Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 42


Saran Boye 42
Viral

No. 42

………….Wani irin zabura Yah Ab yayi tamkar wanda yay gamo da mala’ikin mutuwa. A tsananin razane yace, “Nu’aymah kina nufin Naseer?!!”.
Fashewa tai da wani sabon kukan tana jijjiga masa kanta. “Yah Ab kayi haƙuri, yanzu shine ya fi cancanta da hakan a gareni, kai ma dan ALLAH ina roƙonka ka maida matanka. Dan ALLAH ka kare mutuncin danginmu, karka bari wannan ya zama sanadin rusa zuminci ko saka ƙiyayya a tsakaninmu. Kayimin afuwa mu rungumi ƙaddara, UBANGIJI ya fimu sanin hikimar dake a cikin hakan. Dan……..”
Da sauri ya ɗaga mata hannu jikinsa na wani irin tsuma na yunƙurowar zuciyar tasu ta gado. Ya duba iyayensu da duk sukai tsit suna kallonsu tamkar babu su a cikin falon. Sai kuma ya duba Naser dake ta zuba murmushi idanunsa a lumshe bakinsa na motsawa alamar addu’oin godiya ga UBANGIJI yake jerawa. Batare da yace komai ba ya juya zai fice.
“Abdallah!”.
Baba malam ya kirashi cikin muryar rashin wasa.
Cak ya tsaya, sai dai bai iya juyowa ba. Cikin bada umarni Hajjo tace, “Dawo ka zauna”. Hawayen da suka cika masa idanu ya share. Kafin ya juyo a hankali ya dawo inda yake da, ya sake zama batare da yayi magana ba.
Kallon Nu’aymah dake kuka hajjo tayi. “Zainabu tashi kije mun gama da ke. Ki kuma share waɗan nan hawayen ki kwantar da hankalinki, dan munsan abinda mukeyi”. Kai kawai ta jinjina mata tana miƙewa. Batare da ta sake duban inda su Abdallah suke zaune ba ta fice a falon jikinta duk a sanyaye. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata tamkar ana gasa mata ita bisa garwashin wutar gasa balangu.

★★<>★★

Tun wannan zama da akayi Nu’aymah bata sakeji daga bakin kowa ba a gidansu. Dan zuwa yamma ma gidan sai ya sake cika maƙil da baƙi dake ta sake ɓullowa ta kowanne irin kusurwa saboda walimar da za’a gabatar daga ƙarfe huɗu. Hakama su Yah Ab bata sake ganin kowa ba a cikinsu, harma iyayen nasu. Garama Abba Musbahu taji muryarsa bayan la’asar ɗin ya shigo suna magana dasu hajjo a falo.
Ana idar da sallar la’asar mafi yawan mutanen dake cikin gidan suka fice wajen walimar. Anguwar tayi tsit bakajin komai sai karatun alkur’ani Muhammad ƙaninta ke rairawa cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗi. Lamo tai a kan gadon hajjo dan bata da sha’awar fita wajen walimar. Fitar tata zai iya fama mata ciwuka masu yawa da suka zame mata gyambo a zuciyarta. Hakan yasa ta zaɓi cigaba da zamanta tunda daga nanma tana iya jiyo komai da ake faɗa tamkar tana a wajen.
A wajen walima kam bayan Muhammad ya gama karatu baba malam ya buɗe taro da addu’a ga amare da angwayensu dama al’umar musulmai gaba ɗaya. Daga nan aka fara abinda ya tara mutane.
Duk yanda akaita ragargaza wa’azi mai ratsa jiki a kunnen Nu’aymah ne, duk ba itace amaryarba sai da ta taya su Aunty Hajarah hawaye. Lokacin sallar magrib nayi akaje akai salla aka sake dawowa. Sake ɗorawa da wasu nasihohin sauram manyan malamai abokan su baba malam sukayi. Daga haka akaci aka sha kowa yay haniƙan, aka kuma raba abubuwa kamar yanda suka saba duk lokacin aurar da yaransu ko yaran gidan marayunsu.

Lokacin da aka tashi tuni Nu’aymah data koma sashensu tai barci a falon baba malam. Umm bata sani ba, dan tana can wajen taimakawa baƙin da zasu kwana a sashenta samun wajen kwana. Sai da baba malam ya shigo wajen sha biyu sannan ya ganta kwance a doguwar kujerar falonsa ta naɗe waje guda alamar sanyi takeji. Zama yay a kujerar gefen da kanta yake yana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskar ɗiyar tasa mai tsananin kama da mahaifiyarta abar sonsa da ƙaunarsa. Ɗan murmushi yayi tare da shafa kumatunta sannan ya miƙe. Batare daya tadata ba ya cire babbar rigarsa ya lulluɓa mata. Yana jinta ta sauke ajiyar zuciya, tare da gyara kwanciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya ɗauka remote ɗin ac ya rage mata shi sosai sannan ya wuce bedroom ɗinsa cike da tausayinta.

*_JUMA’A_*

Da asuba baba malam bai wuce massallaci ba sai da ya tada Nu’aymah. Bayan an idar da salla bai jimaba ya dawo dan yau basuyi zaman karatu ba daman. A falo ya iske Nu’aymah inda tai salla tana karatun Al-qur’ani. Zama yay kallonta da sauraren zazzaƙar muryarta da a yau take fita da sanyi matuƙa. Yayi kusan mintuna arba’in sannan Umm ta shigo falon da sallama. Tray ɗin hannunta ta ajiye a gabansa tana kallon Nu’aymahn da mamaki. dan ita dai bataga wucewarta ba. Kallon baba malam tai, ya sakar mata lallausan murmushi tare da maida idanun nasa shima kan Nu’aymah da batasan sunayi ba.
Zama Umm tai a kusa da shi. Cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “Yaushe tazo nan?”. Murmushin ya sakeyi kamar bazaice komaiba, sai kuma ya ɗan sauke numfashi yana riƙo hanun Umm cikin nasa. Cikin wani irin yanayi yace, “Anan ta kwana. Nima na dawo wajen walima na sameta anan da alama bama taje wajen walimar ba”.
Guntun numfashi Umm ta furzar, batare da tace komaiba ta zare hannunta cikin nasa. Shayin daya saba sha duk irin wannan lokacin ta shiga haɗa masa. Yayinda Nu’aymah keta karatunta batare da tasan mi sukeyi ba. Sai dai tana ɗan jin motsinsu kaɗan-kaɗan, dayake hankalinta baya a tare da sune yasa batajin mi suke faɗa.

Duk hidimar da ake a gidan da sake cika da yake yi da baƙi Nu’aymah tana sashen baba malam taƙi fitowa. Yau tare da shi ma sukai breakfast. Sashen nasa ma itace ta gyara masa yau. Bayan yayi wanka ya fito ta shiga ta gyara masa bedroom ɗinsa tsaf, ta dawo falo inda yake zaune shida ƙannensa da huhunan goro dana alawa da aka shigo da su, magana suke ƙasa-ƙasa alamar tattauna wani abu mai muhimanci a garesu. Cike da girmamawa ta gaidasu, duk suka amsa mata da kulawa tare da tambayarta yaya ƙarfin jikinta.
Har zata fice baba malam yace ta koma tai wankan a bathroom ɗinsa tunda mutane sunyi yawa a gidan. Daɗi taji sosai, dan haka ta juya cike da ɗoki ta koma bedroom ɗin baba malam ɗin.

Tsaf Nu’aymah tai shiri da kayan da Umm ta kawo mata ɗakin baba malam ɗin. Lass ne ɗan ubansu sky blue da akaima ɗinkin riga da zani. Ya zauna mata ɗas a jiki tare da haskaka farar fatarta daketa ƙyalli. Ƴar ramar da tayi sai ta sake fiddo ainahin dogon hancinta da manyan idanunta masu matuƙar haske da cikar gashi. Turaren baba malam dana Umm dake a bedroom ɗin babu wanda bata fesa ba. Hakan yasa take zuba uban ƙamshi tamkar tayi wanka da turare. Gashi cakuɗasun da tayi sai ya bada wani irin shu’umin ƙamshi mai narkar da zuciyar mai shaƙa. Ɗan kwalin ta ɗaura bisa gyararren gashinta da hajjo ta matsa jiya Yah Omar ya kaita wajen wankewa tare da su Amal. Ta saka sarƙa da sauran kayan adon sannan ta ɗauki blue gyalen da aka haɗo mata da shi ta ɗora a kafaɗarta. ta zira flat shoes ɗinta suma blue. Tayi ƙyau sosai tamkar ka saceta ka gudu. Kamar yanda Umm ta gargaɗeta akan idan ta shirya ta fito ta gaisa da baƙi batayi musu ba ta nufi sashen Umm ɗin bayan ta kulle falon baba malam ta taho da key ɗin a hannunta.

Tunda ta fito jama’ar dake zazzaune a falon Umm keta ambatar masha ALLAH. Ita dai cikin ɗan jin nauyin wasu daga cikinsu ta shiga risinawa tana gaishesu. Masu tsokanarta kuwa ta kasa maida murtani. Saɓanin da da kowa yasan Nu’aymah bata barin saita kwana ga abokin wasa. da kace kule take cewa cas. Amma yau sai ga bakin ya mutu murus sai ɗan sassanyan murmushi kawai take musu a taƙaice.
Har bedroom ɗin Umm ta shiga inda ƙanen Umm da yayunta ke cike da shi. Nanma gaidasu ta shigayi. Sukam sunata amsawa cike da ƙaunar ɗiyar ƴar uwar tasu. Aunty Hibba dake cin abinci ta jawo hanunta ta zaunar kusa da ita tana faɗin, “Zauna kici abinci. Ni wannan ramar taki sam banason ganinta dota”. A ɗan shagwaɓe Nu’aymah tace, “ALLAH na ƙoshi Umma, munyi breakfast tare da Abba, kuma naci sosai ki tambayi Umm ma kiji”.
“Eh breakfast ai tun ɗazunne, kusan awa uku kenan, wannan abincin rana ne. Ke dama nasani da masifar son masa”. Duk yanda Nu’aymah taso zamewa sai da Aunty Hibba ta dinga bata masar a baki tare da naman. Sai gashi kuwa taɗanci babu laifi ta kuma shanye ƙaramar roban zoɓo data ɗauka.

★★★★

A ɓangaren su baba malam kuwa duk sun ɗunguma massallacin juma’a inda za’a gudanar da ɗaurin aure bayan sallar juma’a insha ALLAHU.
Massallacin ya cika danƙam da manyan mutane daga kowacce kusurwa ta Najeriya harma da wasu ƙasashen ƙetare. Tun daga kan malamai, ƴan kasuwa, harma da masu mulki. Sai abokan arzuƙa da ƴan uwa na kusa dana nesa. gayyar anguna dana jama’ar gari da girma da kimar su baba malam ɗince ta tarasu a wajen.
Bayan kammala sallar juma’a akai ɗaure-ɗauren aure ciki harda na ƴaƴan su baba mala su Aunty Kubrah. Ana kammalawa manyan baƙi suka ɗunguma babban hall ɗin da aka kama domin gudanar da ƙwarya-ƙwaryar walimar cin abinci.
Walimar ce ta jasu har sai bayan la’asar sannan suka koma gida da wasu tawagar baƙin da ba’a ranar zasu wuce gida ba.

Zuwa yanzun kam gidan su Nu’aymah ya sake cika danƙam da mata, dan yau ne Addah ke nata yinin bikin. Hayaniya akeyi sosai babu maijin wani. Dan tun bayan ɗaurin aure su Omar sukaje gidan da labarin yanda komai ya kama.
Nu’aymah na tsakkiyar dangin Umm har yanzu. Sun sakata a tsakkiya anata hirar zuminci cike da farin ciki. Wata Gwaggon su Umm ce, data kasance kaka ga Nu’aymah ta shigo ɗakin tana guɗa. Da mamaki duk suke kallonta har suna rige-rigen faɗin, “Gwaggo an ɗaura ne?”.
“Ƙwarai da gaske an ɗaura. Yanzun ma haka ƴan ɗaurin aure sun dawo, kuma harda sabon albishir na ƙarin amarya”.
Aunty Fareeda tace, “Ƙarin amarya kuma Gwaggo? A cikin yaran gidan dai?”.
“Ƴarku ma kuwa” ta sake basu amsa tana cillara wata sabuwar guɗar. Kafin su gama fita daga ruɗani su Nanah suka shigo suna ƙwala kiran “Nu’aymah amarya”.
Dakatar dasu Aunty Hibba tayi. “Kai mufa kuna sake ɓatar damu, Gwaggo wai mike faruwa?”.
Da sauri “Raudah tace, “Momy baku san Nu’aymah ma an ɗaura mata aure ba yanzu tare da su Aunty Hajarah. Yanzun ƴan ɗaurin aure da suka dawo suke faɗa ai”.
A take ɗakin ha harmutse da murna da taraddadin wanene angon? Miyasa kuma aka ɓoye musu, dan su dai basusan da auren ɗiyar ƴar uwar tasu za’ayi ba. Duk sunzone yima Addah baici kasancewar zumincine mai ƙarfi da kowa ya sani a tsakanin Umm da ita.
Tunda aka fara wanan kace nace Nu’aymah ta ɗora hanunta saman kai ta riƙe. Cusashi tai a tsakanin cinyoyinta jikinta na wani irin tsuma. Ga kanta ya fara sara mata sama-sama. Duk yanda taso ta daure ta kasa. Dan haka cikin ƙarfin hali ta shiga laluben wanda ke a kusa da ita. Cikin sa’a ta damƙo hanun Aunty Magajiya yayar Umm. Hankali tashe Aunty Magajiya ta dubeta, sai kuma yanda taga jikin Nu’aymahr na karkarwane ya sakata ambaton ‘Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un’ da ƙarfi.
Kusan mafi yawan ƴan ɗakin sai hankalinsu ya dawo wajen. A take kuma sai duk sukai tsitt tare da zabura kan Nu’aymah……

Gwaggo Ramma ce ta hana ɗaga maganar mawuyacin halin da Nu’aymah ke a ciki a gidan har lokacin da su baba malam suka dawo. Dan Umm ma bata fasa kai da kawowar da takeyi tsakanin sashen Addah da sashentaba saboda son ganin baƙi kowa ya samu abinci. Yin komai takeyi cike da ƙarfin hali. Sai ta fakaici idon mutane take share hawayen dake cika mata idanu. Duk da kuwa ita tasan da maganar auren. Kuma tana cikin masu goyen bayan ɗaurashi a yau ɗin saboda wasu dalilainsu ita da baba malam da hajjo.
Key da baba malam bai gani bane a inda suke ajiyewa ya sakashi kiran wayarta. Cikin sa’a kuwa wayar tana a tare da ita. Dan haka ta ɗaga ya sanar mata gashi ya shigo amma baiga key ba. Ta kira masa Nu’aymah ko ta canja masa waje.
“To” kawai tace masa ta yanke wayar.
Ɗakinta ta fara shiga inda danginta ke zaune jigum-jigum da Nu’aymah shimfiɗe bisa gado tana fidda wahalallen numfashi tamkar mai Asthma. Aunty Juwairiyya sai shafa mata ruwa take a fuska wasu kuma na tofa mata addu’oi. Wani Key ɗin ta ɗauka a drawer ta fita batare da tace musu komaiba ta fice.
A kallo ɗaya baba malam ya fahimci akwai matsala. Tunkanma ta buɗe ya shiga jero mata tambayoyi akan mike damunta?. Sai da ta buɗe ƙofar suka shiga sannan tai masa bayani. Shima hankalinsa ne ya tashi, dan haka yace taje su maido Aymah sashensa, karsu bari kowa kuma ya fahimci halin da ake ciki. Bara ya kira Doctor.

Tunda aka dawo da Nu’aymah sashen baba malam ALLAH ya bata ikon ganinsa saita damƙe hannunsa tana cigaba da jujjuya kanta da fisgar numfashi a wahalce. A hankali take magana wadda idan ba’a kusa da ita kakeba ma bazakajita da ƙyau ba.
“Abbah kaina, kaina zai fashe Abbah. Kamin addu’a kaina zai fashe, Abba kamar ana kartamin ƙarfuna a ciki. Innalillahi… Abbana zan mutu..”
Cikin rawar harshe baba malam yake girgiza mata kansa da haɗiye abinda ke cinkushe masa maƙoshi da ƙyar. “Bazaki mutuba Mamana kinji, daina magana kiyita addu’a a ranki insha ALLAH ga Doctor nan zuwa kinji”. Ya ƙare maganar da saka ɗan yatsa ya ɗauke hawayen da suka tsatstsafo masa saman fatar ido. Hajjo da Ananah ma hawaye sukeyi. Haka su Abban Abdallah ma duk zukatansu suya suke da tausayinta.
Sallamar da akayi a bakin ƙofarne ya sakasu duk kallon ƙofar tare da amsawa. Ahmad ne ya fara shigowa, yana sanye cikin tattausan farar shadda harda babbar riga. Har yazo tsakkiyar falon sai kuma ya ɗan juya ganin wanda suke tare bai biyosa ba. “A’a Doctor shigo mana”.
Kusan seconds biyar kafin a ɗaga labulen ya shigo bakinsa ɗauke da tausasa kalaman sallama. Sanye yake cikin wata shegiyar bugaggiyar shadda getzner kalar royal blue. Wando da riga harda babbar riga. Sai hular zanna daya murza itama royal blue data samu nutsatstsiyar saƙa. Hatta da agogon dake a tsintsiyar hannunsa kalar blue ne. Wanda bai saniba sai ya ɗauka wannan ɗin itace shigarsa dama can tun fil azal. yayi ƙyau harya gaji a cikin kayan. sun sake fidda masa kwarjini da cikar haiba da kamala. Farar fatarsa ta sake haskawa tamkar wata ɗan daren sha biyar. Yanda sajen fuskarsa da kwantaccen gashin kansa dake baƙi siɗik kwance a ƙeyarsa suke ɗaukar ido babu tababa zaka iya sakashi a jinsin larabawa. Idanba faɗa maka akaiba bazaka taɓa yarda Dr Yoohan ɗan gidan Papa da Madam Chioma ne ba wanda ko hausar bai gama fahimtar inda ta dosa ba balle akai ga larabci.
A hankali ya cigaba da tako ƙafarsa dake sanye cikin baƙar safa cikin falon, dan ya cire takalman a ƙofa.
Tunda yay sallama  Ananah da Hajjo suka zuba masa idanu cike da jin daɗin isowarsa a kan lokacin da ya dace. Umm kam kallo ɗaya tai masa ta maida idanunta ƙasa tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Cikin girmamawa ya gaida su Hajjo. Suma sun amsa masa da kulawa harda ƴar tsokana. Kaɗan gefen bakinsa ya motsa alamar murmushi. Dan bayan gaisuwar baiji mi suka faɗa ba sam tunda da hausa sukai magana.
Baba malam da ya tashi daga inda yake zaune ne ya nuna masa alamar ya zauna anan. Bai musaba ya zauna idanunsa akan Nu’aymah da har yanzu take riƙe da kanta. Sai da yay mata kusan kallon minti ɗaya da wasu sakanni sannan ya ɗago. Ɗan kallonsu yayi sai kuma ya sake maida idanun nasa kan Aymah.
Da sauri Ananah tace, “Ɗan nan ko akwai matsala ne?”. Ya ɗanji wani abu daga zancen nata. Sai dai bai iya haɗasu a jimlace yanda zai fahimta ba. Hakanne ya sakashi kallon Ahmad dake ɗan murmushi. Faɗa masa abinda tace yayi, hakan yasa Yoohan cewa, “No babu damuwa Mama. Sai dai a ringa kula, indai zata ringa shiga irin wannan yanayin akwai matsala. Aikinmu zai dinga komawa baya”.
“Yoni yaro bafa jin wannan yaren naku na masu jajayen kunne nake ba, kai Amadu fassara mana mi yake cewa”. Ananah ta faɗa da iya gaskiyarta.
Gaba ɗaya su baba malam murmushi sukayi dajin zancen Ananah. Umm ma saita nufi ƙofar fita ita dai tana nata murmushin. Cike da ƴar tsokana Ahmad yace, “Gaskiya Abba kubani kwangilar maida Hajjo da Ananah makaranta, dolene su fara jin turanci kwanan nan”.
Daƙuwa Abban Adawiya yay masa. Yayinda Hajjo ta talle masa ƙeya tana faɗin, “Kaci gidanku Ahmadu. Yo turancin banza turanci wofi. tunda munajin yaren da ALLAH yayimu a cikinsa muna kumajin yaren dayafi kowanne daraja, yaran MANZON ALLAH larabci ai mungama nasara. Kune kuka ɗauki amanar kanku kuka miƙama masu jan kunne shiyyasa gashinan kullum sai hanyoyin wajiga rayuwarmu suke ƙara ƙirƙirowa. Shima Yahaya ɗin kwanan nan dan gidansu sai ya fara iya hausar”.
Duk da Yoohan bajin abinda ta faɗa yay ba, baisan sanda murmushi ya kufce masa ba ganin yanda take masifa akan Ahmad tana duddungure masa kai hularsa har tana matsawa baya. Su Baba malan kuwa sai zuba murmushi sukeyi. Sosai abin nasu sai ya birgesa, musamman daya tuna nasa kakannin da kullum babu abinda sukafi ƙwarewa sai masifa da faɗa kamar kajinaye…….
Hannunsa da Nu’aymah ta riƙo ne ya sakashi saurin juyawa gareta. Cikin yanayin ciwo ta sake matse lallausan tafin hanun nasa cikin nata tare da ɗorasa bisa kanta, “Abbah ka riƙemin zai fashe”.
A hankali Yoohan ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. Baiyi magana ba, bai kuma janye hannunsa data ɗora akanta ba ta danne da hannunta kuma.
“Inaga mu bara mu barka kayi aikinka”. Ya tsinkayi maganar Abban Abdallah a cikin kunnensa. Janye idanunsa yay daga kallon da yakema Aymah, sai dai kafin ma ya ɗago su duk sun fice. Hajjo da Ananah da Ahmad kawai aka bari.
Baice komaiba sai hannunsa da yay ƙoƙarin janyewa daga kanta. Amma sai ta sake riƙesa da ƙyau tana faɗin, “Abbah Please karka tafi ka barni, kaimin addu’a kaji Abbana”.
Sosai tausayinta ya sake lulluɓe su Hajjo. Yoohan ya ɗan matsar da kansa kusa da nata kaɗan, a hankali yace, “Ki daina magana zan baki magani yanzu zai daina insha ALLAH”.
Tabbas taji muryar ba Abbahn ta bane, amma halin da take ciki bai bata damar banbance wanene ɗinba sam.
Kallon Ahmad Yoohan yayi, yay masa nuni da box ɗin da suka shigo yana faɗin, “Brother Please ko zaka iya haɗamin allurar nan?”. “Yes! Doctor babu damuwa”. Ahmad ya bashi amsa yana jawo box ɗin.
Wata irin zabura Nu’aymah da zancen ya shigarma kunne tayi, batare da sun fargaba suka ganta tsaye bisa ƙafafunta jikinta na rawa. “Bana son allura, Abbah! Abbah! banason allura…” ta faɗa a wahale tana riƙe kanta da hannu biyu duka tai baya luuuu zata zube.
Cikin zafin nama Yoohan ya miƙe tsayen shima, hakan yasa Nu’aymah faɗawa jikinsa nata jikin na wani irin karkarwa. Saurin riƙota yayi shima yana faɗin, “Relax, Please calm dawn!”
Ina batama san yana faɗa ba, kanta kawai take jujjuyawa a ƙirjinsa da faɗin, “Banason allura, Abbah banaso”.
“Okay shike nan, kinga baza’ai mikiba, ya isa ki daina magana, tana sa miki ciwo kai”. Yay maganar da ɗaukarta gaba ɗayanta ya maida a kujerar zai kwantar. Sake ruƙunƙumesa tai, sautin muryarta na ƙara fita da ƙarfi wajen faɗin, “Abbah karka bari sumin allura dan ALLAH ” ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
Su dai su Hajjo duk wannan drama dake faruwa suna tsaye ne suna kallonsu, Ahmad dake murmushi yace, “Hajjo kumuje kawai mu barsa da ita, nasan zaiyi duk dabarar data dace yay mata insha ALLAH ”.
Cike da gamsuwa suka amsa masa. Allurar ya matsa ya miƙama Yoohan da Aymah ta kanannaɗema jiki kamar mage ta samu katifar audiga. “Gashi, bara mu baka waje kai aikinka Doctor ”.
Yoohan zaiyi magana Ahmad ya ajiye syringe ɗin da sauri yabi bayan su Hajjo da har sun fice abinsu…………✍

Likita bokan turai😉😜.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

 

I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply