Farhatal Qalb Hausa Novel Hausa Novels

Farhatal Qalb 6


Farhatal Qalb 6
Viral

PG: 6_

××××. ××××. ××××.

Tunda asubahi su Umma Hadiza basu koma bacci ba. Kamar ko da yaushe. Ita da Waheedah suka fita zuwa tuqa tuqa suka shigaa zuba ruwa a manyan jarkokin da Najeebu ke garuwa idan rashin lapiar ta lapa musu . Bayan sunyi wanka .

Yan takardun Waheeda data gama amfani dasu ummah hadiza ta dauka ta shiga kunna su a murhu daya bayan daya da ruwan bunu acikin samira. Nan da nan kuwa ya tafasa.

Ta zuba ragowar sukarin daya rage ta zuzzuba musu a kofuna. Can Umma hadiza ta miqe ta fice. Ba jimawa ta dawo da kullin leda hannunta. Biredi ne da kosai mai zafi.

Ta kakkarya ta miqa musu. Kamal ya dafe cikin sa yana bin biredin da kallo.

“Umma ba dai bashi kika sake karbowa ba..”

“Bashi kuma..? A’ah.”

“To ai umma ina kike da kudin fisabilillahi. Dan Allah ki dena karbo bashi ummah. ”

“Dan Allah banason mita. Ku cinye kafin kosan yayi sanyi.”

Ita dai Waheedah na daga gefe tana karyawa. Hawaye na zurara daga idanunta. Tana karasawa ta miqe tana hamdalah.

“Mungode ummah. Allah ya saka miki da mafificin alkhairin sa. Amin Yaa rabbi. ”

“Aamin Waheedah. Maza ki karasa shirya wa ki tafi. ”

“Tohm Ummah.”

Waheedah ta fito daga dakin su Kamal ta shiga dakin da yake kallon sa wanda yake a matsayin nata ita da Umman su .

Bude yar baccon kayanta tayi ta zaro robar ruwan alumun da yaji lemon tsami ta goggoga a hammatar ta. Tana jin dadin hakan. Domin suna tsantsame gumin hammata su kuma kauda tashin da hammata keyi tunda ba halin siyan turaren hammata na deodorant. .

Ta diga turaren ruwan da Kamal ya bata a hannunta. Ta shafe jikinta dashi. Hade da zizara kwalli . Ta daura dankwalinta na shedar prefect ta zura hijabinta. Hadi da goya jakarta ta fice daga dakin zuwa na su Kamal.

Dake gidan irin na da dinnan na masu karamin karfi ne. Babban gidah mai dauke da dakuna 6. Uku na kallon gabas uku na kallon yamma. Sai bandaki da dakin girki.

“Wane dan gaba da wulakancinne ya take mun takalmi saboda kaskanci da karshen wulakanci ?” Cewar Inna Sa’adatu da ke bin takalmin wari daya da kallo. Yar jikakkiyar kasa ce a gefen takalmin kadan.

Waheedah zatayi magana kenan. Umma hadiza ta fito daga dakin su Kamal. Da sauri saboda rashin son tashin hankali ta dauki takalmin ta saka wani guntun kyalle ta goge.

“Kiyi hakuri.”

“Yo idan ban hakura ba zan dake ki ne?”

“Ki deyi hakuri.”

“Ah ni fa banason haka. Wallahi yanzu sai ince sai an biyani sabon takalmi na.” Ta shigaa duba gefe da gefen takalmin nata silifas.

“Toh ya kikeso ayi?”

“Ya da haka Hadiza.? Kina wani zazzaro idanuwa sai kace wata uwar mata. Aikin akwai. Gaskia kada mace ta sake biyemun ta kan takalma . Dan wabillahil lazi anyi na farko anyi na karshe. Idan aka sake maimaici mace zata ga abunda zan mata.”

“Toh Allah ya rufa asiri ya tsare gaba.”

Mtsssssssssssssssssss!!
Taja tsaki hadi da shigewa dakin ta.

Umma hadiza ta juya ta kalleta kawai ta girgiza kai.

“Ungo wuce ki tafi.” Ta mikawa Waheedah nera 20.

” Umma ki basshi.”

“Banason jan magana.”

Ta tsugunna har kasa ta karba tayi mata godia. Ta zura safarta hade da gyara zaman takalmanta .

Zainab ‘yar wajen Inna Sa’adatu sai danna soyayyen kwai take da biredi a baka tana hadawa da shayi dayaji madara.

“Ke wahee ki tsaya ni mana.” Zainab ta fada da sauri tana goge bakinta da bayan hannun ta.

“Dan ubanki tunda bataso kuna tafiya tare makarantar dole ne?”

“Kai Inna ba tafiya nayi ba na barta.” Cewar Waheedah kanta a kasa.

“Dalla rufemun baki munasurar banza. Ke kuma can daya sokuwa tamkar kare ya cinye zuciyar ki. Sai ki bita ai ku tafi.”

Ita dai zainab batace komai ba ta saka safarta tanata sauri.

“Zainabu. ! Zainabu.”

“Na’am marka”

“Ungo kudin tara. ”

“Tohm”

Waheedah na tsaye zainab taje dakin marka ta karbo nera hamsin kudin cin abinci a makaranta.

“Sai kin dawo. Allah ya miki albarka.”

“Amin Marka.”

Hawaye suka cicciko idanun Waheedah saboda tsananin kiyayya da kakarsu take nuna musu.

Haka suka jera suka tafi makarantar bayan Waheedah ta leka tayiwa marka sallama. Wadda ta debeta ta watsar tamkar taga kashi.

×××××

Su waheeda na tafiya ba jimawa najan Isubu tazo gidan da wata mata wadda tayi hanyar aikin.

Umma hadiza ta sauya kayanta zuwa wasu riga da zani da hijabin ta da ya sha karin guga.

Sai data tabbatar ta tanadar wa su Kamal komai.

“Toh zan tafi wajen aiki… Kunce da sauki ko?”

“Allah da sauki Ummah… Ni zan dan watsa ruwa ma na fita insha Allah.”

“Toh Masha Allahu. Kai ma Najib ka danyi ko zaka ji karfin jikin na ka ”

“Insha Allah Umma.”

“Yauwa sai na dawo. “.

Ficewa sukayi zuwa hadaddiyar unguwar dake kusa da su wadda ake kira da NEW GRA SHURAH. Unguwa ce ta masu hannu da shuni. Wanda ke da jijjigaggun gate da manya manyan gidaje luntsuma luntsuma hadi da manyan motoci masu nishi.

No: 194: THE ADAMS FAMILY!! shine sunan da ke rubuce da manyan baki awani kawataccen allon karfe.

“Nanne gidan fa Hadiza .” Cewar Najan Isubu dake tabo Umma hadiza.

“Nan. Tsarki ya tabbata ga Allah. Cancadi.”

“Hmm carkwadidi kai. Kede kallo na gaba ma.”

Tunda suka tura kofar da ke masu gadin sun san da zuwan su. Umma hadiza tsayawa tayi kawai tanabin sarautar Allah da idanu. Gidane daya amsa sunan gidah. Gidah ne wanda alkalami yayi kadan wajen bayyana irin kawatar da yayi. Gidah ne dayaji komai na rayuwa da abubuwan morewa.

“Kinga motoci ko harda titi acikin gidah ko hadiza. ”

“Uhm bari kawai Naja.”

“Kinga wadannan abubuwan kamar kwayayen fitila?”

“Eh fa gasunan birjik.”

“To na’urar bidiyon hadahadar cikin gidan suke nunawa dana waje. Komai . Yanzu haka ma suna kallon mu.”

Umma hadiza ta riqe baki kawai tana kambama lamarin.

Ciki suka shigaa. Wani hadadden parlor daya gaji da haduwa. Ba jimawa wata mata fara tamkar balarabiya ta shigo ciki fuskarta kumshe da fara’a …

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*

*ZAFAFA BIYAR BACTH A*

1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*

2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*

3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4… _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5… _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*

1… _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2… _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3… _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4… _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5… _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1… _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2… _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3… _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4… _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5… _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1… _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2… _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3… _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4… _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5… _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1… _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2… _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3… _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4… _DAB’IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5… _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*

_Duk biyar 1500_

*______________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1… _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2… _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3… _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4… _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5… _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1… _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*

2… _GURBIN IDO_
*(Huguma)*

3… _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*

4… _INAYAH_
*(Mamu gee)*

5… _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*

 

_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*

 

*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*
[11/23, 9:00 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply