Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 34


Saran Boye 34
Viral

No. 34

…………Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana na neman zama babba. Dan kuwa dai rikici sosai ke wakana a tsakanin Abdallah da Naser akan Nu’aymah. Amma sai suka canja taku yanda iyayensu bazasu fahimta ba. A duk sanda Naseer yasa aka kira masa Nu’aymah sai Abdallah yazo ya tsare. Hakama duk lokacin da Abdallah ya buƙaci ganawa da Nu’aymah sai Naser yazo ya hana hakan ta hanyar zama tsakaninsu kamar yanda Abdallahn keyi.
Hajjo da mafi yawan rigimar a sashenta akeyi tana kallonsu amma tai kunnen uwar shegu da su kamar bata ganiba. Wani lokacinma da biyu take sakawa a nemo mata Nu’aymah ta zauna a sashenta dan tasan nanne wajen zaman su Naser ɗin musamman da daddare.
Duk kuma wannan abun dake faruwa Adawiya bata nan, dan kwanansu biyu da zuwa sukai tafiya biki ita dasu Hajarah dangin kakarsu maman su Addah. Da Addah ta ƙarrafa ayi tafiyar da Nu’aymah ma. Sai dai yanayin jikinta yasa Hajjo hanawa. Shiyyasa suka tafi su uku harda Kubrah sai Addahn da sauran ƴaƴanta na ma’auri.

Da farko rikicin nasu Naser nishaɗi yake saka Nu’aymah, amma ganin al’amarin na sake ɗaukar zafi sai hankalinta ya fara tashi. Dan neman birkita mata tunani sukeyi har takan rasa wanene yafi cancanta ta mallakama kan nata?.
Al’amarin bai sake tada hankalin kowaba a gidan sai randa Hajjo take cema Abdallah dama ya haƙura ya barma Naser Nu’aymah. Tunda shi a yanzu gashi yana auren su Yusrah. A fusace yace, “Indai su Yusrah ne zasu masa katanga da mallakar Nu’aymah to lallai zai rusa katangar”.
Babu wanda ya ɗauki furucin nasa da muhimmanci a lokacin da yayisa. Sai dai ga mamakinsu bayan sallar isha’i sai gashi da zungureriyar takarda har guda biyu yazo ya dire gaban hajjo.
Kallonsa tayi fuska a yatsine. “Kai wannan takardun kuma na miye ka ajiyemin kamar wani ɗan saƙon kotu?”. Fuska a turɓune yace, “Hajjo sakamakon katangar da kika tabbatar min zata shiga tsakanina da Nu’aymah ne a ciki. Kinga yanzu sai ki daina min baki ko”.
Sam hajjo bata fahimci zancen nasa ba, amma sai ta saka Omar dake zaune tare da ita ya duba mata. Ɗaukar ɗaya yay yana murmushin diramar kakar tasu da yayansu. Da sauri ya fesar da ruwan da ya ke sha yana faɗin, “What!?” saboda abinda yaci karo da shi a rubuce.
A rikice hajjo tace, “Miya faru Umaru?”. Jikin Omar na ɓari ya ajiye kofin ruwan tare da ɗaukar ɗayarma ya buɗe. Nanma dai abinda ke cikin ta farkon ce a ta biyu, ai baima san lokacin daya furta, “Hajjo wlhy Yah Abdallah ya haukace! ko kuma ya fara shaye-shaye ku bincika!. Hajjo sakin Yusrah da Adawiya fa ya yi…..”
“Saki kuma?!!” Hajjo ta faɗa itama tana miƙewa zumbur.
“Wlhy kuwa Hajjo gashi a rubuce saki ɗai-ɗai”.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un. Abdullahi!!. A wlhy gaskiyarka kuwa Umaru Abdullahi ya haukace. Ni Zainabu na shiga uku. Kaga kiramin ɗan malam duk inda yake yazo gida”.
Ɗan jimm Omar yayi alamar tunani, sai kuma ya dubi Hajjo da ranta ke a matuƙar ɓace. Cikin lallashi yace, “Amma Hajjo inaga kamar dai kiyi haƙuri har ya dawo gida. Kinga yanzu bamusan wane uziri yake kan yiba, kiran da za’ai masa zai iya dagula masa tunani, amma idan kince a kirasan dai sai na kirasa ɗin”.
“Hakane Umaru! Kaima kayi maganar hankali, amma lallai sai na saɓama Abdullahi fiye da zato a gidan nan. Wane irin wawancine wannan? Ashe hankalin da ake ganinsa da shi da girma bashi da shi ɗin?”.
“Kiyi haƙuri Hajjo, ALLAH ya huci zuciyarki. Ni kaina ban taɓa zaton hakan daga garesa ba. Kinga wannan ai tushen ɓata zuminci ne, idan iyayen namu basu kai zuciya nesa ba sai kiga al’amarin ya kawo ɓacin rai. Sannan su kansu yaran an saka wani abu a zuciyarsu gurɓataccen. Dan zasu iya tsanar Nu’aymahr da yace dominta yayi, hakan kuma bashi da amfani”.
Ƙwafa kawai hajjo tayi ranta da zuciyarta na ƙara mata suya da ɗaci. Omar dai yayta lallashinta har sai da yaga ta ɗan kwantar da hankalinta sannan ya fice cike da jimami. Sashensu ya nufa, yaje ya faɗama Momy duk abinda ya faru.
Sosai itama ta rikice hankalinta ya tashi. Dan ta tabbata Abbansu dama wasu a mutanen gidan bazata fita da ga zarginsu ba, musamman ma da akasan taso ya auri ɗiyar ƙanwarta. Waya ta ɗauka ta shiga neman Abdallah. Sai dai harta tsinke bai ɗagaba. Bata gajiya ba wajen cigaba da jera masa kira, amma yaƙi ya ɗaga.

Hajjo, Omar, Momy sun yi yinin yau ne cikin tashin hankali da damuwar ɓarnar da Abdallah ya tafka. Duk da sun ƙagara Baba malam ya dawo gidan ransu cike yake da fargabar sakamakon da zai biyo baya kuma.
Sai bayan sallar la’asar baba malam da Abban Abdallah suka dawo gidan. Dan dama tare suka fita. Sunje wani ƙauyene akan maganar wata katafariyar gona da zasu saya. Sunason gyarata su maidata gidan gona a zuba dabbobi kala-kala na kiwo a ciki. Wannan ma ne dalilin da yasa har yanzu shi da Abba Musbahu basu koma ba. Suna son sai komai ya kammala sannan su ɗauka iyalansu su koma inda suka fito sai kuma biki.
Kamar yanda al’adarsu take ta fara shiga sashen mahaifiyarsu yau ma hakan suna fitowa daga mota can suka nufa. Yanda suke tafe suna firarsu kowanne fuska ɗauke da fara’a dolene su matuƙar burgeka. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci ɗunbin shaƙuwa da ƙaunar juna dake a tsakaninsu.
Sai da sukai sallama Hajjo da ke zaune cikin ɓacin rai har yanzu ta amsa musu da basu izinin sannan suka shiga. Kallo ɗaya sukai mata suka fahimci tana cikin damuwa. Kusan da sassarfa duk suka ƙarasa gareta kowanne na tambayarta tana lafiya?.
Batai magana ba, sai wajen zama data nuna musu. Sai dai maimakon su zauna a kujerun sai suka zauna ƙasa tamkar yanda suka saba. Gaisheta sukayi, sannan suka sake jero mata tambayoyi akan yanayin nata.
Ƙwallar da suka cika mata idanu tasa bakin ɗan kwalinta ta share. Hakan sai ya sake tada musu hankali.
“Inna dan ALLAH ki faɗa mana minene ke damunki? Mune mukai muki laifi? Ko matan mu? Kokuwa a cikin yaran nan ne wani yay miki wani abu?”.
Sake share hawayen data matso tayi da cewar, “Ni babu abinda kukai min ɗan malam, Abdullahi ne kawai keson watsa mana gida”.
Hankali a tashe baba malam da Abban su Abdallah suka kalli juna. Cikin ƙarfin hali baba malam yace, “Innah mi Abdallahn ya aikata?”.
Takardun da Abdallah ya rubuta ta ɗakko ta miƙa musu. Amsa sukayi kowanne ya buɗe guda ɗaya gabansa na faɗuwa. A tare suka ɗago a razane suka kalli juna da ambaton sunan ALLAH. Baba malam har yana tsallaken kalma wajen faɗin, “Innah shi Abdallah ɗinne ya rubuta wannan takardar?”.
“Shine ɗan malam, shine da kansa ya rubutasu ya kuma kawo mani. Wai dan kawai jiya na bashi shawarar cewar yay haƙuri ya barma Nasiru Zainabu tunda shi yanzu yana da matansa har biyu. Shine fa yau ya kawomin takardar sakinsu Adawiya wai gashinan ya rushe katangar dana ce masa tana tsakaninsa da Zainabu”.
Abba da ya gaza cewa komai tun ɗazun yace, “Innalillahi…, wai inna kina nufin su duka biyun ya saka?”.
“Eh mana Lurwanu, baga takardun nan ba duka biyu na baku”.
Da sauri baba malam ya amshi ta hannun Abba, shima ya karɓa ta hannunsa. Da gaske kuwa su duka biyun ya saki. A take tsananin ɓacin rai ya sake bayyana a kan fuskokinsu. Abba ya miƙe a fusace zai fice. Kiransa baba malam ya shigayi amma ina zuciyar gadon ta motsa. Dan haƙuri kawai ya bashi batare da ya juyoba ya fice.

Momy na zaune cikin damuwa da fargabar jiran dawowar mijinta Abba ya shiga. Jiki a sanyaye ta dubesa dan ko sallama baiyi ba
Takardun guda biyu ya watsa mata a jiki. “Da saninki ɗanki yay wannan aika-aikar ko?”.
Gaban Momy na faɗuwa ta ɗauki takardun ta karanta, hawayen da taketa faman dannewa tun ɗazun suka zubo mata a saman kumatu. “Wlhy Abban Abdallah ban sani ba. Nima ina zaune Omar yazo yake sanarmin. na kirashi yafi sau hamsin amma ya ƙi ɗagamin waya ma, kai……..”
Baki ya buɗe zai daka mata tsawa Omar da ya shigo basu sani ba yace, “Abba wlhy babu ruwan Momy, hasalima batasan komaiba akan al’amarin nan sai da nazo na sanar mata. Abba ko kasan dama tunda Yah Abdallah ya dawo gidannan baiyi zaman minti biyar da Momy ba. Da ya shigo ya gaidata da safe bazata sake ganinsa ba sai washe gari. Fushi yake da ita babu gaira babu dalili. Ta sakani na tambayesa amma yacemin idan na sake zuwa masa da zancen Momy sai ya ɓatamin rai. Ita kanta nace zan sanar maka abinda ke faruwa amma ta hanani, wai mu bashi lokaci kozata fahimci abinda ke damunsa”.
Jikin Abba ne yay sanyi, dan tabbas kuwa ya kula tunda Abdallah ya dawo ƙasar nan bai taɓa ganinsa zaune da Momy ba, da farko yaso tambayarta sai kuma yayi tunanin ƙila sai ya fita suke zaman. Wannan ya sakashi yin shiru duk da kuwa yasan yanda matar tashi take da ƙulafucin ƴaƴa musamman Abdallah.
Nannauyan numfashi ya sauke tare da zama yana cire hular kansa ya ajiya…..

A ɓangaren baba malam kuwa Abba na fita waya ya zaro ya shiga neman layin Abdallah. Sai dai kuma abin mamaki switch off. Ajiye wayar yayi ya maida hankali ga Hajjo da ke sharar hawaye har yanzun. Kwantar mata da hankali ya shigayi da bata haƙuri. Yace, “Inna ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, insha ALLAHU mu dai wannan bazai kawo mana rabuwar kawuna ba. Duk inda Abdallah ya shiga kuma na tabbata zuwa dare dole ne ya dawo gida ya kwana ai, insha ALLAHU a daren nan sai ya maidasu su duka biyun”.
“Ɗan malam bazaka gane abinda nake nufi ba, amma duk yanda kake tunanin sauƙi a al’amarin nan da wahala ya kasance hakan. akwai abinda na sani wanda kai da sauran ƴan uwanka baku san da shi ba a gidan nan. Ina barin masu aikatawar ne kawai kafin ranar da zan masu bankaɗa da tonon silili a gaban kowa. Ni dai abinda zan sanar maka yanzu shine da ga Abdullahi har Nasiru ka zaunar da Zainabu ta zaɓi wanda tafi so tunda abin ya zama haka. Kokuma ta auri wani bare can a zauna lafiya. Sannan inason ka nutsu kayi tsai da hankalinka a wannan karon game da kowa a gidannan, koda baka fahimci duka abinda na fahimtaba zaka fahimci wasu daga ciki. Dan kai ne uba a gidan nan, duk da dama nauyi da girman ya rataya a wuyankane tunbayan rasuwar mahaifinku, ina kuma alfahari da yanda ka riƙe hakan, amma sai randa ƙasa ta rufe idanuna zaka sake tabbatar da girman dake bisa kanka da tarin fituntunun da ke kwance a cikin gidannan wanda ALLAH ne kawai hanasu fallasuwa saboda rahamarsa da ikonsa da kuma ƙarfin addu’ar mahaifinku da har yanzu take biye da ku. Kai dai ALLAH ya ƙara maka haƙuri da juriya kawai. Tashi kaje ka huta, ka kumayi ƙoƙarin tausar sauran ƴan uwanka akan duk ma abinda zai iya biyo baya game da wannan gagarumar fitinar da Abdullahi ya ɗaɗɗago mana”.
Kasa cewa komai baba malam yayi. Cike da ruɗanin maganganun Hajjo ya jinjina mata kansa kawai da miƙewa ya fice zuwa nasa sashen. Bai iske kowa a falon ba sai Muhammad dake karatun Al-Qur’ani na haddar da aka basu a islamiyya. Yaron bai dakata daga karatun da yakeyi ba, shima kuma bai masa magana ba ya wuce ɗakinsa.
Komai tsaf a gyare kamar yanda ya saba zuwa ya iske, ga ƙamshi mai daɗi. A ɗaya daga kujerun ya zube hankalinsa har yanzu baya tare da shi. Dan ransa da zuciyarsa cike suke da tarin ruɗanin kalaman mahaifiyar tasu. Shi kansa yasan akwai abubuwan dake kwance a gidan nan ƙwarai da gaske. Waɗanda da yawansu shi da iyalinsa sun cutu matuƙa a cikinsu. Koma yace suna kan cutuwa. Ya kumayi imani da ALLAH babu wani baƙon ido daga waje da zasuce yana aikata su, dolene mai aikatawar a cikin zuri’arsu yake. Yasha yin tunanin tsananta bincike, amma sai zuciyarsa ta gargaɗe sa da yin haƙuri, sannan yana mai tsananin jin tsoron wanda sakamakon ɓarnar zata tabbata a garesa. A ganinsa gara kawai a cigaba da tafiya a lulluɓen dan UBANGIJI mai ji ne kuma mai ganine akan kowa da komai……….
Taɓa shin da akayi ne ya saka tunaninsa katsewa. Duban Umm da tun ɗazun take masa magana yay. Fuskarta cike da damuwa tace, “Malam lafiya kuwa? Wane irin zurfafa tunanine haka? lna fatan dai lafiya ko?”.
“Humm! Jannat lafiyar nan da dauƙi”.
Saurin zama tayi hannunta riƙe da kofin data zuba masa ruwa tana faɗin, “Miya faru?”.
Ruwan ya fara karɓa ya sha, ta sake ƙara masa ya shanye sannan ya ajiye kofin ya labarta mata duk abinda ya faru, harma da zancen da Hajjo tai masa.
Duk da itama ta jima da ji a ranta duk abinda Hajjo ke zargi a kwaishi a gidan hakan bai hanata jin tashin hankali ba. Ita kanta tanason sanin mai aikata musu SARAN ƁOYE a lokuta da dama. Sai dai tsoron wanda zata gani yana aikatawar ke sakata sama ranta haƙuri da barin komai hannun UBANGIJI.

★★★★

A yau dai har dare Abdallah bai dawo gidanba duk jiran da su baba malam sukai zaman yi masa. Dole suka haƙura suka kwanta al’amarin nacin ransu da zuciya.
Washe gari bayan fitowa sallar asuba baba malam da sauran ƴan uwansa suka hallara gaba ɗaya a sashen mahaifiyarsu. Bayan sun gaisheta suka sake haɗuwa gaba ɗaya wajen bata haƙuri akan abinda Abdallah yayi, suka kuma tabbatar mata insha ALLAH zasu dai-daita komai ba sai yayi tsamari ba.
Batace da su komaiba dai, sai dai ta musu addu’ar nasara da nemawa Abdallah dama sauran yaran shiriya gaba ɗaya.

A wannan yinin maganar sakin ta shiga kunnen kowa dake a gidan ciki harda Addah da yaranta dake can suna shan biki. Aiko ba ƙaramin rikita musu lissafi Adawiya tayi ba. Dole babu shiri suka tattaro suka nufo kano zuciyar kowa babu daɗi.

Tunda saƙon saki ya isa kunnen Yusrah kuwa sai wani tarin farin ciki ya kamata. Bama tasan lokacin data shiga dirga tsalle akan gadon ɗakinsu ba. Kafin ta sakko da sauri ta shiga bayi ta ɗauro alwala. Salla tayi raka’a biyu na godiya ga ALLAH daya kawo ƙarewar wannan aure da ko tarewa batayi ba a cikinsa. Dama tunda su Adawiya suka diro ƙasar bata da wani sukuni. Shiyyasa ta koma yinin makarantar Tahfiz ɗin gidansu dan kawai ta gujema ganinsa. Hakan kuwa akayi, dan tunda suka iso sau biyu ta haɗu da shi. Ɗaya da daddare ya shigo sashensu wajen Abba. Na biyu kuma a sashen hajjo taje kai mata abinci. Duka a haɗuwar tasu gaisuwa ce kawai ta shiga tsakaninsu. Yanda baya sakar mata fuska itama bata shiga sabgarsa sam, dan baya wani nuna alamar akwai ko ɗigon haƙƙinta daya rataya a kansa ma. Hakan kuma bai dameta ba, to gashi cikin amincin ALLAH komai ya zama yanda taketa fata a kullum. Ba ƙaramin azumi da ƙiyamullaili tayi ba akan auren nan a cikin watannin nan. Dan ita kaɗai tasan dalilin rashin son auren.

Duk wannan ruguɗai da akeyi Nu’aymah batasan anai ba ita kam, dan Umm da baba malam babu wanda ya sanar mata. Sashen Hajjo kuma yanzu ba wani shigarsa takeba sosai saboda takurawar Nasir da Abdallah da suka maida sashen hajjo wajen zamansu. Ta gwammaci taita zama a sashensu, idan Muhammad na gidan susha shirmensu, idan kuma ya fita makaranta tayi kallo idan akwai wuta ko su zauna hira da Umm. Wani lokacin kuma tai barcinta dan Doctor ya ce ta dinga yawan barci, shiyyasa ma ya saka mata maganin barci a magungunanta.
Yauma tana a ɗaki tasha barcin rana har su Adawiya suka dawo bata saniba. Ta fito wanka tai sallar la’asar, shiri ta farayi da ƙudirin zuwa islamiyya yau dan tanajinta Alhmdllh. Tana tsaka da saka kaya ta jiyo kururuwar kuka kamar muryar Adawiya kuma. Saurin ƙarasa saka kayan tayi ta fito, a mamakinta duk ma sai ta iske ƴan gidan a tsakar gida kowa ya fito an rufu kan Adawiya. Gabantane ya faɗi da tunanin ko Accident sukayi a hanya. Da sauri ta shiga bin kowa da kallo sai taga kowa ma yana nan, harsu Aunty Aysha ma basu wuce gidajensu ba nan sukayo.
Kallon Jafar dake kusa da ita tayi tace, “Jafar miya faru wai?”.
“Aunty Nu’aymah ban saniba nima. Kawai dai naga Aunty Adawiya na kuka tana cewa wai indai aka rabata da Yah Ab zata mutu”.
Kafesa da kallo Nu’aymah tai tana son fassara kalaman nasa amma sunƙi fassaruwa. Dubanta ta kai ga Umm dake lallaɓa Adawiya taje sashensu amma taƙi, hakan ya sake tabbatar mata da lallai ba lafiya ba kuwa. Baba malam daya shigo gidan yanzunne ya dakama Adawiya tsawa. Jiki na rawa ta miƙe tsaye.
“Wane irin rashin hankaline wannan tun daga wajen gate anajin muryarki, tona mana asiri zakiyi da shirme ko mi?. To wlhy bara kuji bama ita ba duk wanda na sakejin bakinsa a wannan maganar saina ɓata masa rai, naga dai Abdallahn a ƙarƙashin ikonmu yake shima, dolene kuma yabi abinda mukeso inhar yana buƙatar gamawa da rayuwarsa lafiya. Kowa ya shige ciki”.
Jan ƙafa kowa ya shigayi zuwa sashensa. Kubrah ta kama hannun Adawiya suka shige tare. Inda suka bar Addah da bata fitaba nan suka isketa zaune. Babu wanda taima magana a cikinsu har suka zazzauna kowa na ƙannun magana. Batace musu komaiba dai har lokacin, saima jingina da tai da kujera ta lumshe idanu.

Nu’aymah suna shiga sashensu ta shiga tambayar Umm abinda ke faruwa. Dan ita harga ALLAH bata fahimci komaiba dai har yanzun. A taƙaice Umm ta faɗa mata, sai ko ta zabura a matuƙar razane. “Ya salam. Umm Yah Ab kuwa yana da hankali?! Wannan ai gogama mutane sharri ne da zai ce saboda ni ya aikata saki ga matansa”.
“Wannan sakaki a cikin da yayi shine ya sake tada mana hankali muma Nu’aymah. Dan zai iya zama wata fitina daban wadda ba’asan iyakar inda zata tsaya ba a gidan nan. Yanzu dai Abbanku ya gano inda yake, ya kuma bashi daga nan zuwa kwana uku idan bai dawo gida ba zai haɗu da ɓacin rai mai tsanani daga garesu”.
“Ai gara yazo ya kwance wannan ƙullin da yay min nikam, a dalilin mi zai sakani tsakkiya, a barni da abinda ya damenima nikam ya isheni Umm”. Tai maganar tana fashewa da kuka.
Tausayinta ne ya kama Umm sosai, ta ruƙo hannunta ta sakata jikinta tana lallashi…………✍

😩 Yah Ab ya zaka mana haka ne?🤦🏻‍♀️🙆🏻‍♀️
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/24, 12:25 PM] +234 806 269 3623: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

Ina fatan ansha weekend lafiya? ☺️🤝🏻😘

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply