Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 49


Bibiyata Akeyi 49
Viral

Page 49

*
Yaya auwal ne bayan yaje yayi sallan da suke kansa, yafito daga mota ya wuce masallaci dake gidan bbu nisa da masallacin, sannan ya gabatar da sallolin dake kansa sannan yawuce Cikin gida. ”
D’akin mama yawuce kai tsaye, ganinsa yasa mama da umma fara juye juye ko zasuga hindu.”
Ganin yazauna yasa umma kasa hakuri Sanda tace wai ina hindatun? ”
D’an zaro ido yayi sannan yace,” umma sun shigo fa tun d’azu da *hanna* . ”
Dankwalo umma tamasa tace ungo naka mu abokanan wasan kane?”
Allah umma bawasa bane hadda Ammah ma, su suka shiga da ita, ”
Jin haka yasa hankalinsu kwanciya,”
Amma mamaki ne fall aransu Jin cewa wai a d’akin Ammah take hakanne ya k’ara tabbatar musu da cewa Ammah ta shiryu, ”
Kuma suma basusan lokacinda *hanna* ta shiga d’akin ba amma hakan yamusu dad’i dan hakan yana nufin ta yafe mata kenan.”
Basu fita ba dan duba adda hindu dan hausawa ansansu da kawaicii idan sukaje dubata hakan yana nufin Basu yarda da irin riqon da Ammah tamata ba, dukda zuciyoyinsu nasan ganinta Ammah sun daure dan sunsan idan sunyi hakuri zuwa gobe zasu ganta.”
K’ofar *hanna* ta kulle sannan itama ta bi adda hindu suka sha bacci.” koda hafsat taji K’ofar akulle kanta tsaye ta koma d’akin mama ta kwanta. ”
K’arfe sha biyu dai-dai, yaron adda hindu yafara kuka tsallara kuka yakeyi bbu ji bbu gani,”
Ga adda hindu baccinta takeyi batasanma yanayi ba, haka *hanna* tayita rarrashinta dak’yar yakoma bacci. ”
Aikuwa befi 1 hour da kwanciya ba yak’ara tashi nanne Ammah taji kukan ta Fito daga d’akinta ta shigo d’akin.”
K’ar6ansa tayi ta fara lallashi, sai can yayi shiru dan tasan kota tashi hindu bbu abunda zaisamu. ”
Nan yak’ara komawa bacci Ammah ta bada shi ta koma d’akinta.”
Yaro kamar wanda ysan amma tafuta yak’ara farkawa, ”
Aranar *hanna* tasan sunyi haihuwa dan ko baccin kirki batayi ba sai asubahi sannan yaron yasamu bacci.”
Haka Allah yad’aurawa *hanna* son yaron sosai, shiyasa takasa bacci ta kwana reno.”
Sanda tayi sallah sannan ta bi yaron suka kwanta, ”
Ita kuwa adda hindu sassafe Ammah ta had’a mata ruwan wanka ta wanketa,”
Kollon Ammah tayi tace Ammah in d’aukoshi ne kimasa wankan? “.
Ammah ne tace A’a kyalesu suyi bacci dan jiya baibari sunyi bacci ba.”
Tausayin *hanna* ne yakama adda hindu da kuma wata soyayarta, dan tasan idan ba d’an uwanka ba bbu wanda zqi maka wannan abun. ”
Ga kuma mamakin halin amma daya sauya, dan da ko isasshen kallo basu isheta ba.”
Amma tasan wannan amsar sai *hanna* tafarka. ”
Shiryawa tayi ta karya sannan tafuto ta nufii shashin mama.”
Ganinta tsaf bbu alamun gajiya ko yunwa ajinkinta, hakan yasa su mama sunji dad’i.”
Tambayan jaririn mama tayi, tace mata ina yaronne kokuma rowa zaki mana? ”
Dariya tayi sannan tace mama yana nan suna bacci shida *hanna* wai jiya bai barta tayi bacci ba.”
Sai kusan 10 kafinnan yaron yatashi kuma yatashi *hanna* . ”
Sai alokacin Ammah tamasa wanka sannan *hanna* ta d’aukoshi suka Fito tareda Ammah suka nufii d’akin mama.”
Zqma sukayi suna hira atsakaninsu hakan kuwa bak’aramin dad’i yamusu ba dan before basu samun wannan had’in kai d’inba. ”
Aranar anan sukaci abincin rana kowa ransa farii kall.”
Koda abba da baba suka samesu ahaka bak’aramin dad’ii sukaji ba, dan sunsan ko bayan ransu yaransu zasu had’a kai. ”
Aranar abba yashirya ya koma shida Yaya jalal dakuma salman.”
K’arfe tara na dare *hanna* nazaune kirqn MG ya shigo dan sai alokacin yasamu dama yakirata. ”
Sanda wayar ta kusan katsewa sannan ta d’auka,”
Cikin husky voice d’insa yayi mata sallama, ”
Sanda ta lumshe ido sannan ta bud’e su,”
Tunda take bata ta6ajin murya mai dad’ii da gard’in nasaba, ”
Duk lokacin da yayi magana saitaji muryan har Cikin jikinta.”
Sayya sauk’ar mata da kasala.”
Dak’yar ta tataro nutsuwarta, ta Gaisheshi, ”
Amsawa yayi da muryarsa wanda kaman tilastshi akeyi saiyayi magana,”
D’an tsaki taja aranta sannan a zuciya tace” yafara yiwa mutane magana da kasaita kenan kamar wanda akasashi dole. ”
Abinda bata saniba shine afili tayi maganar.” murmushi yayi wanda saida kumatunsa suka lotsa. ” Shiru suka d’anyi na’yan secounds. ”
Sannan kaman mai shirin yin kuka tace nifa bakowani irin lokacii nake d’aukan waya ba,”
Amma kai saika kiranii kuma baka Cemun zaka kiraba, ta k’arashe maganar had’eda murguda baki, kaman wanda yake kallonta. ”
Girgiza kai yayi dan dagajin wannan maganar yasan kawai magana take nema.”
To wani irin sanarwa kikeso nayi? ”
Cikin neman rikici tace ohh hakama zakace?”
Aisaika kira na d’akin d’in tukunna, ”
Tafad’a tana shirin kashe wayar,
Saurin katseta yayi yace am srry tam idan zan kiraki zan rinqa miki Massages tukunna amma plz karki ki d’aukan wayana.”
Shiru tayi ba tace komai ba sannan yace mata ”
Idan zaki rinqa futa plz kiringa kulawa, karki na fita akoda yaushe.”
Cikin Jin haushin maganarsa tace ”
Sai kajira dasauran lokaci kafin kafara bani wannan umarnin,”
Dan gani tayi wannan maganar ya matukar raina tane.”
Dafe goshinsa yayi sannan yace, *yah rabb ” sa”iidunii* bahaka nake nufii ba”
Kawai ki kiyaye ne kinsan yanzu sai ahankali mutane kiringa kula daywa ba kowa zaki yarda dashi ba. ”
Cikin halin ko inkula tace To ni tunda bbu wani wanda yacuceni kuma bbu wani mai shirin yin hakan sai yanzu.”
Ganin baxata fahimta ba yasa yaga gwara yayi mata bayani. ”
Cikin murya da kaman wanda kake yiwa k’aramin yaro magana kuma kanaso ya fahimceka yace.”
To yanzu intambayeki,? ”
Tace inajii,”
Idan 6ter d’inki tamiki laipy agida me kike mata? ”
Kinsan dai ta girmeki baza ki mata rashin kunya ba, kuma baza kice zaki daketaba dan tafii k’arfinki.”
Cikin rashin sanin abinda yake nufii tace, wayanta nake 6oyewa. ”
Yawwa yace an dalilin dayasa kike 6oye wayanta?”
Mugud’a baki tayi tace waini meyasa kakemun wannan tambayoyinne kamar wata k’aramar yarinya? ”
Srry but ki amsa.”
Idan kin amsa zaki zami taki amsar. ”
Sabida tanason wayanta,” Tafad’a adak’ile. ”
Ok tam dalilin da yasa zaki kula kenan dan inasonki,”
Hmm tace sannan tace sai kace wani d’an siyasa wanda ake neman kashewa zakace wani na kula?.”
Cikin ransa yace ya rabb wannan yarinya Allah yad’aura mata taurin kai. ”
Yace eh kusan hakan ne tunda ni soja ne kuma kingani yafi d’an siyasa hatsari,”
Kama ha6anta🤔 tayi sannan tace ehh hakafa, ”
Amma ai maganar da kayi kamar akwai wanda suke nemanka ne.”
Ya rabb,, kina fa da surutu yace Cikin gajiya da tambayoyinta, ”
Turo baki tayi sannan tace ai bani nace kakirani ba,”
Balle nadameka da surutu, ”
Tana fad’in haka d’iff takashe wayarta,”
Murmushi yayi sannan ya Girgiza kai, ”
Sannna afili ya furta, Allah ka nunamin rnda yarinyar nan zata daina kashemun waya.”

Sanda ta kashe wayan da yan minute wani abu ya fad’o mata. ”
D’aga wayan tayi sannan takira anty samha da saurii,”
Tana picking tace anty bawa yaya abubakar bbu musu ta miqa masa, yasa kar6a ko gaisawa basuyi ba tace, yaya abubakar shine? ”
Shinewa?” ya tambayeta? ”
Shine?” takara cewa, ”
*Hanna* ban fahimci me kike nufii ba fa kimun bayani.”
Yaa abubakar shine sojan k’asa da k’asa? ”
Sauk’arda ajiyar zuciya yayi sannan yace eh shine *hanna*, Aikuwa Sanda gabanta yafad’ii datajii shine.” sallama tamasa yace *hanna* wani abinne yafaruu? ”
Gyara nutsuwarta tayi sannan tace A’a dama bansani bane nake tambaya,”
Oh ai har hankali na ya kwanta shine, ”
Ok sai anjima.”
Bazan bawa samhan ba?” yatambaya eh kabarta Kawai saida safe tana fad’in haka ta kashe wayar ta. ”
Tana kashewa ta kira amira tana d’auka tace mata beb, ina wannan mutumin da mukajii ana zancen kasheshi lokacin da mukaje office d’in dady?”
Amira ce tace ehh menene yafaru? ”
Kinsan daga baya nace miki naga news an harbeshi.”
Kai beb Kardai haryanzu baki manta da wannan zancen ba, ”
A’a ba haka bane beb shine fa,”
Tsaki amira taja sannan tace shine wa? ”
Um Um ta tsaya cewa dan ita batasan da sunanda zata kirashiba,”
Dan ko sau d’aya bata ta6a kiran sunansa ba ita hasalima batasan asalin sunansa ba tajidai labba nacewa yaya yareema. ”
Amira ne tagaji ta jira tace kefa nake sauraro,”
Cikin saurii kamar wanda takejin shakkan maganar tace shine yayan labba, ”
Wani irin ihuu amira ta kwala wanda Sanda *hanna* tacire wayan a kunnenta,”
Ihuu takeyi tanayi tana rawa da murna iya k’arfinta, ”
Wanda hakan ba k’aramin kularda *hanna* yayiba ta fad’a mata ta tayata jimami amma ihun murna takeyi.”
Sanda tagama ihunta tace beb mun tafii wallhy. ”
Tsaki amira taja sannan tamayar mata yanda sukayi da MG.”
Itama amiran jikinta ne yayi sanyi tace beb kisa aranki bbu wani abu, in sha Allah bbu mai cutarda ke kinji, nan amira tayita kwantar mata da hankali Sannan sukayi sallama, ”
Haka adda hindu tayita zama a d’akin Ammah ranar suna yaro yacii sunan sa Aliyu, sunansa Kawai yaci amma sai yazo dai-dai da sunan mahaifin Ammah, Aikuwa murna awajenta ba’a tonawa dan iya bajinta tayi bajinta asunan,”
Sosai sunan yayi armashi. ”
Anty samha bata samu zuwaba, dan baba ne yahana yace satii biyu kenan da auranta bbu yanda zataje.”
Washe gari umma ta koma kano, yaya jalal ne yazo yad’auketa, ”
Hameeda kam tace idanta koma To k’afarta k’afar amarya.”

 

 

To be continued

 

Ur’s

*Z33yyb3rw3r*
[9/24, 8:59 AM] ‪+234 810 367 2210‬: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

_Godiya mai tarin yawa ga masoyana, naji dad’iin addu’oiinku da kuma kula warku, wannan shafin nakune, ” *mamman hassan, mmn waleed, zainab bawa(namesake), maman fodio, mamn khish, jameelah, ayusher ayuba isma’il, Ameena* nagode da kulawarku.”_

_Y’an group d’ina inasonku sosai Allah yabar k’auna kuna ssakani nishad’i, BIBIYATA AKEYI 1&2 da kuma QUEEN ZEEYY. Allah yabarmunku zeyybawa takuce.”_

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply