Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 47


Saran Boye 47
Viral

No. 47

………..Sosai Nu’aymah tasha barcinta. Dan sai gab da la’asar ta sake farkawa. Yanzun kam Alhmdllh garas take jinta, sai dai jinta take wata fiyau tamkar iska zata ɗauketa ta yada saboda rashin nauyi. Wanka ta fara yowa da alwala. Tazo tai salloli sannan ta kimtsa ɗakin duk da bayyi wani datti ba. Tunda ta buɗe kwanikan dake saman tray ɗin da ke bisa centre table sau ɗaya bata sake ba. Sai ƙunƙuni da ta dingayi akan ita bazataci wannan jagwalgwalon abincin ba yasin. Dan duk da uban naman dake cikin miyar baiko birgeta ba.
Tsaf tai shiri cikin riga da sket na atanfa. Kayan sun mata ƙyau sosai. Tana cikin saka turare aka turo ƙofar. Saurin juyawa tayi danjin babu wani knocking balle a kai ga sallama. Haushi ya tuƙeta ganin Yoohan ne. Ta ɗauke kanta tana ɓata fuska.
Yoohan da waya ke manne a kunnensa alamar magana ya keyi da wani shima ɗin dai kallo ɗaya yay mata ya ɗauke idonsa, zama yay a kan sofa ya cigaba da sauraren abokin wayar tasa dake masa bayani daga can. Ita Aymah ma harta fara tunanin ko wani sabon wulaƙancine ba wayar yake ba. Dan ya kusan mintuna sha biyar wayar na kunnensa amma baice komaiba.. Dai-dai ta ɗago ta kallesa taji ya ɗan sauke numfashi, sai kuma ya fara magana a hankali cike da nutsuwa. Harga ALLAH bazata ɓoye ba muryarsa na mata daɗi. Ita bata buɗe yanda zaka tsorata mai sauraro ba, ba kuma ta sirance kamar ta mata ba. Tana fita da kauri da amo musamman daya kasance shi ma’abocin magana ne a nutse.
Haka ta dinga satar kallonsa harya kammala wayar. Ya cire daga kunne yana ɗago idanumsa kanta. “Am sorry, Assalamu alaiki”. Ya faɗa yana janye idanun kanta lokaci guda. Amsa masa tayi fuska a tsuke, kamar zata ɗauke kanta sai kuma ta sake dubansa. “Nifa yunwa nakeji”.
Da mamaki ya kalleta, sai kuma ya duba tray ɗin dake a jiye a wajen. Tabbas bana safe bane. Kulolin ya buɗe batare da yace mata komaiba. “Shi wannan abincin kuma fa?”. Ya faɗa yana kallonta. Baki ta kunbura tana wani sake tsuke fuska, “Yoni bazanci wannan abincin ba, dan ban iya cinsa ba”.
Shiru ya ɗanyi yana kallon abincin shima. Eba ne da wata miya da suke kira Abak Atama soup (miya ce da mutanen Akwa ibom state suke yinta) taji uban nama sai ƙamshi takeyi. Tabbas yasan da wahala ta iya ci ɗin, tunda abincine irin nasu. “Mi zaki ci to?”. Yanda yay maganar a daƙile ne ya sakata sake jin haushinsa, tai masa harar gefen ido. Kamar bazata faɗa ba sai kuma tace, “Noodles”.
Batare da ya ƙara kallonta ba ya ɗauka waya yay kiran Joy. Ring biyu kuwa ta ɗaga. Ko gaisuwar datai masa bai amsa ba yace, “Dafa min Noodles”. Daga can tace, “Okay Brother, and egg?”. Bai amsata ba, sai duban Aymah da yayi, wadda ya tabbatar tana jinsu tunda a Hans free ya saka. Kanta kawai ta ɗaga masa ta ɗauke idonta daga garesa. Amsa ya bama Joy ɗin da faɗa mata inda zata kawo ya yanke wayarsa.
Daga haka ɗakin ya ɗauki shiru, shi dai wayarsa ya keta latsawa, ita ko tana zaune a stool ɗin mirror ne kawai tana kallonsa ta ciki fuska a kumbure. Ba komai ke cinta ba sai kewar gida da yunwa. Damuwace fal ranta, a kallo ɗaya kuma zaka tabbatar da hakan.
Knocking ɗin da akayi ne ya sakashi faɗin “Shigo” a taƙaice batare da yako ɗago daga abinda yakeyi ba. Gabansa Joy taje ta ajiye tiren batare data kalli inda Aymah take ba, “Broth gashi, nikam inata mamaki, wai kai ne da cin Noodles yau a gidannan?”.
Wani mugun taɓe baki Aymah tayi ta ɗauke kanta daga kallonsu, a ranta kuwa rayawa take saita saita kan joy ɗinnan a layi idan har tace zatai mata hauka. Dan duk da ta girmeta sosai ai ita yanzu matar yayanta ce dan ƙaniyarta. (Madam son girma😚lol).
Yoohan kam da ya gama sauraren Joy a taƙaice yace, “Thanks”. kawai. Duk da Joy tasan halinsa, ba kuma yau ne farauba sai na yau ɗin yay mata zafi saboda agaban Nu’aymah ne. A hasale ta nufi ƙofa tana harar inda Nu’aymah take. yanda ta fisgi ƙofar ɗakin da zata rufe ne ya sakashi ɗagowa, sai dai kafin yace komai ta bar wajen da gudu.
Shiru yay baice komaiba, sai idanunsa daya maido kan Nu’aymah. “Kizo kici zamuje ki gaida Momy da Papa”. Batare data dubesa ba tace, “Badai mai wancan zaƙo-zaƙon farcen bace ta dafa min ko?”. Yanzun kam sosai Yoohan yake kallonta, a ransa yake faɗin, ‘Yarinyar nan muguwar ƴar matsala ce wlhy’. A fili kam fuska ya ƙara tsukewa yana tsatstsare ta da idanu. “Kina ɓatamin lokaci malama, inada abu mai muhimmanci a gabana”. Kanta ta maida gefe tana ƙyaɓe baki, cikin ƙunƙuni da hausa tace, ‘Da waye ya gayyatoka anan balle ka ɗagan hanci’. Ta ƙare maganar tana tasowa inda yake. dan harga ALLAH wata shegiyar yunwa kecin hanjin cikinta.
Shikam baima sake bi takanta ba, ya cigaba da sabgar gabansa a wayar. Ba ƙaramin danne zuciya Aymah tayi ba wajen zaman cin indomie ɗin nan. Dan babu abinda ke zuwa mata a cikin rai sai farcen dake a hannun Joy zaƙo-zaƙo da tarin gashin dokin da akai mata kitso da shi kamar jikar bammali. Ko rabi kuwa bataci ba ta ture gefe.
Kallonta yay fuska a tsuke, cike da ƙosawa yace, “Wazai ci miki wannan ɗin?”. “To oho, ni dai na ƙoshi, yama zaka saka wancan mai farcen da Attachment ɗin kamar ɗiyar bammali taimin girki. Wanda naci ma da wahala ya zauna dan amai nakeji dana tunota. Ga uban bleaching tayi sai ƙarni takeyi”.
Sosai yaji zafin abinda take faɗa akan ƴar uwarsa, amma sai yake mata uzirin ƙuruciya ce kawai ke ɗauwainiya da ita. Watsar da ita yay bai sake duban ko inda take ba har tsahon mintuna uku. Kafin ya miƙe yana zura wayarsa a aljihu. “Muje” ya faɗa a taƙaice yana yin gaba abinsa.
‘Tab! Wai kaji haushi ne dan na faɗa abinda ke raina? Aiko aiki ya sameka, dan bazan ga abin maganaba nai shiru bakina yay wari. Da wani kansa kamar mulmulen furar hajjo’. Tai maganar tana miƙewa. Dan itama zaman ɗakin ya fara isarta kuma. Tanason taga gidan yaya yake?. gyale ta ɗauka da yay dai-dai da atanfar ta biyosa. A falo ta samesa tsaye, batare da yayi magana ba yay gaba ta bisa a baya suka fice.

Tun daga bakin ƙofar sashesa take ƙarema gidan kallo, babu ƙarya gidan ya haɗu, musamman idan kana sama kake kallon tsarin falon ƙasa. Hakama idan kana a ƙasa kake kallon upstairs ɗin. Ga koma tsaf babu wani datti alamar dai ana kula da tsaftar gidan yanda ya kamata. A yanzu haka ma’aikatan gidan daketa shara da goge-gogen yamma sai risinawa suke suna gaishesu. Shi kaɗai yake amsawa. Ita kam binsu kawai take da kallo da takaicin ganinsu ƙattan maza.
Ta saman upstairs ɗin suka nufi sashen Momy dake jikin na papa. Corridor ne mai ɗan faɗi da ƙofofi uku a cikinsa. saɓanin Nasu da zaka iske falo. Knocking ɗin ƙofar tsakkiya yayi. Daga ciki wata murya ta amsa. Juyowa yay ya ɗan kalleta sannan ya tura ƙofar. Ita dai biye take da shi. Yanda taji yace, “Excuse me” itama Excuse me ɗin tace a hankali.
Murmushi madam Chioma dake waya da ƙawarta tana bata wasu dabaru ta saki saboda ganin rabin ranta. A yau ɗin nan duk da zafin zazzaɓin nan da takeji sai taji a ranta garama da take yinsa. Dan koba komai a dalilin zazzaɓin ta samu kusanci da lokacin yaronta mai tsaho tare da ita. A gaba ɗaya yinin yau sai zirga-zirga ya keyi a kanta da son ganin jikinta ya dai-daita. Ɗazuma da taita langare masa yafi awa biyu zaune tare da ita.
A hankali kuma sai fara’ar fuskar tata ta fara gushewa saboda ganin abinda ke a bayansa…….
“Masha ALLAH Mom sauƙi yazo sosai” ya faɗa yana zama a gefen gadon nesa da ita kaɗan batare da ya lura da canjawar fuskar tata ba. Nu’aymah kam dake mata kallon ƙasan ido taga komai da madam Chioma tayi, murmushin farko da canja fuskarta da tai saboda ganinta. Dai-dai Aymah na zama bisa sofa ɗin ɗakinne Momy ke bama Yoohan amsar maganarsa. “Ƙarfin haline kawai my boy, dan dana tashi ma kamar zan kiraka kazo ka sake dubani sai nayi tunanin ko baka a gidan ne?”.
Ɗan murmushi kawai yayi batare da yace komai ba, saboda gaisheta da Nu’aymah keyi. Shiru tayi kamar bazata amsaba, ita kuma Aymah daga gaisuwar nan guda ɗaya bata sake wata ba.
“Mom tana gaisheki fa”. Ya faɗa yana kallonta. Daburcewa ta nema yi, dan batai zaton zai saka baki ba. Cikin kame-kame tace, “Oh Daughter Am sorry, hankalina nakan Son, kina lafiya?”. Cike da mamakinta Aymah tace, “Alhmdllh” daga haka taja bakinta tai tsit fuska babu walwala. Itama Madam Chioma bata sake bi takan Nu’aymah ba. Gaba ɗaya hankalinta naga Yoohan. Sai takalarsa da zance take yaƙi magana ƙwaƙwƙwara, daga guntun murmushi sai um sai a’a. Ita Aymah ma abin dariya yaso bata. A ranta sai gulmar ɗan da uwar takeyi tana kwasar dariya. A fili kuwa fuskarta babu ko ɗigon walwala a cikinta. Ta tsume abinta kamar tama manta da su a ɗakin.
Sosai Yoohan yake lure da ita, amma idan ba shiba bazaka taɓa fahimtar hankalinsa na gareta ba. Agogon hannunsa ya kalla yana faɗin, “Momy bara muje ta gaida Papa nasan ya shigo yanzun”.
“A to muje sai na rakaku ai” ta faɗa tana miƙewa. Da sauri Yoohan yace, “Haba Momy, keda ke fama da kanki”. “Karka damu ai da sauƙi” ta faɗa tana bin bayan Aymah da tunda ya ambaci tafiyar har ta kai ƙofa. Bayansu kawai yabi yana mamakin halin Momynsa.

Koda suka fito Aymah tsayawa tai baya suka wuce gaba tunda sune ƴan gida. Sun shiga sashen papa dake da falo babba, dan har yafi nasu girma ma. bata cuci kanta ba, koda suka zauna sai da ta ƙarema kowace kusurwa ta falon kallo lokacin Momy ta shige bedroom ɗin papa dan basu sami kowa a falon ba. Yoohan kuma yanata latsa waya.
Lokacin da suka shigo shima papan ta ƙasan ido ta gama ƙare masa kallo tsaf. Shima ƙyaƙyƙyawa ne kuma fari, dan suna kama da Yoohan, sai dai Yoohan ya fisa ƙyau da ƙwarjini da ƙuruciya. Da alama dai Yoohan ɗin ya kwaso kamannin wanu bayan shi. Papa na zama Aymah ta zamo ƙasa ta zauna. Ba Yoohan ba har Madam Chioma hakan da Nu’aymah tayi ya bata mamaki. A ranta kuwa ayyanawa take, ‘Wato ni wannan ƴar shilar yarinyar ta raina kenan?, ina zaune sama tana zaune itama a ɗakina’.
Maganar papa ce ta katse madam Chioma. Cikin fara’a sosai yake amsa gaisuwar da Aymah ke masa, harda haɗawa da ƴar tsokanarta. Itako tanata zuba murmushi kanta a ƙasa. Tambayoyi ya rinƙa mata dake nuna kulawarsa a gareta. Hakan ne ya sakata ɗan sakin jiki da shi tana bashi amsar da duk ya buƙata.
Shi dai Yoohan ma abin sai ya bashi mamaki, dan koshi bata sakin jiki da shi kamar hakan. Papa daketa murmushin jin daɗin yanda Aymah ta saki jikinta da shi ya dubi Momy yana faɗin, “Darling a tattaro min duk members na gidan nan da masu aiki, zan gabatar musu da daughter in-low ɗina. Itama na gabatar mata da su.
Cikin ɗan yatsine fuska madam Chioma ta miƙa hannu ga wayar landline dake a table ɗin jikin kujerar da suke zaune ita da papan ta hau danne-danne. Kira tayi, bayan an ɗauka daga can tace, “Joy, ki sanarma kowa na gidan nan yazo Master parlor yanzun nan”.
“Okay maa!”
Joy ta amsa daga can tana ajiye wayar.

Cikin mintuna ƙalilan kowa ya shigo falon, hatta da maigadi bai zaunaba, kulle gate ɗin yayi ya taho. Shi dai Yoohan kamarma baya cikin falon. Babu wanda ya damu da shariyar tasa tunda sunsan halinsa kenan. Victoria ce ma uwar surutu taje jikinsa zata zauna ya harareta. Da sauri ta canja mazauni tana tura baki gaba na shagwaɓa.
Sai da kowa ya nutsu sannan papa ya fara magana. “Na taraku anan ne domin na sake tabbatar muku da ƙaruwar member da family ɗinmu ya samu duk da nasan kun sani. Karku ganta ƴar ƙarama kuce zaku ɗauketa ƙasa da ku, har wani raini ko abu mara ƙyau ya faru a tsakaninku. Duk wanda ya aikata hakan zan saɓa masa da saɓawa mafi ciwo. Dolene kowa na gidannan idan ka cire su mama da Darling dake matsayin kakanni a gareta da Uwa kowa ya bata girmanta. Saboda mata ce ita a wajen John, kowa kuma yasan a gidan nan bayan ni John shine uba, dan shine babban ɗana abin alfaharina. Sunanta Zainab, amma ana kiranta Ayimah. My daughter ko ba haka bane?” ya ƙare maganar yana kallonta. Murmushi Aymah tayi, batare data ɗagoba ta gyara masa da cewar, “Nu’aymah”.
Sake maimaitawa yayi duk da dai yanzunma bai faɗa dai-dai ba. “Nasan dai baku manta da sharaɗin John ba. Zainab ɗago kanki zan nuna miki kowa da sunansa anan kema”.
Babu musu kuwa ta ɗago, dan ganinsu cike da falon baisa taji ko ɗarba a ranta saboda tun fil azal ita ALLAH yayita mutum mara tsoro. “Wannan itace mamana sunanta Mama debora. Itace ta haifeni tare da ƙannena. Maza mu uku, mata su biyu. Gasu nan”  ya nuna ƙannensa biyu mata dake zaune a wajen. Maman Favour, da maman Destiny. “Akwai maza biyu suma zan nuna miki su idan sunzo. Sai wannan itace Maman Darling. Momyn John kenan gata nan” ya nuna madam Chioma da mamanta. Daga haka ya dawo kansu Joy, Gebrail, Abraham, Victoria ƙannen Yoohan kenan. Sai Miracle ɗiyan ɗan uwansa Uncle Mike. Sai Aunty Blessing kuku, daga haka ya koma kansu Solomon daki-daki da ayyukansu a gidan duk ya sanar mata har zuwa kan maigadi.
Cikin murmushi tace, “Nayi murnar haɗuwa da ku duka”.
A tare suma duk suka amsa mata da hakan, duk da dai da yawansu ba har cikin zuciya bane ba. Sun faɗane kawai saboda tsoron Yoohan da duk abinda sukeyi yayi kamar baya falon.

Sallamar ma’aikatan gidan ya farayi, kafin ya sake duban family nasa ya shiga musu nasihar zaman lafiya (Su papa kenan😂lol). Daga haka ya sallami su Miracle ma daketa antayama Aymah harara ta ƙasan ido ita da joy. ya rage daga shi sai su mama debora da su maman Destiny. A gabansu ya fiddo keys ɗin mota guda biyu ya miƙama Nu’aymah ɗaya.
“Dota wannan shine wedding gift ɗinki daga ni. Kai ma John ga naka. ALLAH ya sanya muku albarka a cikin aurenku”. Da hannu biyu Aymah ta amsa bayan taje gabansa ta durƙusa. Tai masa godiya sosai. A ranta kuma tana addu’ar ALLAH ya shiryesa idan yana da rabo, idan baida kuma ALLAH yay maganinsa. Shima oga Yoohan ya amshi nasa. Tare da rungume papansa yana mai nuna masa jin daɗinsa da waɗannan ƙyaututtuka shi da matarsa. Buɗe masa hannaye madam Chioma tayi wai itama ya bata hug…. Kafaɗa ya maƙale mata yana faɗin, “Sai kin bamu naki gift ɗin sannan”.
Kusan a tare duk falon akai dariya. Banda Aymah da sam abin ita bai birgeta ba. Dan haka kawai madam Chioma duk da mahaifiyar mijin nata ce batai mataba ko kaɗan. Su mama debora ma duk sun bama Yoohan ƙyauta, amma basu bama Aymah ba. Ko a jikinta ita kam, dama bata buƙata. Ganinma lokacin salla yayi saita miƙe tana faɗin ita zataje tai salla lokaci yayi.
Papa ne kawai ya amsa mata. Sai Yoohan da ya bita da kallo saboda ganin yanda tai maganar kanta tsaye babu wani inda-inda a ciki. Harga ALLAH ta birgesa, dan da watace sai tai ta nuku-nuƙu musamman data san su ɗin sun rinjayeta a gidan.
Ko kallon inda yake bataiba tai ficewarta, dan tasan zata gane hanya abinta. Acan downstairs ta hango su Miracle sun baje suna kallo, ta girgiza kai da taɓe baki tana faɗin, ‘ALLAH ka rabamu da gafalalliyar rayuwa dai’.
Sai da ta tsaya a falon ta gamai masa kallon tsaf tana jinjina yanda ya haɗu, da jin ƙaunar iyayenta. Ganin zata makara salla ta nufi hanyar bedroom. Tana buɗe ƙofar zata shiga aka buɗe ta falon. Kallon inda ƙofar take tayi, ganin shine ya sakata ƙarasa shigewa batare data nuna alamar tasan da shigowar tasa ba. A fili ta furta, ‘Ai nazata tuban mazuru kayi, bazaka taso kayi sallan ba’.
Oho, shidai baisan tanayi ba. Dan ɗakinsa shima ya shige kai tsaye dan gabatar da sallar, tunda an ja masa makara bai tafi massallaci ba.

________★★★★________

“Wai nikam murmushin mi kike tayi hakane Jannat? Tun jiya ina lura dake Murmushin nan ya kasa barin ƙyaƙyƙyawar fuskarnan taki”.
Murmushin Umm ta sake yi tana kallon mijin nata da take ɗunbin so da ƙauna. Sai da ta miƙa masa kofin ruwan data zuba masa kafin tace, “Wlhy idan na tuno Nu’aymah tabar gidan nan sai naji wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali. Duk da ina fargabar inda ta tsinci kanta kuma a yanzu. Sai dai inaji a raina bazata bari a cuta mataba acan tunda tasan suɗin su wanene. Amma a gidan nan da bakasan wanene mai SARAN ƁOYE ba tayaya zakai taka tsantsan da al’amarinsa. ALLAH ya ƙarama Hajjo tsahon rai da nisan kwana. Dan nasan ita ɗin babbar garkuwa ce a garemu a gidan nan. Kaga yanzu saimu gani, yarinyarmu ce ba’a buƙata a gidan? Komu kanmu ne?”.
“Gaskiyarki Jannat, koni inajin nutsuwa ta musamman a zuciyata tun bayan ɗaura auren mamana. UBANGIJI shine masani akan wannan auren na Yahya da mamana ya ƙumsa. Dan maybe da ɗaya daga cikin su Abdallah ta aura salamar da muke mata fata bazata taɓa samunta ba. Sai ma wasu sabbin fitintunu ne zasu cigaba da bayyana ƙilama har sai mun rasata gaba ɗaya. Amma kinga a yanzu aurenta da yaron nan zan jefa tsuntsu uku ne da dutse ɗaya”.
“Tsuntsu uku kuma Abban Nu’aymah?”.
“Ƙwarai kuwa Jannat. Na farko zan ƙara ƙarfafa gwiwar Yahya akan musulinci, zata taimakesa akan dukkanin ilimin da yake buƙata na sanin musilinci. Na biyu Mamana zatayi ibadar aure, ta kuma samu lafiya da kulawa mai inganci akan lalurarta. Na uku zataimin wani aiki da zuciyata ta kasa daina min kokwanto a kansa. Maimakon inji na ajiye batun, kullum sai sake jin ƙwaɗayin tabbatar da gaskiyarsa nakeyi”.
“Ikon ALLAH, Abban Nu’aymah minene shi kuwa wannan al’amari?”.
“Zan faɗa miki shi Jannat, ki bani lokaci na gama neman zaɓin UBANGIJINA akansa sannan”.
“To UBANGIJI yayi jagora Abban Nu’aymah, ALLAH kuma ya tabbatar da alkairi a cikin al’amarin”.
“Amin ya rabbi Umm-Muhammad. Yanzu yaya batun mai aikin da mamana ta buƙata?”.
“Karka damu za’a nema insha ALLAH, bandama rigima irin tata mizatayi da wata ƴar aiki tunda nasan can gidan bazasu zauna babu ma’aikata ba”.
“Eh duk da haka dai a nema mata. Koba komai zata samu yarenta a cikinsu, ko wani abinne ya dameta ta faɗa mata kafin mu mu sani. Shiyyasama nake ganin ko haƙura zakiyi ki bata Rabi’atu, tunda kinga ta saba da ita sosai, akwai shakuwa tsakaninsu sannan itaɗin ba yarinya bace zata taimakamata da shawarwarin zaman rayuwa”.
“To banƙi ta taka ba Abban Nu’aymah. Sai dai kasanfa ko sanda Nu’aymah na gidan nan ba shan inuwa ɗaya sukeyi da Rabi ba. Inaga ka fara tambayarta idan tanason a bata ita sai taje. Idan bataso sai a aika mata wata ɗin. Dan kasan halin butsutsun yarinyarka ɗin nan ba man kai ne da ita ba sam”.
Dariya baba malam yay tayi da zancen matar tasa. Daga haka suka cigaba da firarsu duk kusan kashi biyu na firar akan Nu’aymah ne. Da kaji kasan cike suke da kewar ɗiyar tasu da begenta. Sai dai dattakonsu ya danne komai suna binta da fatan alkairi a zuci da fatar baki…..

*_ABUJA_*

Nu’aymah bata sake ganin Yoohan ba ko wani a jama’ar gidan har washe gari. Dan tunda ta shiga ɗakinta bayan barowa wajen su papa saita kulle harda murza key. Littatafan ta na islamiyya da aka zubo mata cikin kaya ta ɗauka taita dubawa a hankali har lokacin barcinta yayi ta kwanta.
Washe gari tunda tayi sallar asuba bata koma ba. Gyara ɗakinma tayi har toilet, rashin sabo da zaman ya sata sha’awar fitowa falon shima dan ta ɗan gyara ko ta ƙarajin ƙarfin jikinta ta kuma ɗan rage kewa. Tana buɗe ƙofar ɗakin nata shima yana buɗe tasa ƙofar…………✍

yanzu haka an kusa kai ƙarhe, gamai buƙata zai iya garzayawa ya biya😋😋😋.

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

NO. 48

___________________

I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

_YERWA INCENSE AND MORE _
_(Masarautar K’amshi)_

_We’ve got you covered with our balsamic scented products.. Yerwa scents last longer and linger.. Ba kauri irin na wa’ensu turaren, Chadian kamshi ne na gaske, Kowane irin samfurin turaren wuta munayi, traditional and modern. _

_Akwai Khumrah’s kala kala. Kulaccams, Turaren wanka dana wanki dana mopping, Da tsugunno, Jiki da kaya duk muna dasu. Domin mallakar naki tuntub’e ta number shafin dake kasa, Ko kuma Ki duba shafin mu na manhajar Instagram ta: @yerwaincense_and_more. _

_Kyau, arha, inganci , sai yerwa incense. Muna tura kayanmu ko’ina a fadin nigeria da waje.. Ayi following, Da liking dinmu a Instagram handle dinmu dake sama._

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply