Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 37


Saran Boye 37
Viral

No. 37

…………A tsaitsaye ta iske su Abba gaba ɗaya yanzun kam. Cikin girmamawa ta ƙarasa garesu. Fuskarta ɗauke da murmushi tace, “Congratulations, mun samu nasara babban likitan da ganinsa ke da matuƙar wahala ya amshi gayyatarmu”.
Cike da jin daɗi suka shiga faɗin Alhmdllh.
Da ga haka ta buƙaci magana da su Abbah. Babu musu suka bita office. Bayani tai musu akan ƙa’idar saka hannu da Dr Yoohan ya sanar mata, Abba Musbahu ne ya nuna ai suma iyayen Nu’aymah ne idan sun saka hannun babu damuwa, tunda yayansu baya a kusa, gashi kuma tace za’a shiga aikin ne da gaggawa……..
Ita dai kasa ce musu komai tayi dan suna da girma da kima a idonta, sannan kuma ta tabbatar tunda Dr Yoohan yace a cikin ukun ɗaya ake buƙata dolene hakan za’ayi. Ganin shirun da tayi ne ya saka Abban Adawiya fahimtar akwai matsala, dan haka sai ya kalli ƴan uwansa, “Inaga kawai mu kira Yayan kamar zaifi fa’ida, dan sun fimu sanin muhimmancin sharɗanta hakan”.
Duk sun gamsu da bayaninsa. Abban Abdallah ya ciro waya yay kiran Baba malam. Kirannasa ya shiga wayar baba malam ɗinne dai-dai lokacin da Umm da Hajjo ta shafama ruwa a fuska ta kawo nannauyan numfashi alamar dama suma tayi. Kusan a tare duk suma suka sauke numfashin, musamman ma baba malam da ke jin kamar an tsundumasa a aljanna.
Ba ƙaramin faɗuwa kuma gabansa yayiba ganin kiran ɗan uwansa, amma sai yay ƙarfin halin ɗagawa ya saka a kunne. “Rudwan ta rasu ko?”.
Da dauri Abban Abdallah yace, “A’a Yaya tana da ranta”. Da ga haka yayma baba malam bayanin halin da ake ciki. Kamar baba malam bazaice komaiba. sai kuma ya nisa kaɗan da faɗin, “Shike nan ina zuwa”.

★★★★

Bayan saka hannun baba malam Yoohan da wasu likitocin biyu sai Dr Aysha ta uku suka shiga theatre room da Nu’aymah da ko maƙiyinta ya ganta a wannan lokacin sai ya tausaya mata.
Tun suna irga mintuna har suka koma awanni, dan anyi sallar magrib har isha’i su Yoohan basu fitoba. Duk jikinsu ya kumayin sanyi. amma saboda ƙarfin hali irin na baba malan haka ya bama matan da samarin ƴaƴan nasu umarnin suje gida su huta haka nan. Basu da ikon masa musu akan hakan, amma a kallo ɗaya zaka fahimci ba haka suka so ba, dan Abdallah kasa daurewa yay kansa a ƙasa yace, “Abba da ku kuje kawai, ni zan zauna har su fito insha ALLAHU”.
Da sauri Naser shima yace, “Abba nima ina nan harsu fito dan ALLAH”. Ta ƙasan ido Abdallah ya ballama Naser harara, amma dai baice komai ba.
Shiru kawai baba malam yay yana dubansu, dan shi harga ALLAH tausayi suke bashi. Kafin baba malam yace wani abu Hajjo tace, “Ai mu duka ma tafiyar tamu bamai yuwuwa bace ba, dan ya kamata muga fitowarsu ko ma tafi da ɗan ƙwarin gwiwa. ALLAH dai ya bata lafiya”.
Duk da Amin suka amsa mata. Daga haka kuma babu wanda ya sake cewa komai, suka sake cigaba da zaman jiran tsammani.

Sai kusan ƙarfe tara na dare dai-dai su Yoohan suka fito, duk su baba malam suka miƙe tsaye don son jin yaya ake ciki?  Su Doctor Aysha ne kawai suka tsaya musu bayani, dan Yoohan yana ɗakin bai fito ba tukunna.
A tare suka shiga faɗin Alhmdllhi, Koba komai sunɗan sami kwanciyar hankali duk da ba cewa akai Nu’aymahn ta tashi garas bane ba.
Su Dr Aysha da suma fuskokinsu ke nuna alamar nutsuwar jin daɗin yanda aikin ya kasance suka sanar da su zasu iya tafiya gida. Dan Doctor yace babu wanda zai iya ganin Nu’aymah a yanzu, hasalima ba’a buƙatar kowa a gareta.
Duk da ba haka suka so ba sun gamsu da bayanin Doctor Mubarak ɗin, dan haka baba malam yace su wuce ɗin kawai, dama gashi sun baro Umm ita kaɗai a gida sai su Hajarah da ke a tare da ita.

★★★★‡★★★★

Kamar jiya yau ma baba malam ba shine yaja salla a massallaci ba, hakama bayan an idar bai zauna wajen karatu ba ya shiga gida.
Tun a daren jiya ya gama yanke shawarar da ta dace akan wannan al’amarin, dan haka koda ya shigo gidan waya ya ɗauka, ya rubuta gajeren text massege ya tura. Umm na zaune na azkar tana kallonsa. Yanda baice mata komaiba itama batace ɗinba har sai da ya kammala ya ɗago yana kallonta.
Ɗan Murmushin ƙarfin hali tai masa ta duƙar da kanta. Shima sai ya ɗan murmusa cike da jarumta ya kirayi sunanta a hankali. ɗagowa tai ta sake kallonsa. Muryarsa a sanyaye yace, “Ki ƙara haƙuri Jannat kinji, nasan kina cutuwa matuƙa, amma inason ki ɗauki komai matsayin jarabawa, kinsan ita duniya dama UBANGIJI bai yita dan ta kasance abin jin daɗin ɗan adam ba a kullum”.
Ƙwallar da suka cika mata idanu ta haɗiye da ƙyar, ta maida kanta ƙasa dan karya gani tana faɗin, “Insha ALLAHU, ALLAH ya bamu ikon cinyewa”.
“Amen ya rabbi” ya amsa mata shima.
Shiru ɗakin yayi kowa na nazari a zuciyarsa, a haka har gari ya ƙarasa wayewa tangaran. Duk da Umm bazata iya aiki ba haka ta fita cikin dauriya ta lissafama Rabi abinda zatayi. Ita kuma ta koma ɗakin baba malam inda ta tarar zai shiga wanka.

★★★

A ɓangaren Abdallah kam tun a daren jiya ya karɓa Number Yoohan a wajen Ahmad. Babu irin tambayar da Ahmad ɗin bai masa ba akan mizaiyi da Number amma yaƙi faɗa masa. Dan haka ya ƙyalesa kawai yay kwanciyarsa.
Tun a daren ya fito harabar gidansu ya kira wani abokinsa SSS, bayani ya kora masa akan taimakon da yake son yay masa, babu musu kuwa ya amsa zaiyi. ya buƙaci Number Yoohan a take ya tura masa ita da ƙara jaddada masa dan ALLAH zuwa gobe yake buƙatar result.

A safiyar yau kam kusan ƙarfe bakwai da kwata sai ga kiran abokin nasa. Bayan sun gaisa da ɗan tsokanar juna kamar yanda suka saba ya sanar masa aikinsa ya kammala, yaya yakeso ayi?.
“Wow gaskiya na gode matuƙa Mahmood, amma nayi mamakin jin mai Number wai yana a kano, kasan a yanda naji Abuja yake da zama”.
“Eh to, zata iya yuwuwa kanon yazo, dan a yanzu hakama sai da na sake tabbatar da yana a inda muka gansa jiya sannan na kiraka, dama wannan shine amfanin tracing ɗin ai”.
“Gaskiya kam, aiko nagode sosai. Abu nagaba shine zanzo mu haɗu yanzun, dan ina buƙatar a kama min shi ne”.
Dariya sosai Mahmood ya keyi, yace, “Shegen sama mi yayi maka ne? Halan wata harƙallar kuka ƙulla ya doje?”.
“Ai harƙallar dake tsakanina da wannan shegen ta wuce duk yanda zakai tunani wlhy Mahmood, kai dai faɗamin inda kake nazo na sameka kawai”………

★∆∆★

Sai ƙarfe shida da wasu mintuna ya farka na safiya. ya tashi a ɗan firgice bakinsa ɗauke da addu’ar barci da ALLAH ya bashi ikon riƙewa a lokaci ƙanƙani kamar yanda baba malam ya koyar da shi. Tunda ALLAH yasa ya musulinta yau ne karan farko da zaiyi sallar asubahi a makare. Dan alarm yake sakawa gudun karya makara. Sannan kuma baba malam duk asubahi sai ya kirasa ya tadashi. Hakan na masa daɗi, yana kuma ƙara masa ƙwarin gwiwa. Dalilin makarar tasa ta yau ma dan bai kwanta da wuri bane, dan tun bayan fitowarsu theatre ya duƙufa ne akan binciken matsalar Nu’aymah. Dalilin binciken nema ya sakashi kwana a asibitin, Solomon ne kawai yaje Hotel ya kwana.
Bayi ya shiga ya ɗauro alwala ya fito, ya buɗe jakka ya ciri sallaya da yanzu bai rabo da ita a kayansa duk inda zaije, shimfiɗawa yayi sannan ya zura jallabiya ya tada salla. Yana idarwa saƙo na shigowa wayarsa, sai dai baibi takai ba ya miƙe ya fita dan yana son duba patient ɗinsa.
Kusan mintuna ashirin ya ɗauka a ɗakin da Nu’aymah take sannan ya fito ya koma office. Yanzunma baibi takan wayarba dai ya shiga wanka. Bayan ya fitone ya ɗauka wayar saboda ganin screen ɗin yana haske. Missed calls ne har uku yaci karo da su duk na Mumynsa. Bai kirata ba sai ƙoƙarin duba saƙon da ya gani yay cike da mamakin ganin baba malam ne.
Yana gama duba saƙon yay ƙoƙarin kiran baba malam ɗin. Cikin sa’a kuwa ya ɗaga. Tamkar yana a gabansa haka ya rissina da girmamawa ya gaida shi, shima kuma da ga can baba malam ya amsa masa da kulawa tamkar yanda ya saba.
“Uncle dama naga massege ɗinka ne, ina fatan dai lafiya?”.
“To Alhmdllh Yahya, kawai dai inason ganinka ɗinne, ina fatan bazan shiga aikinka ba?”.
“A’a Uncle babu damuwa, dan yanzu hakama ina cikin kano, insha ALLAHU zuwa anjima zan shigo”.
“Masha ALLAH, ALLAH ya nuna mana”.
Daga haka sukai sallama Yoohan na cigaba da mamakin ganin nasa da baba malam ke buƙatar yi, dan ya ƙara fahimtar kiran nasa nada muhimmanci sosai. Bai kira Momy ba sai da ya shirya cikin ƙanun kaya. Daga wandon har riga duk baƙaƙe ne, sai suka sake fito masa da ainahin farar fatarsa daketa ƙyalli da ɗaukar idanu. Yaɗan saka turare tare da gyara gashinsa da a yanzu yake ɗauke da aski na mutunci, sai sajensa dake kwance luf masha ALLAH.
Jin motsi a office ɗin nasa ya sakashi ɗaukar p-cap ɗinsa jaa ya ɗora a kai, sannan ya zauna bakin gado ya saka takalmansa suma baƙaƙe da ɗan kwalliyar ja kaɗan.

Harya ƙaraso cikin office ɗin da aka gyara tsaf yana zuba ƙamshi Solomon na kallonsa ta ƙasan ido, a ransa kuwa yaba iya ado da kwalliya irinta ogan nasu ya keyi, sai dai yana mamakin ganin a ƴan kwanakin nan gaba ɗaya ya daina saka sarƙa, hakama ƴan kunne baya sakawa. Saurin katse tunaninsa yayi cike da girmamawa ya miƙe tsaye yana faɗin,
“Good Morning sir”.
A taƙaice Yoohan yace, “Same”. Yana zama a kujerarsa. Ɗan kallon Solomon ɗin yayi ya ɗauke kansa da faɗin, “Bani Coffee”.
Solomon na cikin haɗa coffee ɗin akai knocking ƙofar. Izinin shigowa ya bada idonsa akan file ɗin Nu’aymah daya tattara na binciken jiya. Dr Aysha ta shigo hannunta ɗauke da basket. Saman table ɗin ta ɗora tana faɗin, “Good morning Doctor”.
Kaɗan ya kalleta ya ɗauke kansa zai maida ga file ɗin, sai kuma ya sake dubanta ya dubi basket ɗin yana faɗin, “Morning. How are you?”.
“Alhmdllh sir” ta faɗa tana sake faɗaɗa murmushinta ganin yanda yake kallon basket ɗin data ajiye. A taƙaice tace, “Breakfast. ban saniba ko zaka iya cin jagwalgwalon hausawa”.
Ɗan lumshe idanu yay ya buɗe yana maida kansa ga abinda yakeyi da faɗin, “Thanks” a taƙaice.
Bata damuba, sai ma murmushi da ta sakeyi tana amsa gaisuwar da Solomon ke mata fuskarsa a murtuke kamar ma shine boss ɗin. Coffee ɗin daya haɗa ya ajiye gaban Yoohan.
Nanma “Thanks” ɗin Yoohan yace masa batare da ya kallesa ba. Sai da yaja wasu sakanni sannan ya rufe file ɗin ya gyara zamansa da ƙyau yana ɗaukar kofin coffee ɗin da ɗan kallon Dr Aysha da har yanzu take a zaune.
“Matsalar yarinyarnan babbace, ina buƙatar magana da mahaifinta”.
“Sir kana nufin aikin da akai mata jiya ba shine na ainahin matsalarta ba kenan?”.
Sai da ya kurɓa coffee ɗin sannan ya girgiza mata kai, “No ba shi bane dai kai tsaye, dan tana da matsala a ƙwaƙwalwa, wanda shine musabbabin yawaita haddasa mata matsalar saurin suma da wasu matsalolin da akai mata aiki a kansu jiya”.
Cike da tausayawa Dr Aysha tace, “ALLAH sarki, ALLAH ya bata lafiya, gata yarinya ƙarama dan da alama bata wuce 17years zuwa 18 ba”. Yoohan baice komai ba dai. Ganin haka Dr Aysha ta miƙe dan ta bashi damar cin abincin idan yana so. “Bara naje to Doctor, zan duba ko wani cikin ƴan gidan nasu ya shigo”.
Kansa kawai ya ɗaga mata. Ta juya ta fita itama tana jinjina hali irin na Dr Yoohan a ranta. Amma ita duk da haka sam baya ɓata mata rai, sai ma birgeta da ya keyi.
Da harara kuwa Solomon dake can gefe ya raka bayanta.

Dr Aysha na fita su Abdallah na isowa bakin ƙofar office ɗin Yoohan su biyar, dan bayan Abdallah akwai Mahmood da yaransa su uku, sunbar biyu a mota kuma. Mahmood ya ɗaga wayarsa yana faɗin, “Nan shine alama ta nuna, kuma da alama shi ɗinne” ya ƙare maganar yana nuna masa rubutun dake a saman office ɗin mai ɗauke da sunan *_Dr Yoohan Goshpower_*.
Wani Murmushin mugunta da jin daɗi Abdallah yayi, batare da ya jira sunyi knocking ba ya tura ƙofar office ɗin kawai ya shige.

Duk da a yanda aka buɗe ƙofar Yoohan baiko motsaba balle yabar abinda yakeyi. Sai Solomon ne ya miƙe zumbur yay magana cikin daka tsawa. Cikin harshen nasara yace, “Kai wanene zaka shigo nan babu neman izini?”.
Wani banzan kallo Abdallah yayma Solo, sai kuma ya maida idonsa ga Yoohan da har yanzu bai ɗago ya kallesu ba, baima nuna alamar yasan da shigowar tasu office ɗin ba. Hakan sai ya sake fusata Yah Ab, shima a tsawace yace, “Tsaya matsayinka na bodyguard yaro, dan ubangidanka ne dai-dai da ni”.
Solomon zaiyi magana Yoohan da har yanzu ɗin bai ɗago ba ya ɗaga masa hannu alamar kar yace komai. Shirun kuwa Solo yayi ransa na masa ƙuna da takaicin rashin sauran ƴan uwansa.
Cike da ƙasaita Yoohan ya ɗago fuskarsa da ada p-cap ta rufe kusan rabi saboda kansa da ke a duƙe. Manyan idanunsa ya sauke akan Abdallah, sai kuma ya maida kansu Mahmood da ke tsaitsaye suma. Batare da yayi magana ba yay musu nuni da wajen zama cike da basar da yanayin da ya ga fuskokinsu.
Abdallah ne yaja tsaki da ƙarasawa gaban table ɗin Yoohan ɗin, cike da kaushin murya yace, “Ba zaman shan ac da kallon syringe ya kawomu ba, munzo arresting naka ne”.
Ɗan jim Yoohan yayi kamar bazaiyi magana ba, sai kuma ya motsa laɓɓansa a hankali yace, “For……?”. A takaice cike da rainin wayo
A hasale Yah Abdallah ya jefa masa farar envelope ɗin hannunsa.
Da farko Yoohan baiyi niyar dubawa ba, sai dai ganin tsantsar kamannin Abdallah da su baba malam ya sakashi ɗaukar Envelope ɗin, hotunan ciki ya fiddo. A karon farko ƙirjinsa ya ɗan buga saboda cin karo da abinda baiyi tsammanin gani ba. Da kafin ya musulinta ne akazo masa da wannan hoton da yake kissing ɗin Nu’aymah bazai nuna ya damuba, amma a yanzu yana matuƙar sake ƙyamatar wannan ɗabi’ar, idan kuma ya tuna ya aikata akan kuskure yana jin matuƙar takai ci. Kallon na biyu da na ukun yay su ma, amma duk da haka sai ya dake, ya sake tsuke fuska fiye da yanda suka sameta yana jifan Abdallah da yake masa kallon tsana da ƙyama shima da kallo wulaƙanci.
Kafin wani a cikinsu ya samu damar cewa wani abu Dr Aysha ta shigo office ɗin ita da Dr Mubarak, dan sunyi knocking har sau biyu basuji ya amsa ba. A zatonsu ko yayi busy ne shiyyasa suka shigo kawai tunda sunsan babu wani mara lafiya da zai duba bayan Nu’aymah kamar yanda ya sanar musu tunkan yazo.
Da mamaki suke bin su Abdallah da kallon tsoro, sai kuma suka kalli Dr Yoohan ɗin shima. Ganin yanda ya tsuke fuska ya sakasu kasa masa tambayar dake a bakunansu, sai Dr Mubarak ne ya kalli Solomon da ya gama tsumewa da baƙin ciki. “Solomon mike faruwa anan ne?”.
Solomon zai basu amsa Yoohan ya katsesa da faɗin, “Mi kuke buƙata?”. Shiru Solo yayi dan ya fahimci Yoohan ɗin baya buƙatar ya faɗa. Suma jin hakasai duk suka sake maida kallonsu garesa, cike da ƙarfin hali Dr Aysha tace, “Dama mahaifin yarinyar ne ya zo, shine nace a shigo da shi?”.
Kansa kawai ya gyaɗa mata, sannan ya maida dubansa ga su Abdallah “Zaku iya fita ga ƙofa ko”. Ya faɗa cike da tsantsar rainin hankali. Abdallah zaiyi magana Mahmood ya matso da sauri yana nunama Yoohan I’d card ɗinsa. Hakan yayi dai-dai da shigowar Baba malam office ɗin bisa jagorancin Dr Aysha.
Mahmood da ya fara faɗin, “Muɗin jami’ai ne daga hukumar s……” ya kasa ƙarasawa saboda tozali da baba malam. Yoohan ma mamakin ganin baba malam ɗinne ya sakashi sakin hotunan hannunsa saman desk ɗin.
Baba malam kuma da duk ke binsu da kallon mamaki ya sauke idanunsa kan Yoohan a ƙarshe. Takawa yay a hankali zuwa gaban tebirin, ya kai hannu ya ɗiba hotunan dan tun daga inda yake yana hango komai na cikinsu. Ɗauka yay ya sakasu cikin envelope ɗin. Kafin ya samu damar faɗin wani abu saboda nauyi da bakinsa yay masa Abdallah yace, “Abba munafukin nan ashe likita ne anan, dan hak…….”
Baba malam yay saurin girgiza masa kai, mamakinsa na sake bayyana sosai da ganin Yoohan ɗin wai matsayin likita. Koda wasa bai taɓa kawo hakan a ransaba shikam, hasalima ya ɗauka Yoohan ɗan kasuwa ne kawai.
Yoohan dai ya gaza yin magana, kallon baba malam ɗin kawai ya ke ko ƙyafta ido bayayi. Baba malam ya ajiye envelope ɗin yana duban su Mahmood. “Zaku iya tafiya abinku mun gode”. Kamar Abdallah zaiyi magana sai kuma yayi shiru, sai ma alamar su Mahmood suje ɗin kawai yay musu da kai. Batare da Mahmood yace komaiba ya nunama yaransa hanyar fita suka fice badan ransu yaso hakanba.
Bayan fitar tasu babu wanda ya iya sake yin magana a office ɗin har tsahon kusan mintuna biyu, sai Abdallah ne keta antayama Yoohan harara, Solomon kuma na hararsu gaba ɗayansu. Dan duk haushi suke bashi.
Cikin ƙarfin hali Yoohan ya duba Dr Aysha da Solomon. Murya a sarƙe yace, “Kuje zan neme ku”. Babu wanda yay musu a cikinsu suka nufi hanyar fita kowanne da abinda yake kissimawa a cikin zuciyarsa.
“Dama kai likita ne Yahya?”.
Kai Yoohan ya jinjina ma baba malam da yay tambayar, yace, “Eh Uncle”.
Murmushi baba malam yayi a karo na farko, yace, “Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka, yay riƙo da hannunka wajen aikata alkairi ga al’umar MANZON ALLAH ”.
Cike da jin daɗi Yoohan ya amsa da “Amin” kansa a ƙasa dan ya kasa kallon baba malam ɗin, harga ALLAH kwarjini yake masa matuƙa, musamman ma yanzu da yaga hotunan nan duk da bai tabbatar da alaƙar dake tsakanin baba malam ɗin da yarinyar da har yanzu shi ko sunanta ma bai saniba.
Cike da takaici Abdallah yace, “Abba mutum nan fa shineya lalata rayuwar Nu’aymah, ta yaya zamu cigaba da fiskantarsa kamar munajin tsoronsa?”.
Da turanci Abdallah yay maganar, dan haka Yoohan yaji komai, ya kuma fahimci komai. Sai dai kafin yace wani abu baba malam ya kalli Abdallah fuskarsa na nuna ɓacin rai, sai dai kuma baice komai ba. Yanzun ma shiru Abdallah yay badan yaso hakanba, sai dai yanda yake sauke huci zai tabbatar maka cewar zuciyar ƴan mazan a wuya take.
Fuuu ya fice a fusace da ga office ɗin. Da ga baba malam har Yoohan duk binsa sukai da kallo…………✍

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/27, 2:14 PM] +234 806 269 3623: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply