjina ƙyawun daya ƙara da cikar kamala tamkar ba Yah Naser ɗin data sani ba a shekarun baya. Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yanzu kam kuɗi sun zauna a garesa da hutu, dan sai ɗaukar ido yake kamar gasashshiyar kazar gidan gona.

*_Naser yaro ne wajen Alhaji Kabeer Usama dake a garin katsina. Jikane ga Yayar hajjo da suke uwa ɗaya uba ɗaya, dan aurene ya kaita katsina ta zuba zuri’a kuma a can mai albarka. Ita kaɗai kuma ta ragema hajjo a yanzun, shiyyasa take ɗaukarta tamkar uwa. Naseer ya zauna a gidan su Nu’aymah sosai, dan rashin yara a gidan lokacin da su Abdallah sukai Accident yasa hajjo ɗakkosa. A wajensu yay primary ɗinsa har secondary. Jami’a ce kawai ta maidashi garin jos. Yaso nu’aymah shima tun tana ƙarama, dan lokacin takara suka dingayi da Abdallah a kanta duk da kowa bai furta ba saboda ƙuruciya. To sai kuma yazam sanda suka furta ɗin ya zam lokaci guda, sai dai Abdallah ya riga Naser. Dama kuma ya fisa nuna damuwa da Nu’aymah. Hakan ya haddasa rigima sosai tsakaninsu, da Hajjo taga lamarin zai girmama ne tai musu shari’a a tsakani da shaidar cewar Abdallah ya riga Naser ɗin. Wannan shine sanadin yin zuciya ya tattara komansa yabar kano ya koma gidansu. Bai kuma sake zuwa ba sai yau ɗin nan da suka gansa tsulum. Har yanzu kuma baiyi aure ba._*……….✍

To ga dai Naser tsohon masoyin Nu’aymah a kano bayan gudun hijira na shkara takwas da yayi. Ko da wane shiri ya dawo yanzun kuma? Dan da alama kam akwai motsawar tsohon tsumi tattare da shi dama ita kanta, sai mu cigaba da binsa muji YAYA TAKE NE?!!🤗.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/21, 9:18 AM] +234 816 133 8078: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply