Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 74


Gurbin Ido 74
Viral

74

Sun jima a hakan kafin ya bude idanunsa a hankali,sannan ya miqe ya zauna yana kallon cotton din yadinsa fari qal daya ya mutse,ya fara maida button na rigarsa,sannan ya duqa qasan motar a hankali ya lalubo hijabinta ya matsa a tausashe ya miqa mata,bata iya hada ido dashi ba,ta miqa hannu ta amsa ta zura,sai daya tabbatar ta saka sannan ya dage coloured glass din da ya sauke din,ya sanya hannu ba tare da yace komai ba ya buda murfin motar,ya zagaya ya bude mata,ta zura qafafunta a hankali ta fito.

A gaba ya sanyata yana biye da ita kamar wani bodyguard dinta har zuwa office din da ake shigar da dawowar dalibi a register,ya cike komai ya kuma ce kada a sake barin kowa yazo daukanta,sai yazo da kansa ko kuma ya bada umarnin a dauketan,cikin ma’aikatan su suka daukar mata jakankunanta,cike taf da kaya fiye da yadda ta saba zuwa dasu,kamar zata bude qaramin provision.

Tana takawa a hankali zuwa dakunan kwanansu amma tana jin idanunsa cikin jikinta,ta tabbatar yana tsaye yana kallonta,saidai bata waiwaya ba har ta qule.

Nannuyar ajiyar zuciya ya sauke,yana jin kamar an cire zuciyarsa an wurgata can nesa dashi,sai ya waiwaya jiki a mace ya buda motar tasa ya tadata yabar cikin makarantar yana jin duk wani farinciki da yayi saura a zuciyarsa yana raguwa.

Numfashi ta sauke tana duban dakin nasu,tayi missing nasa,saidai yadda ta dauka zatayi farinciki da da dawowa cikinsa sai ta lalubi hakan cikin zuciyarta ta rasa,hasalima wani mutuwar jiki takeji da kasala,sai ta zauna bakin gadon ayman,ta zare socks din qafarta da takalminta ta wuce toilet ta daura alwala.

Sallar la’asar tayi,tana son binsu masallaci amma kuma batason garin murnar nan tasu suyi mata tarere,don haka sai ta bude jakankunanta,ta fara fidda kayanta tana shiryawa.

Kafin wani lokaci ta gama shirya komai yadda ya dace,ta sake kintsa musu dakin,wanka take som yi amma ta kasa,sai ta koma ta kwanta gadon afrah tana jin wata lafiyayyar gajiya tana bin jiki da gabobinta,haka kawai takejin zuciyarta duka babu dadi,walwala da dokin dawowa makarantar duka sun kau,ta lumshe idanuwanta,abun mamaki sai tunaninsa ya soma mamayarta,ta fara hangen fuskarsa a mabanbantan lokutan da suka kasance tare dashi.

Ganin lokaci na tafiya kuma ta gaza hasala komai sai ta yunqura ta miqe tana duban dan qaramin agogonsu dake jikin bango,wanda afra ce ta maqala musu,tace hajjanta wato kakarta ce ta bata shi,yau kamar sun dan gota lokacin dawowarsu,ta miqe ta shiga dube duben dakin babu abinci,kuma yunwa take dan ji,duk da taci abinci kafin su fito,don takeaway ya mata na musamman da abinda taji ranta yana so.

Babu sauran abinci a cikin dakin,da alama ma basu dafa komai ba,a kitchen suka karba abinci,sai ta zari hijabinta har qas ta zura ta sanya slippers ta fito,tana tuna maganar da ja’afar ya gaya mata sanda suna kan hanya,hannunsa na cikin nata

“Please ki kularmin da kanki,ki adanamin kanki da kyau,don babu yadda zanyi ne da anni,kamar uwa take a wajena,banda ita abbi da amma babu wanda ya isa yayimin wannan hukuncin na yarda dashi,zan iya mutuwa wallahi angel……ina da kishi sosai…. please take care of yourself”.

Ajiyar zuciya ta saki ta qarasa shiga kitchen din,mama’s dinsu dake musu girki dukka ta samesu suna nan,kowacce cikin fara’a ta soma mata maraba,ita kuma tana gaidasu cikin matuqar girmamawa,suna son maimunatun sosai saboda yadda take martabasu,ba kamar wasu daliban da suke ganin sun fito daga gidan gata ba,ana.biya musu school fees almost one million naira so babu me takurasu

“Munata jajjabin rashin dawowarki,sai afra tace ai kunyi tafiya ne keda ‘yan gidanku”

“Eh wallahi mama”

“To madalla,an dawo lpy ko?”

“Lafiya lau mama,zan samu abinci kuwa?”

“Eh akwai na rana da akayi,bari na duba miki” ta fada tana buda babbar tukunyar,ta deba mata cikin plate maimunatun ta karba tayi mata godiya kamar yadda ta saba tana cewa

“Idan kun tashi aiki mama kiyimin magana,sai ku karbi tsarabarku” kusan hada baki sukayi wajen mata godiya,indai kyauta ne maimunatun ba daga nan ba,ta juya ta fice da abincin a hannunta.

Sam bata kula da tahowarsu ba,gab da zata isa dakinsu taji an saki ihu,kafin ta waiwayo taji an rungumeta tsam ta bata,ayman da fatima kuma suka zagayo ta gabanta suna riqe da hannunta gam,wanda saura kadan abincin hannunta ya kife a qasa

“Daga ina?,saukar yaushe?,wai mu zakiwa suprise moon?,kin barmu gaba daya makarantar babu dadi?” Murmushi ta sake musu,ita jikinta gaba daya babu wani cikakken qwari

“To sakeni afreen,afwa,wacce tambaya zan amsa miki a ciki?”

“Duka” ta fada tana sakinta gami da zagayowa gabanta tana murmushi,sai kuma ta fidda idanunta waje gaba daya,ayman tayi caraf tace

“Kinga abinda na gani sis afreen?”

“Ko makaho ai dole ya gani….moon?,me captain yake baki?”

“Banason iskanci afreen,zaki fara ko?” Cikin qyalqyala dariyar farinciki tace

“Wallahi Allah am serious,kinga yadda kika qara fresh?,jikinki kamar jini zai diga?,don Allah bai saka miki dokar sanya niqaf ba?”

“Saidai ki bashi shawara ‘yan wulaqanci…..mu qarasa daki don Allah” ta fadi saboda yunwa da gajiya da tsaiwar da tayi.

Cikin dakin suka bude sabuwar hira,gaba daya sun sakata gaba kan irin yadda ta qara kyau da kuma yi fresh da ita

“Wallahi honeymoon tayi kyau,Allah yasa an samo mana dan lagos to johannesburg” afra ta fada tana kwanciya saman gadonta tana dariya,har qasan ranta tana jin dadin canzawar aminiyar tata.

Duka maimunatu ta d’ana mata a bayanta tana cewa

“Mara kunya kawai,ni ba abinda ya shiga tsakanina dashi,ni da sauran kunyata”

“An fada a radio” ta amsa mata tana sake sheqewa sa dariya,dariyar ta baiwa maimunatu,sai kawai ta murmusa itama.

“Allah ko,inda nice ke banga abinda zaisa na dawo makaranta ba,kuma wai boarding tabdi” ayman ta fada tana duban maimunatu,idanu ta fidda

“Yaushe afreen ta bata ku da son aure?”

“Dan sunna yaqi sunna” ayman ta amsa mata tana dariya.

Anan sukayi sallar magariba da isha’i tare,don ko fita cin abinci basuyi ba tsabar hira,fatima ce taje kitchen ta karbo musu, maimunatu ta hada da tsarabar su mama fatiman ta kai musu.

Sai wajen goma na dare kowa yayi shirin kwanciya,saboda gobe suna da shiga lab qarfe takwas,malamin kuma yace duk wadda ya rigata shiga ba zata shiga ba,tasu tsarabar ta ware,dogayen riguna ne masu kyau irin daya,sosai sukayi murna kamar basu taba sawa ba,duk da kowacce a cikinsu tafi qarfin abin,amma hausawa sukace alkhairi dadi gareshi,koda kafi qarfin abun.

Ba’a rufa awa daya ba dakin ya dauki shuru,da alama bacci ya daukesu,sama ko qasa maimunatu ta nemi bacci a idanunta ta rasa,ta dinga juyi tana canza position da wajen kwanciya,saidai still dai kwanciyar babu dadi,ta dinga jan qananun tsaki,gadon ne babu dadi ko kuma katifar?,ko sauyin wajen kwana?,sai ta rasa amsar tambayar,can wani sashe na zuciyarta kuma yanata qoqarin danne abinda ke taso mata,tana ta qoqarin karyata zuciyar tata,yaushe ta sanshi?,yaushe sukayi sabon da zata ji babu dadi don babu shi a kusa?,kwata kwata sai kwanciyar taqi mata dadi,ta runtse idanunta da kyau tana qanqame filo a qirjinta,tana son tilastawa kanta yin baccin ala dole.

Maimakon baccin sai memories dinsu dashi ya dinga dawo mata,haka tayita ganin komai cikin idanunta,ta jima kafin ta samu idanuwanta suyi nauyi,a hankali bacci ya fara sauko mata.

Hannu ya miqa a hankali,ya rage hasken reading lamp din dake saman kyakkyawan zagayayyen table din da ya cikasu da takardu,sai ya koma da baya yayi relaxing yana shafa sumarsa gami da furzar da iska daga bakinsa,ya janyo a gogon dake gefansa a matuqar gajiye yana duba lokaci.

K’arfe biyu harda minto goma na dare,qaramin tsaki yaja ya maida agogon muhallinsa,bai taba ganin dare mai tsahon wannan ba tunda yake a rayuwarsa,ya tsammaci zaman da yayi a nan zai tsinciki kiran sallar asuba ne,saidai gaba daya lokacin ma kamar baya tafiya,kamar a tsaye yake cak.

Maida kansa yayi ya jinginar,ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa yana dan lilo kan kujerar da yake zaune,gaba daya ita ke masa yawo tsakanin idanuwa zuciya zuwa qirjinsa,sau biyu yana attempting kwanciya,amma idan yaje sai yaji ya gaza zaman bedroom din,memory din data bashi yammacin jiya zuwa dare ke dawo masa,sai ya miqe tsaye yana kwasar wayoyinsa gami da kashe fitilar gaba daya ya sake nufar bedroom din.

Sai daya shiga toilet ya daura alwala yayi bursh sannan ya dawo ya kashe qwayayen dakin ya nufa gadon,addu’ar bacci yayi yaja duvet yana rintse idanunsa gami da addu’ar Allah ya kawo masa bacci da wurwuri,saidai inaa,addu’arsa bata ciba,don gaba daya qamshin ta daya maqalewa pillow din data kwanta jiya akai shi kuma yau ya daukeshi yayi amfani dashi shi ya maqale masa a hanci,ya shiga tuna masa da ita gamida tada masa hankali.

Dogon tsaki yaja kamar zai cire harshensa,dukka anni ce taja masa,ta yaya za’ayi mutum da matarsa amaisheshi gauro?,don ya kaita boarding school a baya….ai ya aikata hakanne a sanda baisan daraja da kimarta ba,a yanzun kuwa duk duniya yafi kowa sanin martabarta,da wannan tunanin da kuma kewar ya dinga fama har ya samu baccin ya daukeshi.

°°°°°°°°sati guda kacal amma gaba dayansu kowa ya jikkata a jiki da zuciyarsa,tuni ya sallama cewa soyayyarta ce tayi masa mummunan kamu,irin kamun da yakejin labarinsa a labarai yake kuma qaryatawa,ashe da gaske haka ne?,komai yakeyi tana cikin tunani da zuciyarsa,sai ya fara samun cikas a ayyukansa na office,wasu abubuwan sai yayita mistake,sai jabir ya ankarar dashi,mamaki yanata shigan jabir,lallai gigitaccciyar soyayya ce ta kama ja’afar din

“Kaga masu abu da abunsu,malaman soyayya” ya fada a ransa yana sakin qaramin murmushi.

Yayin da bangaren maimunatu kuma taketa dojewa kan gajiyar tafiya ce ke luguiguitata sanda afra suke mata tsiyan ta faye zama cikin tunani,sannan bata baccin kirki cikin dare,ko tana kewan captain ne?.

Tun tana qaryatasu tare da basu uzurorinta har ta soma sallamawa itama,a hankali ta sake zama so silent,duk da bata yiwa su afrah miskilanci amma a yanzu kamar ta sauya musu su dinma,tafi kebewa ita kadai ta zauna shuru,wanda ba komai take ba illa tunani.

°°°°°°°°°Karfe tara na safiya ne,yana kwance bayan motarsa qiran ferrari,daga gidansa na government house road zuwa gidansa dake zuwa gidansa dake daya baro tun randa ya dauko maimunatun,bai sake komawa ba,koda ta koma makaranta ma a nan gidan yaci gaba da zama,a yanzun ya samu qwarin gwiwar zama a ciki tunda aka kwashe kayan shaheeda daga ciki,akwai takardun da yakeson debowa daga can gidan kafin ya wuce office.

Gaisawa sukayi da masu gadin gidan nasa,sannan ya wuce ciki da dan gaggawarsa yana gayawa driver din nasa kada ya kashe motar yana fitowa.

Bai jima ba ya dauko abinda zai dauko din ya fito,yana saukowa daga stairs din yana sake duba file din don tabbatar da cewa ya dauko komai a ciki da yake buqata.

“Ka kulamin da jaka karka karcemin ita fa” muryar da yaji kenan data samyashi dago kansa,ido hudu sukayi da unaisa,wadda ke takowa cikin gidan,sanye da wata irin mini gown da straight leg trouser,kusan rabin fuskarta mamaye da sun glasses,tana tauna chewing gum.

Cikin tsawa ya bawa mai gadin umarni

“Ina zaka da wannan jakar?”

“Ah….hajiya ce tace a kawo mata ciki”

“Kana qara taku daya da ita a bakin aikinka,koma da ita inda ka daukota” cikin rawar jiki da kuma matuqar tsoron rasa aikinsa ya janye akwatin zuwa baya,bai kuma sake bi takan maganar unaisa dake cewa karya fitar mata da kaya ya qaraso mata da ita ciki.

Wani kallo me cike da qasqanci da kuma qyama ya jefeta dashi,zallar kwarjinin da yake dashi ya daketa,gaba daya sai tayi collapse,har ya qaraso bakin sassan nata da ta zura key da nufin budewa,ya sanya hannunsa ya zare key din ya jefa a aljihunsa ya kewayeta ya fice abinsa ba tare daya ce mata uffan ba.

Sai daya kira dukka ma’aikatan gidan yaja kunnen kowannensu kan kada wani a cikinsu ya kuskura ta sashi abu yayi mata,koda ja mata luggage dinta ne,yaja musu kunne da kakkausar murya kam duk wanda yayi hakan a bakin aikinsa,cikin bin umarni kowa ya amsa mishi,tare da tabbatarwa kansu ba zasuyi wannan gangancin ba,a yanzun samun gidan aiki me cike da kyautatawa da bayan salary dinsu harda allowance ake basu abu ne mai matuqar wahala,bai tsaya sauraren rantse rantse da ban haqurinsu ba ya shige mota ya bawa drivern umarni su fice a gidan.

Ranshi ya baci sosai,amma tun kafin yakai office ya tattara damuwarta ya watsar,abu daya ne ya sani cewa ko sama da qasa zata hadu bazai taba iya zama da ita ba,bazai furta mata komai ba,amma dole takai kanta gida ta kuma gaya musu daga inda take,ta bakinta komai zai fita yana nan yana zuba idanu.

A bakin office dinsa ya tarar da jabir yana jiransa,gaba yayi yana qoqarin shiga tare da fadin

“I come late,am sorry” ya dauki uzuri,sabida ba dabi’arsa bace saba alqawari da lokacin zuwa aiki,binsa da kallo jabir yayi yana qoqarin karantar yanayinsa,gaba daya ja’afar din ya wani sukurkuce a ‘yan kwanakin,duk da yadda yake nuna qarfin hali,anya zai jure?,bazai tayashi baiwa anni haquri ba ta sauka daga kujerar naqin data hau ba?.

Koda ya sameshi a office din bashi lokaci yayi,sai da yaga ya dan nutsu sannan suka gaisa,ya miqa masa takardun ya koma ya jingina da makarin kujerar da yake kai yana kallon ja’afar din duba na kai tsaye.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply