Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 54


Saran Boye 54
Viral

No. 54

…………Ihun Nu’aymah yayi dai-dai da shigowar motocin guards ɗin Yoohan da sukaje taryosa a airport batare da kowa na gidan ya san da dawowar tasa ba. Ba ƙaramin faɗuwa gabansa yayi ba. Ya ɓalle murfin motar da hanzari batare da ya jira an buɗe masa ba ya fice.
A dai-dai wannan lokacin kuma su Momy ma suka dawo daga church. Ihu na biyu da Nu’aymah ta sake ƙwalawa ya sake shiga kunnuwansu suma. Har rige-rigen fitowa suke a mota kowa na zare idanu da kiran Jesus.

A ciki kuwa, tun a ihun farko da Aymah tayi Gebrail ya ruɗe. Yay saurin sakinta daga rungumar da yay mata jikinsa na ɓari. Faɗuwar da tayi a kan hannunta ne yasata sake ƙwalla ƙara ta buyu a take ta sanƙame a sume.
Da lalube ya buɗe ƙofar ya fito, kirif ya kife ƙasa a cikin falon. Goshinsa ne ya bugi tiles sai ga jini. Bai damu ba, ya miƙe da sauri zuciyarsa kamar zata zubo ƙasa saboda firgici da tashin hankali. Ya kai hannu ya murza key ɗin data sakama ƙofar falon, zai buɗe ƙofar kenan aka turo. Da sauri ya koma bayan ƙofar ya maƙale fitsari na zubo masa a jiki dan jin ƙamshin turaren Yoohan, hannu yasa ya danne bakinsa da sauri.
Kasancewar Yoohan a rikice ya ke hankalinsa bai kai ga Gebrail ba, ɗakin Nu’aymah kawai ya tasarmawa yana ƙwala kiran “Zeeynab! Zeeynab!! Where are you?!”.
Da wannan damar Gebrail ya fita a guje zuwa ɗakinsa hannunsa tare da goshinsa dake zubda jini. Akan idanun Uwaliya dake shirin fitowa daga ɗakinta Gebrail ya fito daga sashen Aymah. Sun dawo suma babu jimawa. Sai dai ganin lokacin salla na ƙara wuceta ya sata nufar ɗakinta da nufin sai tayi sallar sannan taje ta sanarma Aymah sun dawo. Blessing kuwa tana can backyard tana tattaro shanyar da tayi kafin su fita. Ihun Aymah kawai taji hakan yasa suka shigo falon kusan a tare da su momy da suka dawo church.
Gaba ɗaya Yoohan yama rikice, ya rasa miya kamata yayi saboda ganin duhu a ɗakin Nu’aymah daya shiga. Da ƙyar ya iya lalubar makunnar fitila ya kunna. Ganinta yashe a ƙasa ya sakashi zabura kanta yana sake ƙwala mata kira da wata irin razananniyar murya data sake rikita su Momy Destiny da ke shigowa sashen.
Gaba ɗayanta ya ɗago zuwa jikinsa, ya sakata a ƙirjinsa yana bubbuga fuskarta da cigaba da kiran sunanta. Fahimtar da yay numfashinta yayi nisa sosai ya sakashi miƙewa da ita gaba ɗaya zuwa gado. Su dai su Momy sunyi cirko-cirko kowa yana tambayar kansa miya sameta?. Babu mai basu amsa, dan haka suka cigaba da kallonsa.
Shimfiɗeta yay a gadon ya shiga murza tafin hannunta. Sai kuma ya koma ƙafafunta. Babu dai alamar zata motsa. Kansa ya dafe yana ambaton sunan ALLAH. Ya kai tsahon seconds sha biyar kafin ya koma ƙasa gaban gadon ya durƙusa saitin fuskarta. Bakinsa ya ɗora saman nata ya toshe mata hanci da yatsunsa biyu ya shiga jawo numfashinta cike da dabararsu ta likitoci. Kusan tsahon seconds ashirin kafin ta kawo wani irin dogon numfashi tare da zabura ta saki wahalalliyar ƙara saboda sakin mata baki da yayi.
Zabura tai ta haye jikinsa dan ya dawo bakin gadon ya zauna yana sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ganin ta farfaɗo. Ta ƙanƙamesa tana faɗin, “Duhu Umm. Banason duhu ki samun fitila. Umm ki kiramin Abbana banason duhu Yaya Yoohannnnn!!”.
Idanu Yoohan ya lumshe a hankali saboda jin yanda taja sunansa akan harshenta, ya saka duka hannayensa ya rungumeta a jikinsa da ƙyau dan jikinta wani irin karkarwa yakeyi. A haka ya ɗora bakinsa saman kunnenta ya shiga hura mata iska a ciki. Hannayensa kuwa na shafa bayanta. A hankali ta fara sassauta surutan da takeyi, rawar jikinta na raguwa. Sai kuma ta koma sauke ajiyar zuciya hawayenta dake fita masu ɗumi na saukar masa a ƙirji.
A haka ta sake sumewa, Hankalinsane ya tashi da wannan sumar, dan sumace da yake da tabbacin mai haɗarice a gareta. sai ji yay ta masa nauyi kawai. Ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na babu adadi, hankalinsa na ƙara afkawa cikin ƙololuwar damuwa. Ya buɗe idanunsa da suka rine da ja yana kallo ahanlinsa dake zagaye da su a cikin ɗakin. Baice komai ba, dan bayason susan komai ɗin, sai kwantar da ita da yayi a hankali yaja bargo ya rufa mata, tare da ɗaukar remote ɗin ac dake a durowar gefen gadon a ajiye ya ƙara gudunsa saboda sanyin da yasan tafi buƙata a yanzun.
Sake maida hankalinsa yay gasu Momy yana musu alamar suje waje. Babu wanda yace komai duk suka fara fitowa shima ya biyo bayansu yaja ƙofar ya rufe mata dan dolene yaje ya nema mafita.
Dukansu babu wanda baibi jinin Gebrail daya fasa kai ba da kallo. Yoohan da yay ƙarshen fitowa ya jinjina kansa kawai yana kallon jinin da tunani barkatai a ransa.
Momy Favour ce ta fara faɗin, “Wai miya sameta ne haka John?”.
Kansa ya girgiza. Muryarsa na nuna alamun damuwa yace, “Aunt ban saniba nima. Ihunta kawai naji dai-dai muna shigowa gidan nan. Sai dai da alama wanine ya shigo ya tsoratata da duhu dan batason ganin duhu”.
Kallon-kallo suka shigayi a tsakaninsu. Momy tace, “Amma babu kowa a gidan nan sai ita da su Blessing. Dan muma shigowarmu kenan daga church muke. Joy da Gebrail suna school. Miracle kuma bata dawo daga wajen aiki ba har yanzu da alama”.
Batare da Yoohan yace wani abuba ya dubi Blessing da Uwaliya. Cikin sauri Blessing tace, “No Sir. na rantse da ALLAH muna bamusan miya sameta ba. Dan bamufi 5minutes da shigowaba mukaji ihunta. Ni inama backyard ina kwashe kayan dana shanya danai wanki ɗazun. Uwaliya kuwa tacemin zataje tai salla sai dai ban saniba ko…….”
“Wlhy nima salla na shigayi banje wajentaba saboda ganin zan makara”. Uwaliya tai saurin tarar numfashin Blessing ɗin.
Hannu Yoohan yasa a goshinsa yana ɗan murzawa. Sai kuma ya furzar da huci mai zafi. Batare da ya sake magana ba ya nufi ɗakinsa kawai.
Suma duk jan ƙafafu sukai gwiwa a sage suka fita harsu mama debora da suka gaza cewa komai. Su Victoria kam dama sunsan idan Yoohan na magana da iyayensu baya buƙatar cewarsu, shiyyasa basu tofa ko ‘A’ ba a maganar. Daka gansu dai kasan tausayin Nu’aymah ya cika musu zukata.

Kowa ɗakinsa ya nufa, sai dai Momy na shiga nata taci karo da Gebrail cikin toilet yana leƙo kansa. Yanajin motsin za’a buɗe kofa yay saurin komawa zai rufe ƙofar. Da sauri momy tace, “Kai waye anan?”.
Jin muryar momynsa ne ya sakashi fitowa jikinsa na rawa. Yay saurin faɗin, “Momy shiii!! Karkiyi magana Please”.
Sosai gabanta ya faɗi ganin yanda jikinsa ke ɓari. Ga jini ya jiƙe handkerchief ɗin daya ɗora a goshinsa inda yaji ciwo garin gudu. Saurin ruƙo masa hannu tayi suka koma cikin toilet ɗin itama nata jikin yana rawa. Ta maida ƙofar ta rufe tana magana a matuƙar tashin hankali. “Gebrail! Badai kaine ka aikata ba?”.
Hawaye na zuba masa a idanu jikinsa na karkarwa yace, “Momy idan Brother John yasan nine kasheni zaiyi. Na rantse tsautsayine momy kuma ban mata komai ba. Na rungumeta ne kawai na kashe wutar ɗakin shine tamin ihu”.
Kai momy ta dafe tana faɗin “Oh my lord”. Sai kuma ta kama kafaɗun Gebrail ta shiga girgizawa. “Gebrail baka da hankali. matar John? Bayan kasan halinsa a gidan nan”.
“Momy na rantse tsautsayi ne, ina sonta da gaba ɗaya zuciyata. Amma nasan Brother Yoohan zai halakani idan ya sani, kasheni zaiyi da hannunsa momy, ki taimakeni karki bari ya gane nine momy”.
Kuka yake sosai jikinsa na karkarwa. Jansa tayi jikinsa ta rungume duk da itama harga ALLAH a mugun tsoracen take. Dan tasan shirun da Yoohan yayi tabbas bazai zama na banza ba. Sai da taji bugun zuciyar Gebrail yaɗan dai-daita sannan ta ciresa a jikinta ta zaunar akan bathtub. Fita tai ta ɗakko First aid box ta dawo toilet ɗin bayan ta murzama ƙofar bedroom ɗinta key. Zuwa tai tai masa dressing wajen. Ta miƙe tana faɗin, “Kayi wanka zanje na ɗakko maka kaya a ɗakinka, dolene kabar gidanann a daren nan Gebrail. Kaje ka kama hotel koka koma cikin hostel ɗin makarantarku har sai wannan ciwon da kaji ya warke. Inba hakaba sai Yoohan ya gano kaine dan kowa yaga jinin daka zubar a sashen. Ka kuma san shi mutumne mai tsanani basira akan duk abinda ya ƙwafa”.
Kansa ya ɗaga mata yana faɗin, “Thanks you momy, thanks you so much”.
Bata sake cemasa komaiba ta fita tana tunanin yanda zata shiga ɗakinsa ta ɗakko kayan cikin dabara ba tare da kowa ya fahimta ba.

★★★★

Tabbas yau Gebrail ya sako Aymah cikin mummunan matsala. Musamman daya kasance a irin wannan lokacin ana lallaɓa lafiyar tata ne, domin aikin da Yoohan keta kaikawo wajen ganin da shine za’ai mata shi saboda haɗarinsa. Sai dai Alhmdllh, isowar Yoohan ɗin akan lokaci ya zama rahama a gareta. Duk da shima kuwa dawowar tasa bata lafiya bace ba. Ciwonsa ne na rashin barci ya dawo, yau kwanakinsa uku kenan baya iya barci, koya ɗaukesa saboda addu’a da yake yi baya gaza mintuna ashirin yake farkawa. Ganin al’amarin nasa na ƙara faɗine ya sakashi tattarowa ya taho gida. Sai gashi kuma ya iske wani tashin hankalin da shima ya nema birkita tashi ƙwalwar kan.
Duk yanda yake tunanin bama Nu’aymah taimako da kansa anan kafin wa’adin da za’ai mata aikin ya fahimci babu mafita. Dole ya yabar ƙasar nan da ita a gobe idan ALLAH ya kaimu, dan inhar ta wuce awa saba’in da wani abu komai zai iya faruwa da ita. Shi a yanzu hakama ya rasa wane taimako zai bata. Duk wata basirarsa ta likitanci ta kufce, man kansa ya tsiyaye tas. Waya ya ɗauka ya shiga nema wata abokiyar aikinsa Dr Shukurah dake anan General hospital na Abuja. Dan itama likitace mai ƙwazo da sanin makamar aiki. Gata babbar mace kuma dan momy ma Yoohan ke kiranta ita kuma tana cemasa Son. Tun ganinta da shi na farko lokacin an turasa bautar ƙasa a asibitinsu kamanninsa da yaron ƙanwarta yaja hankalinta. Ta kuma kasa haƙuri sai da tai maganar kamannin nasu. Sai dai shi Yoohan har yanzu bai ɗauki abin da muhimmanci ba, saboda bai taɓa ganin wancan datake faɗin suna kamar ba. Amma tayi alƙawarin wataran sai ta haɗasu dan wancan duk da ba’a Najeriya yake ba.
Duk da Dr Shikurah ta tashi da ga aiki yanda taji muryar Yoohan ɗin sai yay matuƙar tada mata da hankali. Dan haka ta nema alfarmar mijinta akan zataje. Da yake mutumne shi mai sauƙin kai sai ma yace bara ya kaita da kansa tunda darene duk da bawai can sosai ba.
Kasancewar tasan gidan su Yoohan ɗin dama basusha wani wahalar neman address ba. Cikin mintuna ƙalilan sai gasu sun iso. Solomon ne yay mata iso cikin gidan. Har lokacin su momy na tsaye a ƙofar sashen cirko-cirko kowa da abinda ya damesa. Dan da farko basu ɗauki al’amarin da zafi ba. sai da sukaga yanda Yoohan ɗin ke a birkice ne yanata shige da fice suka sanfa aiki ne babba kenan.
Sama-sama ya iyayma Dr Shikurah bayani akan matsalar Nu’aymah. Itama sosai hankalin nata ya tashi ta shiga faɗa akan dan miyasa za’ai gangancin sakata a duhun? Bayan kuma yana cikin abunda zai iya burkita ƙwaƙwalwar ta a lokaci ɗaya babu jinkiri. A yanzu hakanma basu da tabbacin ba’a samu matsalar da suke tsoronba. Shi dai Yoohan ma ya gaza cewa komai. Sai dai idanunsa sun sake kaɗawa jazur. Yana tsananin tausayin yarinyar nan fiye da tunani. Shiyyasa yake ta lallaɓa yanayin nata har kwanakin da zasu wuce ai mata aikin su cika. Amma dan tsabar zalunci an samu wani yazo yana neman ƙwaɓe masa aiki. Dolene wanda ya aikata wannan ya fuskanci mummunan hukunci daga garesa a gidan nan koda kuwa wanene. Amma a yanzu bashi da lokacinsu sai matarsa ta dawo hankalinta insha ALLAHU.
Dukkan wani taimako daya dace Dr Shikurah ta bama Aymah, dan yau ko allurar nan da yake mata biyu akai mata, dama uku ce ta rage. Ta kuma tunatar dashi akan dolene kafin nan da awanni saba’in aimata aikin da ya sanar mata sun gama booking.
Kansa kawai ya iya jinjina mata, tare da godiya akan ƙoƙarinta. Daga haka yayo mata rakkiya ta wuce.
Sai a lokacinne yacema su Momy ya kamata suje su kwanta abinsu tunda da sauƙi. Dama a ƙage Momy take da kowa ya shige ɗin. Dan har yanzu Gebrail na ɗakinta neman hanyar da zai gudu take bukata.

Dole ranar a ɗakin ya kwana. Dama gashi ba barci yake iya yi ba. Sai dai saɓanin baya da yake kwana cikin ƙunci da baƙin ciki yanzu ba haka baneba. Zuciyar tasa kam a ƙuntacen take, ga ciwon kai mai tsanani. sai dai kuma ya raya kaso biyu bisa uku na daren ne da nafilfili yana miƙama UBANGIJI kukansa. Sauran kaso ɗayan kam duk akan duba na’urorin da aka sakama Aymah ne lokaci-lokacin domin duba yanayin tafiyarsu, sai kuma neman hanyar da zai matso da maganar aikin da za’ai mata kafin waɗanan awannin su cika. Alhmdllh babu wata damuwa har suka wayi gari. Bayan yayi sallar asuba toilet ɗinta ya shiga yay wanka. Sannan yaje ɗakinsa yay shiri ya sake dawowa. Wayarsa ya ɗauka kamar zai kira baba malam sai kuma ya fasa bisa wani tunani da yayi.
Dubata yayi, ya tabbatar kozata iya farkawa sai nan da wasu awa kamar huɗu. Insha ALLAH kuma zuwa sannan zai kammala usirinsa ya dawo. Hannunta ya kama a hankali ya sumbata, kafin ya shafi kumatunta yana mai mata addu’ar samun lafiya mai ɗorewa. Daga haka ya fito. A falo ya iske Uwaliya na gyarawa. Ta gaidashi da girmamawa tana tambayarsa mai jiki. A takaice ya amsa mata. Tare faɗa mata ta ajiye aikin taje ta zauna a ɗakin Nu’aymah. Ta amsa masa da to, ta ajiye kayan sharar ta nufi ɗakin shi kuma ya fita.
Masu gidan duk suna ɗaki, ma’aikatanne kawai ke aikin gyara gidan. Papa baya nan yayi tafiya shima.
Har Yoohan ya nufi downstairs yana amsa gaisuwar da ma’aikatan gidan ke masa sai kuma ya dawo. Ɗakin Momy ya nufa kai tsaye. Ya tsaya a bakin ƙofa yay knocking. Sai da ta bashi izinin shiga sannan ya shigo. Rikicewa tai, dan a bazata ta gansa. Duk zatonta su Victoria ne sukazo mata sallama zasu wuce school. Ta tura wayar da take amsawa ƙarƙashin filo cike da rashin gaskiya. Shi dai da yake hankalinsa ba a jikinsa yake ba yanda ya kamata baima fahimci halin da take ciki ba. Ya gaidata da girmamawa kamar yanda ya saba. Sai dai yanda ta amsa masa murya na rawa da kuma kamar a daburce ne ya bashi mamaki.
“Mom are you ok? Hope you are well?”.
“Y..yes yes Son. It is Okay. Mika gani?”.
“No, dama banga Gebrail bane tunda na dawo. Where is he?”.
Ba ƙaramin bugawa ƙirjin momy yayi ba, harda taune harshenta saboda a bazata tambayar tazo mata. Ta shiga girgiza kanta tana faɗin, “Uh…Uhm ai yayi tafiya ne?”. Tai maganar da sosa ƙeya tana wani washe haƙwara.
“Tafiya? Where did he go?”. Yay maganar yana tsuke fuska da ƙyau.
Sosai Madam Chioma ta ƙara rikicewa. dan gani take kamar Yoohan ɗin ya shinshino wani abune. da ƙyar ta iya control ɗin kanta tace, “Ban sani ba Yoohan. Dama inason ka dawo na zauna da kai akan lamarin Gebrail. Rashin jinsa ya fara yawa. Tunda suka shiga University ɗin nan ƙara kangarewa yakeyi”. Yanda ta ƙare maganar ne tamkar zatayi kuka ya saka Yoohan sassauta muryarsa yana sauke nannauyan numfashin ɓacin rai. Ya cije lip ɗinsa yana miƙewa daga zaman da yayi. “Babu damuwa ki barni da shi. amma Mom kema harda laifinki. Kece ke zama da yaran nan fiye da kowa. Amma miyasa idan kinga irin haka ta fara faruwa bazaki sanar min ba. Yanzu daban tambayaba maybe harna sake barin ƙasar bazaki sanar minba. Zanci ubansane. Tunta bayaji zaiko cigaba da karatu a Nageria”.
Daga haka ya fice batare da ya sake bata damar cewa wani abuba. Itama daɗin hakan taji, dan inhar suka cigaba da zama a haka zata tonama kanta a siri, zata kuma iya aikata abinda ke ranta game da yaron nata. Dan a yanayin da yake na sanyi-sanyi yau sai ya wani tada mata tsuminta. Ji take kamar tai…..
Ta matse idanu da ƙarfi tana faɗawa saman gadon batare data iya ƙarasa ruɗaɗɗen tunanin nata ba. Oho shi Yoohan ma baisan tanayiba. Dan har sun fice daga gidan shi da guards ɗinsa.

__________________

Tunda Yoohan yabar gidan yaketa faman shigi da fici. Duk da azabar ciwon kai dake damunsa haka ya jure yanata kai kawo ko takan breakfast bai bi ba. Baima tunawa da yunwar duk da kuwa jiya ko buɗa bakin kirki baiyi zaman yiba tunda ya kai azumi.
Sai wajen sha biyu saura ya kammala duk abinda ya dace. Ta office ɗin Abban Abdallah ya biya. Suka tarbi juna cike da girmamawa da surukuta. Anan ne Abba ya fahimci kamar baida lafiya. Sai dai bai tambayesa kai tsayeba sai a cikin hikima. Yoohan ɗin bai ɓoye masa ba ya sanar masa.
Kai kawai Abba ya dinga jinjinawa. cike da damuwa yace, “Yahya anya kuwa a lamarinka babu sihiri?”. Yoohan bai fahimci abinda Abba ke nufi ba. Dan haka ya ɗago rinanun idanunsa yana kallonsa. Kai Abban ya sake jinjinawa. Cike da tabbatarwa yace, “Tabbas akwai sihiri a wannan al’amarin. Amma karka damu zanyi magana da Yaya. Insha ALLAH komai zai wuce. bara yanzu nai maka kamu sai na rubuta addu’oin nan idan kaje gida mamana ta zauna tayisu dan duk ta sani. Ka fara shansu su zama kamar ruwa a gareka”.
Godiya Yoohan yay masa. amma sai ya sanar masa ma ai zasu wuce da Nu’aymah ne a yau da daddare dan jikinta ya motsa. Sai dai bayason baba malam ya sani da wuri har sai sun isa can dan karya tada hankalinsa.
Cikin tsananin damuwa Abbah ke jera mata addu’oin samun lafiya. Ya ɗora da faɗin, “Duk da nasan Yaya bazai shiga ɗimuwar da kake hasashen ba na goyi bayan a ɓoye masa ɗin har sai kunje. Amma insha ALLAH muma zamu biyo bayanku ko zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu ne. ALLAH ya ƙara muku lafiya damu baki ɗaya”.
Da amin Yoohan ya amsa masa.
Baibar Office ɗinba sai da Abba yay masa addu’oi sosai, har a cikin ruwa ya bashi ya sha sannan yay masa sallama ya wuce yana maijin ƙaunar waɗanan bayin ALLAH har cikin ƙasan zuciyarsa.

★★

Daga wajen Abbah gida ya koma. Inda ya iske farkawar Nu’aymah kenan kamar an auna da dawowar tasa. Uwaliya kawai ya iske a ɗakin kamar yanda ya gargaɗeta karta bar kowa ya zauna dan ba’a bukatar yin hayaniya komin kanƙantarta. Hakan yasa ƴan gidan duk wanda yazo ya dubata sai ya fice baya zama.
Saurin ƙarasawa yay cikin ɗakin. Hakanne ya saka Uwaliya dake riƙe da hannunta tana jera mata sannu saurin matsawa baya ta bashi waje. Zama yay a bakin gadon kusa da ita. Ya cire duk na’urorin dake manne da kanta da kunne. Yanayi yana addu’ar neman nasara ga UBANGIJI.
Batayi maganaba, sai dai hawaye dake silalo mata a kan fuska a hankali. Sake matsawa yay sosai kusa da fuskarta, ya dafa hannayensa a gefe da gefenta yana mai tsurama hawayen nata ido. Da ƙyar ya haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi, ya ɗan furzar da iska yana lumshe idanu da sake buɗewa akan fuskartata. Hannunsa ɗaya ya ɗaga ya ɗaura akan lallausan fatan kumatunta yana share mata hawayen. Kafin ya ƙara ranƙwafowa kanta sosai fuskarsa gab da tata yay magana a hankali kamar mai raɗa.
“Please banason kuka Zeeynab. Idan zaki iya buɗe idanunki kaɗan-kaɗan na gani”.
Uwaliya dai na tsaye a gefe tana kallonsu a wani yanayi.
Duk maganar da Yoohan keyi Aymah na jinsa, dan haka taɗan shiga motsa idanun nata kaɗan-kaɗan. Tana buɗesu a sannu-sannu harta buɗe kusan rabi a kansa. Murmushin ƙarfin hali ya sakar mata yana lumshe nasa idanun da a kallo ɗaya zaka fahimci shima lafiyar ba isasrsa tayi ba.
“Alhmdllh” ya sake faɗa a hankali yana kamo hannunta cikin nashi. Sake maida idanunta tai ta lumshe itama. Daga haka ɗakin ya ɗauki shiru. Yaja wasu mintuna uku haka kafin ya juya ya kalli Uwaliya. Saurin yin ƙasa tai da kanta tamkar dama ba kallonsu take ba. Bai wani damuba duk da ya fahimci yanzu ne ta duƙar da kan. Shi gulmar ƴan aiki ba irin wadda bai haddace ba.
“Haɗomin ruwa mai ɗumi a roba, tare da towel”.
“Okay sir”. Uwaliya ta faɗa da girmamawa tana nufar toilet ɗin Nu’aymah.
Kansa yaɗan dafe yana yamutsa fuska, dan dauriya ce kawai ya keyi iya jarumta. Cikin mintuna ƙalilan Uwaliya ta dawo da abinda ya buƙata. Tana ajiyewa tace, “Sir ko za’a haɗa mata wani abinci haka?”. Towel ɗin data ajiye ɗin ya ɗauka. Batare daya kalleta ba yace, “Ki duba abu maiɗan ruwa-ruwa haka da kika fahimci tana so sai ki haɗa muga ko zata sha”.
“Okay sir”.
Miƙewa yay yabi bayan Uwaliya data fita. Ya murza key ɗin ƙofar sannan ya dawo yana zame baƙar jacket ɗin jikinsa mai ƙyalli kamar leda daya ɗora akan ƙananun kayan jikinsa. Inda ya tashi ya sake komawa ya zauna. Sake ranƙwafowa yay kan Nu’aymah yaɗan juyata kaɗan ya fara jan zip ɗin rigar jikinta ƙasa………….✍

😪Tabɗi, har words 3600. Kai yau gaskiya kun samu garaɓasa. To harda na gobe😖🚶🏻😒.

 

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 55

_________________
_*HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION._*

_Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:_

_Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours… _

_Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su.._

_Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske_

_Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki…_

_Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya.._

_Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai.._

_Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya… Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection.._

_Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai._

_Akwai page dinta a favebook mai suna *GIDAN KAMSHI* ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304_

_Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE.._

_TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA_

_AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted…!!!_

_Kyau, inganci, Rahusa… Sai kayan HAJARA COLLECTION….!_

_idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi🥰😍🧚🏻‍♂️_

_________________

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply