No. 69
…………“Oh God baby”. Ya faɗa da kamota ya tayar zaune. Sakata yayi cikin jikinsa ya rungumeta. A tare suka sauke ajiyar zuciya kowa kewar ɗan uwansa na ratsashi.
Sake lafewa tai a jikin nasa tana mai shaƙar ƙamshinsa da ke mata daɗi sosai. Yayinda shi kuma ɗumin jikinta ke ratsashi, tare da tausayinta har ƙasan zuciyarsa. Harga ALLAH yana matuƙar son yara. Musamman a yanzu da yayi aure. Badan hakaba daya cire mata cikin nan dan tayi ƙanƙanta yake gani. Duk da kuwa shi likitane daya zaga cikin duniya. Yayi gamo da mutane iri-iri harma waɗanda basu kaita a shekaruba ya gansu da cikin kuma sun haihu lafiya.
Jin tana neman fara barci ya shafa mata fuska. Idanun ta buɗe a hankali da ɗagowa ta kallesa. Sai kuma ta bi jikinsa da kallon mamaki. Sanye yake cikin wata ɗanyar shadda ash color mai duhu. Tasha ɗinkin da yay dai-dai da samarin wannan zamanin. Hardasu hula ƙube. A bazata murmushi ya suɓuce mata. Ta sake kwantawa a jikinsa da zagayesa da hannayenta tana murmushi.
“Hausa man”. Ta faɗa cike da shauƙi.
Murmushi yayi mai faɗi ganin taji daɗin ganinsa da shigar yarenta. Ya miƙe ɗauke da ita yana ƴar dariya da faɗin, “Hausa man mijin hausa girl”. Dariya suka ƙyalƙyale da shi a tare, dan yanda yay maganar dole ya baka dariya. Ta kai hannu kan tattausan sajensa dai-dai yana zama da ita a kujerar. Tace, “Mun haɗu fa da yawa. Dan irinmu a tarihi kaɗanne”.
Murmushi ya sakeyi mai faɗi yana lumshe ido da buɗewa a kanta. Zai bata amsa kira ya shigo wayarsa. Karkatawa yay kaɗan ya ciro wayar a aljihun gefensa. Hakanne ya bama Aymah damar sauka dan ta tuna ko ruwa bata bashi ba. Da kallo ya bita yana sauke wani nannauyan numfashi da har ya kai Osin jinsa da ga can.
Cikin son ƙarfafa kanta ta haɗa masa ruwa da kofi a ƙaramin tire. Duk da ta fahimci bai cika damuwa da kayan lemo-lemon nan ba ta ɗauka masa shima. Falon ta dawo inda ta barsa har yanzu yana waya. Ta ajiye tiren a table taɗan kallesa. Shima idanunsa ƙyam akanta. Lemo ta fara nuna masa, ya girgiza mata kai alamar a’a. Hakan yasa ta buɗe ruwa. Koda ta miƙo masa sai ya haɗa da hannunta ya maidata saman cinyarsa. Jin numfashin daya furzar ya saka Osin faɗin, “Mr X anya kuwa kana cikin nutsuwarka?. Nikam sai anjima. Ina magana kanata min uhm, ah, a’a”.
Murmushi Yoohan yayi mai sanyi yana kai hancinsa bisa dokin wuyan Nu’aymah. Osin bai jira amsarsa ba ya yanke wayar cike da jin haushi dan magana dama yake masa akan su papa. Shi kuma harga ALLAH Yoohan hankalinsa gaba ɗaya Aymah ta tattareshi kojin Osin ɗinma bayayi da ƙyau.
“Yah Yoohan zakasa na jiƙamu fa”. Ta faɗa cike da shagwaɓa”. Tai maganar tana ɗan ture masa kai Jin yana neman ruɗar mata da jiki. Bai iya cemata komaiba. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci ta gama narkar da shi. Ya kamo hannunta da ruwan ke ciki ya kai bakinsa kozai samu sassauci. Dama gashi ƙishin yakeji. Tas kuwa ya shanye shi.
“A ƙaro?”.
Kai ya girgiza mata da lumshe idanu yana jingina kansa da kujera.
Gaba ɗaya ƙoƙarin Nu’aymah neman gazawa yakeyi, cike da son danne halin da take ciki tace, “Muje kayi wanka ga abinci ma”.
Idanun ya buɗe ya zuba mata su. Dan ya fahimci tanayin komai da ƙarfin haline. Yanzu haka har cikin jikinsa jin zafin nata jikin ya keyi. Baice komaiba ya kamata ya miƙar yana faɗin, “Fara bani abincin naci yu nwa nakeji”.
Koda suka zauna a dining ɗin duk sai taji batason ganin abincin kuma duk da itace ta girkashi. Fahimtar hakan da Yoohan yayi ya sashi cemata taje ta kwanta zai zuba. Da sauri kuwa tabar wajen. Binta yay da kallon tausayi, tana ƙoƙarin kwanciya a ƙasa yay saurin faɗin, “No ba ƙasaba. Koma saman kujera ko kije ɗaki”.
Sosai ta ɓata fuska zatai kuka. “Please Yah Yoohan, wlhy banason ko ina sai nan. Yafi min daɗi”.
“Bazai yuwuba Sweet girl, wannan sanyin illane a gareku ai. Indai kika kwanta a wajen nan tofa na fasa baki maganin zazzaɓi kawai zan haɗa da allura….”
Kafinma ya rufe baki ta haye saman kujera tana hawaye. Murmushi ya ɗanyi ganin yanda ta kwanta da juya masa baya. Bai sake yin maganaba ya hau cin abincinsa yana yabama ƙoƙarin ta, dan shikam yanzu ya sallama mata akan iya girki kuma.
Juye-juye Aymah ta dingayi a kujerar tana ƙunƙunin, sam kwanciyar batai mata daɗi ba, ita tafi son ƙasan saboda sanyin tiles. Yoohan dai na kallonta amma baice komaiba. Sai da ya kammala cin abincinsa hankali kwance sannan ya miƙe. Dan yama tuna kaya na waje. Zuwa yay ya shigo da su duka. Duk da Nu’aymah na jinsa bata juyo ta kallesaba. Cike take da haushin an hanata kwanciya a ƙasa. Babban akwatin kayanta da yazo da shi ya kai ciki, ghana must go ɗin kuwa ya barta anan falon dan baisan mine a ciki ba. Amma yanda yakeji ƙamshi-ƙamshin abubuwa yasan dai ba kaya bane. sannan akwai nauyi ma.
Cak ya ɗauki Aymah daga kujerar ya nufi bedroom da ita. Ƙin motsawa tai, sai ma fuska data kumbure na fushi. Shi dai baice komaiba ya kwantar da ita a gado yana sumbatar goshinta. Daga haka ya cire kayansa ya wuce toilet yin wanka.
Koda ya fito ya sameta a gadon bata sauka ba yaji daɗi. Dan baiyi zaton zata haƙura ba. Boxer kawai ya saka ya haye gadon, yanason yaɗan huta daga uwar gajiyar daya kwaso a sati biyun nan.. Sai yanzu ne ya fahinci ashe barci ƴar rigimar tasa tayi, yay murmushi mai ƙayatarwa da sumbatar laɓɓanta da idanu. ‘My Trouble maker an kusa zama mah-mah’ yay maganar yana ɗaga rigarta da ƙara faɗaɗa murmushinsa. Sunkuyawa yay ya sumbaci cikin da babu alamar akwai wata hallita a ciki. Sannan ya fara magana tamkar jinsa ya keyi, “Little boss how are you?. ALLAH ya kareki. ya fiddoki duniya lafiya, yasa kizam mahaddaciyar Al-qur’ani kaman Mie-mien ki. Ki kumayo kamanninta”. ya ƙarasa faɗa da ɗaga kai yana kallon fuskar Aymah dake barci batasan yanayi ba. Kwanciyarsa ya gyara da rungumeta. Kamar kuwa jira take sai ta sake lafewa dan sanyin jikinsa.
Barci sukasha sosai. Sai dai Alhmdllh lokacin da suka tashi zazzaɓin Aymah ya sauka. Tare sukayi wanka bayan Yoohan ya mata gwajin fitsarin da batasan na minene ba. Tsabar wauta kuma bata tsaya tambayarsaba. Ta zata dai ko complain ɗin maganar rashin ganin jinin da sukayi da Umm ne ta sanar masa tunda shi Doctor ne. (Umm ba irinki bace madam😬).
Ta rigashi fitowa. Dan sai da ya jira result sannan ya fito. Duk da ya jima da zargin ɗan tayinsa hakan bai hanashi farin cikiba. Ya ɗagata yanata juyi da ita. Tun tana tambayarsa lafiya harta koma tuntsura dariya kamar yanda yakeyi. Da ƙyar ta samu ya sauketa a godo suna faman hakki.
Yasha murnarsa batare da Aymah tasan dalilinta ba. Dan ya ƙi sanar mata. Acewarsa ba yanzunba. Duk da taso tajin saita share kawai. Musamman da ganin ɗinkinan daya yo mata cike da akwati. Lesss, shadda, atamfa. Dan a cewarsa yana son ganinta a kayan hausawa sosai. Tayi mamakin ganin ɗinkin dai-dai jikinta kuma. Koda ta tambayesa yaya akai yasan seize ɗinta haka? Sai cewa yayi abun sirri ne. Ta fahimci yau jan rai yake mata akan magana. Nanma sai ta share ta shiga jera masa godiya da addu’oi.
Ya ce shifa tabar masa godiya dan akwaima lefenta a kansa wanda baiyiba. Aymah dake dariya tace, “Ai gashi anan kayi my boo”.
Hancinta ya lakace da faɗin, “No. Wancan special ne hausa girl. taso muje kiga saƙon Umm”.
Tunda Aymah taga duk abinda tacema Umm an haɗo mata shi saita haukace da murna har Yoohan na mata dariya. Ta tasa fara gaba ta hau ci harta bashi tausayi. Dan yayi-yayi taci abinci taƙi, tace sai dai suje shagon shan coffee. Haka dole bayan ta gama cin farar da shan su alawar madara ya ɗauketa sukaje shan coffee ɗin. Tako shawosa bana wasaba harda guzirin na anjima. Shi dai gaba ɗaya sai take bashi tausayi, dan yasan da bata shan coffee.
Haka su Nu’aymah suka cigaba da kasancewa suna rainon ɗan tayin cikinsu ita da mijinta abin sonta. Duk da yaƙi faɗa mata gaskiyar zancen cikin, a yanzu bata da abinci sai kayan da Umm ta aiko mata da su. Randa tayi tuwon dawa miyar kuka ta tsare Yoohan wai sai yaci. Dan itama ai taci abincin yarensa lokacin da aka kaita gidansu. Shiru kawai yayi yana kallonta idanu na farfar dan shikam dai harga ALLAH miyar kukar har saka masa tsigar jiki tashi take. Garama tuwon yana masa kallon amalan yoroba. Dan yana ɗanci a dalilin joseph data zama abincin yarensane. Ganin yanda yakeyine ya saka Aymah yin fushi. Marairaice mata yayi akan tayi haƙuri shi wlhy bai iya ci ba. Batama nuna taji miya faɗa ba.
Ganin da gaske fa fushin ta ɗauka ya tilasta masa daurewa ya rintse ido ya matsa kusa da ita. Muryarsa har sarƙewa take wajen faɗin, “To kawo zanci Sweet girl. Shiru ta kuma masa tana cin abinta cike dajin daɗi harda lumshe ido, gashi ya sha yajin daddawa da man shanu kuwa sai ƙamshi yake. Sake marairaice mata yayi cike da lallashi.
“Nace zanci ai ko. Tunda Unborn ɗina yanaci nima a bani zanci, yi haƙuri”.
“Sai dai na baka da hannuna, dan karma kaita zubashi a riga ban saniba daga baya kaje ka zubar”.
Ta bashi dariya, amma sai ya gimtse dan ya kula itafa da iya gaskiyarta take maganarta. Yace, “To na yarda”.
Laumar farko dai Yoohan sai da ya riƙe numfashin sa sannan ya korata da ruwa batare da ya tauna ba. Lauma ta biyuma haka. Ana uku ƴar rigimarsa ta tubure bata yarda ba. Yoohan dai kam yaga takansa. dan rigimar Nu’aymah dabance a rayuwa. Dole-dole kuwa sai da ya tauna lauma ta ukun nan. Daga haka yace. Dan ALLAH tayi haƙuri ta barsa haka tunda koya yakeyi. Dariyar mugunta taita masa kuwa.
Tun daga ranar daya fahimci zatayi tuwo sai ya gudu. Idan kuma ya fita asibiti sai ya bigi cikinta yaji mitaci ko zataci. da yaji batun tuwo sai yaki dawowa da wuri. Tun Aymah bata fahimtaba harta ganosa. Aiko saita daina sanar masa idan zatayi. Haka ta dinga ritsashi akan cin tuwon nan dole. Tun yana gudu bayaso har ya fara masa daɗi. Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci ya iya ci kuwa. Shima kuma komawar da yay Nigeria sau kusan uku duk xuwan da zai dawo sai yazo da wani abinda yasan na yaransune. Sai dai cikin ikon ALLAH kuma ita Aymah ciki ya sakata ci take hankali kwance. Dan yanzu kuma komai ci take anbar coffee. kayan wajen Umm ma duk zuwa sai yazo mata dasu.
Watan su Aymah ɗaya da sati biyu a U.S Juliet ɗin Omar ta haihu mace mai kama da ita. Su Aymah ansha murna. Sai taji itama tanason ta haihu. Tako dage harda addu’a a cikin salla (😂bar wahal da kanki baby Aymah).
Shi Yoohan baisan tana addu’ar ba shiyyasa bai sanar mataba. Dan a lokacinma baya ƙasar shi. Sai da ya dawone yaga baby. Omar ɗinma yana 9ja bayan haihuwar da kwana ɗaya yazo. Dan dama yaso Juliet ɗin taje Nigeria ta haihu taƙi. Yarinya dai taci suna biyu. Aysha & Lisa, Dan shi dai Omar duk abinda ya dace uba musulmi yayi akan ƴaƴansa shi yayi akan baby Aysha. Itako Juliet da yake dama bawani bidi’oin suna sukeba suna kawai ta sakama yarinyarta bayan wanda Omar ɗin ya saka mata. Saima yazam itama yanda Nu’aymah ke kiran sunan Aysha ɗin yana mata daɗi. Sai gashi tafi kiran yarinyar da Ayisha ɗin. Saboda daɗin da Omar yaji har ƙyauta yayma Nu’aymah da godiya. Tare da roƙonta dan ALLAH taita jan Juliet ɗin a jiki ko itama za’a dace ta gane gsky. Aymah ta amsa masa. duk da tasan hakan abune mai wahala ga baturen ba’amuruke irin Juliet. To amma komai ai na ALLAH ne.
_________________★
*_KANO NIGERIA_*
Anan kano ta dabo kam Umm najin daɗin zama da Afrah data ta fara aiwatar da aikinta cike da ƙwarewa da nutsuwa. Gaba ɗaya ta ɗauke musu kewar Aymah. Koda yaushe Muhammad inhar ba makaranta ya wuce ba yana nane da ita. Itama tana matuƙar son yaron, dan yana ɗauke mata kewar ƴan ƙannenta.
Haka ma tana matuƙar jin daɗin zama da baba malam da Umm. Dan mutanene masu dattako matuƙa. Ita da hajjo kam ai ba’a magana. Daka gansu tamkar jika da kaka. Kai gaba ɗayama al’ummar gidan Afrah nada ƙyaƙyƙyawar alaƙa da kowa. Dan malam ƙarami harya ƙyasa. Ita kuma taƙi sanar masa tanada mijin aurenta a hannu. Dan gab ma ake da saka musu ranar aure tunda iyaye duk sun shaida tuni.
A cikin dabarun da ALLAH yay mata a sashe su Nu’aymah ta manna cctv ɗin nan mai kama da stones. Hakama sashen hajjo da duk wasu gurare na cikin gidan batare da kowa ya farga da itaba. Bata da wata ƙawa mai shekarunta a gidan, dan haka taita jan yaran gidan jikinta sosai. Dan su Adawiya ma har yanzu suna Abuja. Admission ma za’a nemar musu su fara karatu tunda na Adawiya yasha kashi. Su baba malam sunso ta koma saudia ɗin ta cigaba hajjo ta hana hakan. Acewarta su jira dai suga iya gudun ruwan Abdallah ɗin.
A cikin kwanaki goma da Afrah tayi a gidan ta kammala aikinta na manna camaras a duk inda ya dace. Sosai Jay yaji daɗin ƙwazon ƴar tasa. Hakama Bily.
Sai kuma ta koma bama Dawood da little, Yoohan, Omar bayanai akan duk motsin ƴan gidan. Da wanna suka fara aywatar da aikinsu batareda jama’ar gidan sunsan sirrin ba. Hatta da Nu’aymah batasan hidimar da akeyiba. Dan koda Yoohan ya koma U.S bai sanar mataba. Takan dai gansa yayi serious a lap-top duk dare. kuma baya zama latse-latsen sai tayi barci. Inko har yazam ta farka to yabar aikin kenan. Dan duk dabarar da zaiyi ya ajiye abinda yake ya sani.
A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa har aka shiga watan azumin Ramadan. Wanda ya kasance na farko ga Yoohan da Omar. Sosai Aymah ta yabama ƙoƙarin Yoohan randa aka kai azumin farko. Dan ko irin nuna yau ya fara ɗin nan bai nunaba. Itacema sai da ta karya nata saboda jiri data dinga gani, daga ƙarshe kuma taita amai.
Omar U.S ya koma domin yin azumi. Hakan yasa kullum anan wajen Nu’aymah yake zuwa shan ruwa. Wani lokacin ma harda Juliet suke zuwa da Baby Ayisha.
Azumi nada kwanaki goma sha biyu hutun Afrah ya ƙare. Ta tattara ta koma Abuja cike da kewar su Umm. Dan ita dai taji masifar daɗin zama da waɗanan bayin ALLAH musamman cikin azumin nan. Su kansu duk sai da sukaji babu daɗi akan komawar tata. Sai dai babu yanda suka iya tunda zata koma kan aikintane.
An kammala azumin watan Ramadhan lafiya. Ansha kuma bikin salla a ƙasashen musulmai. Yayinda su dai su Aymah sai ɗan yawo sukai anan U.S, da ɗanyin nasu bikin sallar anan cikin gida.
Tsakanin Yoohan dasu papa har yanzu basu taɓa masa magana akan dukan Gebrail da yayiba. Dan komawar da yayi 9ja can gidan ma ya sauka abinsa. Sun kuma tarbesa kamar yanda suka saba. Ya iske su momy Destiny sun koma. Hakama maman Madam Chioma. Mama debora kawai ya iske da sauran ƙannensa sai guards ɗin gidan su Solomon daya koma gadin nadam Chioma yanzun. Gebrail kam tunda yaji Yoohan ɗin yazo gidan ya gudu. Har yabar ƙasar kuwa basu haɗuba. Daya sake komawama yay wajen kwana goma shima wasan ɓuya suka dingayi da Gebrail ɗin.
Wannan shiru da sukai ya bama Yoohan mamaki matuƙa. Badan dukan da yayama Gebrail ba. Sai dai maganar Solomon da baiji sun sake tayar masaba. Sai dai kuma shima baiyi magana ba ya bar Solomon ɗin cigaba da kasancewa da shi da sauran guards ɗinsa duk sanda ya shigo Nigeria. Duk inda ya shiga suna tare anan kam.
_____________________
A kwana a tashi babu wahala sai ga cikin Nu’aymah ya shiga watanni shidda. Tun cikin azumi kuwa ta fahimci ciki gareta. Murna taitayi zasu samu baby suma. saɓanin yanda Yoohan yay tunanin zata tayar da hankalinta. Aiki shima yaji daɗin yanda ta nuna murnarta akan Unborn ɗin nasu. Wata ƙaunarta mai girma na sake faɗaɗa masa a rai.
Ganin laulayin ya rage mata a lokacin sai kawai ya shiga ƙoƙarin nema mata admission. Wannan abu ya saka Aymah murna harda kuka. Dan tanason karatu sosai a rayuwarta. Addu’a ta dage ta dingayi babu dare babu rana akkan samun gurbin karatun nan. Su Umm ma sunsha addaba akan su tayata da addu’ar. Har Muhammad tasa ya faɗa a islamiyya wajen ƴan ajinta su mata addu’a.
To Addu’a dama takobin muminine ai. Balle gashi result ɗin Ayman da Yoohan ya amso a gida wani zuwa da yayi dama yayi ƙyau masha ALLAH. Sai gashi kuwa an dace. Ranar kowa yasan Aymah ta samu cikar burinta. Yoohan kam ai yafi kowa shan kallo dacin dariya a wannan rana, sannan kuma yasha tukuyci mai tsoka da ba’a bama yaro mai ƙiwa.
Da taimakon Juliet yay mata komai daya dace, dan itama tanayin wani course ma a cikin makarantar yanzu haka. Sai dai a online take ɗaukar lecture. Da wannan damar Yoohan ma yay amfani akan Aymah. Zata dinga ɗaukar lectures ta online. Idan kuma taso shiga school bai hanata ba bayan ta haihu. Yayi hakane saboda yanayin jikinta.
To da yake itama yanzu lallaɓa cikin take sai ta amince (wa yaga ba sabanba su Aymah za’ayi ƴaƴa😂).
Umm, baba malam, hajjo ne kaɗai sukasan da zaman cikin Nu’aymah a kaf jama’ar gidansu. Dan ko Addah Umm bata faɗamawa ba sam. Tabar abinta a zuciya wai randa Nu’aymah tazo kowa ya gani. To kuma anyi sa’a duk wautar Aymah da surutu ita bamai irin sakin zance ɗin nan bace ako ina. Dan ko su Umm ɗin ai ba fitowa fili tai tace musu tanada ciki ba. Sune suka fahimta ita da hajjo. Baba malam ma a wajensu ya sani.
Cikin ya mata ƙyau sosai a jiki, sai dai yasata ta ƙara ƙiba, kumatun sun fito masha ALLAH. Idan Yoohan najin neman magana yakan tasata gaba yayta dariya. Ita kuma taita hawaye dan yanzun dai kam bakin tsiwarnan duk ya mutu. ta kanta takeyi duk tazama wata shiru-shiru.
★★★★★
Akwai aikin da Yoohan zaizo yi Ƙasar ghana, daga nan kuma zai shigo Nigeria akan case ɗin gidan su Aymah. Dan zuwa yanzu sun tattara abubuwa da yawa ta dalilin Afrah. Sai bayanan sirrin da jay ya tattara ta hanyar camaras ɗin nan wanda shi da bily kawai suka san dasu. Amma suma ɗin basu duba komai ba a yanzu, dan sunbar komai ne ya tattaru, So suna son fara buɗe abubuwa a bayyane insha ALLAH a hankali. Sun san kuwa a wata uku kenan da zaman camaras ɗin a gidan sun naɗi abubuwa iri-iri, musamman daya kasance ansha shagalin bikin ƙaramar salla da babba, duk kuma ahalin gidan sunzo, idan ka cire Abdallah da yay hijira.
Shirinsu na farko dai yanzu shine fara kama Rabi. Daga haka sauran abubuwa zasu cigaba da tafiya a buɗe. Nu’aymah taso biyo Yoohan a wannan karon. Sai dai kuma ya lallaɓata akan ta bari sai hutun ƙarshen shekara idan ALLAH ya kaimu. Tunda baifi saura wata ɗaya da sati biyu ba. Batai masa musu ba, dan yanzu duk ta ƙara yin laushi, danma wahalar cikin ta mata sauƙi sosai zuwa yanzu Alhmdllh. Gashi kuma dama cikin fari. Ga kuma karatunta da ke mata matuƙar daɗi. Dan harya kaita da mantawa da wasu su madam Chioma. Lamarin papa ne dai kam sun tattauna da Omar sosai a wani zuwa da yayi U.S ɗin. Annan take faɗa masa gaskiyar lamari game da hoton data ɗakko a ɗakin papa ɗin, harma da waɗanda ta gani. Abin shima ya bashi mamaki sosai. Nan shima yake sanar mata abinda ya taɓa faruwa tsakaninsu da Jay kwanaki. Itama sai abin ya tsaya mata a rai. Har taji sha’awar son samun kusanci da zuri’ar Jay ɗin. A take Omar ya bata Number Afrah. Dama Afra ɗin ita tanada ta Aymah, kirantane dai bata taɓa yi ba. Dan sanda tana a gidansu sai dai su gaisa a wayar Umm ne. Tun daga sannan suke ɗan kiran juna a hankali, suna kumayin chart lokaci-lokaci kasancewar duk sunyi busy.
To yanzu dai sun ajiye magana akan duk sanda taje 9ja zata bashi hoton ya gani, daga nan sai su san tudun dafawa akan wannan al’amari. Daga haka suka ajiye batun.
Sai dai kuma abinda su Aymah basu saniba ita da Omar shine tun randa Jay yaga Yoohan bai hutar da kansa ba a bincike dabin diddigin papa. A hankali duk wani motsin papa ya kasance akan idon Jay batare da shi yasan hakan na faruwaba. Dan ya rigada yayi imani da cewar ya toshe duk wata hanya ta leƙen asirinsa daga wasu mutane koda jami’an tsarone. Sai gashi shi Jay yama kansa hanyar da yake kallon papan tsirara.
Dirar safe Yoohan yayma 9ja wannan karon. ya kuma sauka a Lagos ne. Sai da ya kwana uku sannan ya ƙaraso Abuja. Kamar ko yaushe ahalin nasa sunyi murna da zuwan nasa. Musamman ma madam Chioma da duk zuwa saita banka masa kayan tsibbunta a abinci yaci. Sai dai duk da bataga wani canjiba daga garesa tana ɗauka aikinta na tafiya dai-dai. Musamman da bata taɓa jin ya zauna yimata zancen Nu’aymah ba.
Tun isowarsa gidan Gebrail ya gudu kamar yanda yakeyi yanzun. Tun dukan da Yoohan yay masa bai sake yarda sun haɗu a inuwa ɗaya ba. da zarar yaji labarin zuwansa yake barin gidan, bakuma zai sake shigowaba sai Yoohan ya koma kokuma yaje wani jahan aiki. Duk da Yoohan na lure da Gebrail ɗin bai taɓa nuna yasan yanayi ba. Gaba ɗaya yi yake tamkar ya manta da wani halitta Gebrail a cikin ƙannensa.
Blessing da su Favour yasa suka gyara masa sashen nasa wannan karonma. Bayan ya watsa ruwa yaɗan miƙe a gado yanason ya huta. Sai da ya fara kiran Aymah suka ɗan taɓa hira sannan ya kwanta. A ƙanƙanin lokaci kuwa barci yay awan gaba da shi.
Madam Chioma da tun shigowar Yoohan gidan yau ta kasa zaune ta kasa tsaye ta fito wankan maganin da boka Bangaruta ya bata a gurguje. Zama tai gaban mirror ta shiga tsara kwalliya kai kace fita zatayi. Sai da ta tsuke cikin wando da riga da sukai mata matuƙar ƙyau sannan ta feshe jikinta da kalolin turarruka masu tsada da ƙamshi. Gashin Attachment ɗin nan sai uban walƙiya yake da ɗaukar ido kasancewar sa mai uban tsada. Cike da takun gayu da ƙasaita ta fito daga sashenta dan papa baya nan yayi tafiya yau kwana biyu. Mama debora dasu Victoria kuwa tasa sunbar gidan a cikin shirinta. Ta aika Blessing kuma kasuwa. Amma abinda bata saniba Blessing ɗin batakai da fitaba saboda toilet daya kamata. Kanta tsaye sashen Yoohan ta nufa, hakan yayi dai-dai da hawowar Miracle sama hannunta ɗauke da five alive da kofi. Waya takeyi da wata ƙawarta tana bata labarin zuwan Yoohan. Saurin ɓoyewa Mira tayi dan kar madam Chioma ta ganta, tare da jan wani shegen wawan tsaki dayin kamar zatai jifa da kwalin lemon. Sai kuma ta fasa saboda uban kuɗin data kashe wajen yima lemon haɗin magunguna saboda Yoohan. Itama kanta cikin gayun take na kece raini. da alama kuma sashen Yoohan ɗin ta nufa. Sai dai gashi Maman Yoohan ta ruguza lamarin. Ranta cike da ƙuna taje ta zauna a kan wasu kujeru biyu dake a upstairs ɗin tana huci da bama ƙawar tata labarin abinda Momyn Yoohan ɗin tai mata. Zugata ƙawar tata take famanyi daga can akan ya kamata Miracle tazo suyi duk yanda zasuyi wajan raba Yoohan da uwar tasa.
A ɓangaren madam Chioma kam ta shiga da dukanin gadaranta sashen ne. Key ta sakama ƙofar falon sannan ta nufi ɗakin Yoohan kai tsaye. Baisa a ransa kowa zai shigoba, musamman da yasan yanzu Momy ta bar masa ɗabi’ar banza na shigo masa sashema gaba ɗaya. Dan duk zuwannan da yakeyi bata shigowa, sai dai idan shine yaje sashenta gaisheta kosu haɗu a falon papa. Shiyyasa yake kwance abinsa daga shi sai boxer yana barci hankalinsa kwance. Ga iskar ac na shiga da ratsa masa ɓargo.
Nanma maida ƙofar tai ta rufe harda saka key. Kafin ta ƙarasa gaban gadon jikinta har tsuma yake saboda ganin a yanda Yoohan ke kwance. Duk da ma yayi rubda ciki ne. A hankali ta zauna a bakin gadon saitin kansa. Ta kai hannu kan sajensa da ke bala’in burgeta. Cike da ƙwarewa a bariki ta kwanto jikinsa tana sauke nannauyan numfashi, sai kuma ta shiga yin sama da hannun nata ta tura cikin sumarsa. Dan tasan tun yana yaro yanason a dinga masa wasa cikin kai. Yanda take da hannun nata a cikin sumarsa ya sakashi sauke ajiyar zuciya a cikin barci. GGashidama mafarkin matarsa yake. Sai abinda madam Chioma ke masa yay tasiri a garesa.
A hankali yay juyi gaba ɗayansa ya koma ringin gine. Kansa kuma ya ɗora akan cinyarta ɗaya dake a gadon. Wani irin daɗine ya kama Madam Chioma dan duk zatonta aikintane yay tasiri. Ranƙwafowa tayi da fuskarta daf da tashi tana wani lasar baki tamkar mayya. Yayinda hannunta ɗaya ke yawo a jikinsa. Tana gab da kai laɓɓanta kan nasa ALLAH ya bashi ikon farkawa a dalilin jin ƙamshi saɓanin na Aymahr sa. A wani irin matsanancin tashin hankali ya angizata daga ranƙwafomasa da tayi, danshi da farkoma yayi zaton Miracle ce…………✍
*_Wayyo tazo kwartanci😱🏃🏃🏃_*
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[7/3, 3:48 PM] Queen Meenali👑: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No one has commented yet. Be the first!